{"id":18933,"date":"2024-06-02T13:07:49","date_gmt":"2024-06-02T12:07:49","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=18933"},"modified":"2024-06-02T13:07:53","modified_gmt":"2024-06-02T12:07:53","slug":"cin-zarafin-takardun-kudin-naira-fahimtar-banbancin-da-ke-tsakanin-hukunce-hukuncen-da-kotu-ta-yanke-a-shariun-bobrisky-da-na-cubana-chief-priest","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/cin-zarafin-takardun-kudin-naira-fahimtar-banbancin-da-ke-tsakanin-hukunce-hukuncen-da-kotu-ta-yanke-a-shariun-bobrisky-da-na-cubana-chief-priest\/","title":{"rendered":"Cin zarafin takardun kudin naira: Fahimtar banbancin da ke tsakanin hukunce-hukuncen da kotu ta yanke a shari\u2019un Bobrisky da na Cubana Chief Priest.\u00a0"},"content":{"rendered":"\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Ciakken bayani&nbsp;<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wulakanta takardun kudin naira ko da kuwa ta yaya ne babban laifi ne. <a href=\"https:\/\/www.cbn.gov.ng\/OUT\/CIRCULARS\/CSD\/2007\/CBN%20ACT%202007.PDF\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Dokar Babban Bankin Najeriya 2007<\/a>, ta hana liki, takawa, yin zane a kai, saidawa da ma lalata takardun kudin.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bisa bayanan sashe na 21(1) <a href=\"https:\/\/www.cbn.gov.ng\/OUT\/CIRCULARS\/CSD\/2007\/CBN%20ACT%202007.PDF\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Dokar CBN 2007<\/a>, duk wanda aka kama ya na cin zarafin takardun kudin ko kuma la\u2019anta sulalla da takardun zai iya samun hukuncin dauri a kurkuku na tsawon akalla watanni shida ko kuma biyan tara na N50,000 (Kwatankwacin dalar Amurka $37 a lokacin da aka yi wannan rahoton) ko kuma duka biyu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kwannan nan wasu sanannun \u2018yan Najeriya sun yi fama da wata badakalar wulakanta kudaden wadda ta kai su kotu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Daga cikinsu akwai dan daudun Najeriya <a href=\"https:\/\/en.wikipedia.org\/wiki\/Bobrisky\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Idris Okuneye<\/a>, wanda aka fi sani da Bobrisky, da kuma <a href=\"https:\/\/www.thecityceleb.com\/biography\/entrepreneur\/businessman\/cubana-chief-priest-biography-age-net-worth-untold-facts-business-more\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Pascal Okechukwu<\/a>, wanda shi kuma aka fi kirarsa Cubana Chief Priest.\u00a0<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan batun dai ya janyo mahawarori da cece-kuce a yanar gizo. Da yawa sun fito sun bayyana ra\u2019ayoyinsu dangane da dalilan da a ganinsu suka sa aka yanke wa Bobrisky hukuncin dauri na tsawon watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba, yayin da shi kuma Cubana Chief Preist ya sami beli bayan da ya biya tara.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da suke mayar da martani dangane da batun. Mai amfani da shafin X RSDX @<a href=\"https:\/\/x.com\/SDX_Trades?t=IZ03fNNjNRFwIj74HooP1A&amp;s=09\">SDX_Trades<\/a>, <a href=\"https:\/\/twitter.com\/SDX_Trades\/status\/1785980841119686810?t=fZH5-EJq4o8j4epGzZAVxw&amp;s=19\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ya rubuta<\/a>, \u201cAbin da kudin Bobrisky ba zai iya ba, kudin Cubana chief priest zai iya yi. Kurungus.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani shi ma mai amfani da shafin na X Olawale Quadri <a href=\"https:\/\/x.com\/QualityQuadry?t=6T2DVYacWJULZFFeM4DtSw&amp;s=09\">@QualityQuadri<\/a>, <a href=\"https:\/\/twitter.com\/QualityQuadry\/status\/1785953548133376194?t=9XKVpTNff8ryYKXzvyybfw&amp;s=19\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ya wallafa<\/a>, \u201cLabari da dumi-dumi kan cin zarafin takardun kudin Nairar da Cubana Chief Priest ya yi&#x2935;&#xfe0f;EFCC, Cubana Chief Priest za su wayne a wajen kotu, amma Bobrisky zai cigaba da kasancewa a daure duk da cewa laifi daya suka aikata.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Cikin wani <a href=\"https:\/\/twitter.com\/Aramideoflagos\/status\/1780633282951909393?t=wKqUG11_nrTHCKxcCYdU2A&amp;s=19\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">bidiyon<\/a> TikTok da wani mai amfani da shafin X, <a href=\"https:\/\/x.com\/Aramideoflagos?t=URuzPpRr-twWMmj-1GN6Lw&amp;s=09\">@Aramideoflagos<\/a>, ya wallafa, mai magana ya <a href=\"https:\/\/twitter.com\/Aramideoflagos\/status\/1780633282951909393?t=wKqUG11_nrTHCKxcCYdU2A&amp;s=19\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">bayyana<\/a> cewa shi Bobrisky an kai shi gidan mazan ne domin ya masa laifin da ya aikata. Yayin da shi kuma Cubana Chief Preist ya ku amsa laifin ya ce bai amince ya aikata ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mai magana a cikin bidiyon ya bayyana cewa sakamakon shari\u2019ar ya kasance haka ne saboda tasirin salon lauyoyin da masu laifin suka dauka. A cewarsa akwai mahimmanci a amincewa da rashin amincewa da aikata laifi bisa la\u2019akari da maganar da ake yawan yi wai ba\u2019a iya tabbatar da cewa wanda ake zargi ya aikata laifi har sai sadda aka gabatar da hujjojin da suka gamsar da kotu, ba tare da wata shakka ba cewa wanda ake zargin ya aikata laifin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sakamakon wannan mahawarar da kuma irin ra\u2019ayoyin da suka bayyana dangane da sakamakon a shafukan soshiyal mediya, musamman shafin X, DUBAWA ta yanke hukuncin tantance wadannan shari\u2019un da aka yi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Fayyace hukuncin Bobrisky da na Cubana Chief Priest&nbsp;<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ranar 5 ga watan Afrilun 2024 <a href=\"https:\/\/www.efcc.gov.ng\/efcc\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa<\/a> (EFCC) ta gurfanar da Bobrisky a wani kotun jihar Legas tana tuhumarsa da aikata <a href=\"https:\/\/www.efcc.gov.ng\/efcc\/news-and-information\/news-release\/9970-lagos-court-jails-bobrisky-six-months-for-naira-abuse#:~:text=He%20was%20arraigned%20on%20Friday,Hundred%20and%20Ninety%20Thousand%20Naira).\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">laifuka hudu<\/a> na cin zarafin takardun kudin naira da wasu biyu kan zargin wanke haramtattun kudade.&nbsp;&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Daga baya, mai shari\u2019a Abimbola Awogboro na kotun tarayyar da ke Legas ya yanke masa hukuncin <a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/regional\/ssouth-west\/685390-just-in-court-sentences-bobrisky-to-six-months-in-jail.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">dauri<\/a> na tsawon watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Lokacin shari\u2019ar, Bobrisky <a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/regional\/ssouth-west\/685390-just-in-court-sentences-bobrisky-to-six-months-in-jail.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ya amsa<\/a> laifukan da aka tuhumesa da su ya kuma fadawa kotun cewa bai san wai karya doka ya ke yi ba sadda ya aikata lafin, ya kuma kara da ce shi infuluwensa ne a soshiyal mediya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cNi infuluwensa ne a soshiyal mediya kuma ina da mabiya miliyan biyar; a kashin gaskitya ban san cewa na karya doka ba ne. Na so dan an yi mun afuwa dan in sami damar yin amfani da shafi na in ilimantar da mutane kan wulakanta takardun kudin Naira,\u201d Bobrisky ya bayyana sadda ya ke neman afuwa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;Sai dai, Alkalin, Justice Awogboro ya sake tunatar da Bobrisky cewa bai kamata ya nemi uzuri kan rashin sanin dokar ba, abin da shi kansa Bobriskyn ya amince da shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mai shari\u2019ar ya bayyana a cikin hukuncinsa cewa \u201cWulakanta takardun kudin Naira ya zama ruwan dare, abin da ke cigaba da lalata kimar kasar a idanun duniya. Ya isa haka nan, ya kamata mutane su daina lalata kudin, kuma wannan hukuncin nasa zai zama abin zai hana na baya karya dokar.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A wani yanayin mai kama da wannam, ranar 17 ga watan Afrilu, hukumar EFCC <a href=\"https:\/\/www.efcc.gov.ng\/efcc\/news-and-information\/news-release\/9980-efcc-arraigns-cubana-chief-priest-for-alleged-naira-abuse\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ta gurfanar<\/a> da Cubana Chief Priest <a href=\"https:\/\/www.efcc.gov.ng\/efcc\/news-and-information\/news-release\/9980-efcc-arraigns-cubana-chief-priest-for-alleged-naira-abuse\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">kan laifuka uku<\/a> na wulakanta takardun kudin Nairar a gaban mai shari\u2019a Justice&nbsp; Kehinde Ogundare a kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sadda aka gurfanar da shi Cubana Chief Priest <a href=\"https:\/\/www.google.com\/amp\/s\/www.channelstv.com\/2024\/05\/02\/naira-abuse-cubana-chief-priest-explores-out-of-court-settlement-with-efcc\/amp\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">bai amsa ko daya daga cikin laifukan <\/a>&nbsp;da aka tuhume sa da shi ba, sa\u2019annan aka ba shi damar biyan belin miliyan 10 na naira, da mutane biyu wadanda za su tsaya mi shi. Daga nan sai aka dage sauraron shari\u2019ar zuwa biyu ga watan Mayun 20245, dan jin ta bakinsa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da suka koma kotu ranar 2 ga watan Mayun, wakilin Cubana chief priest sai ya fadawa mai shari\u2019ar da ke sauraron karar cewa chief preist din ya <a href=\"https:\/\/www.google.com\/amp\/s\/www.channelstv.com\/2024\/05\/02\/naira-abuse-cubana-chief-priest-explores-out-of-court-settlement-with-efcc\/amp\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">bukaci<\/a> da a daidata a wajen kotu. Wannan na nufin cewa akwai bukatar neman janye karar da aka fara shigarwa kafin a nemi yin sulhu.&nbsp;&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A waje guda kuma yayin da ya ke cika wa\u2019adinsa a kurkuku Bobrisky shi ma <a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/news\/more-news\/688305-naira-abuse-bobrisky-appeals-against-sentence.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ya tura wasikar<\/a> daukaka kara wanda ke kalubalantar wa\u2019adin watanni shidan da kotun tarayyar da ke Legas ta yanke masa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Ra\u2019ayin masanin shari\u2019a<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yayin da ya ke fayyace shari\u2019un biyu, wani masanin shari\u2019a, Ibrahim Abiola ya ce amsa laifi ba wai yana nufin yanke hukunci ba ne kuma idan har ana sa a fahimci komai dole a duba batutuwna da ke kewaye da shari\u2019ar Bobrisky daban da na Cubana Chief Preist.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya ce, \u201cA duk sadda mutun ya amsa laifi, ba nan da nan ne kotu za ta yanke hukunci ba. Dole sai masu shigar da kara sun bayar da hujjoji masu gamsarwa ba tare da barin wani hurumin shakka ba kafin a yanke hukunci, kuma abin da ya faru ke nan a shari\u2019ar Bobrisky.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kara da cewa, sai dai a shari\u2019ar Cubana Chief Priest, dole sai an yi la\u2019akari da <a href=\"https:\/\/www.efcc.gov.ng\/efcc\/images\/pdfs\/establishment_act_2004.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">sashi na 14 (2) na dokar EFCC<\/a>. Wannan sashin ya bai wa hukumar ikon kara yawan laifukan ta kuma karbi daidai yawan kudin da ta ga ya dace ta karba, ba tare da ya wuce yawan kudin da aka tanadar a matsayin kudin da ya kamata a karba wajen wanda ya aikata irin wannan laifin ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A nan ba shakka hukumar ta yanke shawarar amfani da tanadin sashi na 14(2) dan haka bai kamata a kwatanta wannan da na Bobrisky ba, tunda shi kai tsaye ya amsa laifin dai nemi yin amfani da damar daidaita komai a wajen kotu ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sashi na 14 (2) na dokar EFCC na cewa \u201cbisa la\u2019akari da tanadin sashi na 174 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (Wanda ke da alaka da ikon Antoni janar na kasa ta girkawa, cigabawa, da dakatar da shari\u2019ar miyagun laifukan wani a kowani irin kotun kasar), hukumar ta na iya hada duk laifukan da za\u2019a iya hukuntawa a karkashin dokar ta karbi yawan kudin da ta ga ya dace a karba a madadin hukunci,&nbsp; ba tare da gota ainihin yawan kudin da aka kiyassa a matsayin darajar kudin da ya kamata mai laifin ya biya idan da an same shi da laifi.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai ba kowani lokaci ba ne za\u2019a iya amfani da sa <a href=\"https:\/\/www.efcc.gov.ng\/efcc\/images\/pdfs\/establishment_act_2004.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">sashe na 14 (2) na dokar EFCC<\/a>, kuma sakamakon wannan shi ne shari\u2019a sosai kamar yadda aka gani a na Biobrisky.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya na da mahimmanci a san cewa sakamakon kowace shari\u2019a na da dangantaka da yadda masu shigar da kara da lauyoyin wadanda abin ya shafa suka gabatar da hujjojinsu a gaban kotu. Wannan kuma ya zama abun la\u2019akari da shi a laifuka irin wannan da za su faru nan gaba. Yayin da sakamakon shari\u2019un ke nuna irin sarkakiyar da ke tattare da yanayin gudanar da shari\u2019a da laifukan fararen hula, tilas ne mutane su san irin tasirin da maganganunsu za su iya yi yayin da shari\u2019arsu ke kotu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Wannan bincike an yi shine a shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 \u00a0 karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari Fellowship da hadin gwiwar The Informant247,\u00a0 a kokari na fito da \u201cgaskiya\u201d a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin Najeriya.<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ciakken bayani&nbsp; Wulakanta takardun kudin naira ko da kuwa ta yaya ne babban laifi ne. Dokar Babban Bankin Najeriya 2007, ta hana liki, takawa, yin zane a kai, saidawa da ma lalata takardun kudin.&nbsp; Bisa bayanan sashe na 21(1) Dokar CBN 2007, duk wanda aka kama ya na cin zarafin takardun kudin ko kuma la\u2019anta sulalla da takardun zai iya samun hukuncin dauri a kurkuku na tsawon akalla watanni shida ko kuma biyan tara na N50,000 (Kwatankwacin dalar Amurka $37 a lokacin da aka yi wannan rahoton) ko kuma duka biyu. Kwannan nan wasu sanannun \u2018yan Najeriya sun yi fama da wata badakalar wulakanta kudaden wadda ta kai su kotu. Daga cikinsu akwai dan daudun Najeriya Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky, da kuma Pascal Okechukwu, wanda shi kuma aka fi kirarsa Cubana Chief Priest.\u00a0 Wannan batun dai ya janyo mahawarori da cece-kuce a yanar gizo. Da yawa sun fito sun bayyana ra\u2019ayoyinsu dangane da dalilan da a ganinsu suka sa aka yanke wa Bobrisky hukuncin dauri na tsawon watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba, yayin da shi kuma Cubana Chief Preist ya sami beli bayan da ya biya tara. Da suke mayar da martani dangane da batun. Mai amfani da shafin X RSDX @SDX_Trades, ya rubuta, \u201cAbin da kudin Bobrisky ba zai iya ba, kudin Cubana chief priest zai iya yi. Kurungus.\u201d Wani shi ma mai amfani da shafin na X Olawale Quadri @QualityQuadri, ya wallafa, \u201cLabari da dumi-dumi kan cin zarafin takardun kudin Nairar da Cubana Chief Priest ya yi&#x2935;&#xfe0f;EFCC, Cubana Chief Priest za su wayne a wajen kotu, amma Bobrisky zai cigaba da kasancewa a daure duk da cewa laifi daya suka aikata.\u201d Cikin wani bidiyon TikTok da wani mai amfani da shafin X, @Aramideoflagos, ya wallafa, mai magana ya bayyana cewa shi Bobrisky an kai shi gidan mazan ne domin ya masa laifin da ya aikata. Yayin da shi kuma Cubana Chief Preist ya ku amsa laifin ya ce bai amince ya aikata ba. Mai magana a cikin bidiyon ya bayyana cewa sakamakon shari\u2019ar ya kasance haka ne saboda tasirin salon lauyoyin da masu laifin suka dauka. A cewarsa akwai mahimmanci a amincewa da rashin amincewa da aikata laifi bisa la\u2019akari da maganar da ake yawan yi wai ba\u2019a iya tabbatar da cewa wanda ake zargi ya aikata laifi har sai sadda aka gabatar da hujjojin da suka gamsar da kotu, ba tare da wata shakka ba cewa wanda ake zargin ya aikata laifin. Sakamakon wannan mahawarar da kuma irin ra\u2019ayoyin da suka bayyana dangane da sakamakon a shafukan soshiyal mediya, musamman shafin X, DUBAWA ta yanke hukuncin tantance wadannan shari\u2019un da aka yi. Fayyace hukuncin Bobrisky da na Cubana Chief Priest&nbsp; Ranar 5 ga watan Afrilun 2024 Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta gurfanar da Bobrisky a wani kotun jihar Legas tana tuhumarsa da aikata laifuka hudu na cin zarafin takardun kudin naira da wasu biyu kan zargin wanke haramtattun kudade.&nbsp;&nbsp; Daga baya, mai shari\u2019a Abimbola Awogboro na kotun tarayyar da ke Legas ya yanke masa hukuncin dauri na tsawon watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba. Lokacin shari\u2019ar, Bobrisky ya amsa laifukan da aka tuhumesa da su ya kuma fadawa kotun cewa bai san wai karya doka ya ke yi ba sadda ya aikata lafin, ya kuma kara da ce shi infuluwensa ne a soshiyal mediya. \u201cNi infuluwensa ne a soshiyal mediya kuma ina da mabiya miliyan biyar; a kashin gaskitya ban san cewa na karya doka ba ne. Na so dan an yi mun afuwa dan in sami damar yin amfani da shafi na in ilimantar da mutane kan wulakanta takardun kudin Naira,\u201d Bobrisky ya bayyana sadda ya ke neman afuwa. &nbsp;Sai dai, Alkalin, Justice Awogboro ya sake tunatar da Bobrisky cewa bai kamata ya nemi uzuri kan rashin sanin dokar ba, abin da shi kansa Bobriskyn ya amince da shi. Mai shari\u2019ar ya bayyana a cikin hukuncinsa cewa \u201cWulakanta takardun kudin Naira ya zama ruwan dare, abin da ke cigaba da lalata kimar kasar a idanun duniya. Ya isa haka nan, ya kamata mutane su daina lalata kudin, kuma wannan hukuncin nasa zai zama abin zai hana na baya karya dokar.\u201d A wani yanayin mai kama da wannam, ranar 17 ga watan Afrilu, hukumar EFCC ta gurfanar da Cubana Chief Priest kan laifuka uku na wulakanta takardun kudin Nairar a gaban mai shari\u2019a Justice&nbsp; Kehinde Ogundare a kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas. Sadda aka gurfanar da shi Cubana Chief Priest bai amsa ko daya daga cikin laifukan &nbsp;da aka tuhume sa da shi ba, sa\u2019annan aka ba shi damar biyan belin miliyan 10 na naira, da mutane biyu wadanda za su tsaya mi shi. Daga nan sai aka dage sauraron shari\u2019ar zuwa biyu ga watan Mayun 20245, dan jin ta bakinsa. Da suka koma kotu ranar 2 ga watan Mayun, wakilin Cubana chief priest sai ya fadawa mai shari\u2019ar da ke sauraron karar cewa chief preist din ya bukaci da a daidata a wajen kotu. Wannan na nufin cewa akwai bukatar neman janye karar da aka fara shigarwa kafin a nemi yin sulhu.&nbsp;&nbsp; A waje guda kuma yayin da ya ke cika wa\u2019adinsa a kurkuku Bobrisky shi ma ya tura wasikar daukaka kara wanda ke kalubalantar wa\u2019adin watanni shidan da kotun tarayyar da ke Legas ta yanke masa. Ra\u2019ayin masanin shari\u2019a Yayin da ya ke fayyace shari\u2019un biyu, wani masanin shari\u2019a, Ibrahim Abiola ya ce amsa laifi ba wai yana nufin yanke hukunci ba ne kuma idan har ana sa a fahimci komai dole a duba batutuwna da ke kewaye da shari\u2019ar Bobrisky daban da na Cubana Chief Preist. Ya ce, \u201cA duk sadda mutun ya amsa laifi, ba nan da nan ne kotu za ta yanke hukunci ba. Dole sai masu shigar da kara sun bayar da hujjoji masu gamsarwa ba tare da barin wani hurumin shakka ba kafin a yanke hukunci, kuma abin da ya faru ke nan a shari\u2019ar Bobrisky. Ya<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":18841,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4073],"class_list":["post-18933","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-4Vn","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4073,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"yemi-sodeeq","display_name":"Yemi Sodeeq","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/bobrisky-and-cubana.jpg?fit=720%2C486&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/18933","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=18933"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/18933\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":18934,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/18933\/revisions\/18934"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/18841"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=18933"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=18933"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=18933"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=18933"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=18933"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}