{"id":14703,"date":"2023-05-11T03:44:30","date_gmt":"2023-05-11T02:44:30","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=14703"},"modified":"2023-05-11T03:44:34","modified_gmt":"2023-05-11T02:44:34","slug":"kalaman-malami-kan-kariya-da-tsaron-yan-jarida-a-najeriya-ba-gaskiya-ba-ne","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/kalaman-malami-kan-kariya-da-tsaron-yan-jarida-a-najeriya-ba-gaskiya-ba-ne\/","title":{"rendered":"Kalaman Malami kan kariya da tsaron \u2018yan jarida a Najeriya ba gaskiya ba ne\u00a0"},"content":{"rendered":"\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da \u2018yan makwanni kalilan kafin karshen mulkinsa, shugaba Muhammadu Buhari da jami\u2019an gwamnatinsa, na cigaba da bayyana abubuwan da a ra\u2019ayinsu su ne manyan\u00a0 <a href=\"https:\/\/leadership.ng\/we-have-implemented-high-impact-projects-across-nigeria-buhari\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nassarorin <\/a>\u00a0\u00a0da gwamnatin ta sa ta\u00a0 yi, yayin da a waje guda kuma su ke kokarin kwaskware wasu daga cikin himmomin da suka yi kafin barin\u00a0 karagar mulkin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ranar 26 ga watan Afrilun 2023, Majalisar Zartarwar Kasar FEC ta sanar da amincewar da ta yi da ani shirin da wa\u2019adinsa ke tsakanin 2022 da 2026 wanda zai habaka ya kuma kare hakkin dan adam a Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da ya ke jawabi a taron, antoni janar kuma ministan shari\u2019ar kasar Abubakar Malami ya ce gwamnatin Buhari ta amince da shirin ne a wani mataki na mutunta shari\u2019r Hukumar Kula da Hakkin Dan Adam Ta Kasa (NHRC) da ma biyan diyyan Nera miliyan 135 ga iyalan wadanda aka kashe ranar 18 ga watan Satumban 2013, a abun da aka fi sani da Apo-Six Killings ko kuma kissar mutane 6 a Apo.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cIdan ba ku manta ba, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kafa tarihi da kasancewarta gwamnatin farko a tarihin kasar da ta taba yin la\u2019akari da yunkuri da ma aiwatar da hukuncin da Hukumar Kare Hakkin Bil adama ta yanke,\u201d a cewar ministan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ministan wanda ya ambaci rahoton Kwamitin Tabbatar da Tsaron \u2018yan Jarida na CPJ ya <a href=\"https:\/\/youtu.be\/uDTN_S0_qVA\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ce<\/a> Najeriya ce kadai kasar Afirkar da a shekarar 2022 ta yi la\u2019akari da duka sharuddan da aka gindaya na kare hakkokin \u2018yan jarida.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kuma cigaba da <a href=\"https:\/\/www.nannews.ng\/2023\/04\/27\/fg-approves-human-rights-protection-action-plan\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">zargin<\/a> cewa babu dan jaridar da ya mutu a Najeriya a karkashin gwamnatin Buhari saboda dalilan da ke da nasaba da aikin shi\/ta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cKuna kuma sane da yadda kwamitin kare \u2018yan jarida wanda kwamitin kasa da kasa ne, ya ce Najeriya ce kadat kasar Afirkar da a bara ta mutunta sharruddan kare hakkokin \u2018yan jarida bisa la\u2019akari da cewa babu dan jaridar da ya mutu a kasar sakamakon wani abun da ke da danganta da aikin su.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan furucin na sa ya zo ne yayin da ake samun <a href=\"https:\/\/www.google.com\/amp\/s\/businessday.ng\/amp\/news\/article\/taraba-nuj-urges-govt-officials-to-stop-harassment-of-journalists\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">zarge-zarge<\/a> na laifukan da suka shafi takke hakkin dan adam a bangaren gwamnatin Najeriya da ma kuntatawa \u2018yan jarida, ta hanyar hannu su wallafa irin labaran da su ke so su wallafa a kasar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Zargin farko (1): Mr Malami ya ce Najeriya ce kadai kasar Afirkar da a 2022 ta cika tandin sharuddan kare \u2018yan jarida bisa la\u2019akari da rahoton CPJ.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A wata sanarwa ranar juma\u2019a CPJ ta karyata zargin Malami, <a href=\"https:\/\/www.google.com\/amp\/s\/cpj.org\/2023\/04\/nigerian-justice-minister-misrepresents-cpj-research-on-attacks-on-journalists\/amp\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">inda a cewar ta<\/a> ministan bai fassara sakamakon rahotin daidai ba da ya zo amfani da shi wajen gabatar da matsayarsa. Shugabar shirin CPJ na Afirka, Angela Quintal, ta ci Allah wadai da sanarwar ministan inda ita ma ta ce \u201cbinciken CPJ dangane da \u2018yancin \u2018yan jarida a Najeriya, mai nuna shekarun da aka shafe ana cin zarafin masu dauko labarai &#8211; har da kissa \u2013 ya sabawa kalaman Antoni Janar, kuma ministan shari\u2019a Abubakar Malami dangane da halin da \u2018yancin walwalar \u2018yan jarida ke ciki a kasar. Yadda Malami ya yi amfani da binciken abun ban tsori ne da tausayi ganin yadda ake yawan cin zarafin \u2018yan jaridan Najeriya bisa zarginsu da wallafa labaran karya\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kungiyar ta kuma ce ministan ba daidai ya ke amfani da bayanan binciken ba a duk lokutan da ya riga ya yi amfani da su domin yana ikirarin cewa gwamnatin Najeriya na kula da \u2018yan jaridar yadda ya kamata.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/news\/headlines\/554436-press-freedom-attacks-on-nigerian-journalists-increase-in-2022.html?tztc=1\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Bayana<\/a>i daga binciken da aka samu daga shafin <a href=\"https:\/\/www.pressattack.africa\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Press Attack Tracker <\/a>ya tabbatar da abun da \u2018yan jaridan Najeriyar ke fuskanta. Shafin binciken wadda cibiyar \u2018yan jarida na koyon sabbin dabaru da tabbatar da cigaba CIJD ta kirkiro ya nuna cewa \u2018yan jarida 52 ne suka fuskanci hare-hare a shekarar 2022 kuma jami\u2019an gwamnati ne yawancin wadanda suka muzgunawa \u2018yan jaridar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shafin ya kuma cigaba da bayyana cewa a shekaru hudun da suka gabata (2019 &#8211; 2022) \u2018yan jarida 179 suka fusakanci cin zarafi a Najeriya (wadanda ma aka sani ke nan). Yawancin wadannan hare-haren kuma na zuwa ne da ma\u2019aikatan gwamnati da jami\u2019an tsaro.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hare-hare sun kama daga harin jiki, kamen da babu gaira babu dalili yawancin wadanda ma basu halatta ba, zuwa kurkuku, barazana, sa ido, hana damar shiga wurare ko samun bayanai, shigar da kara kotu dan hana \u2018yan jaridar yin aikinsu yadda ya kamata za hanyar (SLAPPs) kwace kayayyakin aiki, lalata kayayyakin aikin ko kuma ma kissa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A wannan shekarar, kungiyar Reporters Without Borders, ta bai wa Najeria <a href=\"https:\/\/rsf.org\/en\/index\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">matsayin<\/a> 129\/180 a cikin jaddawalin kasashen da ke kare \u2018yan jarida.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cNajeriya na daya daga cikin kasashe masu hadari da wahala wa masu aikin jarida a yankin yammacin Afirka saboda ana yawan sa mu su ido, kai musu hari, tsare su ba tare da kwararan dalila ba kuma a wasu lokutan har kissa.\u201d rahoton ya bayyana.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Gwamnatin Najeriya ta fuskanci zarge-zarge da dama wadanda ke da nasaba da irin manufofin da ke kasancewa kalubale ga tabbatar da lafiya, da \u2018yancin walwalar&nbsp; \u2018yan jarida a kasar.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Irin wadannan dokokin sun hada da dokar aikata miyagin ayyuka a yanar gizo wato <a href=\"https:\/\/www.tvcnews.tv\/2022\/12\/nuj-calls-for-a-review-of-the-cybercrime-act-2015\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Cybercrime Act 2015<\/a>, da dokar da ke hana bata suna <a href=\"https:\/\/www.google.com\/amp\/s\/cpj.org\/2020\/05\/nigerian-journalist-kufre-carter-detained-for-1-month-charged-with-defamation-and-conspiracy\/amp\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Defamation Act<\/a>, da dokar hana ta\u2019addanci da ta hukumar kula da kafofin yada labarai ta NBC code da kuma dokokin NITDA. Duk wadannan dokoki ne da ake amjani da su wajen hukunta kafofin yada labarai da \u2018yan jarida <a href=\"https:\/\/radionigeria.gov.ng\/2023\/04\/01\/nbc-slams-channels-tv-with-n5m-fine\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">a kai-a kai<\/a> .Sai dai kuma dokokin sun sabawa dokokin kada da kasa kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama su dade suna dukar yadda ake amfani da dokokin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Misali, kotun ECOWAS ta yanke <a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/news\/top-news\/520361-rights-violations-ecowas-court-orders-nigerian-government-to-amend-cybercrime-law.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">hukuncin <\/a>&nbsp;cewa <a href=\"https:\/\/prnigeria.com\/2022\/12\/08\/understanding-cybercrime-act\/#:~:text=Authorities%20in%20Government%20have%20attempted,internet%20otherwise%20known%20as%20cyber\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">sashe na 24<\/a> na dokar miyagun laifuka a yanar gizo ba daidai ya ke da sharudan da aka sani ba dan haka bai halata ba kuma yana bukatar kwaskwarima. Shirin SERAP ne ya shigar da <a href=\"https:\/\/www.mfwa.org\/ecowas-court-orders-nigeria-to-align-its-cybercrime-law-with-its-international-obligations\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">karar<\/a>, inda ya bayyana cewa kararraki 12 na zargin cin zarafi, fin karfi, tsarewa, kama mutun ba tare da bin tanacin doka ba, shigar da kara kotu da kullewar da ake wa \u2018yan jarida a jihohin Najeriya da dama daga watan Agustan shekarar 2015 zuwa Nuwamban 2018 duk an dauka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">To sai dai har yanzu ba\u2019 a kai ga aiwatar da tanadin hukuncin na kotun ECOWAS ba, wanda ya sabawa zargin cewa Najeriya na bin sharudan da aka gindaya na tabbatar da kariyar \u2018yan jarida sawu da kafa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun yi kokarin tuntubar Malami mu tambaye shi ko wani rahoton na CPJ ne ya ke ambata, amma bai amsa wayoyinmu ko sakonnin tes din da muka aika masa ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ko da shi ke a watanni hudu na farko na shekarar 2023, kasancewar shi lokacin zabe, binciken farko ya gano cewa akalla \u2018yan jarida 45 aka kai wa hari, kuma harin jiki ne adadin da ya fi yawa a cikin wannan alakaluman.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"12180\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/how-true-is-claim-babies-can-be-grown-in-a-bag-instead-of-womb\/false-5-13\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-5.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-5\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-5.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-5.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-12180\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Sakamakon Bincike: Karya! Bisa bayanan da aka wallafa a sahfin Press Attack Tracker wanda ke daukar bayanai dangane da yawan \u2018yan jaridan da aka ci zarafi, \u2018yan jarida 52 ne aka kai wa hari a Najeriya a shekarar 2022. Bacin haka Malami bai yi amfani da rahoton CPJ daidai ba, bayanin da ya yi ya sabawa sakamakon binciken.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Zargi na biyu (2): \u201cBabu dan jaridar da ya hallaka a Najeriya sakamakon wata matsalar da ke da dangantaka da aikin su\u201d &#8211; Mr Malami.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani <a href=\"https:\/\/www.mfwa.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/state-of-Press-freedom-Nigeria-NUJ.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">rahoto<\/a> na shekarar 2021 wanda Gidauniyar Kafofin Yada Labarai na Afirka ta Yamma (MFWA) ta wallafa tare da hadin giwar kungiyar kwadagon \u2018yan jaridar Najeriya NUJ ya ce an kashe \u2018yan jarida takwas a karkashin gwamnatin Buhari. Sai dai ba duka 8 din suka hallaka yayin da suke gudanar da aikinsu a matsayin \u2018yan jarida ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Rahoton ya bayyana cewa, \u201cMisali a shekarar 2017, \u2018yan harida hudu suka hallaka a lokuta daban-daban, kuma har yanzu babu wani bincike mai sahihanci dangane da dalilin da ya sa suka hallaka, ko ma dan a gano wadanda suka aikata abun ashan. Su hudun masu daukan hotunan bidiyo ne, wadanda suka hada da daya daga gidan talibijn na jihar Anambra Ikechukwu Onubogu; Lawrence Okojie daga NTA a jihar Edo, edita da gidan rediyon Glory FM da ke jihar Bayelsa, Famous Giobaro da wani dan jarida a jihar Ekiti, Abdul Ganiyu Lawal.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cWasu karin \u2018yan jarida hudu su ma sun hallaka a yanayin da har yanzu ba\u2019a riga an tantance ta hanyar bincike mai sahihanci ba. Kissar da aka yi ranar 22 ga watan Yulin 2019 na Precious Owolabi, wani dan jarida da gidan talibijin din Channels a Abuja yayin da ya ke daukan rahoton zanga-zangar kungiyar IMN ta \u2018yan shi\u2019a ya sosa rai sosai.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mutuwar Owolabi ta same shi yana bakin aiki. Alex Ogbu wani edita da jaridar Indeoendent, daya daga cikin rassan jaridar Regent Africa Times shi ma ya <a href=\"https:\/\/regentafricamedia.org\/tears-as-widow-of-slain-journalist-cries-out-demands-killer-of-alex-ogbu\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">gamu da ajalinsa ya na bakin aiki<\/a> lokacin da ya hallaka yayin da yake daukar rahoto na zanga-zanga ranar 21 ga watan Janairu. Duk wadannan sun faru lokacin Buhari na mulki.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A waje guda kuma bayanai daga shafin <a href=\"https:\/\/www.pressattack.africa\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Press Attack Tracker<\/a> sun nuna cewa \u2018yan jarida 610 a Najeriya aka kai wa hari daga shekarar 1985 zuwa yanzu. A cikin wannan adadin, \u2018yan jarida 21 aka kashe a cikin kasar. Dan jaridar da aka fara samun labarin kissansa shi ne Dele Giwa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ana iya samu karin bayani dangane da halin rayuwar da wasu daga cikin iyalan da aka kashe musu \u2018yan uwa yayin da suke aikin jarida <a href=\"https:\/\/dailytrust.com\/families-of-slain-journalists-recount-travail-call-for-justice\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">a wannan shafin<\/a>.&nbsp;<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"12180\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/how-true-is-claim-babies-can-be-grown-in-a-bag-instead-of-womb\/false-5-13\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-5.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-5\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-5.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2022\/08\/FALSE-5.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-12180\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Sakamakon bincike: Zargin cewa babu wani dan jaridan da aka kashe a bakin aikin shi sadda shugaba Muhammadu Buhari ke mulki ba gaskiya ba ne. Akalla lokuta biyu na rubuce yanzu cikin shekaru takwas din da ya shafe yana mulki.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Zargin Malami na cewa Najeriya ce kadai kasar Afirkar da ta bi sharuddan da aka gindaya na kare \u2018yan jarida sawu da kafa a shekarar 2022 , da kuma wai babu dan jaridar da ya hallaka a bakin aiki a wannan lokacin ba gaskiya ba ne. Shafin <a href=\"https:\/\/www.pressattack.africa\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Press Attack Tracker<\/a> da sauran rahotannin kafofin yada labarai sun nuna cewa har yanzu rayuwar \u2018yan jarida na fuskantar hadari.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Cikakken bayani Da \u2018yan makwanni kalilan kafin karshen mulkinsa, shugaba Muhammadu Buhari da jami\u2019an gwamnatinsa, na cigaba da bayyana abubuwan da a ra\u2019ayinsu su ne manyan\u00a0 nassarorin \u00a0\u00a0da gwamnatin ta sa ta\u00a0 yi, yayin da a waje guda kuma su ke kokarin kwaskware wasu daga cikin himmomin da suka yi kafin barin\u00a0 karagar mulkin. Ranar 26 ga watan Afrilun 2023, Majalisar Zartarwar Kasar FEC ta sanar da amincewar da ta yi da ani shirin da wa\u2019adinsa ke tsakanin 2022 da 2026 wanda zai habaka ya kuma kare hakkin dan adam a Najeriya. Da ya ke jawabi a taron, antoni janar kuma ministan shari\u2019ar kasar Abubakar Malami ya ce gwamnatin Buhari ta amince da shirin ne a wani mataki na mutunta shari\u2019r Hukumar Kula da Hakkin Dan Adam Ta Kasa (NHRC) da ma biyan diyyan Nera miliyan 135 ga iyalan wadanda aka kashe ranar 18 ga watan Satumban 2013, a abun da aka fi sani da Apo-Six Killings ko kuma kissar mutane 6 a Apo. \u201cIdan ba ku manta ba, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kafa tarihi da kasancewarta gwamnatin farko a tarihin kasar da ta taba yin la\u2019akari da yunkuri da ma aiwatar da hukuncin da Hukumar Kare Hakkin Bil adama ta yanke,\u201d a cewar ministan. Ministan wanda ya ambaci rahoton Kwamitin Tabbatar da Tsaron \u2018yan Jarida na CPJ ya ce Najeriya ce kadai kasar Afirkar da a shekarar 2022 ta yi la\u2019akari da duka sharuddan da aka gindaya na kare hakkokin \u2018yan jarida. Ya kuma cigaba da zargin cewa babu dan jaridar da ya mutu a Najeriya a karkashin gwamnatin Buhari saboda dalilan da ke da nasaba da aikin shi\/ta. \u201cKuna kuma sane da yadda kwamitin kare \u2018yan jarida wanda kwamitin kasa da kasa ne, ya ce Najeriya ce kadat kasar Afirkar da a bara ta mutunta sharruddan kare hakkokin \u2018yan jarida bisa la\u2019akari da cewa babu dan jaridar da ya mutu a kasar sakamakon wani abun da ke da danganta da aikin su.\u201d Wannan furucin na sa ya zo ne yayin da ake samun zarge-zarge na laifukan da suka shafi takke hakkin dan adam a bangaren gwamnatin Najeriya da ma kuntatawa \u2018yan jarida, ta hanyar hannu su wallafa irin labaran da su ke so su wallafa a kasar. Zargin farko (1): Mr Malami ya ce Najeriya ce kadai kasar Afirkar da a 2022 ta cika tandin sharuddan kare \u2018yan jarida bisa la\u2019akari da rahoton CPJ. Tantancewa A wata sanarwa ranar juma\u2019a CPJ ta karyata zargin Malami, inda a cewar ta ministan bai fassara sakamakon rahotin daidai ba da ya zo amfani da shi wajen gabatar da matsayarsa. Shugabar shirin CPJ na Afirka, Angela Quintal, ta ci Allah wadai da sanarwar ministan inda ita ma ta ce \u201cbinciken CPJ dangane da \u2018yancin \u2018yan jarida a Najeriya, mai nuna shekarun da aka shafe ana cin zarafin masu dauko labarai &#8211; har da kissa \u2013 ya sabawa kalaman Antoni Janar, kuma ministan shari\u2019a Abubakar Malami dangane da halin da \u2018yancin walwalar \u2018yan jarida ke ciki a kasar. Yadda Malami ya yi amfani da binciken abun ban tsori ne da tausayi ganin yadda ake yawan cin zarafin \u2018yan jaridan Najeriya bisa zarginsu da wallafa labaran karya\u201d Kungiyar ta kuma ce ministan ba daidai ya ke amfani da bayanan binciken ba a duk lokutan da ya riga ya yi amfani da su domin yana ikirarin cewa gwamnatin Najeriya na kula da \u2018yan jaridar yadda ya kamata. Bayanai daga binciken da aka samu daga shafin Press Attack Tracker ya tabbatar da abun da \u2018yan jaridan Najeriyar ke fuskanta. Shafin binciken wadda cibiyar \u2018yan jarida na koyon sabbin dabaru da tabbatar da cigaba CIJD ta kirkiro ya nuna cewa \u2018yan jarida 52 ne suka fuskanci hare-hare a shekarar 2022 kuma jami\u2019an gwamnati ne yawancin wadanda suka muzgunawa \u2018yan jaridar. Shafin ya kuma cigaba da bayyana cewa a shekaru hudun da suka gabata (2019 &#8211; 2022) \u2018yan jarida 179 suka fusakanci cin zarafi a Najeriya (wadanda ma aka sani ke nan). Yawancin wadannan hare-haren kuma na zuwa ne da ma\u2019aikatan gwamnati da jami\u2019an tsaro. Hare-hare sun kama daga harin jiki, kamen da babu gaira babu dalili yawancin wadanda ma basu halatta ba, zuwa kurkuku, barazana, sa ido, hana damar shiga wurare ko samun bayanai, shigar da kara kotu dan hana \u2018yan jaridar yin aikinsu yadda ya kamata za hanyar (SLAPPs) kwace kayayyakin aiki, lalata kayayyakin aikin ko kuma ma kissa. A wannan shekarar, kungiyar Reporters Without Borders, ta bai wa Najeria matsayin 129\/180 a cikin jaddawalin kasashen da ke kare \u2018yan jarida. \u201cNajeriya na daya daga cikin kasashe masu hadari da wahala wa masu aikin jarida a yankin yammacin Afirka saboda ana yawan sa mu su ido, kai musu hari, tsare su ba tare da kwararan dalila ba kuma a wasu lokutan har kissa.\u201d rahoton ya bayyana. Gwamnatin Najeriya ta fuskanci zarge-zarge da dama wadanda ke da nasaba da irin manufofin da ke kasancewa kalubale ga tabbatar da lafiya, da \u2018yancin walwalar&nbsp; \u2018yan jarida a kasar.&nbsp; Irin wadannan dokokin sun hada da dokar aikata miyagin ayyuka a yanar gizo wato Cybercrime Act 2015, da dokar da ke hana bata suna Defamation Act, da dokar hana ta\u2019addanci da ta hukumar kula da kafofin yada labarai ta NBC code da kuma dokokin NITDA. Duk wadannan dokoki ne da ake amjani da su wajen hukunta kafofin yada labarai da \u2018yan jarida a kai-a kai .Sai dai kuma dokokin sun sabawa dokokin kada da kasa kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama su dade suna dukar yadda ake amfani da dokokin. Misali, kotun ECOWAS ta yanke hukuncin &nbsp;cewa sashe na 24 na dokar miyagun laifuka a yanar gizo ba daidai ya ke da sharudan da aka sani ba dan haka bai halata ba kuma yana bukatar kwaskwarima. Shirin SERAP ne ya shigar da karar, inda ya bayyana cewa kararraki 12 na zargin cin zarafi, fin karfi, tsarewa, kama mutun ba tare da bin tanacin doka ba, shigar da kara kotu da kullewar da ake wa \u2018yan jarida a jihohin Najeriya da dama daga watan Agustan shekarar 2015 zuwa Nuwamban 2018<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":14660,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"","_twitter_share_type":"","_linkedin_share_type":"","_pinterest_share_type":"","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[1548],"class_list":["post-14703","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-3P9","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":1548,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"benedicta-akpede","display_name":"Benedicta Akpede","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/66159a127e5c24dfe1509291d4c3c81e4d809a6ea3a5c1705171e9e2b3e75444?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2023\/05\/image-2.png?fit=628%2C488&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/14703","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=14703"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/14703\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":14704,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/14703\/revisions\/14704"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/14660"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=14703"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=14703"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=14703"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=14703"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=14703"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}