|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana cewa babu rashin tsaro a jihar Sokoto sannan duk wanda ke cewa mahara na gudanar da ayyukan su a jihar karya yake yi inda ya bayyana tafiyar da ya yi va mota zuwa Silame ba tare da matsala ba.

Hukunci: Yaudara ce. Rahotanin sun nuna cewa abin da gwamnan ya fadi ba shine ke faruwa ba zahiri.
Cikakken Bayani
Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule da ya ziyarci jihar Sokoto ranar 2 ga Satumba 2026 ya yi bayanin kan rashin tsaron da ake fama da shi a jihar.
Yayin da ya kadamar da gadar Silame da wasu hanyoyi a yankin karkara da gwamnati ta gina gwamnan a tsokacin da ya yi da Hausa ya ce ya bi hanyar zuwa karamar hukumar Silame a mota domin tabbatar da karyan da wasu gidajen jaridu ke yi domin koran masu samar da ci gaba .
Ya ce ya bi hanyar ba tare da ya hadu da mahara ba duk da gargaddin da aka rika yi masa game da hanyar. Sule ya shaida cewa wadanda ke yada labaran rashin tsaro a jihar karya suke yi.
Duk da haka Sule ya tabbatar cewa babu jija a Najeriya da bata fama da matsalar rashin tsaro inda ya yi kira ga mutane da shugabanin kan fadan alheri game da jihohinsu domin samun ci gaba a tattalin arziki.
Mutane da dama sun yi korafi kan maganar da gwamnan yayi musamman yadda bada dadewa ba yankin karkara a jihar suka rika fama da hare-haren mahara.
Wani Bashir Jelani ya bukaci gwamnonin jihohin Nasarawa da Sokoto da su baiwa mutane hakuri saboda wannan magana da Sule ya yi.
“Na kasa fahimtar yadda gwamna daga kawai ya bi hanya sau daya zai karyata matsalar rashin tsaro da ayyukan maharani da mutane a Sokoto kef ama da shi ba.
Dan takaran kujeran gwamnan jihar daga jam’iyyar ADC, Manir Muhammad Dan’iya ya kalubalaci maganar da Sule ya yi game da rashin tsaro a jihar.
Muhammad ya ce samar da ingantaciyyar tsaro na yiwuwa ne idan mutane na iya gudanar da harkokin rayuwar sub a tare da fargaba ba.
Tantancewa
Bisa ga rikodin din taron ya tabbatar cewa Gwamnan Sule ya fadi abin da ya fada.
Gwannan ya bayyana yadda aka rika bashi labarin yadda mahara suka hana matafiya bin haryar Sokoto zuwa Silame inda yake cewa labaran da mutane ke badawa karya ne musamman yadda ya bi hanyar tare da jerin gwanon motocinsa ba tare da maraha sun tare su ba.
Sai dai kuma DUBAWA ta gudanar da bincike domin tabbatar da hakan.
Abin Da Bincike Ya Nuna
Labaran da gidajen jaridu ke wallafawa da wasu rubuce-rubucen da wasu suka yi sun karyata haka inda suka tabbatar cewa jihar na fama da rashin tsaro.
A ranar 26 ga Agusta 2026 mahara sun kai wa kauyen Gorau dake karamar hukumar Goronyo hari.
Bisa rahotan harin da Gidan jaridar Vanguard ta wallafa ya nuna cewa maharan sun kashe mutane hudu, bakwai sun ji rauni kuma sun yi garkuwa da wasu mutane hudu.
Wannan abin takaicin ya faru bayan ‘yan kwanaki da aka yi hadarin jirgin ruwa a wannan hanya.
A wannan rana gidajen jaridun The Whistler da The Star sun rawaito cewa sojoji sun fatattaki maharan da suka yi kokarin kai wa sansanin sojoji hari dake Sifawa a karamar hukumar Bodinga wanda ke da nisan kilomita 25 daga birnin jihar.
Rahotan ya nuna cewa sojoji biyu sun ji rauni a dalilin harin.
A ranar 31 ga Agusta 2026 mahara sun kama wasu manoma a Ghandi.
Gidajen jaridun The Punch da Legit.ng sun rawaito cewa maharani sun buda wa manoman wuta inda suka kashe mutum 8 daga cikin su tare da raunana biyar kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar.
Baya ga kai wa mutane hari kungiyoyin mahara sun rika saka wa mutane a kauyukan jihar haraji masu yawa.
Kakakin rundunar ‘yan dandan jihar ya tabbatar wa DUBAWA cewa a ranar 2 ga Satumba 2026 mahara sun saka wa mazauna kauyen Kebbe harajin naira miliyan 40.
Shin Yin Tafiya Da Jami’an Tsaro Zai Iya Kawo Karshen Rahen Tsaro?
Gwamna Sule ya biya wannan hanya a jerin gwanon motocinsa tare da jami’an taro a matsayinsa na gwamna wanda hakan bai isa ya ce babu matsalar rashin tsaro a jihar ba.
Bayanai game da ayyukan mahara da suka shafi yin garkuwa da mutane domin karban kudaden diyya da kai wa mutane hari inda da dama sun mutu wasu sun ji rauni musamman a kananan hukumomin Goronyo, Rabah, Bodinga da Kebbe sun tabbatar cewa rashin tsaro ya tabarbare a jihar.
A Karshe
Bayanan da gwamna Abdullahi Sule ya yi cewa wadanda suke bada labarin rashin tsaro a jihar Sokoto makaryata ne yaudara ce kawai. Gwaman ya bi hanyar Sokoto zuwa Silame ba tare da yin arangama da mahara ba amma rahotanin musamman daga rundunar ‘yan danda da gidajen jaridu sun tabbatar cewa mahara na nan na gudanar da muggan ayyukan su a jihar.
Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).
