{"id":13315,"date":"2023-02-15T13:27:48","date_gmt":"2023-02-15T12:27:48","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=13315"},"modified":"2023-02-15T13:27:50","modified_gmt":"2023-02-15T12:27:50","slug":"buhari-ya-nuna-amincewarsa-da-takarar-tinubu-a-gangamin-zaben-jamiyyar-a-adamawa-wanda-ya-saba-wa-zargin-wani-mai-amfani-da-tiwita","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/buhari-ya-nuna-amincewarsa-da-takarar-tinubu-a-gangamin-zaben-jamiyyar-a-adamawa-wanda-ya-saba-wa-zargin-wani-mai-amfani-da-tiwita\/","title":{"rendered":"<strong>Buhari ya nuna amincewarsa da takarar Tinubu a gangamin zaben jam\u2019iyyar a Adamawa, wanda ya saba wa zargin wani mai amfani da tiwita<\/strong>"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Zargi: Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da takakarar Bola Ahmed Tinubu na kujerar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam\u2019iyyarsa ta APC lokacin gangamin da su ka yi a jihar Adamawa ba<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"12168\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/video-shot-in-ghana-used-to-depict-support-for-atiku\/false-3-15\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-3.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-3\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-3.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-3.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-12168\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Zargin wai shugaba kasa bai marawa takarar Tinubu baya ba, ba gaskiya ba ne, domin bincikenmu ya nuna mana cewa Buhari ya goyi bayan takarar Bola Tinubu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Cikakken bayani<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Jam\u2019iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zabenta a birnin Yola, jihar Adama ranar litini 9 ga watan Janairun 2023. Sa\u2019anan a karon farko tun bayan da jam\u2019iyyar ta fara gangamin zaben a birnin Jos na jihar Filato a bara, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sa\u2019o\u2019i kadan kafin kaddamar da yakin neman zaben, wata mai amfani da shafin Tiwita NKEM #PeterObi2023(@Nkemchor) ta ce shugaba Muhammadu Buhari bai amince da takarar wanda ke neman shugabancin kasar a karkashin jam\u2019iyyarsa ba wato Bola Ahmed Tinubu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mai shafin ta danganta wannan zargin na ta da wani bidiyo mai tsawon minti daya da dakiku biyu wanda aka nada a taron gangamin wanda ta samo daga wani shafin tiwitan na @MuchTalksBlog1, na wani mai suna Chinaza #PeterObi-HypeMan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kafin gangamin na Yola, wasu sun rika rade-radin cewa shugaba Muhammadu Buhari na kaucewa daga yi wa dan takarar jam\u2019iyyar ta sa kamfe ne sakamakon wadansu shakkun da ake kyautata zaton ya na da su, abin da ya janyo zargin cewa ba haka kawai ne ake sa tafiye-tafiyen shugaba Buharin a dai-dai lokacin da jam\u2019iyyar za ta je yakin neman zabe ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Domin sarkakiyar da irin wannan batu ya ke da shi musamman a lokacin zabe, da ma yadda batun ya dauki hankalin jama\u2019a DUBAWA ta ga ya dace a tantance gaskiyar lamarin<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;Mun fara da binciken mahimman kalmomi wanda ya nuna mana cewa Buhari ya nuna amincewarsa da takarar Tinubu lokacin gangamin da aka yi a Yola. Wani bidiyo mai tsawon sa\u2019a guda da mintoci 23 na gangamin jam\u2019iyyar ta APC da mu ka gano a YouTube, wanda gidan talibijin na TVC ya sanya da ma gajejjerun da Channels da TV360 su ma su ka sa a shafin duk sun yi bayanin yadda shugaba Buhari ya nuna goyon bayansa ga Tinubu har ma ya nemi jama\u2019a da su mara mi shi baya, da shi da abokin takararsa Kashim Shettima.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Haka nan kuma, shugaba Buharin a shafin na Tiwita ya sanar da dan takarar shugaban kasar na APC da abokin takarar ta sa a matsayin mutane masu rikon amana.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bincikenmu bai kai mu ga rahotanni daga kafofin yada labarai masu nagarta da su ka amince da zargin ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yayin da muka kalla mu ka kuma saurari dogon shirin gangamin da aka yi a Adamawa, mun kula cewa bidiyon da Nkemchor_ ya wallafa ya mayar da hankali ne a kan abin da shugaba Buhari kadai ya fada. Wanda ya hada bidiyon ya yanki wannan barin ne kadai domin ya fadada na sa manufofin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A bidiyon mai tsawon sa\u2019a guda da minti 23 wanda gidan talibijin na TVC ya wallafa a YouTube, mun ji shugaba Buhari yana cewa ya na jihar Adamawa ne domin ya gabatar da dan takarar mukamin shugaban kasa a jam\u2019iyyarsa, Bola Tinubu ( Ya yi hakan ne yayin da ya ke daga hannun dan takarar) da dan takarar mukamin gwamna, Aishatu Binani. Bayan haka ne ya mika tutar jam\u2019iyyar ga wa kowanne daga cikin \u2018yan takaran biyu. Sa\u2019annan ya kara da kira ga jama\u2019a da su zabi APC, inda ya bayyana abubuwan da za su amfani jam\u2019iyyar. Daga bisani kuma ya kara da kwatanta irin \u2018yan takaran da ya dace wadanda su ka cancanci kada kuri\u2019ar su zaba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shawarar da ya bayar kan irin \u2018yan takaran da ya kamata a zaba ne aka yi amfani da shi a bidiyon da aka wallafa a shafin Tiwita.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shugaba Buhari ya kuma yi magana da harshen hausa. Jawabin wanda wani ne ya fassara zuwa Hausar ya bayyana cewa shugaban kasar ya yi kira ga jama\u2019a da su zabi Tinubu domin zai aiwatar da burin jam\u2019iyyar. Ya kuma bukaci mutane su jefawa \u2018yar takarar gwamnan a jihar Adamawa kuri\u2019ar su.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe&nbsp;<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Zargin wai shugaba kasa bai marawa takarar Tinubu baya ba, ba gaskiya ba ne, domin bincikenmu ya nuna mana cewa Buhari ya goyi bayan takarar Bola Tinubu.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Zargi: Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da takakarar Bola Ahmed Tinubu na kujerar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam\u2019iyyarsa ta APC lokacin gangamin da su ka yi a jihar Adamawa ba Zargin wai shugaba kasa bai marawa takarar Tinubu baya ba, ba gaskiya ba ne, domin bincikenmu ya nuna mana cewa Buhari ya goyi bayan takarar Bola Tinubu. Cikakken bayani Jam\u2019iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zabenta a birnin Yola, jihar Adama ranar litini 9 ga watan Janairun 2023. Sa\u2019anan a karon farko tun bayan da jam\u2019iyyar ta fara gangamin zaben a birnin Jos na jihar Filato a bara, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarta. Sa\u2019o\u2019i kadan kafin kaddamar da yakin neman zaben, wata mai amfani da shafin Tiwita NKEM #PeterObi2023(@Nkemchor) ta ce shugaba Muhammadu Buhari bai amince da takarar wanda ke neman shugabancin kasar a karkashin jam\u2019iyyarsa ba wato Bola Ahmed Tinubu. Mai shafin ta danganta wannan zargin na ta da wani bidiyo mai tsawon minti daya da dakiku biyu wanda aka nada a taron gangamin wanda ta samo daga wani shafin tiwitan na @MuchTalksBlog1, na wani mai suna Chinaza #PeterObi-HypeMan. Kafin gangamin na Yola, wasu sun rika rade-radin cewa shugaba Muhammadu Buhari na kaucewa daga yi wa dan takarar jam\u2019iyyar ta sa kamfe ne sakamakon wadansu shakkun da ake kyautata zaton ya na da su, abin da ya janyo zargin cewa ba haka kawai ne ake sa tafiye-tafiyen shugaba Buharin a dai-dai lokacin da jam\u2019iyyar za ta je yakin neman zabe ba. Domin sarkakiyar da irin wannan batu ya ke da shi musamman a lokacin zabe, da ma yadda batun ya dauki hankalin jama\u2019a DUBAWA ta ga ya dace a tantance gaskiyar lamarin Tantancewa &nbsp;Mun fara da binciken mahimman kalmomi wanda ya nuna mana cewa Buhari ya nuna amincewarsa da takarar Tinubu lokacin gangamin da aka yi a Yola. Wani bidiyo mai tsawon sa\u2019a guda da mintoci 23 na gangamin jam\u2019iyyar ta APC da mu ka gano a YouTube, wanda gidan talibijin na TVC ya sanya da ma gajejjerun da Channels da TV360 su ma su ka sa a shafin duk sun yi bayanin yadda shugaba Buhari ya nuna goyon bayansa ga Tinubu har ma ya nemi jama\u2019a da su mara mi shi baya, da shi da abokin takararsa Kashim Shettima. Haka nan kuma, shugaba Buharin a shafin na Tiwita ya sanar da dan takarar shugaban kasar na APC da abokin takarar ta sa a matsayin mutane masu rikon amana. Bincikenmu bai kai mu ga rahotanni daga kafofin yada labarai masu nagarta da su ka amince da zargin ba. Yayin da muka kalla mu ka kuma saurari dogon shirin gangamin da aka yi a Adamawa, mun kula cewa bidiyon da Nkemchor_ ya wallafa ya mayar da hankali ne a kan abin da shugaba Buhari kadai ya fada. Wanda ya hada bidiyon ya yanki wannan barin ne kadai domin ya fadada na sa manufofin. A bidiyon mai tsawon sa\u2019a guda da minti 23 wanda gidan talibijin na TVC ya wallafa a YouTube, mun ji shugaba Buhari yana cewa ya na jihar Adamawa ne domin ya gabatar da dan takarar mukamin shugaban kasa a jam\u2019iyyarsa, Bola Tinubu ( Ya yi hakan ne yayin da ya ke daga hannun dan takarar) da dan takarar mukamin gwamna, Aishatu Binani. Bayan haka ne ya mika tutar jam\u2019iyyar ga wa kowanne daga cikin \u2018yan takaran biyu. Sa\u2019annan ya kara da kira ga jama\u2019a da su zabi APC, inda ya bayyana abubuwan da za su amfani jam\u2019iyyar. Daga bisani kuma ya kara da kwatanta irin \u2018yan takaran da ya dace wadanda su ka cancanci kada kuri\u2019ar su zaba. Shawarar da ya bayar kan irin \u2018yan takaran da ya kamata a zaba ne aka yi amfani da shi a bidiyon da aka wallafa a shafin Tiwita. Shugaba Buhari ya kuma yi magana da harshen hausa. Jawabin wanda wani ne ya fassara zuwa Hausar ya bayyana cewa shugaban kasar ya yi kira ga jama\u2019a da su zabi Tinubu domin zai aiwatar da burin jam\u2019iyyar. Ya kuma bukaci mutane su jefawa \u2018yar takarar gwamnan a jihar Adamawa kuri\u2019ar su. A Karshe&nbsp; Zargin wai shugaba kasa bai marawa takarar Tinubu baya ba, ba gaskiya ba ne, domin bincikenmu ya nuna mana cewa Buhari ya goyi bayan takarar Bola Tinubu.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":12888,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"","_twitter_share_type":"","_linkedin_share_type":"","_pinterest_share_type":"","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3778],"class_list":["post-13315","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-3sL","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3778,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"rasheedat-oladotun-iliyas","display_name":"Rasheedat Oladotun Iliyas","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2023\/01\/Buhari-and-Tinubu.jpeg?fit=1500%2C1000&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/13315","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=13315"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/13315\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":13316,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/13315\/revisions\/13316"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/12888"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=13315"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=13315"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=13315"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=13315"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=13315"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}