Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya wallafa (posted) wani hoto da ke nuna yadda Peter Obi ya durkusawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Hukunci: Yaudara ce! Bincikenmu ya gano cewa hoton da aka wallafa jirkita shi aka yi ta hanyar dabarun gyara hoto.
Cikakken Sakon
Zaben Najeriya mai cike da hamayya (2023 Presidential election) ya nunar da yadda aka samu rabuwar kawuna a yayin yakin neman zabe (divisive campaign) tsakanin bangarori na adawa da ke kan gaba wato, All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) da Labour Party (LP). bayan da aka fafata zaben jam’iyyar APC ta yi nasara da zama ta daya sai PDP da ta zama ta biyu da jam’iyyar LP da ta zo ta uku kamar yadda sakamakon hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya Independent National Electoral Commission ya nunar.
Duk da cewa an kammala da zaben, masu goyon bayan ‘yansiyasa da masu suka sun ci gaba da caccakar juna.
A ranar 29 ga watan Maris 2024 wani mai amfani da shafin X Ayekooto, ya yi wata wallafa mai taken, “Ka mutunta wanda ya fika.”
Hoton da aka dora a wannan wallafa ya nunar da dantakarar shugabancin Najeriya karkashin tutar jam’iyyar LP Peter Obi, na durkuso a gaban Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, kuma a gaban dantakarar shugabancin na Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar NNPP Rabiu Kwankwanso.
Ya zuwa ranar Litinin 1 ga watan Afrilu, 2024 wannan hoto ya samu wadanda suka kalla 63,000 (views), da wadanda suka nuna sha’awa 1,173 (likes), da wadanda suka sake wallafa labarin 138 (reposts), a shafin na X, idan kuwa aka duba masu sharhi ga su nan kala-kala a shafin.
Victor Benakin ya rubata cewa, “Idan ka mutunta magabata mahaliccinka zai yi maka albarka da girmamawa da samun ci gaba.”
Fidel Otuya ya rubuta, “Yaushe ne aka dauki wannan hoto?”
Mario ya rubuta “Ka fada wa wanda ke hada maka hoto ba kwararre ba ne ko ba kwararriya ba ce.”
Ganin yadda wannan batu ke kara janhankali da martani kala-kala daga wadanda ke amfani da shafukan na sada zumunta, DUBAWA ya shirya gudanar da bincike don gano hakikanin gaskiya.
Tantancewa
Bincike ta hanyar amfani da madubin (Google Lens) dama wani karin binciken da (exact matches search) sun fito da wani hoto tsoho na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka yi a ranar 26 ga watan Afrilu, 2023 inda aka ga hannunsa da na shugaban rukunin kamfanonin Dangote Aliko Dangote suna gaisawa hannu da hannu handshake.
Wannan hoton ne dai da duk yanayi nasa aka dauko aka yi masa dabaru na masu sauya hoto aka cusa hoton Peter Obi a cikinsa. A lokaci guda wani hoton na Rabiu Musa Kwankwaso a wata ganawa meeting da Shugaba Tinubu a ranar 25 ga watan Agusta,2023 aka dauko shi shima aka yi masa dabaru ko gyara, wannan hoto idan aka yi masa kallo na kurulla, za a ga yadda wasu wuraren basu fito sosai ba alamu na an yi wasu dabaru kenan.
Wani binciken na DUBAWA har ila yau ya kuma gano cewa babu shafin wata kafar yada labarai sahihiya da ta yi wannan labari da hoton da wannan mai amfani da shafin na X yayi amfani da shi.
Akwai kuma wata kalma da ke makale a kasan hoton “Caveat Lector” wacce ke nuna cewa hoton an jirkita shi ko an masa wasu dabaru . Abin da kalmar ke nufi shine “A bari mai karatu ya sani……”Kuma irin wannan wallafa wani mai amfani da shafin na X a baya ya taba yinta Luca Brasi-5.0, a ranar 19 ga watan Agusta,2023.
Kammalawa
A karshe bincikenmu ya gano cewa hoton wani mai amfani da shafin na X ya wallafa shi bayan ya sauya shi ta hanyar jirkitawa da cushe tun a ranar 26 ga watan Afrilu na 2023, Hakan na nufin da’awar yaudara ce.
Mai binciken yayi wannan aiki ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024, karkashin shirin samun kwarrewa na Kwame KariKari da hadin gwiwar gidan rediyon Diamond 88.5 FM Nigeria, a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin kasar.