Babu isasshen hujjar tabbatar da kissar shahararren dan bindiga Kachalla Haire a jihar Zamfara.

No sufficient evidence bandit kingpin Kachalla Haire was killed in Zamfara
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Spy Nigeria a shafinsa na Facebook ya ce sojoji sun kashe shahararren dan bindiga Kachalla Haire a wani farmakin da suka yi a Bungudu zuwa Gusami zuwa Gusau a jihar Zamfara.

Babu isasshen hujjar tabbatar da kissar shahararren dan bindiga Kachalla Haire a jihar Zamfara.

Hukunci: Rashin isashiyyar huja. Rahotanin da aka wallafa a watan Mayu 2026 sun nuna cewa kachalla Haire ya gamu da ajalinsa a wani batakashi da kungiyoyin mahara suka yi. Sai dai kuma babu hujar da ta tabbatar cewa Haire ya mutu ko kuma ya tsire da ransa a wannan hari da aka yi a watan Satumba. Rundunar sojin Najeriya wanda ayyukanta ke da alaka da mutuwar dan bindigan sun kasa tabbatar da mutuwar Haire.

Cikakken Bayani

Spy Nigeria a shafinta na Facebook a ranar Laraba 2 ga Satumba ta wallafa wata da’awa dake cewa shahararren dan bindiga Kachalla Haire wanda aka fi sanin sa da sunan ‘Mala’ikan Mada’ ya mutu a wani farmakin da sojoji suka yi kwana-kwanan nan .

Da’awar da aka saka a (nan) ya nuna cewa Haire tare da sauran mahara da dama sun mutu a Bungudu dake Gusami zuwa Gusau bayan maharani sun fita kai hari wani waje.

Da’awar ya ce harsasan sojoji sun ji wa Haire  mummunar rauni sannan abokan aikinsa a haka din ne suka kawo shi gida inda a gida ya mutu.

Da’awar ya nuna hoton Haire dauke da bindiga inda a tsakiyar hoton aka rubuta ‘AN KASHE SHI’

Zuwa ranar Litini 7 ga Satumnba 2026 mutum 382 sun duba da’awar, 141 sun maida martani da 38 sun sake wallafawa.

Wasu a shafukansu sun yi maraba da wannan nasara da aka samu wasu kuwa sun yi shakkan kashe dan bindigan.

Stephen Ademola ya rubuta cewa “Na samu labari da dama kuma da dadewa cewa wai an kashe wannan dan bindiga. Ina fatan cewa ba zai kara bayyana ba kamar yadda ake yi a fim ba.

Sankey Jumbo ya rubuta cewa “Kun yi kokari. Haka muke so ana yi musu kisan dauki dai-dai tare da wadanda ke da iko a gwamnati.

An ga rubutun ra’ayoyin mutane da dama irin haka a shafukansu na Facebook a nan, nan da nan.

Ganin yadda aka alakanta mutuwar Haire da ayyukan sojoji ya sa DUBAWA ta gudanar da bincike kan rahotanin da suka nuna ya mutu a kwanakin baya sannan da samun tabbacin mutuwarsa daga wajen jami’an tsaro.

Tantancewa

DUBAWA ta tattaro rahotanin mutuwar Haire musamman wadanda suka kareda yanar gizo a watan Satumba.

A ranar 10 ga Mayu 2026 wani masanin ayyukan mahara Zagazola Makama ya rawaito cewa Haire wanda aka fi sani da sunan ‘Mala’ikan Mada’ yam utu a ranar 8 ga Mayu a wani harin da kungiyoyin mahara suka yi a jihar Zamfara.

Bisa ga rahotan majiya daga rundunar tsaro sun ce rikicin y afara ne yayin da maharan ke raba bindigogi da sauran makamai da kaya masu daraja da wani kwamandan su ya mutu ya bari.

A watan Mayu wani gidan jarida ta dauki rahotan abin da ya faru da aka saka a nan,nan, nan da nan. Bakatsine (@DanKatsina50)  ya yada mutuwar dan bindigan a X sannan gidan jaridar  Daily Post Nigeria ta dauke labarin.

Sai dai kuma duk da yawan rahotanin da aka wallafa kan mutuwar Haire basu tabbarae cewa ya mutu a farmakin da sojoji suka yi a watan Satumba ba.

DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano rahotanin da gidajen jaridu suka yi inda sakamakon ya nuna cewa Haire ya tsira da ransa sannan har ya ci gaba da ayyukansa amma babu rahotanin da suka shaida cewa Haire ya tsira da ransa ko yana cikin koshin lafiya kafin da bayan farmakin da aka yi a Satumba ba.

Rashin tabbacin mutuwar dan bindigan ya karu musamman bayan da Daily Post Nigeria ta wallafa rahoto a ranar 2 ga Satumba 2026  da taken ‘Shahararren dan bindiga Haire ya mutu a Zamfara’. Rahotan bai  nuna alakan sa da rahotan mutuwar dan bindigan da ta yi a watan Mayu ba.

DUBAWA ta yi kokarin ganawa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara DSP Yazid Abubakar inda bai masa kira ko sakonin tes din da aka aika wa wayar hannun sa ba sannan rundunar bata fitar da takarda ba dake bayyana ko dan bindigan ya mutu ba.

Gidan jaridar ta gana da kodinatan yada labarai na rundunar sojin Najeriya Manjo-jana Michael Onoja ranar Alhamis 3 ga Satumba inda ya bayyana cewa sojoji sun yi bata kashi da wasu mahara a jihar inda suka kashe wasu da dama said ai babu tabbacin ko Haire na cikin wadanda aka kashe.

Ya ce rundunar ba ta da tabbacin mutuwar Haire amma za ta ci gaba da bincike tare da sa ido kan lamarin.

A ranar Asabar 5 ga Satumba 2026 DUBAWA ta tuntubi Onoja domin gano ko runduran ta tabbatar da mutuwar dan bindigan inda ya shaida cewa har yanzu babu wani tabbaci.

Ya tabbatar cewa jami’an sun a nan a yankin inda a dalilin zaman su maharani sun kasa ci gaba da ayyukan su. Ya tabbatar ceewa za su sanar da gidan jaridar da zaran sun samu karin bayani.

Rundunar sojin Najriya ta kasa tabbatar da cewa Haire ya mutu a harin da suka yi a watan Satumba ba sannan ta kasa tabbatar da ko ya tsira da rans aba.

A Karshe

Babu tabbacin cewa Kachalla Haire yam utu a farmakin da sojoji suka yi ranar 2 ga Satumba 2026 amma rahotanin da aka yi a watan mayu sun nuna cewa Haire ya mutu a dalilin rikicin da kungiyoyin mahara suka .

Sai dai kuma DUBAWA ta kasa samun hujjan da ya tabbatar cewa Haire yam utu a Mayu ko ya tsira da ransa kuma ya ci gaba da rayuwa har zuwa watan Satumba ba.

Rundunar sojin Najeriya wanda aka alakanta ayyukan ta da mutuwar dan bindigan sun kasa tabbatar da mutuwar dan bindigan.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).