{"id":18937,"date":"2024-06-02T14:24:10","date_gmt":"2024-06-02T13:24:10","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=18937"},"modified":"2024-06-02T14:27:35","modified_gmt":"2024-06-02T13:27:35","slug":"duk-abubuwan-da-ya-kamata-a-sani-dangane-da-taken-kasar-da-aka-fara-amfani-da-shi-yanzu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/duk-abubuwan-da-ya-kamata-a-sani-dangane-da-taken-kasar-da-aka-fara-amfani-da-shi-yanzu\/","title":{"rendered":"Duk abubuwan da ya kamata a sani dangane da taken kasar da aka fara amfani da shi yanzu"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A \u2019yan makwannin da suka gabaci 29 ga watan Mayun 2024, ba\u2019a ga jama\u2019a suna dokin zagayowar bukukuwan da ke karrama Ranar Dimokiradiyya ta \u2018yan Najeriyar kamar yadda aka saba ba. Wannan hakan ne saboda <a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/news\/headlines\/271397-breaking-buhari-declares-june-12-democracy-day-to-honour-abiola.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">an sauya ranar<\/a> gudanar da bukin a karkashin gwamnatun Muhammadu Buhari daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni dan martaba M.K.O Abiola wanda ya kamata a ce ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi ranar 12 ga watan Yunin 1993. Haka nan kuma a maimakon dokin, a wannan karon an yi ta jita-jitar da aka yi ta yayatawa na cewa za\u2019a sauya taken kasa ne zuwa tsohuwar da aka fara da ita \u201cNigeria, We Hail Thee\u201d ta gamu da shakku da mamaki<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2018Yan Najeriya da dama sun gaza fahimtar yadda wannan bangaren kasar mai cike da tarihi zai kasance abin da za\u2019a sauya a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin da suka fi wannan mahimmanci, kamar yanayin tabarbarewar tattalin arziki da zamantakewar kasar. To sai dai tun kafin a kai ko\u2019ina suka lura cewa fa babu gudu, babu ja da baya domin da wayewar garin 29 ga watan Mayu kowa ya tashi ya gamu da abin da ke zahiri: Jita-jitar gaskiya ne. Shugaban kasa mai ci, Bola Tinubu <a href=\"https:\/\/punchng.com\/breaking-tinubu-signs-bill-returning-old-national-anthem-into-law\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ya sa hannu<\/a> kan kudurin dokar taken kasa na 2024 kuma ya zama doka. Sobada haka taken Najeriya ta koma wadda aka rika rairawa kafin \u2018yancin kai a hukumance.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A bayam taken Najeriya ya fara ne da \u201cArise, O Compatriots,\u201d kuma a shekarar 1978 aka fara amfani da shi \u2013 taken mai shkaru 46 yanzu, mutane biyar suka rubuta wadanda suka hada da John A. Ilechukwu, Eme Etim Akpan, B.A. Ogunnaike, Sotu Omoigui, da P.O. Aderibigbe\u2013 ya kuma kasance kira ne ga hadin kan kasa, kishin kasa da aiki tare wajen gina babbar kasa bayan bala\u2019in shekaru uku na yakin basasar da aka kammala a shekarar 1970. Kafin \u201cArise, O compatriots,\u201d taken da ake amfani da shi, \u201cNigeria, We Hail Thee,\u201d shi ne aka yi amfani da shi daga lokacin da aka sami \u2018yancin kai a shekarar 1960 har zuw ashekarar 1978. Wannan taken wanda ma\u2019aikatan mulkin mallakar Burtaniya,&nbsp; Lillian Jean Williams da Frances Berda suka tsara suka kuma rubuta ya nuna alfahari da kyakyawar fatan kasar a shekarunta na farko bayan&nbsp; ta sami \u2018yancin kai.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Kalaman taken<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ga kalaman da ake fada a taken da ake amfani da shi yanzu,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;\u201cNigeria, We Hail Thee:\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Nigeria we hail thee,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Our own dear native land,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Though tribe and tongue may differ,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">In brotherhood we stand,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Nigerians all are proud to serve<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Our sovereign Motherland.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Our flag shall be a symbol<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">That truth and justice reign,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">In peace or battle honoured,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">And this we count as gain,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">To hand on to our children<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A banner without stain.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">O God of all creation,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Grant this our one request,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Help us to build a nation<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Where no man is oppressed,<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">And so with peace and plenty<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Nigeria may be blessed.\u201d<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Martanonin Jama\u2019a<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A watan Mayu aka fara yunkurin sauya taken sadda aka fara gabatar da kudurin dokar kafin nan da nan ya sami amincewar duka majalisun tarayyar guda biyu. \u2018Yan majalisar sun jaddada mahimmancin sake saita alkiblar kasar da tarihinta tare da al\u2019adunta na asali. Ya wuce karatu na farko da na biyu duk a ranar 23 ga watan Mayun 2024, bayan da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya kira da a yi zabe a kan shi kafin ya tura shi zuwa kwamitocin Shari\u2019a, Hakkin dan Adam, Al\u2019amuran Sharia da harkokin cikin gida dan daukar sauran matakan da doka ta tanadar. To sai dai, amincewar da shugaban kasa ya yi da dokar \u2013 wuni guda bayan da ta wuce karatu na uku a Majalisar Dokoki \u2014 ya tayar da damuwa ganin cewa ko kundin tsarin mulki ta tanadi da a jira har zuwa kwanaki 30 bayan dokar ta wuce karatu na uku kafin a bayar da amincewa na karshe.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Tsakanin \u2018yan majalisar,&nbsp; sun nuna cewa tun da dadewa ya kamata a yi wannan sauyin inda wadansun su ke <a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/news\/headlines\/696962-bill-to-change-nigerias-national-anthem-passes-second-reading-at-senate.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">da&#8217;awar cewa<\/a> taken mai shekaru 46 bai bayyana irin hadin kan da ake bukata dan tabbatar da daidaito a irin rikice-rikicen da ake fama da su masu tayar da hankali. Sauya taken ke nan abu ne da ake gani sai sake jaddada hadin kai da asalin da ke tabbatar da \u2018yan kasa a matsayin tsintsiya madaurinki daya kuma abin alfahari.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">To sai dai da yawa na nuna damuwa dangane da yawan kudin da za\u2019a kashe wajen aiwatar da wannan sauyin, inda suke mahawarar cewa gara a yi amfani da wannan kudin a wani wurin da aka fi bukata a wannan lokacin da kusan kowa ke cikin wani hali na ha\u2019ula\u2019i. Daya dagani cikin mahimman kwatancen da ake mi shi a soshiyal mediya shi ne rashin sanin ya kamatan gwamnati.&nbsp; Kusan <a href=\"https:\/\/guardian.ng\/news\/ezekwesili-ongbinde-others-criticise-tinubu-over-return-to-old-national-anthem\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">wannan ne<\/a> ra\u2019ayin da mutane da yawa suka bayyana, har da manyan \u2018yan Najeriya irin su Reno Omokri da Oby Ezekwesili. KO da shi ke al\u2019ummar kasa da kasa ta yi tsit ba ta ce komai ba tun bayan wucewar kudurin dokar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Gwamnatin ta kaddamar da gangamin da zai koya wa \u2018yan kasa kalaman da yadda ake raira taken da ma mahimmancin shi dan ganin cewa mutane sun amince da shi. Shugaban Hukumar Wayar da Kan \u2018Yan Kasa Malam Lanre Issa-Onillu ya umurci duka ma\u2019aikatan hukumarsa da ke kananan hukumomin kasar 774 da su bayar da kai wajen haddace sabon taken kafin litinin uku ga watan Yunin 2024 kamar yadda wata <a href=\"https:\/\/www.noa.gov.ng\/new-national-anthem-noa-dg-directs-community-officers-to-learn-new-anthem-within-72-hours\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">sanarwa mai sa hannun <\/a>&nbsp;mataimakin darektan da ke hulda da \u2018yan jarida, Paul Odeniyi, ya bayyana, a matsayin wani bangare na yunkurin ganin sabon taken ya shiga harkokin yau da kullun na \u2018yan kasa. Daga yanzu za\u2019a fara amfani da wannan taken lokacin duk wasu shirye-shirye da bukuwan kasa, wadanda suka hada da wasanni da kuma ayyukan kasa da kasa bayar da shugaba Tinubu ya kai <a href=\"https:\/\/www.youtube.com\/watch?v=5eRuNY1cLZQ\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ziyara<\/a> majalisar dokoki ranar 29 ga watan Mayu, inda aka raira sabon taken.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shawarar sauya taken Najeriya ya bi duka dokokin da aka tanadar, duk da cewa an yi gaggawa wajen fara amfani da shi, wato tun ma kafin a sami hadin kan kasa da irin fadakarwar da ya kamata, yiwuwar raba kai sakamakon kalaman da ke cikin taken ya yi haifar da rashin gamsuwa da shakku tsakanin \u2018yan kasa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A \u2019yan makwannin da suka gabaci 29 ga watan Mayun 2024, ba\u2019a ga jama\u2019a suna dokin zagayowar bukukuwan da ke karrama Ranar Dimokiradiyya ta \u2018yan Najeriyar kamar yadda aka saba ba. Wannan hakan ne saboda an sauya ranar gudanar da bukin a karkashin gwamnatun Muhammadu Buhari daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni dan martaba M.K.O Abiola wanda ya kamata a ce ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi ranar 12 ga watan Yunin 1993. Haka nan kuma a maimakon dokin, a wannan karon an yi ta jita-jitar da aka yi ta yayatawa na cewa za\u2019a sauya taken kasa ne zuwa tsohuwar da aka fara da ita \u201cNigeria, We Hail Thee\u201d ta gamu da shakku da mamaki \u2018Yan Najeriya da dama sun gaza fahimtar yadda wannan bangaren kasar mai cike da tarihi zai kasance abin da za\u2019a sauya a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin da suka fi wannan mahimmanci, kamar yanayin tabarbarewar tattalin arziki da zamantakewar kasar. To sai dai tun kafin a kai ko\u2019ina suka lura cewa fa babu gudu, babu ja da baya domin da wayewar garin 29 ga watan Mayu kowa ya tashi ya gamu da abin da ke zahiri: Jita-jitar gaskiya ne. Shugaban kasa mai ci, Bola Tinubu ya sa hannu kan kudurin dokar taken kasa na 2024 kuma ya zama doka. Sobada haka taken Najeriya ta koma wadda aka rika rairawa kafin \u2018yancin kai a hukumance.&nbsp; A bayam taken Najeriya ya fara ne da \u201cArise, O Compatriots,\u201d kuma a shekarar 1978 aka fara amfani da shi \u2013 taken mai shkaru 46 yanzu, mutane biyar suka rubuta wadanda suka hada da John A. Ilechukwu, Eme Etim Akpan, B.A. Ogunnaike, Sotu Omoigui, da P.O. Aderibigbe\u2013 ya kuma kasance kira ne ga hadin kan kasa, kishin kasa da aiki tare wajen gina babbar kasa bayan bala\u2019in shekaru uku na yakin basasar da aka kammala a shekarar 1970. Kafin \u201cArise, O compatriots,\u201d taken da ake amfani da shi, \u201cNigeria, We Hail Thee,\u201d shi ne aka yi amfani da shi daga lokacin da aka sami \u2018yancin kai a shekarar 1960 har zuw ashekarar 1978. Wannan taken wanda ma\u2019aikatan mulkin mallakar Burtaniya,&nbsp; Lillian Jean Williams da Frances Berda suka tsara suka kuma rubuta ya nuna alfahari da kyakyawar fatan kasar a shekarunta na farko bayan&nbsp; ta sami \u2018yancin kai. Kalaman taken Ga kalaman da ake fada a taken da ake amfani da shi yanzu, &nbsp;\u201cNigeria, We Hail Thee:\u201d Nigeria we hail thee, Our own dear native land, Though tribe and tongue may differ, In brotherhood we stand, Nigerians all are proud to serve Our sovereign Motherland. Our flag shall be a symbol That truth and justice reign, In peace or battle honoured, And this we count as gain, To hand on to our children A banner without stain. O God of all creation, Grant this our one request, Help us to build a nation Where no man is oppressed, And so with peace and plenty Nigeria may be blessed.\u201d Martanonin Jama\u2019a A watan Mayu aka fara yunkurin sauya taken sadda aka fara gabatar da kudurin dokar kafin nan da nan ya sami amincewar duka majalisun tarayyar guda biyu. \u2018Yan majalisar sun jaddada mahimmancin sake saita alkiblar kasar da tarihinta tare da al\u2019adunta na asali. Ya wuce karatu na farko da na biyu duk a ranar 23 ga watan Mayun 2024, bayan da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya kira da a yi zabe a kan shi kafin ya tura shi zuwa kwamitocin Shari\u2019a, Hakkin dan Adam, Al\u2019amuran Sharia da harkokin cikin gida dan daukar sauran matakan da doka ta tanadar. To sai dai, amincewar da shugaban kasa ya yi da dokar \u2013 wuni guda bayan da ta wuce karatu na uku a Majalisar Dokoki \u2014 ya tayar da damuwa ganin cewa ko kundin tsarin mulki ta tanadi da a jira har zuwa kwanaki 30 bayan dokar ta wuce karatu na uku kafin a bayar da amincewa na karshe. Tsakanin \u2018yan majalisar,&nbsp; sun nuna cewa tun da dadewa ya kamata a yi wannan sauyin inda wadansun su ke da&#8217;awar cewa taken mai shekaru 46 bai bayyana irin hadin kan da ake bukata dan tabbatar da daidaito a irin rikice-rikicen da ake fama da su masu tayar da hankali. Sauya taken ke nan abu ne da ake gani sai sake jaddada hadin kai da asalin da ke tabbatar da \u2018yan kasa a matsayin tsintsiya madaurinki daya kuma abin alfahari. To sai dai da yawa na nuna damuwa dangane da yawan kudin da za\u2019a kashe wajen aiwatar da wannan sauyin, inda suke mahawarar cewa gara a yi amfani da wannan kudin a wani wurin da aka fi bukata a wannan lokacin da kusan kowa ke cikin wani hali na ha\u2019ula\u2019i. Daya dagani cikin mahimman kwatancen da ake mi shi a soshiyal mediya shi ne rashin sanin ya kamatan gwamnati.&nbsp; Kusan wannan ne ra\u2019ayin da mutane da yawa suka bayyana, har da manyan \u2018yan Najeriya irin su Reno Omokri da Oby Ezekwesili. KO da shi ke al\u2019ummar kasa da kasa ta yi tsit ba ta ce komai ba tun bayan wucewar kudurin dokar. Gwamnatin ta kaddamar da gangamin da zai koya wa \u2018yan kasa kalaman da yadda ake raira taken da ma mahimmancin shi dan ganin cewa mutane sun amince da shi. Shugaban Hukumar Wayar da Kan \u2018Yan Kasa Malam Lanre Issa-Onillu ya umurci duka ma\u2019aikatan hukumarsa da ke kananan hukumomin kasar 774 da su bayar da kai wajen haddace sabon taken kafin litinin uku ga watan Yunin 2024 kamar yadda wata sanarwa mai sa hannun &nbsp;mataimakin darektan da ke hulda da \u2018yan jarida, Paul Odeniyi, ya bayyana, a matsayin wani bangare na yunkurin ganin sabon taken ya shiga harkokin yau da kullun na \u2018yan kasa. Daga yanzu za\u2019a fara amfani da wannan taken lokacin duk wasu shirye-shirye da bukuwan kasa, wadanda suka hada da wasanni da kuma ayyukan kasa da kasa bayar da shugaba Tinubu ya kai ziyara majalisar dokoki ranar 29 ga watan Mayu, inda aka raira sabon taken.&nbsp; A karshe Shawarar sauya<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":18909,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3263],"class_list":["post-18937","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-4Vr","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3263,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"phillip-anjorin","display_name":"Phillip Anjorin","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/98daaf5d9d7a2c5cd4ce1c417532d1cfa2ca293247710cf46a925146cc2e90e1?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Tinubu-Ahmed.png?fit=1024%2C576&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/18937","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=18937"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/18937\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":18940,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/18937\/revisions\/18940"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/18909"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=18937"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=18937"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=18937"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=18937"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=18937"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}