{"id":13503,"date":"2023-02-24T02:00:00","date_gmt":"2023-02-24T01:00:00","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=13503"},"modified":"2023-02-24T00:04:07","modified_gmt":"2023-02-23T23:04:07","slug":"zaben-2023-hakkokinku-na-ranar-zabe-a-matsayin-wadanda-suka-cancanci-kada-kuria","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/zaben-2023-hakkokinku-na-ranar-zabe-a-matsayin-wadanda-suka-cancanci-kada-kuria\/","title":{"rendered":"<strong>#Zaben 2023: Hakkokinku na ranar zabe a matsayin wadanda suka cancanci kada kuri\u2019a<\/strong>"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hana sauyi kamar yadda ya faru a shekarun&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.bbc.com\/news\/world-africa-31221545\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">2015<\/a>&nbsp; da&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/news\/headlines\/313199-its-official-inec-postpones-all-nigerias-general-elections.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">2019<\/a>, mutane fiye da <a href=\"https:\/\/inecnigeria.org\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">miliyan 84&nbsp; <\/a>suka yi rajistar jefa kuri\u2019unsu domin zaben shugaban kasar Najeriya na 16 kuma na 6 a cikin wadanda aka zaba bisa turbar dimokiradiyya wanda za\u2019a yi 25 ga watan Fabrairu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A baya fitowa zabe ya kan kasance babban kalubale kuma ana yawan danganta wannan da yadda hakkokin masu zabe ke raguwa. Akwai <a href=\"https:\/\/www.semanticscholar.org\/paper\/VOTERS%E2%80%99-EDUCATION-AND-CREDIBLE-ELECTION-IN-NIGERIA%3A-Oduola\/e901178d72c193f6281513a2730a322f27e8b96a\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">binciken<\/a> da Saheed Olasunkanmi ya yi dangane da \u201cilimantar da masu zabe da zabuka masu sahihanci a Najeriya: Batutuwa da Kalubalen babban zaben 2019\u201d wanda ya nuna cewa akwai gibi sosai idan ya zo ga irin ilimin da \u2018yan kasa ke da shi dangane da zabe sakamakon irin kutsen da mulkin sojoji ya yi a kasar.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Domin kaucewa rashin yin zabe, ilimantar da jama\u2019a kan tsarin zabe da samar da cibiyoyin zabe masu nagarta na da mahimmanci sosai wajen samun nasara a gudanar da zabe,musamman a yunkurin da Najeriya ke yi wanje inganta tsarin demokiradiyyarta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da kudurin dokar da aka zartar ranar 25 ga watan fabrairun 2022, akwai sauye-sauyen da suka shafi \u2018yan takara, jam\u2019iyya da sauran masu ruwa da tsaki wadanda har yanzu ba\u2019a san su ba.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Wadanne hakkoki ne masu zabe ke da shi ranar zabe, kuma yaya za su kare su?<\/h2>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><\/h2>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li>\u2018<strong>Yancin kada kuri\u2019a<\/strong><\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bisa tanadin kundin tsarin mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara) duk wani dan kasa wanda ya cika duka sharudan da doka ta gindaya zai iya yin zabe kuma zai iya tsayawa takara,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da katin zaben da ke nuna duka bayanan wanda ke rike da shi, wanda ya cancanci kada kuri\u2019a na da \u2018yancin yin zabe bayan an tantance ko shi wane ne kafin zaben ya fara<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wanda ke tsayawa takara ma tilas ne ya cika wadannan sharudan . Bayan an cika duk tanade-tanaden doka kafin ranar zabe, dan takara a inuwar jam\u2019iyyar da ya ke takara na da \u2018yancin yin zabe.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\" start=\"2\">\n<li><strong>Zabin yin zabe cikin sirri<\/strong><\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Masu jefa kuri\u2019a na da \u2018yancin yin haka cikin sirri. Kasancewar rumfunan zabe ma yana tabbatar da kariya ga masu zabe da kuma taimaka mu su wajen yin zabin su cikin sirri.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Idan aka shiga wani yanyi na tashin hankali ko kuma dai wata tarzoma, irin wadanda aka cika gani lokutan zabe a nahiyar Afirka, rumfunan zabe na tabbatar da kariya da tsaro ta wannan fannin.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\" start=\"3\">\n<li><strong>\u2018Yancin samun bayanai dangane da zaben<\/strong><\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Lokacin zabe, wanda ya cancanci kada kuri\u2019a na da \u2018yancin yin tambayoyi dangane da abubuwan da bai fahimta ba ba tare da fargabar hukunci daga jami\u2019an tsaro ko jami\u2019an zabe ba. Tilas ne jami\u2019an da ke wurin zabe su amsa tambayoyin da suka dangance tsarin yadda ake jefa kuri\u2019ar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Haka nan kuma duk wanda zai yi zabe yana da \u2018yancin samun bayanai dangane da zaben ko bayan an kammala. Kudurin Dokar \u2018Yancin Samun Bayanai, wanda ya zama doka a shekarar 2011, na bai wa duk wani wanda ya cancanci kada kuri\u2019a \u2018yacin tambaya da kuma samun bayanan da ke hannun mahukunta. Da kudaden jama\u2019a ake zabe, shi ya sa wajibi a baiwa masu zabe duk wani bayanin da suke bukata.<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\" start=\"4\">\n<li>Sanya ido kan sakamakon zabe<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk wanda ya yi zabe zai iya zaunawa ya jira har sai sadda za\u2019a bayyana sakamakon zaben. Babu jami\u2019in da ya isa ya kalubalanci masu hefa kuri\u2019a har ma ya kore so daga rumfar zabe a lokacin, kafin, ko kuma lokacin da ake kidayar kuri\u2019u ko ma bayan zaben.&nbsp;&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Masu zabe za su iya kidaya tare da wadanda ke yi dan a tabbatar an yi komai a bayyane. Haka nan kuma suna da \u2018yancin su tambayi jami\u2019an zabe idan sun ga wadansu abubuwan da ba su gane ba. Sai dai kuma babu mai zaben da ya isa ya tsoratar da jami\u2019in zabe ko ma ya sa shi yin irin aikin da ba shi ne ba ne wajen kidayar kuri\u2019un.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hana sauyi kamar yadda ya faru a shekarun&nbsp; 2015&nbsp; da&nbsp; 2019, mutane fiye da miliyan 84&nbsp; suka yi rajistar jefa kuri\u2019unsu domin zaben shugaban kasar Najeriya na 16 kuma na 6 a cikin wadanda aka zaba bisa turbar dimokiradiyya wanda za\u2019a yi 25 ga watan Fabrairu. A baya fitowa zabe ya kan kasance babban kalubale kuma ana yawan danganta wannan da yadda hakkokin masu zabe ke raguwa. Akwai binciken da Saheed Olasunkanmi ya yi dangane da \u201cilimantar da masu zabe da zabuka masu sahihanci a Najeriya: Batutuwa da Kalubalen babban zaben 2019\u201d wanda ya nuna cewa akwai gibi sosai idan ya zo ga irin ilimin da \u2018yan kasa ke da shi dangane da zabe sakamakon irin kutsen da mulkin sojoji ya yi a kasar.&nbsp; Domin kaucewa rashin yin zabe, ilimantar da jama\u2019a kan tsarin zabe da samar da cibiyoyin zabe masu nagarta na da mahimmanci sosai wajen samun nasara a gudanar da zabe,musamman a yunkurin da Najeriya ke yi wanje inganta tsarin demokiradiyyarta. Da kudurin dokar da aka zartar ranar 25 ga watan fabrairun 2022, akwai sauye-sauyen da suka shafi \u2018yan takara, jam\u2019iyya da sauran masu ruwa da tsaki wadanda har yanzu ba\u2019a san su ba. Wadanne hakkoki ne masu zabe ke da shi ranar zabe, kuma yaya za su kare su? Bisa tanadin kundin tsarin mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara) duk wani dan kasa wanda ya cika duka sharudan da doka ta gindaya zai iya yin zabe kuma zai iya tsayawa takara, Da katin zaben da ke nuna duka bayanan wanda ke rike da shi, wanda ya cancanci kada kuri\u2019a na da \u2018yancin yin zabe bayan an tantance ko shi wane ne kafin zaben ya fara Wanda ke tsayawa takara ma tilas ne ya cika wadannan sharudan . Bayan an cika duk tanade-tanaden doka kafin ranar zabe, dan takara a inuwar jam\u2019iyyar da ya ke takara na da \u2018yancin yin zabe.&nbsp; Masu jefa kuri\u2019a na da \u2018yancin yin haka cikin sirri. Kasancewar rumfunan zabe ma yana tabbatar da kariya ga masu zabe da kuma taimaka mu su wajen yin zabin su cikin sirri. Idan aka shiga wani yanyi na tashin hankali ko kuma dai wata tarzoma, irin wadanda aka cika gani lokutan zabe a nahiyar Afirka, rumfunan zabe na tabbatar da kariya da tsaro ta wannan fannin.&nbsp; Lokacin zabe, wanda ya cancanci kada kuri\u2019a na da \u2018yancin yin tambayoyi dangane da abubuwan da bai fahimta ba ba tare da fargabar hukunci daga jami\u2019an tsaro ko jami\u2019an zabe ba. Tilas ne jami\u2019an da ke wurin zabe su amsa tambayoyin da suka dangance tsarin yadda ake jefa kuri\u2019ar. Haka nan kuma duk wanda zai yi zabe yana da \u2018yancin samun bayanai dangane da zaben ko bayan an kammala. Kudurin Dokar \u2018Yancin Samun Bayanai, wanda ya zama doka a shekarar 2011, na bai wa duk wani wanda ya cancanci kada kuri\u2019a \u2018yacin tambaya da kuma samun bayanan da ke hannun mahukunta. Da kudaden jama\u2019a ake zabe, shi ya sa wajibi a baiwa masu zabe duk wani bayanin da suke bukata. Duk wanda ya yi zabe zai iya zaunawa ya jira har sai sadda za\u2019a bayyana sakamakon zaben. Babu jami\u2019in da ya isa ya kalubalanci masu hefa kuri\u2019a har ma ya kore so daga rumfar zabe a lokacin, kafin, ko kuma lokacin da ake kidayar kuri\u2019u ko ma bayan zaben.&nbsp;&nbsp; Masu zabe za su iya kidaya tare da wadanda ke yi dan a tabbatar an yi komai a bayyane. Haka nan kuma suna da \u2018yancin su tambayi jami\u2019an zabe idan sun ga wadansu abubuwan da ba su gane ba. Sai dai kuma babu mai zaben da ya isa ya tsoratar da jami\u2019in zabe ko ma ya sa shi yin irin aikin da ba shi ne ba ne wajen kidayar kuri\u2019un.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":12510,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"","_twitter_share_type":"","_linkedin_share_type":"","_pinterest_share_type":"","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3263],"class_list":["post-13503","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-3vN","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3263,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"phillip-anjorin","display_name":"Phillip Anjorin","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/98daaf5d9d7a2c5cd4ce1c417532d1cfa2ca293247710cf46a925146cc2e90e1?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/11\/election-officials.jpg?fit=1600%2C900&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/13503","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=13503"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/13503\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":13504,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/13503\/revisions\/13504"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/12510"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=13503"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=13503"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=13503"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=13503"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=13503"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}