African LanguagesHausa

Bincike: Baba Aisha, ‘Likitan’ karyar Najeriya cinye kudin jama’a kawai ya ke yi maganin shi ba ya aiki

A Abuja, babban birnin tarayya yawancin mazauna kan sha ‘jikon Baban Aisha’ wani tsimi da ake yi da ganayayyakin gargajiya ana saidawa N100 wanda kuma ake kiraren yana warkar da cututtuka da yawa. A wannan binciken wanda muka shafe watanni biyar muna yi, Kemi Busari ya yi amfani da kumiyya wajen bin diddigin abun da ke cikin hadin da ake saidawa yayin da ya ke sanya ayar tambaya kan sahihancin hukumomin da ya kamata su sanya ido kan irin wannan magugunan ganin yadda magani irin wannan ya sami karbuwa ba tare da an tantance hadarin shi ba.

Da rana ta fara sauka a kan titunan Abuja, za’a fara jin muryoyi iri-iri kan lasifika a kauyukan da ke kewaye da birnin, muryoyin da ke bayani kan kyakyawar fata da waraka, kuma a kan motocin da ke dauke da wannan lasifikar sune masu sayar da magunguna gargajiya wadanda kowane da irin wakar da ya k rairawa wa duk wanda ke so ya saurara.

Daga cikin zabin magungunan da ake saidawa, guda daya ne ya fi samun karbuwa mai suna: Ganyen Sacra, ko kuma maganin gargajiyar Baba Aisha. Daga kasuwannin da ke bakin hanya zuwa manyan kasuwanni da tashoshi a Kubwa, Lugbe, Nyanya, Jabi, Kuje da Kurudu — Hasali ma kuwan kowace al’umma a babban birnin tarayya — ana iya ganin masu sayar da wannan maganin suna tallan shi, suna alkawarin yadda maganin ke warkar da kusan kowace cuta a farashi mai rahusa na  N100.

Yau, Baba Aisha, gajeren mutumin da ke bayan daular maganin gargajiyar Sacra shi ne jigon wata talla mai tsawon minti tara wadda ake sakewa ta lasifikar da aka dora kan wata mota kirar Honda da a ko da yaushe ana iya ganin ta a mahadar Kurudu.

Talla ta fara ne da addua daga wanda ya hada tallar, wadda shi ne kuma ya dauki nauyin gabatar da bayanai a tallar. Ya fara da gabatar da kansa a matsayin Dr. Salisi Sani Na Wagini (Baba Aisha) sa’annan ya yi addu’a ga ma’aiki da kare masu sauraron shi daga bala’i da talauci da asara.

Cikin raha da annashuwa, watakila dan ya boye rashin iya turancinsa, Baba Aisha ya fara bayar da shaida daga kwastamominsa da szka gamsu da maganin yayin da ya ke lissafa yawan cututtukan da maganinsa ta ganye Sacra ke warkarwa: Sun hada da Typhoid, Malaria, ciwom ciki, ciwon sanyi, ciwon kwankwaso, basir da sauransu. Ya bukaci masu sauraron shi su dauki kwalba mai yawan mil 120 sau biyu kowace rana sa’annan sun tabbatar sun ci abinci kafin su yi haka.

Daga nan tallar sai ta koma ga lissafa alamun cututtukan da aka cika samu inda ya kan kara da yin bayani dangane da bincike mai zurfin da ya kan ce ya yi da ma irin kwarewar da ake amfani da shi wajen samar da abun da ake sanyawa cikin kowace kwalba. Bayan haka ne kuma sai ya fara kira ga mutane da su guji zuwa asibiti da alkawuran karyar da ake musu dangane da magungunan zamani kuma a maimakon haka su yi imani kawai da karfin da maganin Baba Aisha ke da shi musamman ga kananan yara.

“Ko da ma kuna da niyyar zuwa asibit, ni Dr Salisu Sani na ce kada ku je. Ko da kun je, za su ce yaranku na bukatar karin ruwa ko kuma su kara musu jini,” ya ce a cikin tallar. “Ba kowa ba ne da karfin zuwa ya sayi jini… amma idan kuma zo wuri na da dan kudi kalilan, za ku iya shan maganin gargajiyar mu kuma ba za ku sake jin wani ciwo a jikinku ba,” ya kara da cewa kafin ya bar masu sauraro da fatan cewa wannan hadin ne amsa ga duka cututtukan da suke fama da su.

Sai dai a bayan wadannan alkawuran, wata ‘yar kwalba ce mai dauke maganin gargajiyar da ke da manyan alamun tambaya. Tambayoyi dangane da mafari ko kuma tushen maganin, kayayyakin da aka sa a ciki, yadda ake hadawa, tambayoyi dangane da yadda ake bayar da maganin da kuma cancantar wanda ke hadawa da ma dai mafi mahimmanci, tsarin sanya idon da wanna maganin ke amfani da shi yana samun cigaba

Ga mutanen Abuja da wadanda ke zama a yankunan da ke kewaye da wuraren da aka fi amfani da maganin, ganyen Sacra, na da arha kuma hanya ce ta samun magani a duk sadda mutun ke fama da rashin lafiya ko kuma suka ji kamar ba su jin dadin jikinsu. Amma duk da haka watannin bincike, wanda ya hada da gwada maganin a dakin gwaje-gwaje ya sanya mu shakka dangane da sahihancin maganin.

Magani ko kuma dai a ce tsimi mara rajista 

Abun da Baba Aisha ke kira magani a tallar, wani tsimi ne kawai cikin roban da ba’a like ba, wai yawan 120ml. Kowace roba na dauke da tsimin mai launin ruwan kwai da wani abu mai kama da dudduga a kasa. Bincikenmu ya bayyana mana cewa launin da ma duddugar da ake samu duk ya ta’allaka ne a kan yawan wani garin hodar da masu saidawa kan kara a cikin tsimin kafin su sayar bayan sun karba daga wurin shi Baba Aishan.

A jikin robar akwai bayani dangane da kayayyakin da aka hada aka yi tsimin, sunayen cututtukan da tsimin ke warkarwa, yawan da ya kamata a sha, yadda ya dace a adana maganin, lambar rajista, bayanan kamfanin, lambobin waya da hotun wanda ke sarrafa maganin. A wurare 14 da muka kai ziyara a Abuja, duk wadannan bayanan haka iri dayane.

Wata hanya mai sauri na gane cewa maganin jabu ne shi ne robar na dauke da lambobi biyu na rajista da hukumar NAFDAC. Ita Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) na sanya ido, da kuma kula da yadda ake sarrafawa, fitarwa, shigarwa, tallatawa, rarrabawa, sayarwa da amfani da abinci, magugnguna, kayan shafe-shafe, na’urorin aikin likita, sinadaran daban-daban da ruwan shan da ake saidawa a Najeriya.

Dokar NAFDAC ta Abinci, Magunguna da sauran Kayayyakin da ke da dangantaka da su ta ce bai kamata a sarrafa maganin gargajiya, a fitar da shi, a tallata ko a rarraba shi ba tare da an yi mi shi rajista a Najeriya ba. Amma yanzu ga maganin gargajiyar Sacra da lambobin rajista har guda biyu – A7-2551L da A7-2590L- wadanda aka kwatanta da ‘NAFDAC REG NO’ kan kowace kwalba.

Mun yi amfani da shafin tantance sahihancin kambobin NAFDAC din da hukumar ta tanadar dan ganin ko lambobin na kwarai ne, nan da nan shafin ya bayyana su a matsayin ‘bogi’ wato fake kamar yadda aka fi sani da turanci.

Tare da shakka, mun cigaba da binciken inda muka sake gano wadansu rahotanni wadanda suka tabbatar mana da bayanin da muka samu. A watan Satumban 2017 hukumar NAFDAC ta kwace wasu magungunan Sacra bayan da mai sarrafa magungunan ya gaza kammala yin rajistan maganin ta yadda zai bayar da cikakkun bayanan da ake bukata dangane da maganin. Dan haka me ya faru tun bayan nan? Shin daga Baya Baba Aisha ya dawo ya kammala rajistan? Mun rubuta wa NAFDAC dan samun karin bayani.

A martaninta, hukumar ta ce an sake shigar da maganin dan neman nagartattun lambobin rajista a watan Janairun 2018. Daga nan an bayar da amincewa bayan da “kamfanin ya bi duka hanyoyin da suka wajaba kuma sun bayar da duka bayanan da aka bukata daga wajen su.”

NAFDAC ta ma kara da bayanin cewa ta sake samun bukatar sabunta lambobin rajistan maganin a watan Augustan 2020. Sai dai ba ta bayar da amincewarta ba saboda ba ta cika ka’idojin tantance ingancin masana’antar da ake sarrafa maganin ba, wanda aka fi sani da Good Manufacturing Practice (GMP)

Idan har ana bin ka’idoji ya kamata a ce an cire wannan maganin daga kasuwa tun bayan da wa’adin lambobin farko da aka bai wa kamfanin ya cika, amma sai ya cigaba da zama tamkar ‘dauk’i ga mazauna wadanda suke ganin shi kamar magani mai rahusa. Hasali ma yawancin mutane na kwatanta irin motocin da ake sayar da magungunan a matsayin ‘asibitoci’

Kadan daga cikinsu wadanda suka yi kokarin tantance sahihancin maganin sun ce sun amince da ingancin shi bayan da suka ga cewa yana dauke da lambobin rajistan NAFDAC, wata kila tunda ba su yi la’akari da cewa lambobi biyu ne ma ke kan maganin a maimakon dayan da aka saba.

A wata wasikar da ta rubuto mana, NAFDAC ta tabbatar cewa lallai A7-2590L ita ce lambar da aka bai wa kamfanin a shekarar 2018. Sai dai ta ce ba’a sabunta rajistar lambar ba tun bayan da wa’adinta ya cika a shekarar 2020.

“NAFDAC ba ta bayar da lambobinta guda biyu a sanya a abun sarrafawa guda daya,” kamfanin ta bayyana yayin da ta ke cewa ba ta san da dayan lambar ba mai kamar haka: 

Wasu karin laifukan da suka sabawa ka’idoji; da sanin NAFDAC

Mun yi magana da masu amfani da maganin fiye da 20, kuma yawancinsu sun bayyana kyawawan abubuwa dangane da maganin. Sun ce za su cigaba da amfani da ‘maganin’ tunda hukumar NAFDAC ta bayar da amincewarta. Sai dai a yanzu haka dai NAFDAC ta keta wannan amanar da aka ba ta kamar yadda bincikenmu ya nuna.

Mu fara da bin diddigin rajistar da aka ce an yi a shekarar 2018. Bisa tanadin dokokin NAFDAC na sake sabunta rajistar magungunan gargajiya da wadanda ke inganta abinci, duk wanda ke neman yin rajistan kayayyakin da ya ke sarrafawa, dole ne ya cika wadansu takardu wadanda suka hada da: shaidan cewa sana’ar na karkashin kamfanin da aka yi wa rajista da Hukumar Kula Harkokin Kamfanoni da ba su Lasisi  wato (CAC), da kuma shaidar rajistar alamar kasuwanci da Hukumar rajistar alamar kasuwanci na ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, sai kuma cikakken satifiket na nazari da tantance inganci daga dakin gwajin da ke tantance ingancin kayayyaki, da dai sauransu. Bincikenmu ya nuna mana cewa kamfanin Sacra Multi-Links bai kammala cika wadannan ka’idoji ba a shekarar 2018 sadda aka ba shi lambobin NAFDAC na farko.

Binciken da muka yi sau da yawa a shafin CAC dan gano kamfanin Sacra Multi-Links ya nuna mana cewa babu wani kamfani mai wannan sunan a cikin kundin kamfanoninsu a duk sadda muka sa sunan martanin da muke samu shi ne “search not found” wanda ya nuna mana cewa kamfanin ba shi da rajista. Daga nan sai muka dauki lauya dan ya yi mana nazarin kamfanin ya gano ko ta cika sharuddan da doka ta tanadar ko kuma dai tana aikata laifuka ne. 

“Kamfanin bai yi rajista da CAC ba,” lauya Olalekan Idowu ya ce bayan da ya kammala bincikensa. “Bisa tanadin doka, ba wanda zai iya yin amfani da ko da sunan yankansa ne ya yi kasuwanci idan har bai yi rajistan sunan ba,” ya bayyana.

Dokar da ya ke magana a kai, ita ce dokar CAMA Company and Allied Matters Act wadda ta ke Kula da Harkokin Kamfanoni da Sauran Batutuwan da suka shafi Dangantaka ta Hadin Gwiwa, wadda a sashi na 863 ta ayyana cewa “mutun ko kungiya ko hadakar mutane ba za su iya gudanar da harkokin kasuwanci a Najeriya a matsayin kamfani ba, ko hadakar kasuwanci irin wanda alhakin shi ke da iyaka, ko hadakar kasuwanci mai iyaka, ko kuma dai a karkashin sunan da ba’a yi wa rajista ba a karkashin wannan dokar.”

Mun kuma iya tantnace ko kamfanin ya cika sharadin yin rajistar tambari da hukumar rajistan tambari da alamun Najeriya bisa tanadin doka. A wasikar da suka rubuta mana yayin da suke amsa tambayarmu dangane da wannan batun, Hukumar rajistan alamun ta bayyana mana cewa kamfanin ta mika takardun rajista ranar 23 ga watan Nuwamban 2016, sai dai ba ta kai ga kammalawa, har zuwa yanzu, shekaru shida bayan nan. Dan haka hukumar ta ce Sacra Multi-Links “ba ta sami matsayin rajista ba a takardunta”

Lauyoyi biyu wadanda suka yi tsokaci dangane da wannan cigaban sun ce kamfanin na da akalla matakai biyu wadanda ya kamata a ce ta cika – wallafa alamarta a kasidar alamun kamfanoni da kuma samun satifiket — kafin ta kammala rajistar. Wadannan matakan biyu na bukatar akalla watanni takwas kafin a kammala, a cewar lauyoyin biyu.

 ‘Ka da ku je asibiti’

A Najeriya kusan ko ina ka shiga akwai masu sayar da magungunan gargajiya, amma ba safai ake kula da su ba, kuma ma ba wuya an mance da su. Wata kila irin hadin da suke yi ma da bai dauki hankalin wannan dan jaridan ba idan ba da dan tallan maganin da ya ji ba, wanda ke cike da irin bayanan da ke yaudaran jama’a. 

A tallar ta minti tara wadda muka sa a kasa, Baba Aisha ya yi kira ga jama’a da su daina zuwa asibiti, su kuma daina kai yaran su; ya ma yi zargin cewa asibitoci karin ruwa da na jini ne kadai suke wa jama’a wa kusan kowace irin cuta; wato ke nan shi ya bayar da magani tun ma kafin ya yi nazarain abun da ke damun mutun, ba tare da ya yi karatun likita ba ko ma wata kwarewa irin wadda ake bukata domin bai wa mutane magani. Sa’anan ya yi zargin cewa yana da maganin da zai warkar da cututtukar — cututtukan da kowanensu ke da na sa tushen ba lallai ne ma su kasance suna da alamu iri daya ba.

Sautti: tallar Baba Aisha

Ga wanda ya iya karatu da rubutu, zai saurari wannan tallar kamar wani nau’in na barkwanci, saboda salon muryar da mai magana ke amfani da shi da ma irin gwagwarmayar da ya ke da turancin tunda bai iya sosai ba, to amma abun da yawancin kwastamomin shi suka bukaci ji ke nan su daina zuwa asibiti.

Alice John, mai shekaru 50 na haihuwa, ta yi korafin cewa tana samun ciwo a idanunta da wasu gabobin jiki daga farkon shekarar 2022. Inda ta fara zuwa shi ne wani asibiti na al’umma. Bayananta da aka dauka sun nuna cewa tana fama da abubuwa uku wadanda suka hada da glaucoma – wanda ciwon ido ne inda jijiyar da ke hada ido da kwakwalwa ke lalacewa, sar corneal ulcer –  wadda wata yana ce ki fitowa kamar jin ciwo a kan ido wanda yawance kwayar cuta ce ke janyo ta, sai kuma hawan jini. Daga nan sai aka ba ta magunguna, amma ciwon bai warke ba abun da ya sanadin ta fara neman magungunan da za su maye gurbin wadanda aka ba ta tunda ba su aiki. Wannan sai ya zo a kalaman Baba Aishan da ta saurara a lasifikan da ke motar da aka ajiye a mahadar hanyar zuwa gidan Mrs. John

“Makota sun ce maganin da ake talla na aiki… Allah ne ke warkar da mutane amma na yi imani da wannan maganin,” ta ce tana jaddada cewa tun bayan da ta fara shan wannan hadin a watan Yunin 2022 ba ta sake zuwa asibiti ba.

Tallar, a cewar dokokin NAFDAC dangane da Magungunan Gargajiya da sauran Kayayyaki Makamantansu wadanda aka wallafa a shekarar 2021, ya kamata a ce hukumar ta amince da tallar kafin aka fara amfani da ita. Dokokin sun tanadi cewa, duk wata tallar da aka yi dangane da irin wadannan magungunan bai kamata ta bayar da tabbacin cewa magungunan ba su da lahani ba ko kuma tabbacin samun waraka idan aka yi amfani da shi saboda yana dauke da wani sinadari na musamman. Dokar ta kuma kara da cewa irin wadannan tallace-tallacen yawanci suna dauke da bayanan karya ko kuma irin bayanan da za su iya sa mutane su baude, da bayanai marasa tushe, wadanda ke amfani da kalamai marasa hujjoji da ma sa mutane tunanin cewa kayansu sun fi na kowa ko kuma ma zargin cewa magani daya na iya warkar da cututtuka da yawa. Maganin Baba Aisha ya sabawa wannan da masu wasu da yawa!

Da kashi 63 cikin 100 na mutane miliyan 200 da ake hasashe adadin al’ummar Najeriya cikin talauci da kuma yadda tsarin insorar lafiya ta kasa ke kula da kashi uku cikin 100 kacal na al’umma, magungunan gargajiya su ne zabin da da yawa ke da shi.

Zai yi wuya a iya kayyade daidai yawan maganin da ke yawo a kasar yanzu da ma yawan da ake sha, amma hirarrakin da muka yi da masu saidawa na nuna mana cewa daruruwan kwalabe zuwa dubbai ake saidawa kowani wata.

Mun rubuta wa NAFDAC wasika muka tambaye ta ko da amincewarta ake amfani da tallar, ai dai hukumar ba ta amsa ba. A waje guda kuma dokar ta baiwa NAFDAC ikon shigar da kara da kuma cin tara a kan wadanda suka take dokokinta ko kuma ma daure mutane a kurkuku idan har aka same su da laifi bayan shari’a.

Ba mu iya tantance ko takardun bogi ne Baba Aisha ya turawa mahukuntan NAFDAC har suka ba shi lambar rajista ta farko ba tare da ya cika duka sharuddan ba, amma  ko ma dai me ake ciki, kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce hukumar ta gaza wajen aiwatar da aikinta na sanya ido kan abubuwan da ka iya cutar da al’umma tun da bata gudanar da aikinta yadda ya kamata ba.

“Mutane ba za su sake gudanar da bincike kan ingancin abun da suka riga suka ga yana dauke da lambar rajistar NAFDAC ba,” a cewar Lawal Bakare, wani likitan hakora kuma kwararre kan kiwon lafiyar al’umma. “Saboda ‘yan Najeriya sun yarda da NAFDAC, ya kamata hukumar ta san cewa wannan babban nauyi ne da ya rataya a wuyarsu.”

Mun sake rubuta wa NAFDAC muna tambayarta ta bamu takardun da Baba Aisha ya ba ta na neman rajista, amma ba ta bamu amsa ba. Mun gabatar wa hukumar da hujjojinmu muka kuma tambaye ta karin bayani dangane da hanyoyin yin rajista, nan ma ba ta amsa mu ba.

Baba Aisha bai amsa gayyatar da muka mika masa na hira ba duk da cewa ya amsa wayoyin da muka rika yi masa,

Kamar yadda muka bayyana, hadin kan NAFDAC ko kuma rashin bin diddigin da ta yi na tsawon shekaru da dama ya sanya rayukan miliyoyin wadanda ke amfani da maganin Sacra cikin hadari, maganin da za’a iya cewa shi ne mafi suna a Abuja, amma yaya girman irin hadarin da wadannan mutanen suka sanya kansu ciki?

Me ke cikin kwalbar Baba Aisha?

A shekarar 2018, Odigie Okai ya yi fama da malariya na wani tsawon lokaci, wadda ko ta tafi sai ta sake dawowa abun da ya rika mayar da shi asibiti da kuma sayen magunguna a kai-a kai na tsawon watanni biyu. “Har sai da ya kai lokacin da makota na suka ce mun me ya sa na ke son zuwa asibiti? Suka ce ai bata kudi na kawai na ke yi; ban taba jin labarin Baba Aisha ba ne?”

Da ya dauki shawararsu, Mr. Okai ya ce sai ya sayi kwalabe uku na ‘maganin’ Baban Aisha a kan cewa kwalba daya kowace rana.

“Na sha daya a ranar farko; lokacin yamma ta kusa, sai na fara jin ciwo a ciki na. Washegari, na sake shan kwalba na biyu, sai abun ya kara rikicewa har sai da na suma,” Mr Okai ya bayyana.

Da Mr Okai ya farfado ya gan shi a gadon asibiti, sai aka ce mi shi yana da Malariya da Taifod ne a hade kuma maganin da ya sha ya sake ta’azzara abun.

Wannan abun da ya faru da shin ya yi kama da wanda ya faru da Isa Ismaila, wani mai tuka keke Napep wanda shi kuma aka ce ya rika shan kwalabe uku na maganin ganyen na Sacra hade da gishiri kowace rana, saboda cutar taifod wani lokaci a shekarar 2022. Bayan da ya sha kwalbar farko, Mr Ismaila ya ji ya fara zufa, yana jin hajijiya sa’anan kuma ya ji dungun bai ma gane wa jikinsa ba. Sai da ya je kemis ya sayi wasu magungunan kafin ya sami kansa.

“Baki daya cikin daren nan ban iya baci ba. Ba zan sake shan wannan maganin ba, “ ya bayyana dangane da abun da ya faru da shi.

Ta yaya za’a ce maganin da aka sha dan samun waraka kuma zai ta’azzara rashin lafiyar da ke jikin mutun? Mun bukaci samun amsoshi daga Mols & Sims, wani dakin gwaji mai zaman kansa da ke jami’ar Afe Babalola, (ABUAD) Ado Ekiti, jihar Ekiti. 

Da muka tuntube shi, Olaposi Omotuyi, farfesa a fannin harhada magunguna da ilimin magungunan da ke warkar da cututtuka, tare da tawagarsa ya amince ya gudanar da bincike kan ingancin maganin ya ga ko yana da karfin da zai warkar da wadannan cututtukan da ake zargin yana warkarwa, inda ya ce zai fara da malariya. Masu binciken sun kuma ce zasu tantance ko maganin na da ingancin da ya cancanci a ce dan adam na iya sha. Kwalabe 20 na maganin Sacra muka saya daga wurare hudu Abuja – biyar daga kowane yanki — muka tura wa dakin gwajin dan gudanar da bincike.

“Dan gudanar da wannan binciken, zamu yi amfani da dabbobi a matsayin samfuranmu, zamu kirkiro nau’o’in cutar malariya mu sanya wa dabbobin sai mu ba su maganin mu ga ko zasu warke, a kuma kwatanta da wadanda su za’a yi mu su amfani da chloroquine dan binciken ko akwai kwayoyin da ke yaki da malariya,” Prof Omotuyi, wanda ba da dadewan nan ba ya jagoranci masana kimiyar da suka gano sinadarin Virucidine Liquid, wanda aka amince a yi amfani da shi wajen warkar da cutar COVID-19, ya bayyana daga farkon gwajin. 

Sigogin da masana kimiyar za su yi amfani da su wajen gane ko berayen sun kamu da cutar bayan an sa musu kwayarta sun hada da zafin jiki, zubewa, rashin cin abinci, da mutuwa sakamakon kwayar cutar malariyar, sa’annan bayan nan za’a duba mahimman gabobin jikinsu.

Masan kimiyar sun kasa dabbobin zuwa rukunnai biyar kowanne da beraye takwas wadanda suka hada da rukunin da ba’a sa mu su komai ba, da rukunin da aka sa musu malariya ba tare da an basu magani ba, da rukunin da aka sanya musu malariyar amma kuma aka basu maganin cholroquine sai kuma rukunin da aka sa musu malariya sa’annan aka basu maganin Sacra dan kankani (30mg), kafin daga karshe akwai rukunin da aka sa musu malariyar sa’annan aka ba su maganin Sacra da yawa (100mg).

A takaice, bayan binciken da ya dauki wata daya ana amfani da ka’idojin kasa da kasa, masana kimiyar sun gano wasu mahimman abubuwa kamar haka:

●       Dabbobin da ke rukunnai biyun da aka yi musu amfani da maganin Sacra (100mg da 30mg) basu bayyana wani sauyin da ya nuna cewa maganin ya warkar da su, ba abun da ya yi wa cutar malariyar da aka sanya musu. Dan haka, maganin gargajiyar ta Sacra ba za ta iya warkar da malariya ba kamar yadda masu sarrafa maganin ke zargi. 

●       Dabbobin da aka bai wa maganin chloroquine ana amfani da nauyinsu a kan 5mg per kan kowani kilo, ba su bayyana wani sauyi a halayyarsu ba kuma maganin ya warkar da su. Dan haka chloroquine ne ainihin maganin cutar malariya.

●      Da ma idan har mutun na dauke da cutar malariya akwai wasu kwayoyin jikin da ke raguwa sosai wadanda sukan koma yadda suke bayan an sha magani cutar ta warke, sai dai a dabbobin da aka baiwa maganin Sacra suma ana amfani da nauyinsu a kan 30mg kowani kilo da 100mg kowani kilo a rukunnai biyu, ba’a ga wani sauyi a yawan kwayoyin jikin ba duk da yawan maganin da aka dura musu.

●       dabbobin da aka bai wa maganin Sacra 100mg sun samu lahani a koda da hanta, kuma ko wadanda suka kasance a rukunin da aka sanya musu kwayar cutar malariyar ba tare da an ba su magani ba basu sami lalacewar hanta da koda kamar yadda wadanda suka sha maganin Sacra suka samu ba. “Wannan abu ne da ke nuna cewa akwai wadansu sinadaran da ke da lahani ga jikin dan adam a cikin wannan hadin,” rahoton dakin gwajin ya bayyana.

●       Har wa yau, dabbobin da suka sha maganin Sacra 100mg kan kowani kilo sun yi fama da karancin sinadarin glutathione – abun da kan taimakwa jiki wajen fitar da abubuwan da ba ya so, sun kuma yi fama da karyewar garkuwar jiki abun da ya sanya su cikin hadarin kamuwa da cututtukan da suka shafi huhu. Dan haka a cewar masan kimiyyar shan wannan maganin a kai-a kai na iya janyo cutar da ke sarkake numfashi wanda aka fi sani da (ARDS) 

 ●     Duka dabbobin da ke rukunnai biyun da aka bai wa maganin Sacra sun mutu cikin kwanaki uku zuwa shidda, abun da ke nufin cewa maganin ba ya aiki. Ya na kuma nufin cewa maganin babban hadari ne ga masu amfani da shi.   

 “Ya kan hana koda da hanta aiki. Wannan na nufin duk wanda ya sha wannan maganin na fuskantar hadarin samun lahani a koda wata kila ma sai ya dade yana shan magani saboda lahanin da kodar za ta samu,” Prof Omotuyi ya bayyana yayin da ya ke nazarin sakamakon. “Idan har ya kai matsayin da dole sai an rika shan magani na wani tsawon lokaci, dole a fara tunanin neman sabuwar kodar da za’a yi aiki a sa, wannan kuma ba wai ya na da arha ba ne, idan ma har mutun ya sami wanda zai ba shi kodar ke nan; kuma haka nan zai kasance da hantar ita ma har ma da huhu. Wannan ce hanyar kwatantawa yadda kowa zai gane cewa wannan maganin bai kamata a sha ba a yadda ya ke a haka yanzu.”

Duk da cewa ba’a kai ga tantancewa a hukumance ba, wadanda suka yi amfani da maganin, irin su Mr.Okai da Mr. Isamila wata kila sun sami matsala da wasu daga cikin mahimman gabobin jikinsu a cewar kwararru na fanin likitan da suka yi nazarin lamarin. Wata sa’a wannan zai iya kai ga lalacewar koda ko hanta ko kuma ma mutuwa, a cewar su.

“Muna ganin marasa lafiyar da ke zuwa ganinmu da matsalar koda,”  a cewat Usman Bashir, wani malamin da ke koyar da yanayin kiwon lafiya al’umma a sahsen kiwon lafiyar al’umma da ke jami’ar Ado Bayero wanda kuma likita ne a asibitin koyarwa ta Aminu Kano. “Hukumomin da ke sanya ido, ya kamata su tashi tsaye su dauki matakan da za su haramta wa wasu daga cikin masu sayar da magungunan gargajiyar nan saidawa domin suna kara mana cututtuka ne a al’umma, suna kara mana yawan marasa lafiya a asibitoci kuma yawancinsu sukan zo wajenmu ne sadda lokaci ya riga ya kure.”

A cewar rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wadanda kasidu da dama suka yi amfani da su, cututtukan koda da huhu su ne suka fi hadari a Najeriya. Wannan binciken tare da wasu da dama kuma sun bayyana cewa shan magungunan da aka hada da ganyayyaki da jijiyo ne yawanci ke sanadin kaso mafi yawa na wadanda ke kwanciya a gadon asibiti sakamakon cututtukan koda da hanta a kasar.

Domin bayyana yawan adadin yadda ya ke a zahiri, kungiyar kwararru kan hanta ta ce kusan mutane miliyan 20, wanda ke zaman kashi 10 cikin 100 na yawan al’ummar kasar na rayiwa da cutar koda. Abun da ya fi tayar da tsigar jiki kuma shi ne, ba da dadewana nan ba kwararru suka yi  kiyasin cewa ‘yan Najeriya 45,000 ke mutuwa kowace shekara sakamakon cutar koda. 

Haka batun ya ke wa cuuttukan hanta. Wani rahoton watan Fabrairun 2023 da WHO ta fitar ya nuna cewa ‘yan Najeriya fiye da miliyan 20 ke rayuwa da cutar Hepatitis B, ko C, ko kuma duka biyun, kuma bugu da kari fiye da kashi 80 cikin 100 na wadanda ke rayuwa da cutar ma ba su sani ba. 

Wasu daga cikin mace-macen da ake samu sakamakon irin wadannan magungunan masu arha ne, magunguna irin su ganyen maganin Sacra, wadanda ake sha a sunan samun waraka. Sai dai akwai wasu karin abubuwa masu lahanin gaske da ke cikin ‘yar kwalbar nan ta Baba Aisha.

Masu amfani da maganin na fuskantar hadarin kamuwa da kansa

Zaradeen, mai sayar da maganin baban Aisha a Jabi, da Isa mai saidawa a Lugbe, da Yusuf mai saidawa a Nyanya da ma Ahmed wanda ke saidawa a Kurudu, duk ba su san abun da ya sa maganin ke da launi mai ruwan kwai ba.

Ko da shi ke rahotannin farkon da aka samu daga binciken ingancin maganin ya bayyana cewa launin na da dangantaka da fentin rinin da ake sanyawa wanda launinsa ruwan kwai ne. 

Launin wanda aka fi sani da Tartarzine a turanci wani launi ne da ake yawan sanyawa a magunguna da abinci ta yadda za su rika daukar ido.  Bincike  da dama sun nuna cewa da zarar jikin mutun ya yi yunkurin sarrafa sinadarin na tartazine ta yadda zai iya amfani da shi ya kan zama wani sinadari ne wanda ke da lahani sosai ga jikin dan adam wanda kuma ka iya janyo matsaloli dama a ciki har da rashin jini ko kuma anaemia, jin ciwo a kwakwalwa da hanta da koda da saifa, kuma wadannan tun ma kafin a kai ga yadda sinadarin zai kai hari kan garkuwar jikin mutun ke nan da ma marurai da yiwuar kamuwa da cutar daji.

“Da muka yi nazarin maganin Sacra, mun iya tantance cewa lita daya na maganin na dauke da miligram 5,000 na tartrazine wanda ke nufin kowani kwalba mai yawan mil 250 (kimanin kwalba biyu ke nan a yadda baba Aisha ke saidawa) zai kai miligaram 1,25o idan aka hada. Dan haka duk wanda ya taba shan wannan maganin ya sha yawan da akan bayar da shawrar a sha har sau uku ke nan.

“Wannan na nufin duk wadanda ke shan wannan maganin na sanya gabobin jikinsu cikin hadari ke nan domin sinadarai irinsu tartrazine ba shakka sune suka yi sanadiyyar mutuwar dabbobin da aka yi amfani da su,” Prof Omotuyi ya bayyana yana kira da a haramta amfani da wadannan magungunan da ma sayar da su nan take.

Ya ce miligram 7.5 ne kadai aka ce dan adam zai iya sa wa a baki.

Masan kimiyyan ba su iya cigaba da gudanar da gwajin da zai tantance ko maganin Baba Aishan na warkar da suk sauran cututtukan da ya ke zargi maganin na yi domin dura wa dabbobi wannan maganin da aka riga aka tantance cewa bai kamata a ci ba zai tama wani batu na da’a kuma.

Ana mutuwa ana murmushi

Ga mutane irin su Saleh Ahmed, mai kabu-kabu da keke mai kafa uku, da Mohammed Sani mai babur na haya, Alice John mai sayar da ayaba, da wasu mutane fiye da 20 masu amfani da maganin Sacra wadanda muka yi hira da su wajen hada wannan rahoton, maganin na cigaba da kasancewa abun da suka yi imanin zai maye musu gurbin magungunan zamani

“Da in je asibiti gara na sha maganin Baba Aisha,” a cewar Mr Ahmed, wanda ke ma alfaharin cewa ya yi shekaru biyu yanzu rabon da ya sha maganin asibiti. “Zan iya ce wa wani ya sha maganin Baba Aisha ko da ya na da kudin zuwa ganin likita.”

Idan muka yi la’akari da irin wannan bayanin, sai mu ga kamar ma binciken da muka sa aka yi a dakin gwaji ba gaskiya ba ne amma kuma kwararru sun ce wannan hadarin kusan kamar ma zai fi abun da ake gani yanzu.

“Matsaikacin nauyi a dan adam shi ne kilo 70. Yawancin lokuta, idan aka yi amfani da dabbobi wajen gwaji, kuma suka mutu cikin kwanaki, irin lahanin da ya kashe su yawanci ya kan dauki shekara daya ko biyu kafin a gan shi a dan adam,” a cewar Dr Oritoke Okeowo, wani masanin magunguna a ABUAD.

An average man is about 70kg. Most time, when you have an animal used (for lab tests), and the animal dies within four days, it can (take) up to a year or two or longer time before they see any kind of damage (in humans),” says Dr Oritoke Okeowo, a pharmacologist at ABUAD.

Sauran kwararrun wadanda su ma suka yi nazarin wannan batun sun yi bayani makamancin wannan — watakila masu amfani da maganin na mutuwa a hankali ba tarre da saninsu ba. Sun kuma ce watakila akwai kadan daga cikin kayayyakin da ake sa wa a cikin hadin da ke aiki, wanda shi ya sa wasu su kan sami sauki na wani gajeren lokaci, amma dai baki daya ba da kyau ake hada wa ba, kuma zai cigaba da kasancewa babban hadari ga jama’a.

Dr Okeowo na fargabar cewa idan har mutane suka cigaba da shan maganin Sacra da sauran magunguna masu hadari irin shi, za’a samu karuwa a adadin wadanda ke fama da cututtukan hanta da koda wanda zai kai ga matakin da za’a gaza yin dashensu domin a  yanzu haka ana kiyasin samun sabon koda na tsakin nera miliyan 15 da 25, shi kuma hanza daga nera milyan biyar zuwa 15.

Da muka fara samun sakamako daga dakin gwaji, mun sake zuwa ganin Ms. John dan mu bayyana mata mahimman abubuwan da binciken ya gano mu kuma fada mata wasu daga cikin hadurrukan da ta ke fuskanta idan har ta cigaba da amfani da maganin. Ta fada mana cewa har yanzu tana shan maganin, kwalba uku a rana.

Bayan da Ms. John ta sami labarin sakamakon gwajin, daga farko ta amince a gwada kodarta da hanta, amma daga baya ta ce ta fasa saboda tsoro, masu iya magana sun ce abun da baka sani ba, ba zai kashe ka ba

“Allah ya riga ya wanke duk wata cutar da ke jiki na. Duk wata cutar da shaidan ke so ya sa mun ta wannan maganin, Allah zai kawar da ita,” ta fada da karfi, tana yin watsi da amincewar da ta yi ta je a yi mata gwajin da farko. 

Can a dakin gwaji, Dr Okeowo na damuwa domin a ra’ayinta, yawan maganin da Baba Aisha ke baiwa jama’a zai janyo lahani sosai a jikin masu amfani da shi.

“Mun bai wa berayen mil100 kan kowane kilo na nauyinsu, abun da ke nufin kowani kilo daya na samun mil 100. Idan muka lissafa, nauyin dan adam kilo 70ne; hakan na da yawan gaske,” ta bayyana. Ko da wani abu na aiki, yawan lokutan da ake cewa a sha maganin zai hana mutun bin maganin daki-daki dan haka ba lallai ne a kammala shan maganin ba.”

A tallan shi, Baba Aisha ya ce ana iya bai wa kananan yara rabin kwalba na maganin. Ya fadi haka ne ba tare da ya bayyana shekaru ko nauyinsu ba. Dr Okeowo ta yi gargadi dangane da yin hakan.

“Ko da ma wani iri hali ake ciki , zan ce ka da a taba bai wa karamin yaro wannan maganin saboda jikinsu ba shi da nauy,” ta ce. Idan babba ya sha maganin bai suma ba, zai fi yin tasiri a kan kananan yara.”

Daga ina ‘maganin gargajiyar Baba Aisha’ ya fito? 

A watan oktoban 2021 wani sanannen mai amfani da shafin twitter Kelvin Odanz (@MrOdanz), cikin wani yanayi na zance ya tambayi masu bin shi a shafin, su wajen fiye da 100, 00 ya ce wane ne likitan gargajiyar da ya fi suna a Najeriya? Ya ce shi a ra’ayinsa Baba Aisha ne, yayin da yawancin mabiyansa su ma suka bayyana hakan.

A gurbin da ake tsokaci, sun yi ta labarin cewa yanzu haka Baba Aisha na can na hada wani maganin wanda zai warkar da COVID-19, da ma yadda turancinsa ke kayatar mu su da tafiyar zuwa gida da yamma bayan sun taso aiki da ma irin rayuwa da abubuwan da mutanen da ke shan maganin ke fuskanta. Wadansu daga cikinsu sun yi tambaya dangane da dalilin da ya sa ake ganin ire-iren magungunan gargajiyar a ko’ina ba tare da an san ainihin inda suke fitowa ba.

Wani adireshin da aka rubuta a kan kwalban ya bamu damar zuwa wani wuri dan gano inda kamfanin ya ke.

Kafin mu fara tafiyar zuwa Tafa, wani gari da ke tsakanin Kaduna da Abuja, inda ake sarrafa kusan kowane magani, mun tuntubi Mall Hamza wanda ya hada mu da dan uwan Baban Aisha.

Bayan da muka yi ta waya na tsawon ‘yan kwanaki sai ya amince ya gana da wannan dan jaridan saboda yiwuwar shiga kasuwanci da tattauna maganin. Mall. Hamza ya zo, sai dai ya hakikance kan cewa ba zai kai mai rubuta wannan rahoton wurin da ake sarrafa maganin ba. Ko da muka kira Baba Aishan da kansa muka roke shi, dukkansu biyu sun hana.

Hakikancewarsu abu daya ya tabbatar mana. Maimakon wani ginin da ke bin ka’idojin kasa da kasa, ana hada maganin ne a tsakar gida nan a cikin daya daga cikin gidajen da ke unguwar. Inda mai rubuta wannan rahoton da kansa ya je ya gano.

Wani mai sayar da maganin gargajiyar a Tafa, wanda ya bukaci a sakaya sunarsa dan kada a kama shi, ya ce babu wani banbanci tsakanin gidan da suke zama da inda ake sarrafa maganin. Mai tallar ya kara da cewa da yawa akan sarrafa maganin bisa bukatar da aka samu daga masu sha’awa.

Duk da cewa ba mu iya tantance gaskiyar haka da idanunmu ba, tunda an hana mu shiga, daga yadda na ga ginin na san cewa ta take duka dokokin da haukumar NAFDAC ta bayar.

Akwai ka’idojin sarrafa magungunan gargajiya wadanda NAFDAC ta tanadar a ka’idojinta na nagartattun hanyoyin sarrafa kayayyaki ko kuma Good Manufacturin Practice GMP.  GMP ya kunshi ka’idoji da dama, kama daga kwarewar ma’aikata, wurinda masana’antar ta ke, tsabta, wuraren ajiya, yadda ake kula da kayayyakin aiki har zuwa tsarin samar da ruwa.

Baba Aisha ya ki ya yi magana dangane da abubuwan da muka bankado.

Yaya batun tsari da ka’ida?

Ba safai ake sanya ido kan magungunan gargajiya a Najeriya ba. Yawancin lokuta irin magungunan ba su bukatar rajista ko wani bincike mai zurfi. Na tsawon shekaru da dama, mutanen da sukan yi yawo a kan titi suna kiran kansu ‘likitoci’ sun cutar da mutane da tallace-tallace masu yaudaran jama’a ba tare da an dauki matakin ladabtarwa a kan su ba.

A lokuta daban-daban, mahukunta sun yi kokarin daidaita fannin, sai dai har yanzun hakonsu ba ta cimma ruwa ba. Daga cikin irin wannan yunkurin akwai na Sanata Ibrahim Oloriegbe, wanda ya ce ra’ayinsa, ya kamata duk wanda zai sayar da magungunan gargajiya ya zamana yana da takardun cancanta wanda tilas ya kunshi iya karatu da rubutu.

A shekarar 2022, shugaban kasa ya amince da kurin dokar dan majalisar wanda ya tanadi samar da kwalejin nazarin ire-iren magungunan gargajiyar da za’a iya karawa a kan na asibiti da kuma har wa yau magungunan gargajiyar da za’a iya sha a madadin na asibiti. Hasali ma a halin yanzu ana jiran ma’aikatar kiwon lafiya ta aiwatar da dokar ne. Shekaru biyu kafin nan, gwamnatin tarayya ta amince da dokar da ta tanadi girka majalisar masu maganin gargajiya, magungunan da gargajiyar da za su iya maye gurbin na asibiti da na magungunan da za su iya kara inganta aikin magungunan asibiti a kasar.

“Dokar kwalejin na da burin inganta horaswar ma’aikatan da ke matakin tsakiya wajen amfani da magungunan gargajiya dan samar da ingantattun magunguna ga ‘yan Najeriya,” a cewar Oloriegbe. “Dokar idan har aka amince da it, za ta tabbatar da ka’idojin aiki masu nagarta wajen sarrafa magungunan gargajiya ta yadda za’a dakile matsalar masu magungunan jabu a kuma tabbatar da kariyar duk wadanda ke da sha’awar amfani da magunguna,” ya bayyana.

Ba za’a iya cimma wannan buri ba idan har ba’a sami hadin kan masu sayar da magungunan gargajiya ba. Kungiya daya, Kungiyar Masu Magungunan Gargajiya a Najeriya (NANTMP) na kokarin ganin ‘yan kungiyar sun samar da nagartattun ka’idojin sarrafa magungunan.

“Kungiyar ta na yunkurin dakatar da gurbatattu,” a cewar Shaba Maikudi, shugaban kungiyar. “Akwai kwamitin da ke jagorantar wannan. Sun riga sun kai matakin da za su iya korar gurbatattu su kuma yi amfani da dabarun gano wadanda suke cigaba da baiwa fannin bakin suna. Muna yin haka ne domin mu iya cimma ka’idojin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta gindaya, kuma idan har ba mu fitar da masu sayar da gurbatattun magunguna ba, ba za mu taba cimma wannan burin ba.

“Wadanda suke saidawa a kan hanya, muna so mu san abun da ke cikin magungunan da suke saidawa jama’a. Dan haka zamu dauke su mu ilimantar da su kan yadda za su iya kyautata shi har mutane su yi amfani da shi ba tare da hadarin samun wani lahani ba. Muna kuma so mu san ko maganin ya gurbace. Sa’annan mu tabbatar cewa sun yi rajista saboda mu san fannonin da suke da kwarewa ko ma dai inda suka fi shahara,” ya bayyana.

Mall. Maikudi ya tabbatar mana cewa Baba Aisha mamba ne a kungiyar, kuma ya yi mana alkawarin cewa za su wallafa sunayen magungunan da aka yi musu rajista a yanar gizo-gizo kafin karshen shekarar 2023. Ya bayyana cewa kungiyarsu tare da Hukumar Tabattar da Cigaban Magungunan Gargajiya da Ma’aikatar Lafiya za su fara gwada magungunan gargajiyan a wani ginin da aka yi na musamman dan gwada magungunan a Legas.

Me ya rage a gaba?

Mun tura bayanan binciken da muka yi zuwa ga NAFDAC, da Ma’aikatar Lafiya da Hukumar da Kare Masu Amfani da Kayayyakin da aka Sarrafa da Hukumar da ke Tabbatar da Ka’idojin Aikin Masana’antu da ma wasu kungiyoyin farar hula ta yadda za’a dauki mataki dangane da batun.

Bisa tanadin ka’idojin NAFDAC da sauran dokoki, Baba Aisha da sauran wadanda ke sayar da gurbatattun magunguna na iya fuskantar hukunci idan har aka same su da laifi.

NAFDAC ba ta kai ga amsa tambayoyin mu dangane da matakan da za’a dauka a kan bayanan da muka samu ba.

Haka nan kuma, can a dakin gwajin, Farfesa Omotuyi ya yi imanin cewa maganin Baba Aisha ma za’a iya gyara shi ta yadda ba zai kasance hadari ga masu sha’awa ba.

“Ban san abun da ya hada dan ya kirkiro maganin ba, amma kuma ya kamata shi ma ya fito fili ya bayyana mana abubuwan da ya a ciki,” a cewa farfesa Omotuyi. “Dole ya yi aiki da masana kimiyya wadanda zasu taimaka mi shi ya fara da tabbatar da kariyar jama’a.”

Sai dai ra’ayoyin Baba Aisha sun banbanta. Ya yi imanin ba wanda ba zai iya warkewa ba daga maganin sa inda ma ya jaddada cewa, “Idan dai har kai dan adam ne ba aljani ko ruhu ba, zaka kira mu ka ce mana maganinmu na aiki.”

Sai dai a duk lokacin da muke binciken ko daya Baba Aisha bai tambayi masu binciken wani abu ba. Kuna iya kallon bidioyn a nan.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button