{"id":17021,"date":"2023-12-19T12:12:07","date_gmt":"2023-12-19T11:12:07","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=17021"},"modified":"2023-12-19T12:12:10","modified_gmt":"2023-12-19T11:12:10","slug":"kwararru-sun-ce-turara-alaurar-da-mata-ke-yi-na-da-hatsarin-gaske-ga-lafiyarsu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/kwararru-sun-ce-turara-alaurar-da-mata-ke-yi-na-da-hatsarin-gaske-ga-lafiyarsu\/","title":{"rendered":"Kwararru sun ce turara al&#8217;aurar da mata ke yi na da hatsarin gaske ga lafiyarsu"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin Facebook <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/permalink.php?story_fbid=pfbid0ZWSMgH1P7UDDxTJvrKkz9KADn8caw8VyCSiBS4PkzbueFLR72UMvgDg1iPr5jSdwl&amp;id=100007220317733\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ya rubuta<\/a> cewa tafasa ganyayyaki masu kamshi tare da gishiri abu ne da kan warkar da cutar fibroids da warin al\u2019aura da ciwon haila.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"16153\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/image-of-the-newly-constructed-roundabout-is-emelogu-aba\/false-4-15\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/FALSE-4.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-16153\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Sakamakon bincike: Karya! Babu hujjojin da aka samu a kimiyance dangane da wannan batun. Likitocin mata kuma ba su goyi bayan turara farjin ba.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-cikakken-bayani\"><strong>Cikakken bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/www.webmd.com\/women\/menstrual-cramps\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Ciwon haila<\/a>&nbsp; ciwo ne na ciki can kusa da marar mace inda ta kan rika ji zafi mai radadin gaske a duk lokacin da lokacin jininta ya zagayo. Irin wannan radadin ya danganta da yanayin jikin macen akwai wadanda sukan zo da sauki babu radadin sossai, akwai wadanda kuma dole sai sun nemi magani kafin su sami sauki.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mutumi mai suna Muhammad a shafin <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/permalink.php?story_fbid=pfbid0ZWSMgH1P7UDDxTJvrKkz9KADn8caw8VyCSiBS4PkzbueFLR72UMvgDg1iPr5jSdwl&amp;id=100007220317733\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Facebook<\/a> ya rubuta cewa mata na iya sa ruwan zafi cikin wani kwano sa\u2019annan su zuba gishiri da wasu ganyayyaki masu kamshi dan rage cutar fibroids, tumbi, cututtukan da a kan dauka a bayi da ma ciwon haila. Daga nan ya kwatanta yadda ake turara farjin, inda ya ke cewa ya kama a yi shi a daidai sadda aka kammala haila. Ya kuma ce kamata ya yi mata su zauna a kan kwanon dan tururin ya shiga sosai.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan da\u2019awar dai an raba shi sau 1,024, an latsa alamar like sau 402 sa\u2019annan kuma an yi tsokaci sosai a karkashin batun tun bayan da aka wallafa shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ganin yadda ya ke da nasaba da kariyar al\u2019umma ne muka yanke shawarar tantancewa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-tantancewa\"><strong>Tantancewa&nbsp;<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mene ne turara farji?<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/my.clevelandclinic.org\/health\/body\/22469-vagina\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Farjin mace<\/a> gaba ce da ke mikewa wadda kuma ke da mahimmanci wajen haihuwa. Ana yawan jita-jitar cewa turara farji ya na taimakawa da radadi, kuma ya kan wanke farjin ya cire duk abubuwan da ba su da kyau har ma a mahaufa, sa\u2019annan kuma ya rage kumburin ciki. To sai dai farjin mace yana iya wanke kan shi ta yadda zai iya daidaita sinadaran da ke wurin yadda ya kamata ba tare da wani tallafi ba. Dan haka duk wani salo kamar turarawa da sauransu ba su da amfani wajen tabbatar da lafiyar farji.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Tabbatar da tsabta a farji ta yadda zai kasance a bushe ba tare da wani mai ko turare ba shi ne kadai hanyar da ya fi dacewa wajen kula da farjin. Dan haka bai kamata mata su rika turara farji ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Turara farji na iya lalata sinadarin da farjin kan fitar dan kare kansa, wanda kuam shi zai iya bai wa kwayoyin cuta damar shiga su janyo ciwo. Bacin haka zai iya sauya yanayin fajin da yadda farjin zai fuskanci hatsarin kamuwa da cututtuka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Fatar wurin na da laushi sosai dan haka ba wuya an raunata shi. Dan haka idan aka sa shi cikin tururi mai zafi, zai iya kona fatar. Wannan ba yana nufin cewa ganyayyakin ba su kawo waraka ba ne, suna iya kawo wa, amma babu wata hujja ta kimiya da ke nuna cewa turara farji na kawo sauyi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-ra-ayin-kwararru\"><strong>Ra\u2019ayin Kwararru<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Gwyneth Paltrow, <a href=\"https:\/\/drjengunter.com\/2015\/01\/27\/gwyneth-paltrow-says-steam-your-vagina-an-obgyn-says-dont\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ta bayyana <\/a>&nbsp;cewa farjin mace (da mahaifa da al\u2019aurar) abubuwa ne da ya kamata a rika wa kallon tanda irin wadanda ke wanke kansu sa kansu. Gabobin da ke sama da wadanda ke taimakawa wajen haihuwa daga kasa na da hanyoyi masu sarkakiya na kula da lafiyarsu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cewarta kuma, akwai yiwuwar cewa \u201ctururin\u201d da ke fitowa daga ganyayyakin da aka jika cikin ruwan zafin na dauke da sinadaran da ke da hadari ga al\u2019aurar mace. Inda ta ce hanyar da za\u2019a iya bi a kula da al\u2019aura ita ce kawowa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Dr Sesan Oluwasola, likitan mata a wata jami\u2019ar koyarwa da ke kudancin Najeriya ya fadawa <a href=\"https:\/\/factcheck.afp.com\/experts-say-sitting-over-mixture-scented-leaves-and-hot-water-dangerous-women\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">sashen binciken gaskiya na kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP<\/a> cewa turara farji abu ne da ba zai taba bayar da shawarar a yi ba. Dr Oluwosola ya ce yin hakan ya kan \u201clalata yanayin sinadaran da ke wurin dan kare farjin\u201d kuma ana iya jin ciwo ko samun konewa. \u201cIdan har wurin da ya kone ya warki zai iya kai ga abun da ake kira&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.nationwidechildrens.org\/conditions\/vaginal-stenosis#:~:text=What%20Is%20Vaginal%20Stenosis%3F,to%20do%20or%20potentially%20painful.\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">vaginal stenosis<\/a> (wato tsukewa),\u201d ya bayyana.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/my.clevelandclinic.org\/staff\/25681-talia-crawford?_gl=1*1xl2gi4*_ga*MTcyMjA0MzE0My4xNzAwNTU0NjA1*_ga_HWJ092SPKP*MTcwMTY4MjcxOC41LjEuMTcwMTY4MjcxOC4wLjAuMA..\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Talia Crawford<\/a>, ita ma likitar mata, <a href=\"https:\/\/health.clevelandclinic.org\/vaginal-steaming\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ta bayar da shawarar cewa<\/a> turara farji na da hatsarin gaske saboda ya na iya jin ciwo.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cIdan har ana so farji ya kasance cikin lafiya dole ya iya ajiye kwayoyi masu kyau,\u201d a cewar Dr Crawford. \u201cDan haka, wankewa da sabulu ko wasu nau\u2019o\u2019in mai masu&nbsp; kamshi na iya haddasa cuta. Amfani da ruwa kawai shi ne ya fi mahimmanci.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ta ce yawancin wadanda ke fama da ciwon al\u2019aura ko wari duk ya kamata su yi magana da likita dan samun bayani dangane da matakan da ya kamata a dauka.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-a-karshe\"><strong>A karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kwararru ko daya ba su goyin bayan turara farji ba saboda ya na da hadari. A maimakon haka, shawararsu ita ce a yi amfani da ruwa kawai a wanke, idan har ana fama da wata cuta ce kuma a tuntubi likita dan samun irin taimakon da ya dace.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya rubuta cewa tafasa ganyayyaki masu kamshi tare da gishiri abu ne da kan warkar da cutar fibroids da warin al\u2019aura da ciwon haila. Sakamakon bincike: Karya! Babu hujjojin da aka samu a kimiyance dangane da wannan batun. Likitocin mata kuma ba su goyi bayan turara farjin ba. Cikakken bayani Ciwon haila&nbsp; ciwo ne na ciki can kusa da marar mace inda ta kan rika ji zafi mai radadin gaske a duk lokacin da lokacin jininta ya zagayo. Irin wannan radadin ya danganta da yanayin jikin macen akwai wadanda sukan zo da sauki babu radadin sossai, akwai wadanda kuma dole sai sun nemi magani kafin su sami sauki. Wani mutumi mai suna Muhammad a shafin Facebook ya rubuta cewa mata na iya sa ruwan zafi cikin wani kwano sa\u2019annan su zuba gishiri da wasu ganyayyaki masu kamshi dan rage cutar fibroids, tumbi, cututtukan da a kan dauka a bayi da ma ciwon haila. Daga nan ya kwatanta yadda ake turara farjin, inda ya ke cewa ya kama a yi shi a daidai sadda aka kammala haila. Ya kuma ce kamata ya yi mata su zauna a kan kwanon dan tururin ya shiga sosai.&nbsp; Wannan da\u2019awar dai an raba shi sau 1,024, an latsa alamar like sau 402 sa\u2019annan kuma an yi tsokaci sosai a karkashin batun tun bayan da aka wallafa shi. Ganin yadda ya ke da nasaba da kariyar al\u2019umma ne muka yanke shawarar tantancewa. Tantancewa&nbsp; Mene ne turara farji? Farjin mace gaba ce da ke mikewa wadda kuma ke da mahimmanci wajen haihuwa. Ana yawan jita-jitar cewa turara farji ya na taimakawa da radadi, kuma ya kan wanke farjin ya cire duk abubuwan da ba su da kyau har ma a mahaufa, sa\u2019annan kuma ya rage kumburin ciki. To sai dai farjin mace yana iya wanke kan shi ta yadda zai iya daidaita sinadaran da ke wurin yadda ya kamata ba tare da wani tallafi ba. Dan haka duk wani salo kamar turarawa da sauransu ba su da amfani wajen tabbatar da lafiyar farji. Tabbatar da tsabta a farji ta yadda zai kasance a bushe ba tare da wani mai ko turare ba shi ne kadai hanyar da ya fi dacewa wajen kula da farjin. Dan haka bai kamata mata su rika turara farji ba. Turara farji na iya lalata sinadarin da farjin kan fitar dan kare kansa, wanda kuam shi zai iya bai wa kwayoyin cuta damar shiga su janyo ciwo. Bacin haka zai iya sauya yanayin fajin da yadda farjin zai fuskanci hatsarin kamuwa da cututtuka. Fatar wurin na da laushi sosai dan haka ba wuya an raunata shi. Dan haka idan aka sa shi cikin tururi mai zafi, zai iya kona fatar. Wannan ba yana nufin cewa ganyayyakin ba su kawo waraka ba ne, suna iya kawo wa, amma babu wata hujja ta kimiya da ke nuna cewa turara farji na kawo sauyi. Ra\u2019ayin Kwararru Gwyneth Paltrow, ta bayyana &nbsp;cewa farjin mace (da mahaifa da al\u2019aurar) abubuwa ne da ya kamata a rika wa kallon tanda irin wadanda ke wanke kansu sa kansu. Gabobin da ke sama da wadanda ke taimakawa wajen haihuwa daga kasa na da hanyoyi masu sarkakiya na kula da lafiyarsu. A cewarta kuma, akwai yiwuwar cewa \u201ctururin\u201d da ke fitowa daga ganyayyakin da aka jika cikin ruwan zafin na dauke da sinadaran da ke da hadari ga al\u2019aurar mace. Inda ta ce hanyar da za\u2019a iya bi a kula da al\u2019aura ita ce kawowa. Dr Sesan Oluwasola, likitan mata a wata jami\u2019ar koyarwa da ke kudancin Najeriya ya fadawa sashen binciken gaskiya na kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa turara farji abu ne da ba zai taba bayar da shawarar a yi ba. Dr Oluwosola ya ce yin hakan ya kan \u201clalata yanayin sinadaran da ke wurin dan kare farjin\u201d kuma ana iya jin ciwo ko samun konewa. \u201cIdan har wurin da ya kone ya warki zai iya kai ga abun da ake kira&nbsp; vaginal stenosis (wato tsukewa),\u201d ya bayyana. Talia Crawford, ita ma likitar mata, ta bayar da shawarar cewa turara farji na da hatsarin gaske saboda ya na iya jin ciwo. \u201cIdan har ana so farji ya kasance cikin lafiya dole ya iya ajiye kwayoyi masu kyau,\u201d a cewar Dr Crawford. \u201cDan haka, wankewa da sabulu ko wasu nau\u2019o\u2019in mai masu&nbsp; kamshi na iya haddasa cuta. Amfani da ruwa kawai shi ne ya fi mahimmanci.\u201d Ta ce yawancin wadanda ke fama da ciwon al\u2019aura ko wari duk ya kamata su yi magana da likita dan samun bayani dangane da matakan da ya kamata a dauka. A karshe Kwararru ko daya ba su goyin bayan turara farji ba saboda ya na da hadari. A maimakon haka, shawararsu ita ce a yi amfani da ruwa kawai a wanke, idan har ana fama da wata cuta ce kuma a tuntubi likita dan samun irin taimakon da ya dace.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":16934,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"","_twitter_share_type":"","_linkedin_share_type":"","_pinterest_share_type":"","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3793],"class_list":["post-17021","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-4qx","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3793,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"lademi-aborisade","display_name":"Lademi Aborisade","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/vaginalsteaming_torontobirthandpostpartumdoula.jpg?fit=1000%2C667&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/17021","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=17021"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/17021\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":17022,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/17021\/revisions\/17022"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/16934"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=17021"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=17021"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=17021"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=17021"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=17021"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}