Zargi: wani sakon twitter ko kuma tweet kamar yadda aka fi sani, ya bayyana cewa an kashe wasu ‘yan Najeriya 20 a bainar jama’a a kasar Saudiyya bayan da aka kama su bisa zargin su da safarar miyagun kwayoyi.

Sakamakon Bincike: Babu cikakken gaskiya. Duk da cewa bidiyon ya yi kama da gaskiya, bincikenmu ya nuna cewa bidiyon na kan yanar gizo-gizo tun a shekarar 2015. Bacin haka, ba mu ga wata hujjar da ta tabbatar mana cewa wadanda ke cikin bidiyon ‘yan asalin Najeriya ba ne.
Abun da da yawa suka kwatanta a matsayin matsanancin hukunci, hukuncin kissa shi ne hukunci mafi tsanani a cikin hukunce-hukuncen da akan zartar wa masu laifi.
Ba da dadewan nan ba, PSAFLIVE, wani gidan talibijin da ke Afirka ta Kudu a tasharta da ke sharhi kan lamuran siyasa, ta yi zargin cewa an kashe wasu ‘yan Najeriya 20 a gaban al’umma bayan da aka kama su da laifin safarar kwayoyi. Tashar ta wallafa labarin ne a shafinta na twitter. Domin kara yada labarin, an yi amfani da hoton wani bangaren bidiyon wanda ke nuna wasu mutanen da ke sanya da Thawb – kayan Larabawa, yayin da su ma ‘yan kallon suka yi shiga irin wannan.
“…. ‘Yan Najeriya 20 sun gamu da ma’aiki bayan da aka kama su da laifin safarar kwayoyi da sayarwa,” wani bangaren sakon ya bayyana.
“Lura: Ba za mu iya sanya hoton bidiyon ba saboda yadda ya ke da tayar da hankali,” ya cigaba da bayyanawa.
Tun bayan da aka wallafa labarin mutane 2,911 sun danna alamar like kuma mutane 1,150 sun sake raba labarin. Daya daga cikin wadanda suka tsokaci a karkashin labarin @ismailsalajee, shi kuma dora bidiyon ya yi.
Bidiyon ya nuna wadansu maza a kan guwawunsu da idanunsu rufe da tsumma kuma sun nade hannuwansu a baya. A bayansu kuma akwai ‘yan sanda tsaye suna sanye da kayayyakinsu. ‘Yan kallo kuma wadansunsu na ihu yayin da mai zartar da hukuncin ya shigo sanye da na shi rigunan ya fille kan mutanen da takobi.
Duk da cewa mutane kalilan ne suka bayyana shakkunsu dangane da sahihancin batun, wasu sun yarda cewa gaskiya ne. A cikinsu akwai @NicolMaimela, wanda ya ce ya goyi bayan hukuncin. A cewarsa: “Na yadda cewa masu safarar kwayoyi sun cancanci irin wannan hukuncin.”
Sai dai ba kamar shi ba @Speaktruth_x, wani mai amfani da shafin kai tsaye cewa ya yi labarin karya ne wato “fake news.”
Ganin yawan mutanen da suka yi ma’amala da wannan labarin ne ya sa muka ga kamar zai iya janyo matsala kuma ya kamata mu tantance gaskiyar.
Tantancewa
Mun gudanar da bincike kan wannan zargi ta yin amfani da manhajar da ke tantance hotuna ya ga mafarinsu. Wannan ya kan yi amfani da hoton kadai ba sai an rubuta wani abu ba.
Sakamakon binciken ya nuna mana cewa wannan bidiyon na kan yanar gizo-gizo tun shekarar 2015 wato fiye da shekaru bakwai yanzu.
Haka nan kuma bisa bayanan jaridar the Middle East Eye, wata jarida mai zaman kanta, wadda ke daukar rahotannin abubuwan da ke faruwa a yankin arewacin Afirka da Gabas Ta Tsakiya, akwai zargin cewa wani mai suna Ali Dubaisy wanda mai rajin kare hakkin bil adama ne dan asalin Saudiyya ya dora bidiyon a YouTube. Ana kyautata zaton a boye ya dauki bidiyon domin an haramta dauakar bidiyo a lokutan da ake zartar da irin wannan hukuncin.
Dubaisy ya fadawa Middle East cewa da shi da kansa ya sami bidiyon hannun wani mai yawon bude ido daga birnin Jeddah da ke tekun bahar maliya wanda ya dauki bidiyon a wayarsa.
Dubaisy ya ce bai ma san cewa an kashe mutane uku ba, amma kwanan nanya faru. Sunayen mutanen ko ma dalilin da ya sa aka kashe su ma har yanzi ba’a sani ba,” a cewar rahoton.
Banda wannan labarin, sauran binciken da muka yi a YouTube sun nuna cewa an fitar da bidiyon ne tun 2015. Bacin haka babu wani abu takamaimai da ya bayar da hujjar cewa ‘yan Najeriya ne.
Wani abu mai mahimmancin da muka lura da shi dangane da salon shafin da ya wallafa wannan labarin shi ne yadda suke abubuwansu. Kamar dai babban burin shafin talla ne tunda wata sa’a zai sanya labarai masu sosa zuciya da wadanda ke harzuka jama’a. Daga an fara cece-kuce kzma sai su wallafa wani abun da suke saidawa daga kasa dan dai kawai mutane su gani su ce za siya.
A Karshe
Zargin ya yi mafari ne daga wani tsohon bidiyo wanda aka sanya a yanar gizo tun a shekarar 2015. Bacin haka babu wata hujjar da ta tabbatar cewa mutanen ‘yan Najeriya ne. Wannan batun yaudara ce kawai.