Zargi: Matasan da ke tsakanin shekarun 15 – 35 a Najeriya na da yawan kashi 65 cikin 100 na al’ummar kasar wanda ke zaman milliyan 130 cikin miliyan 200 da ake kiyasi shi ne yawan al’ummar kasar
Hujjojin ba su isa ba
Cikakken bayani
Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, Bola Tinubu daya daga cikin manyan ‘yan takarar shugabancin kasar ya fitar da kudurin zaben shi inda ya ke bayyanawa ‘yan Najeriya irin shirye-shirye da zai aiwatar idan har su ka zabe shi.
Tinubu ya cigaba da nanata alakarin cewa zai maimaita irin nasarorin da ya yi lokacin da ya ke gwamna a jihar Legas a matakin gwamnatin tarayya da zarar aka zabe shi da abokin takararsa Kashim Shettima.
Tsohon gwamnan na Legas ya kara da cewa zai mayar da hankali kan fannoni daban-daban kama daga tattalin arziki zuwa tsaro. Tinubun ya ce gwamnatinsa ba za ta manta da matasa ba masu dimbin yawa a Najeriya musamman marasa aikin yi.
A cikin kudurin wanda ya kunshi manufofin na sa Mr. Tinubu ya ce matasan da ke tsakanin shekarun 15 da 35 su ne mafi yawa a kasar domin suna zaman kashi 65 cikin 100 na yawan al’ummar wanda ke zaman miliyan 30.
Bisa bayanan worldometer wanda ke bayyana yawan al’ummomin kasashen duniya, al’ummar Najeriya na da yawan miliyan 200.
A watan Yulin 2022, Sashen kula da tattalin arziki da yanayin zamantakewa na Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa kiyasinta na yawan al’ummar duniya na shekarar 2022. A cewar rahoton, yawan al’ummar duniya zai kai biliyan 8.5 a shakarar 2030.
Rahoton ya kuma sake yin kiyasin cewa a cikin shekaru goma masu zuwa Najeriya za ta kasance a mataki na uku a jerin kasashen masu yawan al’umma da mutane kusan miliyan 372 yayin da matasa za su kasance miliyan 262 na wannan adadin.
“Al’ummomin kasashe da dama a yankin kudu da saharan Afirka za su ribanya kansu tsakanin shekarun 2022 da 2050, abin da zai kara matsain kaimi kan albarkatun da ake da su ya kuma kalubalanci manufofin da aka riga aka sanya na rage talauci da rashin daidaito,” a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
A wani rahoton da aka fitar kafin wannan, Majalisar Dinkin Duniya bayyana cewa nahiyar Afirka ce kadai ke da al’ummar da fi yawan matasa, inda kusan kashi 70 cikin 100 na al’ummar nahiyar na da shekarun haihuwa kasa da 30, har ma ta kara da cewa wannan babbar dama ce ta samun bunkasa.
To sai dai, wasu masu ruwa da tsaki sun bayyana damuwarsu dangane da ko gwamnatocin wadannan kasashe, har da Najeriya, a shirye su ke su samar da irin ababwn more rayuwar da ake bukata domin cin gajiyar gudunmawar da matasan za su iya baiwa kasahsen. Kwanan nan Hukumar Kididdiga ta Kasa ta ce mutane fiye da milliyan 130 a duniya su ke fama da talauci a fannoni daban-daban na rayuwa.
Matsalar rashin aikin yi a kasar na cigaba da tabarbarewa. Alkaluman da aka fitar kwanan nan na nuna cewa rashin aikin yi na kan kashi 33.3 cikin 100 a karshen shekarar 2020.
Tantancewa
Shafin kididdiga Statista ya nuna cewa rabin al’ummar kasar na kasa da shekaru 19 na haihuwa, a yayin da a cikin wannan rukunin kuma wadanda ke da shekaru kasa da hudu na haihuwa ne su ka fi yawa domin sun kai kashi 16.3 na wannan rukunin.
Wadanda ke biye da su, su ne masu shekaru tsakanin 5 da 9. Kason maza a wannan rukunin ya kai kashi 7.4 cikin 100 a yayin da mata ke zaman kashi 7.1 cikin 100. Wannan shafin ya kuma kara da cewa Najeriya ce ke da al’ummar da wadanda ke da mafi karancin shekaru a duniya.
Wadansu alkaluman da su ka fitar ba da dadewan nan ba dangane da yanayin shekarun ‘yan Najeriya ya nuna cewa yara wadanda ke da shekaru tsakanin 0-14 na zaman kashi 43.3 cikin 100 a yayin da rukunin wadanda su ka fi yawa kuma ke zaman masu shekaru 15 zuwa 64 da kaso 53.9 cikin 100 na yawan al’ummar kasar baki daya.
Baya ga haka, wani bayanin da aka samu daga Bankin Duniya a 2021 shi ma ya bayyana abin da statista su ka fada na cewa masu shekaru 0-14 na zaman kashi 43.3 cikin 100, masu shekaru 15-64 na zaman 53.7 cikin 100 a yayin da wadanda ke da shekaru 64 sama suke zaman wadanda ke da kaso mafi karanci a kasar wato kashi 2.98 cikin 100.
Babu wani bayanin da ya mayar da hankali kan wadanda ke da shekaru tsakanin 15 da 35. Dan haka, ba zamu iya tantance inda Tinubu ya samo na sa alkaluman dangane da yawan matasan da ke al’ummar Najeriya ba.
A kan wayar tarho mun yi ta kokarin samun Festus Keyamo mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ba tare da yin nasara ba, kuma har zuwa lokacin da muka yi wannan rahoton ba mu same shi ba.
Mun tura mi shi da sakon text, shi ma ba mu sami amsa ba.
A Karshe
Babu kwararan hujjojin da suka goyi bayan ikirarin cewa mutane miliyan 130 ne ke Najeriya, ko kuma ma kashi 65 cikin 100 na alummar matasa ne masu shekaru 15 -35.