African LanguagesHausa

Bidiyon da ke zargin wai ‘yan Arewa sun koyi amfani da na’urorin zabe, gabanin zabukan 2023 ba gaskiya ba ne

Zargi: Wani bidiyo da ke ta yawo a WhatsApp na zargin wai ‘yan arewa sun fara koyon amfani da na’urar zabe gabannin zaben 2023 mai zuwa.

<strong>Bidiyon da ke zargin wai ‘yan Arewa sun koyi amfani da na’urorin zabe, gabanin zabukan 2023 ba gaskiya ba ne</strong>

Zargin wai ‘yan arewa sun koyi amfani da na’urorin zabe kafin kowane yanki saboda shugaba Buhari dan arewa ne karya ne. Wannan bidiyon ya fara bulla a shekarar 2018 ne lokacin da ake kwatanta nasarar sabbin na’urorin zabe a jihar Kaduna

Cikakken labari

Kwanan nan wani bidiyo ya bulla a WhatsApp ya na zargin wai ‘yan arewa sun riga sun fara koyon amfani da na’urar yin zabe gabanin zabukan da ake sa ran yi a 2023.

Labarin na kira ga ‘yan kudu da su “farka” inda wadanda su ka wallafa bidiyon ke kokarin nuna cewa wai bidiyon ya fallasa shirin da arewa ke yi cikin sirri don samun fa’ida a zaben na 2023.

Tun farko an raba Najeriya bisa yanayin kasa da kabila inda a yankin arewacin kasar Hausawa da Filani ne su ka fi yawa. A yankin kudancin kuma akwai Yarubawa da Iyamurai da wasu kabilu da dama.

A cikin bidiyon, an ga wasu a cikin wani daki sun sunkuya kusa da wata na’urar zabe suna gudanar da abin da ake zargi ya yi kama da zabe.

Labarin ya yi bayani kamar haka, “‘Yan arewa sun riga sun fara koyon yadda ake amfani da na’urar zabe. Mu nawa mu ka san cewa ana iya yin haka? Buhari da mukarrabansa a yankin arewacin Najeriya sun riga sun fara gwada amfani da na’urar.”

Bacin haka, mai rubutun ya kara da rokan ma’abota shafin na shi na Fecebook (‘Yan Kudancin Najeriyar) da su tura bayanan ga dik wadanda ya dace “Idan kun yarda, ku tura wannan bayanin ga duk mutanen kudun da ke baci, ko ce mu su su farka sun zauna da idanunsu a bude.”

Ganin irin hadarin da irin wadannan kalaman ke da shi da irin matsalolin da za su iya janyowa ga kasa baki daya ya sa DUBAWA tantance wannan batun.

Tantancewa

Da DUBAWA ta yi amfani da manhajar tantance hotunan bidiyo na InVid ta gano cewa an fara daukar hoton ne a wani zaben da aka yi a jihar Kaduna a shekarar 2018 lokacin da jihar ta kaddamar da sabon salon yin zabe da na’urorin wajen gudanar da zaben ciyamomi ko kuma shugabanin kananan hukumomi.

Da DUBAWA ta binciki tarihin bidiyon a Facebook ta gano cewa an fara wallafa shi ne a shafin jam’iyyar Legacy ko kuma Legacy Party of Nigeria Suleja Chapter (reshen Suleja) ranar 31 ga watan Janairun 2018. A wancan lokacin, shafin ya wallafa hoton bidiyon tare da tsokacin da ke gabatar da tsarin zaben da kuma karin bayani dangane da yadda jihar Kaduna ta yi amfani da shi kamar haka.

“Daga kasan wannan shafin, kuna iya ganin samfurin na’urar zaben da majalisar dokoki na 8 ta amince da shi wajen gudanar da zabuka masu zuwa . Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da aka amince a gwada amfani da shi domin tabbatar da kaifin aikin shi  lokacin zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli,” a cewar tsokacin.

Baya ga wannan shafin bidiyon ya sake bulla a shafin Movement for the Protection of Plateau Heritage and Dignity wato kungiyar kare gadon mutanen Filato da  mutuncinsu, shi ma a Facebook ranar 8 ga watan Fabrairun 2018.

Abun da ya bayyana a fili shi ne a duk shafukan da DUBAWA ta ga an wallafa wannan bidiyon a shekarar 2018 dukansu sun danganta shi da zaben na Kaduna babu wanda ya kwatanta shi a matsayin wani abin da aka yi a boye.

Na’urar zaben ko kuma EVM ba ta da nauyi kuma ana iya kai ta ko’ina cikin sauki, nauyin ta bai wuce kilo 10 ba kuma idan aka sanya mata batiri tana iya kai wa sa’o’i 10 zuwa 16 ba ta mutu ba, tana tafiya ne ba tare da wata tangarda ba domin tabbatar da cewa an irga kuri’u ba tare da kuskure ba.

Ranar asabar 12 ga watan Mayun 2018 masu zabe a Kaduna su ka kafa tarihi lokacin da suka kasance masu zabe na farko su yi amfani da na’urar zaben wajen zaben ciyamomi da kansiloli a kananan hukumomi 23 na jihar 

A Karshe 

Bidiyon da ke zargin nuna son kai a wasu yankuna gabanin zaben 2023, tsoho ne kuma ba’a bayyana gaskiyar abin da ke faruwa cikin bidiyon ba. Wadanda su ka wallafa bidiyon sun sakaya gaskiyar ne da nufin batar da jama’a. A shekarar 2018 aka dauki bidiyon lokacin da aka fara amfani da na’urar zabe a jihar Kaduna wajen gudanar da zaben Ciyamomi da Kansiloli. Wannan zargin ba gaskiya ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button