Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya NAFDAC ta mayar da martani dangane da binciken da DUBAWA tare da Premium Times suka yi a kan maganin gargajiyar Baba Aisha.
Binciken, wanda aka wallafa ranar ASabar, 10 ga watan Yuni, ya mayar da hankali ne kan abubuwan da dokokin sanya indo kan kirkirowa da sayar da magungunan gargajiya suka kunsa, ganin yadda ‘yan Najeriya da dama ke dogaro da ire-iren magungunan.
Bayan da aka shafe watanni biyar ana bincike, Premium Times ta gano cewa maganin na dauke da lambobin rajistan NAFDAC guda biyu wanda babban hadari ne ga tabbatar da kariyar jama’a.
Bincike mai zurfi da kuma nazarin da aka yi a dakunan bincike su ma sun nuna cewa cigaba da shan ire-iren wadannan magungunan a yadda su ke yanzu na iya kasancewa sanadin cututtuka ko kuma ma jin ciwo a koda, huhu da hanta.
Binciken ya kuma sanya karkatar da hankulan al’umma a kan hukumar NAFDAC, yayi suka rika tambayar yadda aka yi mai kirkiro maganin ya sami lambar rajista ba tare da ya cika halatattun sharuddan da aka gindaya ba, da ma wasu karin laifukan.
NAFDAC ta kaddamar da bincike
A martanin da ta bai wa Premium Times a hukumance, NAFDAC ta ce ta kaddamar da bincike kan abubuwan da jaridar ta gano nan take.
Hukumar ta kuma kara da cewa sashen shi na kula da bincike da tilastawa (I&E) ta fara daukan matakai dangane da maganin gargajiyar Baba Aisha da sauran wadanda ke sarrafa abubuwan da lambobin da aka ba su sun riga sun cika wa’adinsu.
“Rahoton “maganin Baba Aisha” sabo ne. I&E ya fara bincike kan lamarin. Sakamakon farko da muke samu yanzu ya nuna mana cewa lallai ya yi rajista da mu tunda maganin na dauke da lambobin rajistan NAFDAC sai dai wa’adin lambobin sun cika ya kamata a sabunta. Iya saninmu a yanzu shi ne kamfanin bai riga ya fara daukar matakan sabunta lasisin ba.
“Saboda haka mun fara aiwatar da matakan tilastawa a kan duk wadansu magungunan da ake saidawa ba tare da lasisin da ya kamata ba,” wani bangare na wasikar da aka turawa jaridar ya bayyana.
NAFDAC ta yi alkawarin za ta cigaba da bai wa Premium Times karin bayani dangane da na ta binciken.
Hukumar ta kuma bayyana cewa ba da dadewan nan ba ta gudanar da bincike kan wani daga cikin abubuwan da kamfanin Baba Aisha na Sacra Multi-Links Limited ke sarrafawa.
“Sashen binciken hukumar (I&E) ya yi aiki kan wani maganin da Baba Aisha ke sarrafawa mai suna – Abun shakka na musamman mai suna Hajiya Ayisha AK47 a watan Afrilun 2023.”
Hukumar ba ta yi mana karin bayani dangane da abun shakan ba ko kuma ma sakamakon binciken da ta yi.
Tambayoyin da ba su amsa ba
Yunkurin NAFDAC na bin diddigin binciken har yanzu ya bar wasu tambayoyi a baya wadanda ba ta kai ga amsawa ba.
Alal misali, hukumar ta gaza bayyana yadda aka yi kamfanin Baba Aisha ya sami lambobin rajistan tun farko a shekarar 2018.
Bincikenmu ya nuna mana cewa kamfanin Sacra Multi-Links ba ta cika ka’idojin da suka wajaba wajen samun lambobin rajistan NAFDAC ba, amma duk da haka aka ba ta. Wasu daga cikin ka’idojin sun hada da yin rajista da CAC wato hukumar kula da kamfanoni, sai kuma rajista da hukumar da ke amincewa da tambarin kamfanoni, da gabatar da rahoton dakin gwaje-gwaje wanda ke bayyana sakamakon tantance ingancin kayayyakin da ake saidawa.
Yayin da muke bincike, dan jaridan ya tambayi NAFDAC wadannan rahotanni amma ba su bayar da su ba.
Haka nan kuma, hukumar ba ta fayyace mana ko ita ta bayar da izini ko kuma ma ta tantance tallar da masu sayar da maganin ke sa wa dan jan ra’ayin al’umma ba.
Bisa tanadin dokokin NAFDAC wadanda suka shafi tallar magungunan gargajiya da sauran makamantansu, na 2021, tilas ne hukumar ta saurari tallar ta bayar da amincewarta kafin a yi amfani da ita.
Dokar ta ce bai kamata tallar ta ambaci cewa maganin gargajiyar na da wani matsayi na mussamman, ko za ta iya tabbatar da kariy ako waraka.
Dokar ta gargadi sanya bayanan karya a tallar ko bayanan da za su yaudari jama’a ko su nuna cewa na su maganin ya fi na wani da ma dai duk wani targi mara tushe dangane da maganin. Musamman na cewa babu cutar da maganin ba za ta iya warkarwa ba.
A halin da ake ciki dai, ‘yan Najeriya sun kira ga NAFDAC da ta dauki matakan da su ka dace dangane da magunguna a ciki har da haramta amfani da maganin.