{"id":11623,"date":"2022-05-20T15:00:00","date_gmt":"2022-05-20T14:00:00","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=11623"},"modified":"2022-05-20T14:31:53","modified_gmt":"2022-05-20T13:31:53","slug":"tantance-gaskiyar-furucin-peter-obi-mai-cewa-da-ya-karbi-bashi-dan-batarwar-yau-da-kullun-gara-kowa-ya-zauna-da-yunwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/tantance-gaskiyar-furucin-peter-obi-mai-cewa-da-ya-karbi-bashi-dan-batarwar-yau-da-kullun-gara-kowa-ya-zauna-da-yunwa\/","title":{"rendered":"Tantance Gaskiyar Furucin Peter Obi Mai Cewa \u201cDa Ya Karbi Bashi dan Batarwar Yau da Kullun Gara Kowa Ya Zauna da Yunwa\u201d"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-black-color has-cyan-bluish-gray-background-color has-text-color has-background wp-block-paragraph\"><em><strong>Zargi: Wani mai amfani da shafin Tiwita ya yi zargin wai dan takarar mukamin shugaban kasa a zabukan 2023, Peter Obi, ya ce da ya karbi bashin kudi domin Najeriya ta kashe a kan gudanarwa na yau da kullun ya gwammace kowa ya zauna da yunwa<\/strong><\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra na neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam\u2019iyyar PDP. Tsohon gwamnan ya kasance dan takarar mukamin mataimakin shugaban kasa a jam\u2019iyyar a zabukan da aka gudanar a shekarar 2019.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kwanan nan wani mai amfani da shafin Tiwita mai suna Jack (@Jack_ng01), ya wallafa wani zargin mai cewa Peter Obi ya ce gara a zauna da yunwa da ya karbi bashi dan a kashe kan gudanarwar yau da kullun.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>\u201cA karkashin jagoranci na, ba kwabon da za\u2019a ara wai dan a lakume kan aiyukan yau da kullun, da haka gara mu zauna cikin matsanancin yunwa,\u201d<\/em> aka rawaito shi yana cewa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wanda ya wallafa wannan labarin ya hada da hoton wani bidiyo daga gidan talbijin na Arise inda ya ke zargi wai a nan ne Obin ya yi wanann furucin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da yawa daga cikin masu amfani da shafin sun bayyana ra\u2019ayoyinsu dangane da batun a wurin yin tsokaci. Wani mai suna Comcombility (@A_zhed) ya ce babu kasar da ke rayuwa ba tare da cin bashi ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>\u201cShi ne ya taba cewa babu kasar da ta taba rayuwa ba tare da cin bashi ba, bacin haka Najeriya ma za ta iya kara ciwo bashin. Sai dai abin da ya fi mahimmanci shi ne abin da ake kashe kudin a kai,\u201d<\/em> ya ce.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai suna Austyno (@AustynoUsh) kuwa cewa ya yi bangaren furucin da aka yi amfani da shi bai mi shi adalci ba tunda ba abin da ya ke nufi ke nan ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>\u201cKa na magana kamar nufinsa shi i ne ya jefa jama\u2019a cikin yunwa alhali kuma ba abin da ya ke nufi ke nan,\u201d<\/em> a cewar @AustynoUsh<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Francis Eze (@francisneze) tambaya ya yi game da hikimar karbar aron kudi dan a cinye, inda ya ce dan takarar ba ya adawa da karbar bashi, kashe bashin kan abubuwan da ba za\u2019a ga alfanun shi da ido ba ne ya ke adawa da shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>\u201cBa ya adawa da bashi. Ya na adawa ne da sanya kudin a abubuwan da za su lakume shi ba tare da an ga wani tasirinsu a al\u2019umma ko ma tattalin arzikin kasar baki daya ba. Ana karbar bashi dan kashewa a kan abinci ne kadai?&nbsp; idan aka yi haka, ta yaya za\u2019a biya ke nan?<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shin Peter Obi ya yi wannan furucin da gaske ko dai an dauki maganar da ya yi ne an kara mi shi gishiri?<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun yi bincike mun gano ainihin bidiyon hirar da ya yi a gidan talbijin na Arise. An yi wa bidiyon taken \u201cMuna bukatar wanda zai fitar da mu daga (APC) &#8211; Peter Obi\u201d Lokacin da muka ga bidiyon, ranar 19 ga watan Afrilun 2022 mutane sama da 110,000 suka kala.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da mu ka kalli bidiyon mai tsawon minti 38 da sakan 15 mun lura cewa wajen minti 13 da 16 na birar. Mr. Obi ya yi maganan kan yadda Najeriya ke ciyo bashi dan kashe wa kan ayyukan yau da kullun bayan da aka yi mi shi tambayar ko ya gamsu da yanayin bashin Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>\u201cYa kamata mu fayyace abin da mu ke ciyo wa bashi; ya yi mun tambaya, ya ce me zan yi? Ni zan yi abin da ya banbanta da abin da ake gani yanzu. Idan zan ciyo bashi, \u2018yan Najeriya za su san dalilin cin bashin kuma tilas a yi amfani da shi wajen sarrafa abubuwa. Babu wanda zai kashe kwabo ko dala kan ayyukan yau da kullun, da a yi haka gara an zauna da yunwa. Shi ya sa na fada wa kowa cewa ba abin da za\u2019a sake rabawa, dole mu sake gina kasarmu dan \u2018ya\u2019yanmu su sami kyakyawar makoma.\u201d<\/em><\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bincikenmu ya nuna mana cewa zargin wai dan takarar shugaban kasa Peter Obi ya ce da a ci bashi dan lakume shi a ayyukan yau da kullun gara an zauna da yunwa gaskiya ne. Dan takarar kuwa ya bayyana hakan ne domin ya jaddada adawarsa da cin bashi dan batarwar yau da kullun abin da a ra\u2019ayinsa babbar matasal ce ga ci-gaban tattalin arziki.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Zargi: Wani mai amfani da shafin Tiwita ya yi zargin wai dan takarar mukamin shugaban kasa a zabukan 2023, Peter Obi, ya ce da ya karbi bashin kudi domin Najeriya ta kashe a kan gudanarwa na yau da kullun ya gwammace kowa ya zauna da yunwa Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra na neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam\u2019iyyar PDP. Tsohon gwamnan ya kasance dan takarar mukamin mataimakin shugaban kasa a jam\u2019iyyar a zabukan da aka gudanar a shekarar 2019. Kwanan nan wani mai amfani da shafin Tiwita mai suna Jack (@Jack_ng01), ya wallafa wani zargin mai cewa Peter Obi ya ce gara a zauna da yunwa da ya karbi bashi dan a kashe kan gudanarwar yau da kullun. \u201cA karkashin jagoranci na, ba kwabon da za\u2019a ara wai dan a lakume kan aiyukan yau da kullun, da haka gara mu zauna cikin matsanancin yunwa,\u201d aka rawaito shi yana cewa. Wanda ya wallafa wannan labarin ya hada da hoton wani bidiyo daga gidan talbijin na Arise inda ya ke zargi wai a nan ne Obin ya yi wanann furucin. Da yawa daga cikin masu amfani da shafin sun bayyana ra\u2019ayoyinsu dangane da batun a wurin yin tsokaci. Wani mai suna Comcombility (@A_zhed) ya ce babu kasar da ke rayuwa ba tare da cin bashi ba. \u201cShi ne ya taba cewa babu kasar da ta taba rayuwa ba tare da cin bashi ba, bacin haka Najeriya ma za ta iya kara ciwo bashin. Sai dai abin da ya fi mahimmanci shi ne abin da ake kashe kudin a kai,\u201d ya ce. Wani mai suna Austyno (@AustynoUsh) kuwa cewa ya yi bangaren furucin da aka yi amfani da shi bai mi shi adalci ba tunda ba abin da ya ke nufi ke nan ba. \u201cKa na magana kamar nufinsa shi i ne ya jefa jama\u2019a cikin yunwa alhali kuma ba abin da ya ke nufi ke nan,\u201d a cewar @AustynoUsh Francis Eze (@francisneze) tambaya ya yi game da hikimar karbar aron kudi dan a cinye, inda ya ce dan takarar ba ya adawa da karbar bashi, kashe bashin kan abubuwan da ba za\u2019a ga alfanun shi da ido ba ne ya ke adawa da shi. \u201cBa ya adawa da bashi. Ya na adawa ne da sanya kudin a abubuwan da za su lakume shi ba tare da an ga wani tasirinsu a al\u2019umma ko ma tattalin arzikin kasar baki daya ba. Ana karbar bashi dan kashewa a kan abinci ne kadai?&nbsp; idan aka yi haka, ta yaya za\u2019a biya ke nan? Shin Peter Obi ya yi wannan furucin da gaske ko dai an dauki maganar da ya yi ne an kara mi shi gishiri? Tantancewa Mun yi bincike mun gano ainihin bidiyon hirar da ya yi a gidan talbijin na Arise. An yi wa bidiyon taken \u201cMuna bukatar wanda zai fitar da mu daga (APC) &#8211; Peter Obi\u201d Lokacin da muka ga bidiyon, ranar 19 ga watan Afrilun 2022 mutane sama da 110,000 suka kala. Da mu ka kalli bidiyon mai tsawon minti 38 da sakan 15 mun lura cewa wajen minti 13 da 16 na birar. Mr. Obi ya yi maganan kan yadda Najeriya ke ciyo bashi dan kashe wa kan ayyukan yau da kullun bayan da aka yi mi shi tambayar ko ya gamsu da yanayin bashin Najeriya. \u201cYa kamata mu fayyace abin da mu ke ciyo wa bashi; ya yi mun tambaya, ya ce me zan yi? Ni zan yi abin da ya banbanta da abin da ake gani yanzu. Idan zan ciyo bashi, \u2018yan Najeriya za su san dalilin cin bashin kuma tilas a yi amfani da shi wajen sarrafa abubuwa. Babu wanda zai kashe kwabo ko dala kan ayyukan yau da kullun, da a yi haka gara an zauna da yunwa. Shi ya sa na fada wa kowa cewa ba abin da za\u2019a sake rabawa, dole mu sake gina kasarmu dan \u2018ya\u2019yanmu su sami kyakyawar makoma.\u201d A Karshe Bincikenmu ya nuna mana cewa zargin wai dan takarar shugaban kasa Peter Obi ya ce da a ci bashi dan lakume shi a ayyukan yau da kullun gara an zauna da yunwa gaskiya ne. Dan takarar kuwa ya bayyana hakan ne domin ya jaddada adawarsa da cin bashi dan batarwar yau da kullun abin da a ra\u2019ayinsa babbar matasal ce ga ci-gaban tattalin arziki.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":0,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"","_twitter_share_type":"","_linkedin_share_type":"","_pinterest_share_type":"","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[3245,285],"verdict":[],"ppma_author":[1106],"class_list":["post-11623","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-african-languages","category-hausa","tag-did-peter-obi-say-hell-let-everybody-starve","tag-peter-obi"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-31t","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":1106,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"lois-ugbede","display_name":"Lois Ugbede","avatar_url":{"url":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2019\/11\/Lois.jpg","url2x":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2019\/11\/Lois.jpg"},"author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/11623","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=11623"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/11623\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":11624,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/11623\/revisions\/11624"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=11623"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=11623"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=11623"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=11623"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=11623"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}