|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: @VOLTOXf a shafinsa na X ya wallafa wani bidiyo da ya nuna wani yaro karami na koyon harbin bindiga a wani bishiya cikin wata hamada inda ake zargin wai bidiyon ya nuna yadda ake horar da wani yaro bafulatani yadda zai kashe kiristoci.

Hukunci: Yaudara ce! Bidiyon bai bada hujjan cewa yaron bafulatani bane ko dan Najeriya ba ko kuma ana horar da shi yadda zai kashe kiristoci ba. Sakamakon binciken da aka gudanar ya nuna mutanen dake bidiyon na magana da harshen Arabi na ‘yan kasar Sudan babu yare ko daya na Najeriya.
Cikakken Bayani
A ranar Talata 1 ga Satumba 2026 wani VOLTOX (@VOLTOXf) a shafinsa na X ya wallafa wani bidiyo da aka saka (a nan) inda ke nuna wani yaro karami a wani wuri kamar hamada rike da bindiga.
Bidiyon ya nuna yadda yaron ya yi magana da wasu da Kamaran bai dauki hoton su ba sannan yad aga bindigar ya harba ga wani bishiya.
VOLTOX ya ce “Yadda yaro karami bafulatani ke koyon yadda zai kashe kiristoci.
A ranar Alhamis 3 ga Satumba mutum 2,762 sun duba bidiyon, 42 sun sake wallafa shi, 38 sun nuna shi’awa, 4 sun mai da martani da 2 sun saka Alamar takarda.
Wani Abdullmuminu @KAbdullmum55597 ya yi korafi kan wurin da aka dauki bidiyon da yaran da ake yi inda ya ce “Wannan wurin ba Najeriya bane… ka fahimci yaren da ake yi a bidiyon”.
VOLTOX a martanin da ya maida ya yi tambaya “Su Musulmai ne?.
Okanumee Uchechukwu (@okanumee27) ya kara karfaffa maganar inda yake cewa sakataren tsaro na kasar Amurka, Pete Hegseth, firayam ministan kasar Masar Benjamin Netanyuhu da kungiyar kare hakkokin dan adam.
DUBAWA ta gano cewa an wallafa bidiyon a Facebook da X a nan da nan.
Tantancewa
Dubawa ta gudanar da bincike kan bidiyon. A bidiyon wani yaro dake zaune kan wani tudun kasa a wani wuri dake kama da hamada a dauke bindiga ya saita ga wani kayan lanbu da aka makala a jikin wani bishiya. Da yaron ya mike sai ya dauki fankon harsashin da ya harba yana murmushi tare da yin hannun sa na Alamar salama ga wasu da Kamaran bai dauki hoton su ba.
Bidiyon bai nuna alamun na tuta ba ko wani riga da za a iya gani barayin duniyan da aka dauki bidiyon ko wani abu a muhallin da aka dauki bidiyon da har za a iya alakanta shi da Najeriya ko kuma ‘yan kabilar Fulani.
DUBAWA ta yi amfani da ‘Google Lens’, reverse-image searches’ da ‘nVID verification’ inda sakamakon binciken ya nuna cewa an dauki bidiyon a Najeriya.
Gidan jaridar ta ji muryoyin wasu maza biyu da suke magana da yaron inda bayan ya harba bindigar sai ba su kara magana ba ko da harshe Fulfulde, Hausa ko Pidgin English.
DUBAWA ta gusanar da bincike domin fasara harshen da ake magana da shi a bidiyon inda ta yi amfani da ElevenLabs wajen yin haka.
Fasarar farko ya ce “A sama yake. Maza tashi mu je, daya biyu. Ya wargaje”
Fasara ta biyu ya ce “Ya kamata ka gane wannan abin. Tashi, mu tafi, daya, biyu. Sai ka samu na uku”.
DUBAWA ta yi amfani da Google Gemini domin kara fasara abin da ake fada.
Google Gemini ya nuna cewa harshen da ake magana da shi Arabic din kasar Sudan ne.
Sun ce; “هيكون؟ يلا، واحد، اثنين…” “Zai yi aiki? Maza, DAYA biyu…”) daga sakan 0:05 zuwa 0:07
Ya kuma fasara “أبو الزفت ذاته!” “Wannan ya fi muni!/ Wannan shirme ne! kuma ka yaba bayan ka harba.
“قسم بالله ولد… شاطر!” “Na rantse da Allah wannan yaro… na da baiwa/ yana da wayo.
A takaice dai an gano cewa wadannan mutane Fulani makiyaya ne ‘yan Najeriya ko kuma mahara ke samun horo a Areacin Najeriya.
A Karshe
Bidiyon da ake cewa wai ana horar da wani yaro bafulatani domin ya kashe kiristoci a Najeriya karya ne. bidiyon ya nuna wasu dake magana da harshen Arabic din ‘yan kasan Sudan ne dake horar da wani yaro yadda zai harba bindiga sannan bidiyon da ya dade yana shawagi a yanar gizo ana amfani da shi domin tada kiyayyar kabilanci da adini.
Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).
