{"id":11639,"date":"2022-05-24T15:58:17","date_gmt":"2022-05-24T14:58:17","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=11639"},"modified":"2022-05-24T16:00:16","modified_gmt":"2022-05-24T15:00:16","slug":"osinbajo-ba-ya-raba-wa-yan-najeriya-tallafin-dubu-33","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/osinbajo-ba-ya-raba-wa-yan-najeriya-tallafin-dubu-33\/","title":{"rendered":"Osinbajo ba ya raba wa \u2018yan Najeriya tallafin dubu 33"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-black-color has-cyan-bluish-gray-background-color has-text-color has-background wp-block-paragraph\"><strong>Zargi: Wabi sakon WhatsApp na zargin wai mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo na rabawa \u2018yan Najeriya tallafi na nera dubu talatin da uku uku\u00a0<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Zaben shugaban kasa na shekarar 2023 na kara matsowa kusa-kusa inda \u2018yan Najeriya za su yanke shawara kan wanda zai jagoranci lamuran kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Karbar kudin tukuici daga wurin \u2018yan takara ya zama al\u2019ada ganin yadda \u2018yan siyasa ke amfani da tukuicin wajen jan hankalin wadanda suka cancanci yin zabe a Najeriyar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A shekarar 2017 ta wallafa wadansu hotunan da ke nuna irin abin da \u2018yan siyasa ke yi lokacin zabe dan jan ra\u2019ayin \u2018yan Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Saboda irin arzikin da \u2018yan siyasa suka yi a shekarun da suka gabata, DUBAWA ta yi binciken irin wadannan zarge-zargen da dama domin akwai masu zamban da su ke amfani da hotunan \u2018yan siyasa su aikata ta\u2019asa. Alal misali, mun fallasa cewa akwai mayaudaran da su ke amfani da sunan Tinubu suna damfarar mutane a shafukan yanar gizo-gizo.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kwanan nan wani sakon da ake yadawa a WhatsApp, tare da zagin cewa mataimakin shugaban kasa kuma mai neman tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar Farfesa Yemi Osinbajo na bayar da dubu 33 kyauta ga \u2018yan Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cewar sakon wanda ke dauke da wani adireshi, na cewa kudin ya fito daga asusun yakin neman zaben mataimakin shugaban kasar ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Domin kaifin wanann zargin da ma irin tasirin da zai iya yi kan masu zabe, DUBAWA ta ga ya kamata a binciki zargin.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi inda ta yi amfani da sunan mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo dan ganin ko akwai wani labarin tallafin da aka danganta da shi.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\"><strong>Abubuwan da ke sanya alamar tambaya ga sahihancin labarin<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Binciken kwa-kwaf a shafin Domainbigdata &#8211; wanda ke tantance adiresoshin yanar gizo-gizo na kwarai da na bogi, mun ga cewa mutane da dama sun kai karar shafin suna zargin shi da karya doka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani abun da aka cika samu a shafuka irin wannan shi ne shaidun karya wadanda za su fito su rika cewa sun sami alfanu daga duka abin da aka rubuta a ire-iren shafukan. Yawanci wadanda ke zamba a yanar gizo na amfani da wanann salon dan ta haka su ke jan hankalin wadanda ba su ji ba su gani ba. Haka nan kuma duk wani adireshi da ke kan shafin ba\u2019a iya latsawa ko ziyartar shafin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bacin haka kuma shafin na cike da kura-kurai na nahawu da alamun rubuta, ko daya ba dadin karantawa.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai sakon ya yadu sosai saboda wadansu sharuddan da aka yi amfani da su a shafin. Misali duk wanda ya karanta sakon ana bukatar shi ya raba da \u2018yan uwa da abokan arziki. Masu yaudara na yawan amfani da wannan salon dan sun san duk wanda ya shiga shafin zai cika wannan sharadin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun kuma ga wani katin da aka ce a latsa idan ana neman karin bayani. Shi ma mun latsa amma bai kai mu ko\u2019ina ba.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bincikenmu ya nuna mana cewa Farfesa Yemi Osinbajo ba ya bayar da wani tallafin nera 33,000 ga matasa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Zargi: Wabi sakon WhatsApp na zargin wai mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo na rabawa \u2018yan Najeriya tallafi na nera dubu talatin da uku uku\u00a0 Zaben shugaban kasa na shekarar 2023 na kara matsowa kusa-kusa inda \u2018yan Najeriya za su yanke shawara kan wanda zai jagoranci lamuran kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Karbar kudin tukuici daga wurin \u2018yan takara ya zama al\u2019ada ganin yadda \u2018yan siyasa ke amfani da tukuicin wajen jan hankalin wadanda suka cancanci yin zabe a Najeriyar. A shekarar 2017 ta wallafa wadansu hotunan da ke nuna irin abin da \u2018yan siyasa ke yi lokacin zabe dan jan ra\u2019ayin \u2018yan Najeriya. Saboda irin arzikin da \u2018yan siyasa suka yi a shekarun da suka gabata, DUBAWA ta yi binciken irin wadannan zarge-zargen da dama domin akwai masu zamban da su ke amfani da hotunan \u2018yan siyasa su aikata ta\u2019asa. Alal misali, mun fallasa cewa akwai mayaudaran da su ke amfani da sunan Tinubu suna damfarar mutane a shafukan yanar gizo-gizo. Kwanan nan wani sakon da ake yadawa a WhatsApp, tare da zagin cewa mataimakin shugaban kasa kuma mai neman tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar Farfesa Yemi Osinbajo na bayar da dubu 33 kyauta ga \u2018yan Najeriya. A cewar sakon wanda ke dauke da wani adireshi, na cewa kudin ya fito daga asusun yakin neman zaben mataimakin shugaban kasar ne. Domin kaifin wanann zargin da ma irin tasirin da zai iya yi kan masu zabe, DUBAWA ta ga ya kamata a binciki zargin. Tantancewa DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi inda ta yi amfani da sunan mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo dan ganin ko akwai wani labarin tallafin da aka danganta da shi. Abubuwan da ke sanya alamar tambaya ga sahihancin labarin Binciken kwa-kwaf a shafin Domainbigdata &#8211; wanda ke tantance adiresoshin yanar gizo-gizo na kwarai da na bogi, mun ga cewa mutane da dama sun kai karar shafin suna zargin shi da karya doka. Wani abun da aka cika samu a shafuka irin wannan shi ne shaidun karya wadanda za su fito su rika cewa sun sami alfanu daga duka abin da aka rubuta a ire-iren shafukan. Yawanci wadanda ke zamba a yanar gizo na amfani da wanann salon dan ta haka su ke jan hankalin wadanda ba su ji ba su gani ba. Haka nan kuma duk wani adireshi da ke kan shafin ba\u2019a iya latsawa ko ziyartar shafin. Bacin haka kuma shafin na cike da kura-kurai na nahawu da alamun rubuta, ko daya ba dadin karantawa.&nbsp; Sai dai sakon ya yadu sosai saboda wadansu sharuddan da aka yi amfani da su a shafin. Misali duk wanda ya karanta sakon ana bukatar shi ya raba da \u2018yan uwa da abokan arziki. Masu yaudara na yawan amfani da wannan salon dan sun san duk wanda ya shiga shafin zai cika wannan sharadin. Mun kuma ga wani katin da aka ce a latsa idan ana neman karin bayani. Shi ma mun latsa amma bai kai mu ko\u2019ina ba. A Karshe Bincikenmu ya nuna mana cewa Farfesa Yemi Osinbajo ba ya bayar da wani tallafin nera 33,000 ga matasa.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":5102,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"","_twitter_share_type":"","_linkedin_share_type":"","_pinterest_share_type":"","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[3351],"verdict":[],"ppma_author":[3014],"class_list":["post-11639","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa","tag-osinbajo-ba-ya-raba-wa-yan-najeriya-tallafin-dubu-33"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-31J","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3014,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"muktar-balogun","display_name":"Muktar Balogun","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2020\/06\/Prof-Yemi-Osinbajo.jpg?fit=1200%2C675&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/11639","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=11639"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/11639\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":11642,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/11639\/revisions\/11642"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5102"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=11639"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=11639"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=11639"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=11639"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=11639"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}