African LanguagesHausa

Abba Kyari ba ya Australia kamar yadda ake Zargi

Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargin wai an ga Abba Kyari a Australia, sa’o’i kadan bayan harin da aka kai kan gidan yarin Kuje.

Abba Kyari ba ya Australia kamar yadda ake Zargi

Bincikenmu ya nuna mana cewa, shi kan shi adireshin yanar gizon da aka yi amfani da shi wajen wallafa labarin na bogi ne. Mai magana da yawun hukumar da ke kula da gidajen kurkukun Najeriya kuma ya karyata zargin dan haka labarin ba gaskiya ba ne.

Cikakken labari

Bayan harin da ake zargi ‘yan Boko Haram ne su ka kai kwanan nan kan gidan ajiye masu aikata miyagun laifukan da ke Kuje, inda daruruwan fursunoni suka kubuce, wani labari ya bulla, wanda ke zargin wai tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari shi ma ya kubuce ya tsere zuwa kasar Australia.

Masu zargin sun yi amfani da hotuna guda biyu a cikin labarin. A hoto guda an nuna bayan wani mutun yana kokarin shiga wata motar da ke tsaye. A hoto na biyun kuma ana iya ganin fuskar Abba Kyarin ya na sanye da rigar ‘yan sandan shi.

A cewar zargin: Sa’o’i bayan harin da aka kai kurkukun Kuje, an hango Abba Kyari a Australia.

Daya daga cikin labaran wanda ya riga ya sami tsokaci 109, aka kuma raba sau 75 sa’anan mutane 524 sun yi ma’amalla da shi ya janyo mahawara sosai tsakanin wadanda suka amince batun gaskiya ne da wadanda ke ganin da walakin goro a miya.

Alal misali, Oluebube Abel ya ce lallai dama an shirya kubutar da Abba Kyari ne

“Ba zan yi shakka ba. Wannan dabara ce su ke yi domin su sami wadanda za su tayar da tarzoma lokacin zaben 2023 kuma ba za su yi nasara ba,” ya ce.

Sai dai Isabella Stevenson ba ta ji batun gaskiya ne “Ba yadda za’a yi a ce an gan shi a Australiya cikin sa’o’i, Australiya ba kamar nan da Dubai ba ne inda mutun zai sami visa cikin sa’o’i 24,” ta rubuta.

Wane ne Abba Kyari?

Mr Kyari tsohon mataimakin kwamishanan ‘yan sanda ne wanda aka dakatar da shi bisa zarginsa da rashin da’a

Kafin aka kama shi “ya taka rawar gani sosai a fagen yaki da miyagun laifuka a Najeriya a ciki har da kama shahararru wajen yin garkuwa da mutane irin su Evans wanda aka kama a jihar Legas da kuma Wadume wanda aka kama a Taraba. Shi ne kuma ya jagoranci tawagar ‘yan sandar da ta je ta kwato wani dan uwan shugaba Muhammadu Buhari daga maboyar masu yin garkuwa da mutanen a Kano.

A watan Maris 2022, bayan da aka tuhume shi da laifin safarar miyagun kwayoyi tare da wasu mukarrabansa guda 6, Babban Kotun Tarayya ta yanke mi shi hukuncin dauri a kurkukun Kuje.

A baya, DUBAWA ta lura da cewa irin wadannan zarge-zargen yawanci ba su da tushe shi ya sa ta ke so ta yi binciken gaskiyar labarin.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da bin adireshin labarin da ke wannan zargin. Kamar yadda aka kwatanta a kanun labarin, ya kamata adireshin ya kai mai sha’awar karanta labarin zuwa hoton bidiyon da ke nuna Mr. Kyari a Australia sai dai maimakon haka, adireshin sai ya kai mu kan wani labarin da ba shi da alaka da abin da aka fada.

Ba kamar yadda sauran taskokin labaran blogs ke barin mutun ya karanta labaran da aka wallafa kai tsaye ba, wannan shafin mai suna “worlnews.space” ya kan fara nuna talla ne. Duk yunkurin da muka yi wajen rufe tallar ya ci tura daga nan sai ya bukaci mai amfani da shafin ya sauke wata manhaja.

Daga nan ne DUBAWA ta binciki sahihancin shafin ta yin amfani da Scamvoid, manhajan da ke gano miyagun shafuka. Sakamakon binciken ya nuna cewa ba’a dade da kirkiro shafin ba domin watannin shi biyar kacal a lokacin da muka yi wannan binciken.

DUBAWA ta kuma sake gudanar da binciken mahimman kalmomi a cikin google inda ta gano wani labarin da jaridar Premium Times ta rubuta wanda ke tabbatar da cewa Abba Kyari yana hanun jami’an kurkuku har yanzu, bai je ko’ina ba.

Rahoton ya ji ta bakin mai magana da yawun hukumar kula da kurkukun kasa (NCoS), Umar Abubakar wanda ya yi karin bayani dangane da harin ya kuma ba mu tabbacin cewa Kyari bai gudu ba.

Jaridun Vanguard da Daily Trust da wadansu karin jaridu masu nagarta su ma sun dauki labarin.

A Karshe

Binciken mu ya nuna mana cewa adireshin yanar gizon da aka yi zargin na bogi ne. Haka nan kuma mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yarin kasa ya ba mu tabbacin cewa Abba Kyari na cigaba da kasancewa a hannunsu. Dan haka, wannan zargin karya ne

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button