{"id":18072,"date":"2024-04-02T13:53:37","date_gmt":"2024-04-02T12:53:37","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=18072"},"modified":"2024-04-02T13:53:40","modified_gmt":"2024-04-02T12:53:40","slug":"tsoffin-hotuna-ne-aka-yi-amfani-da-su-a-sunan-sabon-harin-da-aka-kai-wata-alumma-a-jihar-neja","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/tsoffin-hotuna-ne-aka-yi-amfani-da-su-a-sunan-sabon-harin-da-aka-kai-wata-alumma-a-jihar-neja\/","title":{"rendered":"Tsoffin hotuna ne aka yi amfani da su a sunan sabon harin da aka kai wata al\u2019umma a jihar Neja"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Wasu shafukan sada zumunta sun yi amfani da wani hoto wajen kwatanta harin da aka kai al\u2019ummar Madaka da ke jihar Neja.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"136\" height=\"59\" data-attachment-id=\"17961\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/viral-footage-shows-miners-arrested-in-taraba-not-bandits-in-niger-state\/misleading-4-6\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/MISLEADING-4.png?fit=136%2C59&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"136,59\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"MISLEADING-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/MISLEADING-4.png?fit=136%2C59&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/MISLEADING-4.png?resize=136%2C59\" alt=\"\" class=\"wp-image-17961\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#7f7e07\">Hukunci: Hoton da aka yi amfani da shi wajen kwatanta harin da aka kai kwanan nan a kan al\u2019ummar Madaka da ke jihar Neja ba shi da alaka da harin. Wannan bayanin yaudara ce kawai.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-cikakken-bayani\">Cikakken bayani<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ranar 21 ga watan Maris 2024, abun takaici ya faru a al\u2019ummar Madaka wadda ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja. Kamar <a href=\"https:\/\/punchng.com\/traders-feared-killed-as-bandits-invade-niger-market\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">yadda rahotannin<\/a> suka bayyana dangane da harin da \u2018yan bindiga suka kai wata \u2018yar kasuwar da ke kauyen. Wannan harin ya kai ga hallakar wani adadi mai yawa na \u2018yan kasuwa da kwastamomin da ba\u2019a bayyana ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayan wannan harin ne wani hoto ya bayyana ya fara yawo a kafofin sadarwa na soshiyal mediya da zargin cewa abin da ke cikin hoton yanayin da ya kasance ke nan a kauyen bayan da aka kai wannan mummuman harin, har ma da zargin da ke cewa sama da mutane 30 suka hallaka. Hoton ya kuma gwado wasu gawawwakin da aka nade cikin likafani ana kokarin shirin yi musu sujada kafin a bizine su.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da shafin X <a href=\"https:\/\/twitter.com\/IGkagara\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">I.G Kagara<\/a>, wanda ya <a href=\"https:\/\/twitter.com\/IGkagara\/status\/1771103791405842709\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">wallafa<\/a> hotonya ce ana shirya gawawwakin ne dan a rufe su duka a tare a wani wuri da ke daga wajen al\u2019ummar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/twitter.com\/iyksarkinruwa\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Ibrahim Kagara<\/a>, wani shi ma mai amfani da shafin <a href=\"https:\/\/x.com\/iyksarkinruwa\/status\/1771143451137937627?s=48&amp;t=JJ_kU-DCmOvKdMneAYU-tw\">wanda shi ma ya wallafa<\/a> wani hoto makamancin wannan, ya bayyana takaicinsa dangane da wannan jarin inda ya sanar cewa an ma rufe wadanda suka riga mu gidan gaskiyar bisa tanadin addinin musulunci.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mutane kusan 3,000 suka kalli hotunan an kuma sake wallafa su sau 47, tare da tsokace-tsokace da ke bayyana takaici, makoki da addu\u2019o\u2019in Allah ubangiji ya sa sun hutawa. DUBAWA ta gudanar da bincike dan tantance gaskiyar wannan batun.<\/p>\n\n\n\n<h1 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-tantancewa\">Tantancewa<\/h1>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ta yin amfani da manhajar tantance hotuna, DUBAWA ta gano cewa an yi amfani da wannan hoton da ke yawo sau da yawa a shafin Facebook tun shekarar 2021. Bacin haka,&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-table\"><table><tbody><tr><td>Labarin da aka sa a shafinFACEBOOK&nbsp;<\/td><td>Kwanan Wata<\/td><td>MAJIYA<\/td><td>Bayanin da aka yi tare da hoton<\/td><\/tr><tr><td><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/photo\/?fbid=293421279598787&amp;set=a.107282904879293\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Labari<\/a> 1<\/td><td>Maris 16, 2022<\/td><td><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/profile.php?id=100079571354932&amp;__cft__[0]=AZVvTyaaouY6Hp9qFIq401WXzvOyKD7HOtZZCYRXucTCBvhYHwUTZ-5aUXDgGEmW_4qPfghquFo9Lz7Aj97jgz0crJpME-ekEosScY72z2cILlHHpcsNVtJf2J7drKOl3bTaEiNcqQVF4ETw9NlWK6FxDpoLYAxD-F3u2-onM7LvkSjqkUmiJXta7OmaoqMXwRg&amp;__tn__=-]C%2CP-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Nafisa Labarina<\/a><\/td><td>Wadannan gawawwaki ne na mutane 42 wadanda ba su ji ba su gani ba, \u2018yan bindiga suka kashe su da harbin bindiga a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina.<\/td><\/tr><tr><td><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/UmmiRahab0?__cft__[0]=AZUxTOztDQttbap7APsLdVXOw0PZNarAtGo3YjffGI6T4WSrYUR2nsmZgP4VwKRhQpcrUI0mwvUjUA6tMiJblhEeTVS-rIEyJbsarup00DxvG66niq9lhm68VLcfh-Y_YgcCUmp6QgHNAZ0TLRm925jsRP-NQcfqFDO_9Ccs589HKgy2xlYGkJNg4zVeO68DYDI&amp;__tn__=-]C%2CP-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Labari<\/a> 2<\/td><td>Maris 16, 2022<\/td><td><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/UmmiRahab0?__cft__[0]=AZUxTOztDQttbap7APsLdVXOw0PZNarAtGo3YjffGI6T4WSrYUR2nsmZgP4VwKRhQpcrUI0mwvUjUA6tMiJblhEeTVS-rIEyJbsarup00DxvG66niq9lhm68VLcfh-Y_YgcCUmp6QgHNAZ0TLRm925jsRP-NQcfqFDO_9Ccs589HKgy2xlYGkJNg4zVeO68DYDI&amp;__tn__=-]C%2CP-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Ummi Rahab<\/a><\/td><td>Wadannan gawawwaki ne na mutane 42 wadanda ba su ji ba su gani ba, \u2018yan bindiga suka kashe su da harbin bindiga a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina. Bari ubangiji ya jikansu da rahama, Amin, mu kuma idan lokacinmu ya yi Allah sa mu cika da imani. Amin.&nbsp;<\/td><\/tr><tr><td><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/groups\/883208065823008\/user\/100067733514365\/?__cft__[0]=AZVIyab4inqCbY-EPv2Ry_WnBbzXjoUfj9o2S48u9rv9x15JhctgTEotAXWHJQP447IulhUI6nlFvEaGMQ2zZqp3gqJ0e_EnGHJf_mp2NVLmOJ5iR6fWm6G0fCUTWpNhkyAiKvTjQSBdTuc5qWQn-2YPDKry0PkFMQPmUSq42xaeggzSapp75n3ol4wUAGNuQjnKIfbyZtTb9ZgqqNb5WqzTxfeuAPl1AF_7Hm0dKVHZtQ&amp;__tn__=-UC%2CP-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Labari<\/a> 3<\/td><td>Yuli 28, 2022<\/td><td><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/groups\/883208065823008\/user\/100067733514365\/?__cft__[0]=AZVIyab4inqCbY-EPv2Ry_WnBbzXjoUfj9o2S48u9rv9x15JhctgTEotAXWHJQP447IulhUI6nlFvEaGMQ2zZqp3gqJ0e_EnGHJf_mp2NVLmOJ5iR6fWm6G0fCUTWpNhkyAiKvTjQSBdTuc5qWQn-2YPDKry0PkFMQPmUSq42xaeggzSapp75n3ol4wUAGNuQjnKIfbyZtTb9ZgqqNb5WqzTxfeuAPl1AF_7Hm0dKVHZtQ&amp;__tn__=%2Cd-UC%2CP-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Zuwaira Juwairiya<\/a><\/td><td>Wadannan gawawwaki ne na mutane 42 wadanda ba su ji ba su gani ba, \u2018yan bindiga suka kashe su da harbin bindiga a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina. Bari ubangiji ya jikansu da rahama, Amin, mu kuma idan lokacinmu ya yi Allah sa mu cika da imani. Amin. Ka da ku manta ku raba da kungiyoyi akalla biyar dan a yi \u2018yan uwanmu musulmi addu\u2019a.<\/td><\/tr><tr><td><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/ykauramaifata?__cft__[0]=AZW6vjf95cTEX-JCHz0UjcFNRZ7BWpCUERdBbQi0knq0tIKJAe3q1tH18TYTQPrzd21ZsVAVu4WpmVotkF-GeKCMbxSnlHFLz5nNg69tnpoC_-qvi7Xpy2K46ESD4biDQ1H92WjtdRbiyJgF6TvsPOjksEXUgw5CL8wR2AQCEqYN4yPAttja2zUx4yIDwGsQXJg&amp;__tn__=-]C%2CP-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Labari<\/a> 4<\/td><td>Yuni 12, 2021<\/td><td><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/ykauramaifata?__cft__[0]=AZW6vjf95cTEX-JCHz0UjcFNRZ7BWpCUERdBbQi0knq0tIKJAe3q1tH18TYTQPrzd21ZsVAVu4WpmVotkF-GeKCMbxSnlHFLz5nNg69tnpoC_-qvi7Xpy2K46ESD4biDQ1H92WjtdRbiyJgF6TvsPOjksEXUgw5CL8wR2AQCEqYN4yPAttja2zUx4yIDwGsQXJg&amp;__tn__=-]C%2CP-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Yusuf Ridwan Mai Fata<\/strong><\/a><\/td><td><strong>Allah ya ba mu zaman lafiya a Zamfara, Allah ya kawo mana zaman lafiya a Zamfara.<\/strong><\/td><\/tr><\/tbody><\/table><figcaption class=\"wp-element-caption\"><strong><em>Jaddawalin shafuka da labaran da aka wallafa da hoton tun shekarar 202<\/em><\/strong>2<\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Baya ga wadannan wadanda aka wallafa a shafin Facebook, Cibiyar Bincike Mai Zurfi na Kasa da kasa a aikin Jarida (ICIR) ita ma ta <a href=\"https:\/\/www.icirnigeria.org\/police-denies-reports-that-60-persons-were-killed-in-zamfara-attack-says-only-over-30-died\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">wallafa<\/a> wannan hoton a shafinta da taken cewa \u201c\u2018yan sanda sun karyata zargin cewa mutane 60 sun hallaka a harin zamfara, sun ce \u201830 kadai\u2019 suka hallaka.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan rahoton ya fito ne ranar 12 ga watan Yunin 2021, ya kuma yi bayani dalla-dalla kan yadda aka kashe mutane 60 a karamar hukumar Zurmi da ke jihar. Wannan kan shi ya nuna cewa hoton ba shi da wata alaka da abun da ya faru a jihar Neja.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-a-karshe\">A karshe<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hoton da aka yi amfani da shi wajen kwatanta kisar da aka yi a al\u2019ummar Madaka a jihar Neja yaudara ce. Tsoho ne kuma ba shi da wata alaka da abun da ya faru a jihar Neja.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wasu shafukan sada zumunta sun yi amfani da wani hoto wajen kwatanta harin da aka kai al\u2019ummar Madaka da ke jihar Neja. Hukunci: Hoton da aka yi amfani da shi wajen kwatanta harin da aka kai kwanan nan a kan al\u2019ummar Madaka da ke jihar Neja ba shi da alaka da harin. Wannan bayanin yaudara ce kawai. Cikakken bayani Ranar 21 ga watan Maris 2024, abun takaici ya faru a al\u2019ummar Madaka wadda ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja. Kamar yadda rahotannin suka bayyana dangane da harin da \u2018yan bindiga suka kai wata \u2018yar kasuwar da ke kauyen. Wannan harin ya kai ga hallakar wani adadi mai yawa na \u2018yan kasuwa da kwastamomin da ba\u2019a bayyana ba. Bayan wannan harin ne wani hoto ya bayyana ya fara yawo a kafofin sadarwa na soshiyal mediya da zargin cewa abin da ke cikin hoton yanayin da ya kasance ke nan a kauyen bayan da aka kai wannan mummuman harin, har ma da zargin da ke cewa sama da mutane 30 suka hallaka. Hoton ya kuma gwado wasu gawawwakin da aka nade cikin likafani ana kokarin shirin yi musu sujada kafin a bizine su. Wani mai amfani da shafin X I.G Kagara, wanda ya wallafa hotonya ce ana shirya gawawwakin ne dan a rufe su duka a tare a wani wuri da ke daga wajen al\u2019ummar. Ibrahim Kagara, wani shi ma mai amfani da shafin wanda shi ma ya wallafa wani hoto makamancin wannan, ya bayyana takaicinsa dangane da wannan jarin inda ya sanar cewa an ma rufe wadanda suka riga mu gidan gaskiyar bisa tanadin addinin musulunci. Mutane kusan 3,000 suka kalli hotunan an kuma sake wallafa su sau 47, tare da tsokace-tsokace da ke bayyana takaici, makoki da addu\u2019o\u2019in Allah ubangiji ya sa sun hutawa. DUBAWA ta gudanar da bincike dan tantance gaskiyar wannan batun. Tantancewa Ta yin amfani da manhajar tantance hotuna, DUBAWA ta gano cewa an yi amfani da wannan hoton da ke yawo sau da yawa a shafin Facebook tun shekarar 2021. Bacin haka,&nbsp; Labarin da aka sa a shafinFACEBOOK&nbsp; Kwanan Wata MAJIYA Bayanin da aka yi tare da hoton Labari 1 Maris 16, 2022 Nafisa Labarina Wadannan gawawwaki ne na mutane 42 wadanda ba su ji ba su gani ba, \u2018yan bindiga suka kashe su da harbin bindiga a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina. Labari 2 Maris 16, 2022 Ummi Rahab Wadannan gawawwaki ne na mutane 42 wadanda ba su ji ba su gani ba, \u2018yan bindiga suka kashe su da harbin bindiga a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina. Bari ubangiji ya jikansu da rahama, Amin, mu kuma idan lokacinmu ya yi Allah sa mu cika da imani. Amin.&nbsp; Labari 3 Yuli 28, 2022 Zuwaira Juwairiya Wadannan gawawwaki ne na mutane 42 wadanda ba su ji ba su gani ba, \u2018yan bindiga suka kashe su da harbin bindiga a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina. Bari ubangiji ya jikansu da rahama, Amin, mu kuma idan lokacinmu ya yi Allah sa mu cika da imani. Amin. Ka da ku manta ku raba da kungiyoyi akalla biyar dan a yi \u2018yan uwanmu musulmi addu\u2019a. Labari 4 Yuni 12, 2021 Yusuf Ridwan Mai Fata Allah ya ba mu zaman lafiya a Zamfara, Allah ya kawo mana zaman lafiya a Zamfara. Jaddawalin shafuka da labaran da aka wallafa da hoton tun shekarar 2022 Baya ga wadannan wadanda aka wallafa a shafin Facebook, Cibiyar Bincike Mai Zurfi na Kasa da kasa a aikin Jarida (ICIR) ita ma ta wallafa wannan hoton a shafinta da taken cewa \u201c\u2018yan sanda sun karyata zargin cewa mutane 60 sun hallaka a harin zamfara, sun ce \u201830 kadai\u2019 suka hallaka.\u201d Wannan rahoton ya fito ne ranar 12 ga watan Yunin 2021, ya kuma yi bayani dalla-dalla kan yadda aka kashe mutane 60 a karamar hukumar Zurmi da ke jihar. Wannan kan shi ya nuna cewa hoton ba shi da wata alaka da abun da ya faru a jihar Neja. A karshe Hoton da aka yi amfani da shi wajen kwatanta kisar da aka yi a al\u2019ummar Madaka a jihar Neja yaudara ce. Tsoho ne kuma ba shi da wata alaka da abun da ya faru a jihar Neja.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":18013,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"","_twitter_share_type":"","_linkedin_share_type":"","_pinterest_share_type":"","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4087],"class_list":["post-18072","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-4Hu","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4087,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"juliet-buna","display_name":"Juliet Buna","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/pasted-image-0-7.png?fit=1200%2C675&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/18072","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=18072"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/18072\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":18073,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/18072\/revisions\/18073"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/18013"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=18072"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=18072"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=18072"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=18072"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=18072"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}