Zargi: An wallafa wadansu hotuna a shafukan sada zumunta ana zargin wai yawan mutanen da suka halarci yakin neman zaben dan takrarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu ke nan a jihar Katsina
Hotunan tsoffi ne wadanda aka dauka a 2019 lokacin da Buhari kansa ya je Katsinar yana neman yin tazarce
Cikakken bayani
Ranar 25 ga watan Fabrairu ‘yan Najeriya za su kada kuri’ar da zai zabi sabon shugaban kasa. Mutane 18 suka yi rajista da hukumar zabe mai zaman kanta na INEC domin neman mukamin mafi mahimmanci a kasar.
Gabannin wannan zabe da ake kosa ya zo, jam’iyyun siyasa da magoya bayansu na cigaba da yin iya kokarinsu wajen rinjayar jama’a su jefa musu kuri’a
Abun ya ma zama babbar takara tsakanin jam’iyyun da magiya bayansu wadanda ke kokarin nuna jam’iyyar da ta fi tara mutane wanda shi ne tamkar ma’aunin yanayin karbuwar jam’iyyar ko ma dai dan takarar a wajen al’umma.
Bacin hakan ba lallai ne ya kara yawan kuri’un dan takara ba, magoya bayan jam’iyyun suna ztuwa shafukan sada zumunta irin su Twitter domin su wallafa hotunan gangaminsu a jihohi daban-daban suna yabawa ‘yan takarar da suka tara jama’a su kuma yi dariya wa wadanda ba su tara jama’a sosai ba.
Saboda irin tsananin damuwar da wasu magoya bayan suka yi da abin da mutane za su ce, wadansunsu sun fara wallafa hotunan da bidiyoyin da aka dauka a baya a sunan abubuwan da aka yi a shekarar 2023, wanda ke yawan yaudarar jama’a.
Al misali,, wannan gangamin na APC wanda aka yi a jihar Katsine raar 6 ga watan Fabrairu.
Dogo Shettima wanda shi ne mataimaki na musamman na Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, kwanan nan ya wallafa wadansu hotuna a shafin Twitter ya na cewa yadda yakin neman zaben APC ya kasance ke nan a Katshina. Wajen tsokacin ya ce Mr Tinubu ya tara jama’a sosai a Katsina saboda irin goyon bayan da ya ke da shi daga jama’ar Katsnia.
“Abun da idanu na suka gani a Katsina baki na ba zai iya fada ba …..@officialBAT ya yi sa’ar samun Allad da @MBuhari a gefensa. Jihar Katsina ta bayar da tabbacin cewa @MBuhari nasu ne,” ya rubuta tare da hotunan da ke nuna shugaba Buhari cikin wata mota tare da magoya bayansa
An sake wallafa wadannan hotunan a wadansu shafukan wadanda suka hada da nan, nan da nan.
To sai dai bisa bayanan binciken DUBAWA Wadansu daga cikin hotunan tsofaffi ne
Tantancewa
DUBAWA ta fara da amfani da manhajar da ke tantance hotuna dan gano ainihin mafarin hotunan da ma sadda aka fara wallafa su a duniyar gizo-gizo.
Sakamakon da aka samu daga google ya nuna cewa wasu daga cikin hotunan an dauke su ne a shekarar 2019 lokacin da Buhari ya je yakin neman zabe Katsina a watan Fabrairun 2019
Bisa dukkan alamu, da gangar Mr Shettima ya hada hotunan da wadanda aka dauka a yakin neman zaben jam’iyyar a 2019 dan a yaudari wadansu wadanda ba su ji ba su gani ba.
Mai aiki da gwamnan bai dauki lokaci ya banbanta hotunan ba ya fayyace wa jama’a cewa wasu tsoffi ne a yayin da wasu kuma sabbi – wanda da zai fada wa jama’a gaskiyar abin da ke faruwa a cikin hotunan.
DUBAWA ta gano cewa ainihin hotunan sun kasance cikin wani rahoton da jaridar TheCable ta yi inda ta sa hotunan shugaban lokacin yana neman yin tazarce, kuma a cikin hoton yana tare da Aminu Masari, gwamnan jihar Katsinar.
A Karshe
Wasu daga cikin hotunan yakin neman zaben Tinubu a Katsinan da aka wallafa a shekarar 2019 aka dauka lokacin da jam’iyyar ta APC ta je yakin neman zaba a katsina tare da shugaba Buhari.