African LanguagesHausa

Alakaluman da Buhari ya bayar na adadin wadanda suka yi allurar rigakafi ba dai-dai ba ne

Zargi: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce mutane miliyan 38.7 wadanda ke zaman kashi 35 cikin 100 na mutanen da aka yi niyyar mu su rigakafin COVID-19 sun duk sun karbi allurar

Alakaluman da Buhari ya bayar na adadin wadanda suka yi allurar rigakafi ba dai-dai ba ne

Bayanan da mu ka samu daga hukumar kula da lafiya da cigabar al’umma (NHCDA) sun nuna cewa jimilar ‘yan Najeriyar da su ka yi allurar rigakafin COVID-19 ta wuce miliyan 45 wanda ke nufin kashi 40.3 cikin 100 na rukunin mutanen da gwamatin ta ce tilas su karbi allurar.

Cikakken bayani

Ranar 17 ga watan Oktoba na 2022 a taron da ya yi na bitar abubuwan da gwamnatinsa ta yi, ya ce mutane milliyan 38.7 wato kashi 35 cikin 100 wanda ke zaman yawan mutanen da dama gwamnatin ta kuduri aniyar yi mu su allurar rigakafin COVID-19 duk sun sami allurar.

Wannan ikirarin na cikin sanarwar da mashawarcin shugaban kan kafofin yada labarai da hulda da jama’a Femi Adesina ya bayar.

Tun bayan barkewar COVID-19 daga karshen shekarar 2019, aka rika samun damuwa dangane da hanyoyin kariya da ma yiwuwar tsira daga cutar musamman a kasashe masu tasowa a nahiyar Afirka tunda asibitoci kalilan ne, kuma a wasu wuraren ma kusan babu irin kayayyaki da ma kwarewar da ake bukata don shawo kan matsalar.

Hukumar Lafiya ta Duniya a watan Afrilun 2020 ta yi gargadin cewa Afirka ce za ta zama dandalin annobar inda ma har ta yi kiyasin cewa cutar za ta kashe akalla mutane dub 300 a Afirka ta kuma kara sanya wasu miliyan 30 cikin talauci

Bisa bayanan da aka samu daga masu kididdiga na Worldometers, daga 18 ga watan Oktoban 2022, a duniya baki daya, mutane 630,670,164 suka kamu da cutar coronavirus a yayin da wasu 6,573,608 kuma suka hallaka a dalilin cutar. A cikin wannan adadi 265,741 kacal ne aka tabbatar a Najeriya  sa’annan wasu 258,993 sun warke yayin da mutane 3,155 suka hallaka bisa bayanan da aka samu a jihohi 36 da babban birnin kasar wato Abuja.

Tantancewa

Dama Najeriya ta kuduri aniyar samar da allurar rigakafi ga akalla kashi 40 cikin 100 na al’ummarta mai yawan milliyan 200 kafin karshen shekarar 2021, sa’anan ta kai kashi 70 cikin 100 kafin karshen 2022 bisa la’akari da shawarar da WHO ta ba ta.

Gabanin kaddamar da allurar rigakafin, babban darektan NPHCDA Faisal Shu’aib ya yi bayanin cewa gwamnatin tarayyar ta yi niyyar yin allurar rigakafin wa duk wadanda suka cancanta daga shekaru 18 zuwa sama har da masu juna biyu.

To sai dai kawo yanzu Najeriya ba ta kai ga cika wannan buri ba. A karshen 2021 sa’annan kuma zuwa watan Agustan 2022 mutane miliyan 27.7 daga cikin adadin wadanda suka cancanci samun allurar kadai suka samu.

Karin binciken da DUBAWA ta yi a kan shafin NPHCDA ya nuna cewa ya zuwa ranar 16 ga watan Oktoban 2022, mutane 45,044,523 kadai suka yi allura. Wannan adadin na zaman kashi 40.3 cikin dari a maimakon kashi 35 din da shugaba Buharin ya ambata.

Bacin hakan, labaran da  ke shafin dangane da rigakafin na COVID-19 ya nuna cewa mutane 12,734,476 wato kashi 11 cikin 100 na wadanda suka cancanci samun rigakafin sun yi allurar amma ba su cika ka’idar allurai biyu ko ukun da ya dace a karba ba.

A Karshe

Ikirarin shugaba Buhari na Najeriya na cewa kashi 35 na al’umma ta sami allurar rigakafin COVID-19 ba gaskiya ba ne. Adadin gaskiya shi ne kashi 40.3 cikin 100.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »