Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa wasu hotunan dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Leba wato Peter Obi tare da Paparoma Francis ya na zargin cewa dan siyasar ya je neman addu’a daga babban malamin addinin gabannin zabukan 2023
Bincikenmu ya nuna mana cewa a shekarar 2019 aka dauki wadannan hotunan kuma ba su da wata alaka da zabukan 2023
Cikakken labari
Peter Obi dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar Leba na cigaba da kasasncewa kan gaba a tattaunawar jama’ar Najeriya a duk wani dandali na soshiyal mediya, kamar dai sauran abokan hamayyarsa.
Kwanan nan wani mai amfani da shafin Facebook Victor Ifeanyi Ugwu ya wallafa hotunan Obi tare da Paparoma Francis da taken wai dan takarar ya gana da paparoman dan “ayyukan nan gaba.”
Ugwu ya rubuta : “Labari da dumi-dumi… Peter Obi ya gana da Paparoma Francis da samun addu’o’i domin ayyukan nan gaba..”
Da yawa daga cikin masu amfani da shafin na Facebook irin su Boldoracle House su ma sun wallafa hotuna masu kama da wannan a shafukan su.
Duk da cewa wadanda suka sanya hotunan ba su ambaci shekarar 2023 ba wadanda suka karanta labarai sun dauka ganawar kwanan nan ne kuma Obi ya sami goyon bayan Paparoman.
Misali, Victor Ifeanyi Ugwu ya mayar da martanin da ke cewa, “Za mu kai bawa mai biyayya zuwa fadar Aso Rock 2023.
Wani mai tsokacin shi ma ya ce “wannan abin kayatarwa ne” yayin da Emmanuel Ebbi shi ma ya ce “an fara motsawa..”
DUBAWA ta nemi fayyace gaskiyar wannan batun domin kwatantawa masu zabe abubuwan da ‘yan takara ke yi domin yana iya tasiri sosai a kan irin shawarar da masu zabe za su yanke dangane da wanda za su zaba.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomin domin tantance ko Obi ya gana da Paparoma Francis kwanan nan.
Mun gano cewa jaridar The Eagle Online ta yi rahoto dangane da ganawar Peter Obi da Paparoma Francis a 2018 lokacin da Obi ya ke takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP. Sai dai hoton da aka sanya a labarin ba iri daya ba ne da hotunan da suka bulla a Facebook.
Dan haka DUBAWA sai ta sake sanya hotunan cikin manhajan binciken hotuna na google dan gano inda mai zargin ya samo hotunan da ya yi amfani da su a shafin shi.
Wannan ne ya kai mu shafin tiwitar Peter Obin kan sa zuwa wani labari da ya wallafa a 2019 mai cewa “Najeriya na fama da rashin ci-gaba saboda rashin kulawar da ake bai wa ilimi. Ina farin cikin aiki da gidauniyar ofishin paparoma na Scholas Occurentes, @InfoScholas, wani yunkuri na @Pontifex domin kawo ci-gaba a fannin ilimi da wasannin motsa jiki a Najeriya.
Jaridar The Herald ma ta dauki wannan labari na ganawar Paparoma da Peter Obi a 2019, kuma makasudin ganawar shi ne kawo ci-gaba a fannonin ilimi da wasannin motsa jiki.
A Karshe
Mun gano cewa hotunan na labarin sadda Peter Obi ya gana da Paparoman ne a 2019. Dan haka ba su da wata alaka da da wasi “ayyukan nan gaba” wanda wata kila wadanda su ka karanta suka dauka a matsayin zabukan da za’a gudanar a 2023.