{"id":13084,"date":"2023-02-04T06:45:02","date_gmt":"2023-02-04T05:45:02","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=13084"},"modified":"2023-02-04T06:45:04","modified_gmt":"2023-02-04T05:45:04","slug":"duk-da-sabuwar-dokar-laberiya-mai-takardar-wata-kasa-ban-da-ta-laberiyar-ba-zai-iya-neman-kujera-a-majalisun-wakilai-da-na-dattawa-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/duk-da-sabuwar-dokar-laberiya-mai-takardar-wata-kasa-ban-da-ta-laberiyar-ba-zai-iya-neman-kujera-a-majalisun-wakilai-da-na-dattawa-ba\/","title":{"rendered":"Duk da sabuwar dokar Laberiya mai takardar wata kasa ban da ta Laberiyar ba zai iya neman kujera a majalisun wakilai da na dattawa ba"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Zargi: \u2018Yan Laberiyan da ke da halatattun takardun \u2018yan kasa na kasashe biyu za su iya tsayawa takara dan samun kujeru a majilaisun wakilai da na dattawa a kasar.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"12176\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/recurring-conspiracy-theory-claims-covid-19-vaccines-infect-users-with-hiv\/false-4-14\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-4.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-12176\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Babu inda dokokin kasar su ka tanadi bai wa masu takardun &#8216;yan kasa na kasashe biyu damar tsayawa takara don neman kujerua a majalisar wakilai da na dattawa<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Cikakken bayani<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayi wadanda da su ka sami \u2018yancin kansu daga wadanda su ka saye su a Amurka ne suka girka kasar Laberiya a shekarar 1847 a matsayin wata \u201cmafaka ko masauki na \u2018yantattun mutane masu bakar fata.\u201d Kundin tsarin mulkin kasar ya yi amfani da irin kalaman wancan lokacin wajen kwatanta masu bakar fata inda ya ce mutanen da suka kasance \u201cNegro ko kuma masu zuri\u2019a Negro.\u201d A nan Negro kalmar da ta ke nufin mutun mai bakar fata ke nan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Na tsawon shekaru da dama yanzu matsalar wadanda ke da takardun \u2018yan kasa a kasashe biyu ke kasancewa babbar mahawara a kasar tun bayan yakin duniya. Wannan ya kasance haka ne domin lokacin da kasar ta yi fama da yakin basasa, \u2018yan Laberiya da yawa suka bar kasar zuwa wadansu kasashen dan samun mafaka musamman a kasashen Turai da Amurka inda daga baya kuma suka dauki takardun zama \u2018yan kasa a wadannan kasashen da suka ba su mafakar bisa dalilai daban-daban.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Dokar ta yi tanadin sharuddan da suka bayyana cikakken dan kasa wadda ake kira da turanci Old alien and Nationality Law ya ce. \u201c Yaro\/yarinya wanda ya kasance dan Laberiya bisa tanadin karamin sakin layi (b) wannan sashen zai rasa matsayin shi na dan kasa muddin bai zauna a Liberiya a mafi yawan rayuwarsa ba, sai dai idan kafin ya cika shekaru 23 na haihuwa ya je gaban jakadan Laberiya ya yi rantsuwar mubaya\u2019a ga jamhuriyar Laberiyar wanda ake bukata idan har mutun na so ya tabbatar da matsayin shi na dan kasa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan dokar ta kuma kara da cewa \u201c(a) Mutumin da ya kasance mai bakar fatam ko kuma tsatson bakake, wanda aka haifa a Laberiya wanda kuma ke karkashin dokokin kasar. (b) Mutumin da aka haifa a wajen Liberiya wanda mahaifinsa (i) an haife shi a Laberiya; (ii) Dan Laberiya ne a lokacin da aka haifi dan, kuma (iii) ya zauna a Laberiya kafin lokacin da aka haifi yaron\/yarinyar.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sadda ya hau karagar mulkin kasar Laberiya a shekarar 2018, Shugaba George Manneh Weah yayin da ya ke jawabinsa na farko ya ce kundin tsarin mulkin kasar na nuna wariya, kuma ba shi mahimmanci sa\u2019annan kuma bai dace da kasar ba dan haka ya yi alkawarin cire dokar da ta hana baki zuwa su zama cikakkun \u2018yan kasa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Matsayarsa ta sake samun karfi a shekarar 2019 lokacin da aka yi wata shari\u2019ar da babban kotun Laberiyar ta yanke hukuncin cewa kasancewa dan kasa \u2018yanci ne da ba za\u2019a iya sokewa ba tare da an je kotu ba. To sai dai, wasu sun yi imanin cewa akwai \u2018yan Laberiyar da ke da takardun fasfo na kasashe biyu a boye musamman masu hannu da shuni.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bacin mahimmancin shari\u2019ar, hukuncin da aka yanke bai bai wa \u2018yan Laberiya \u2018yancin daukar fasfon guda biyu ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Dan haka an cigaba da gwagwarmayar samar da dokar da za ta baiwa \u2018yan kasa \u2018yancin daukar takardun wata kasar daura da ta su inda mazauna kasashen waje su ka taka muhimmiyar rawa. Bayan an shafe shekaru ana jayayya har ma da kuri\u2019ar jin ra\u2019ayin da ta tanadi a yi watsi da dokar dokar Dual Citizenship a watan Disemban 2020, yanzu kasar ta amice \u2018yan kasar su dauki fasfo biyu a sabuwar dokar da ake kira Dual Citizens 2022.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">To sai dai har yanzu ana jayayya dangane da irin \u2018yancin da ya kamata a baiwa masu amsa kasashe biyun. Lokacin wani shirin da aka watsa a gidan rediyon Okay 99.5 FM ranar laraba 10 ga watan Ogosta, 2022, Dixon Seboe wakilin gundumar Montserrado ya yi zargin cewa a karkashin dokar da aka yi wa kwaskwarima wato dokar Old Aliens and Nationality Law of Liberia, masu takardun kasashe biyu za su iya tsayawa takarar neman kujerun \u2018yan majilasar dokoki da na dattawa amma ba za\u2019a iya zaben su a matsayin kakakin majalisar dokoki ko kuma ma jagirar majalisar dattawan ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan zargin ya bulla a wajen minti 14 na shirin rediyon wanda aka sa kai tsaye a shafi Facebool inda mutane fiye da dubu biyu su ka kalla wasu 150 kuma su ka yi tsokaci a kai. Wannan shirin na daya daga cikin wadanda \u2018yan Liberiya su ka fi sauraro.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ganin yadda batun ke tattare da sarkakiya na tsawon shekaru da dama yanzu da ma yadda ya ke cigaba da daukar hankali sakamakon dokar da aka kwaskware kwanann ne ya DUBAWA ta dauki matakin tantance zargin da Dixon Seboe ya yi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wanda ya tantance wannan labarin ya fara da yin la\u2019akari da tanade-tanaden wannan dokar da ake neman sauyawa. Dokokin na ainihi sun kunshi Kashi na III Babu na 20, sashe na 20.1; Babi na 21, sassan 21.30, 21.31, 21.51, da 21.52 da Babi na 22, Sassan 22.1, 22.1 da 22.4 na Aliend and Nationality Law of the Liberian Code of Law Revised Vol.II<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Daga nan sai DUBAWA ta nemi wanda aka kwaskware kafin majalisa ta amince da shi domin gano ko zargin wakilin gaskiya ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ana iya samun kadan daga cikin dokar da aka kwaskware a cikin wani rahoton da aka yi wanda ya yi amfani da sassan da suka fi mahimmanci ga mahawarar da ake yi kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cDan Laberiyar da ke takardun wata kasa ba zai iya tsayawa takarar a wani gurbin siyasa ba muddin yana rike da takardun wata kasa ta daban banda Laberiya,\u201d a cewar majalisar dokoki<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cIdan mutumin na so ya yi takara, dole sai ya yi watsi da takardun dayan kasar akalla shekara guda kafin ya nemi tsayawa takarar da Hukumar Zabe ta Kasa ya kuma nuna ma ta hujjar cewa ya yanke dangantaka da kasar sa\u2019anan ya bayyana haka a kotun Laberiya\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cHaka nan kuma mutumin da ke rike da izinin kasancewa dan kasa a wata kasa daban ban da Laberiya ba zai iya samun mukamin gwamnati a ma\u2019aikatar Kudi da Tsare-Tsare, da Ma\u2019aikatar Tsrao da ma gwamnan babban bankin kasar ta Laberiya.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kamar yadda mu ka gani yanzu dokar ta hana masu izinin \u2018yan kasa a kasashe biyu takara da ma rike mukaman gwamnati a fannonin kudi, tsaro da babban bankin kasar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kafafen yada labarai da jaridu sun yi sharhi sosai dangane da kwaskwarimar da aka yi wa dokar wandanda za\u2019a iya samu a shafuka daban-daban.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Binciken da DUBAWA ta yi dangane da zargin da dan majalisa Dixon Seboe ya yi ya nuna cewa yayin da dokar ta halatta wa \u2018yan Laberiya samun izinin kasancewa \u2018yan kasa a wadansu kasashen banda Laberiya,&nbsp; ta haramta musu yin takara ko kuma ma kasancewa a mukamai&nbsp; masu mahimmanci da sarkakiya a kasar.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Zargi: \u2018Yan Laberiyan da ke da halatattun takardun \u2018yan kasa na kasashe biyu za su iya tsayawa takara dan samun kujeru a majilaisun wakilai da na dattawa a kasar. Babu inda dokokin kasar su ka tanadi bai wa masu takardun &#8216;yan kasa na kasashe biyu damar tsayawa takara don neman kujerua a majalisar wakilai da na dattawa Cikakken bayani Bayi wadanda da su ka sami \u2018yancin kansu daga wadanda su ka saye su a Amurka ne suka girka kasar Laberiya a shekarar 1847 a matsayin wata \u201cmafaka ko masauki na \u2018yantattun mutane masu bakar fata.\u201d Kundin tsarin mulkin kasar ya yi amfani da irin kalaman wancan lokacin wajen kwatanta masu bakar fata inda ya ce mutanen da suka kasance \u201cNegro ko kuma masu zuri\u2019a Negro.\u201d A nan Negro kalmar da ta ke nufin mutun mai bakar fata ke nan. Na tsawon shekaru da dama yanzu matsalar wadanda ke da takardun \u2018yan kasa a kasashe biyu ke kasancewa babbar mahawara a kasar tun bayan yakin duniya. Wannan ya kasance haka ne domin lokacin da kasar ta yi fama da yakin basasa, \u2018yan Laberiya da yawa suka bar kasar zuwa wadansu kasashen dan samun mafaka musamman a kasashen Turai da Amurka inda daga baya kuma suka dauki takardun zama \u2018yan kasa a wadannan kasashen da suka ba su mafakar bisa dalilai daban-daban. Dokar ta yi tanadin sharuddan da suka bayyana cikakken dan kasa wadda ake kira da turanci Old alien and Nationality Law ya ce. \u201c Yaro\/yarinya wanda ya kasance dan Laberiya bisa tanadin karamin sakin layi (b) wannan sashen zai rasa matsayin shi na dan kasa muddin bai zauna a Liberiya a mafi yawan rayuwarsa ba, sai dai idan kafin ya cika shekaru 23 na haihuwa ya je gaban jakadan Laberiya ya yi rantsuwar mubaya\u2019a ga jamhuriyar Laberiyar wanda ake bukata idan har mutun na so ya tabbatar da matsayin shi na dan kasa. Wannan dokar ta kuma kara da cewa \u201c(a) Mutumin da ya kasance mai bakar fatam ko kuma tsatson bakake, wanda aka haifa a Laberiya wanda kuma ke karkashin dokokin kasar. (b) Mutumin da aka haifa a wajen Liberiya wanda mahaifinsa (i) an haife shi a Laberiya; (ii) Dan Laberiya ne a lokacin da aka haifi dan, kuma (iii) ya zauna a Laberiya kafin lokacin da aka haifi yaron\/yarinyar.\u201d Sadda ya hau karagar mulkin kasar Laberiya a shekarar 2018, Shugaba George Manneh Weah yayin da ya ke jawabinsa na farko ya ce kundin tsarin mulkin kasar na nuna wariya, kuma ba shi mahimmanci sa\u2019annan kuma bai dace da kasar ba dan haka ya yi alkawarin cire dokar da ta hana baki zuwa su zama cikakkun \u2018yan kasa. Matsayarsa ta sake samun karfi a shekarar 2019 lokacin da aka yi wata shari\u2019ar da babban kotun Laberiyar ta yanke hukuncin cewa kasancewa dan kasa \u2018yanci ne da ba za\u2019a iya sokewa ba tare da an je kotu ba. To sai dai, wasu sun yi imanin cewa akwai \u2018yan Laberiyar da ke da takardun fasfo na kasashe biyu a boye musamman masu hannu da shuni. Bacin mahimmancin shari\u2019ar, hukuncin da aka yanke bai bai wa \u2018yan Laberiya \u2018yancin daukar fasfon guda biyu ba. Dan haka an cigaba da gwagwarmayar samar da dokar da za ta baiwa \u2018yan kasa \u2018yancin daukar takardun wata kasar daura da ta su inda mazauna kasashen waje su ka taka muhimmiyar rawa. Bayan an shafe shekaru ana jayayya har ma da kuri\u2019ar jin ra\u2019ayin da ta tanadi a yi watsi da dokar dokar Dual Citizenship a watan Disemban 2020, yanzu kasar ta amice \u2018yan kasar su dauki fasfo biyu a sabuwar dokar da ake kira Dual Citizens 2022. To sai dai har yanzu ana jayayya dangane da irin \u2018yancin da ya kamata a baiwa masu amsa kasashe biyun. Lokacin wani shirin da aka watsa a gidan rediyon Okay 99.5 FM ranar laraba 10 ga watan Ogosta, 2022, Dixon Seboe wakilin gundumar Montserrado ya yi zargin cewa a karkashin dokar da aka yi wa kwaskwarima wato dokar Old Aliens and Nationality Law of Liberia, masu takardun kasashe biyu za su iya tsayawa takarar neman kujerun \u2018yan majilasar dokoki da na dattawa amma ba za\u2019a iya zaben su a matsayin kakakin majalisar dokoki ko kuma ma jagirar majalisar dattawan ba. Wannan zargin ya bulla a wajen minti 14 na shirin rediyon wanda aka sa kai tsaye a shafi Facebool inda mutane fiye da dubu biyu su ka kalla wasu 150 kuma su ka yi tsokaci a kai. Wannan shirin na daya daga cikin wadanda \u2018yan Liberiya su ka fi sauraro. Tantancewa Ganin yadda batun ke tattare da sarkakiya na tsawon shekaru da dama yanzu da ma yadda ya ke cigaba da daukar hankali sakamakon dokar da aka kwaskware kwanann ne ya DUBAWA ta dauki matakin tantance zargin da Dixon Seboe ya yi. Wanda ya tantance wannan labarin ya fara da yin la\u2019akari da tanade-tanaden wannan dokar da ake neman sauyawa. Dokokin na ainihi sun kunshi Kashi na III Babu na 20, sashe na 20.1; Babi na 21, sassan 21.30, 21.31, 21.51, da 21.52 da Babi na 22, Sassan 22.1, 22.1 da 22.4 na Aliend and Nationality Law of the Liberian Code of Law Revised Vol.II Daga nan sai DUBAWA ta nemi wanda aka kwaskware kafin majalisa ta amince da shi domin gano ko zargin wakilin gaskiya ne. Ana iya samun kadan daga cikin dokar da aka kwaskware a cikin wani rahoton da aka yi wanda ya yi amfani da sassan da suka fi mahimmanci ga mahawarar da ake yi kamar haka: \u201cDan Laberiyar da ke takardun wata kasa ba zai iya tsayawa takarar a wani gurbin siyasa ba muddin yana rike da takardun wata kasa ta daban banda Laberiya,\u201d a cewar majalisar dokoki \u201cIdan mutumin na so ya yi takara, dole sai ya yi watsi da takardun dayan kasar akalla shekara guda kafin ya nemi tsayawa takarar da Hukumar Zabe ta Kasa ya kuma nuna ma ta hujjar cewa ya yanke dangantaka da kasar sa\u2019anan ya bayyana haka a kotun Laberiya\u201d \u201cHaka nan kuma mutumin da ke rike<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":12119,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"","_twitter_share_type":"","_linkedin_share_type":"","_pinterest_share_type":"","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[3533,115],"verdict":[],"ppma_author":[3532],"class_list":["post-13084","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa","tag-dual-citizenship-in-liberia","tag-fact-check"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-3p2","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3532,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"jackson-c-clay-jr","display_name":"Jackson C. Clay Jr.","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/4a1a3a0ffb70288fc47151919d35bfbf84da6ab614d08ddda46c3d772f23f39b?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/Dual-citizens-cannot-be-elected-as-Representatives-Senators-despite-new-law.png?fit=1200%2C676&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/13084","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=13084"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/13084\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":13085,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/13084\/revisions\/13085"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/12119"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=13084"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=13084"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=13084"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=13084"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=13084"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}