Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Mai amfani da shafin Facebook na da’awar cewa akwai mata 11 wadanda ke zaman manyan darektoci da shugabannin bankuna a Najeriya

Hukunci: Gaskiya ce! Bayanan da muka samu a kan shafukan bankuna 11 sun tabbayar mana cewa bankunan na da darektoci mata. Mun kuma samu rahotanni da dama daga kafofin yada labarai masu nagarta da ke tabbatar da cewa matan ne ke rike da mukaman a zahiri.
Cikakken bayani
Matan Najeriya kan fuskanci matsaloli sosai wahen cimma burakansu idan ya zo ga batun siyasa da shugabanci. Yawancin matsalolin da sukan fuskanta kuma na da nasaba ne da wariya ko banbancin jinsi.
Wadansu sassan da matan Najeriya kan fuskanci irin wadannan matsalolin sun hada da yin nasara a zabuka da kuma samun manyan mukaman shugabanci.
A fakaice, adadin mata a matakan shugabanci a manyan kamfanoni kashi 23 cikin 100 ne kadai, wato 23%. Wannan adadin ma ya fi kankanta a yawancin kamfanonin da ba su yi suna sosai ba inda a nan ma mata ke da yawan kashi 14 cikin 100 kadai.
Stephen Esabu ya rubuta a shafin Facebook cewa yawancin bankunan Najerita mata ne ke mukaman MD ko kuma Manajin Darekta, da kuma shugaba wato CEO. Ya bayyana hakan ne dan nuna cewa mata sun fi yawa a mukaman shugabanci a fannin bankuna.
Ya bayyana sunayen manyan bankuna irin su Guaranty Trust Bank (GTB), Union Bank, Access Bank da Fidelity Bank. Ya kuma kammla da bai wa iyaye shawarar cewa su zuba jari sosai a ‘ya’ya mata kamar yadda su ke yi a ‘ya’ya maza.
An yayata wannan da’awar a shafukan sada zumunta irinsu WhatsApp da X. Har wa yau mutane 104,000 suka yi ma’amala da labarin wasu 1000 suka latsa alamar like, sa’annan 300 suka sake wallafa labarin wasu 41 kuma suka ajiye labarin yadda za su iya samun shi cikin sauki, tun bayan da aka wallafa batun ranar 23 ga watan Maris 2024 a shafin X.
Yadda labarin ya shiga kusan ko’ina cikin sauri ne da ma sarkakiyar da batun ke da shi ya sa DUBAWA ta ce za ta tantance batun.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike na mahimman kalmomi inda ta ga wani rahoto a jaridar This Day da ke cewa “Yayin da mata a Najeriya ke tashe a fannin banki.”
Rahoton ya bayyana cewa 10 daga cikin manyan bankunan kasar na karkashin jagorancin mata ne domin a daidai lokacin ne bankin Access ya bayyana Bolaji Agbede a matsayin shugaba ko kuma CEO na wucin gadi na babban kamfanin Access. Sauran kuma sun hada da Yemisi Edun ta First City Monument Bank, Miriam Olusanya ta GT Bank, Halima Buba ta SunTrust Bank, Ireti Samuel-Ogbu ta Citibank Nigeria, Nneka Onyeali-Ikpe ta Fidelity Bank, Tomi Somefun ta Unity Bank, Kafilat Araoye ta Lotus Bank, Bukola Smith ta First Securities Discount House Limited(FSDH) Merchant Bank, da kuma Yetunde Oni taUnion Bank.
Mun kuma ga wani labarin a jaridar The Cable wanda ke tattauna mata a manyan bankuna. Labarin ya tattauna bayani dangane da mata 11 wadanda ke zaman manyan shugabannin bankuna a kasar.
Mun gudanar da bincike kan sunayen matan da aka ambato da bankunan da suke aiki dan tantance mukaman da aka ce suna da shi a shafukan bankunan nasu.
A cewar bayanan da muka samu a shafukan bankunan, Miriam Olusanya ita ce manajin (MD) darektar GT Bank, Bolaji Agbede ita ce CEO na rikon kwarya na Access Bank, Halima Buba ita ce MD/CEO na SunTrust Bank, Yemisi Edunita ce MD na FCMB, Ireti Samuel-Ogbu ita ce MD a Citibank Nigeria, Nneka Onyeali-Ikpe ita ce MD/CEO na Fidelity Bank, Tomi Somefun, ita ce MD/CEO na Unity Bank, Kafilat Araoye, ita ce MD na Lotus Bank, Bukola Smith ita ce MD na (FSDH) Merchant Bank, Yetunde Oni, ita ce MD/CEO na Union Bank sai kuma Adaora Umeoji, wadda ke zaman MD/CEO na Zenith Bank.
A Karshe
Bayanin Facebook din da ke da’awar cewa mata 11 ne ke jagorantar wasu daga cikin manyan bankunan Najeriya gaskiya ce. Shafukan bankunan sun tabbatar da hakan. Har wa yau akwai rahotanni daga kafofin yada labarai masu nagarta dangane da yadda mata ke taka muhimmiyar rawa da ma irin wakilcin da suke da shi a fannin banki.