{"id":19205,"date":"2024-06-28T05:04:20","date_gmt":"2024-06-28T04:04:20","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=19205"},"modified":"2024-06-28T05:04:24","modified_gmt":"2024-06-28T04:04:24","slug":"ba-haka-ba-ne-nysc-ba-ta-shirin-sauya-wa-masu-yi-wa-kasa-hidima-rigar-inifam","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/ba-haka-ba-ne-nysc-ba-ta-shirin-sauya-wa-masu-yi-wa-kasa-hidima-rigar-inifam\/","title":{"rendered":"Ba haka ba ne! NYSC ba ta shirin sauya wa masu yi wa kasa hidima rigar inifam"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: wani mai amfani da shafin Facebook na <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/kbTgo5uWVJWezWo4\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">da&#8217;awar<\/a> cewa Hukumar NYSC na so ta dinkawa masu yi wa kasa hidima sabbin inifam<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"17979\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/false-nokia-3310-does-not-contain-gold\/false-4-16\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/FALSE-4.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-17979\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Hukunci: Karya ce! Shafin da hukumar ke amfani da shi a hukumance bai yi wani bayani kamar haka ba. Sa\u2019annan binciken mahimman kalmomin dada muka yi bai nuna mana labarin a shafukan kafofin yada labarai masu sahihanci ba.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hukumar Kula da Masu yi wa kasa hidima (NYSC) shiri ne da gwamnatin Najeriya ta samar a zamanin mulkin sojoji dan damawa da matasan Najeriyar da suka kammala karatun jami\u2019a da sauran makarantun da akan kammala bayan sakandare wajen gina al\u2019umma da bunkasa kasa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da Tiktok Classy Pee ya wallafa a <a href=\"https:\/\/vm.tiktok.com\/ZMrekvGE1\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">shafinsa<\/a> cewa hukumar na so ta dinka sabbin inifam ma masu yi wa kasa hidimar. Hoton da ya hada da labarin ya nuna wani mutun ya na sanye da sabbin kayayyakin da ake da\u2019awar za\u2019a fara amfani da su, wanda kuma ya nuna irin banbance-banbancen da ke tsakanin tsohon da sabon.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan hoton bidiyon da aka yi wa taken \u201cproposed new NYSC kits\u201d ya sami alamar likes gida 2,543 an yi tsokaci 504 yayin da aka kuma sake raba labarin sau 134 tun bayan da aka wallafa labarin ranar daya ga watan Yunin 2024. Wannan bidiyon dai ya shuhura a shafukan <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/muMLwEssdjj9SN2Q\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Facebook<\/a> da <a href=\"https:\/\/vm.tiktok.com\/ZMrdrNGvC\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">TikTok<\/a>.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">@Lola___, yayin da take mayar da martani dangane da hoton da ta gani a TikTok cewa ta yi, \u201cYanzu da ya kai lokaci na na yin NYSC inifam din ya zama irin na \u2018yan banga.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da shafin kuma @bignelly, ya bayyana rashin gamsuwarsa ya rubuta cewa, \u201cNi dai gara in sa tsohon in gama kafin a canza. Ba na son wannan.\u201d Mutane da dama kuma sun yi tambaya ne kan sahihancin wannan bayanin baki daya a wurin tsokacin.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yadda wannan labarin ya shiga ko\u2019ina ne da ma hukumar da ake magana a kai ya sa muka dauki nauyin tantance batun.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shafin NYSC na da wani gefe inda ake iya ganin duka sabbin abubuwan da hukumar ke yi, amma da muka duba wurin babu wani abun da ke bayani kan rigunan na NYSC wanda ya fara sa mu shakkar sahihancin wannan bayanin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Haka nan kuma mun lura cewa rigunan da aka nuna kamar an yi amfani da manhajar AI ne wanda ke kwaikwayon dabi\u2019un dan adam. Dan haka kusan kowa zai iya yin wannan zanen ko kirkiro irin wannan hoton dan ya yaudari jama\u2019a&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta kuma yi binciken mahimman kalmomi dan ganin ko za ta sami karin bayani daga dangane da batun, musamman a sauran kafafen yada labarai masu sahihanci, amma ba mu sami komai ba, wanda ya kara sa mu shakka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Daga nan mun kuma duba shafin hukumar ta NYSC a X da sauran shafukan da ta mallaka <a href=\"https:\/\/www.nysc.gov.ng\/contactus.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">a sochiyal mediya<\/a> dan ganin ko ita da kanta ta yi labari kan sabbin kayayyakin, inda a nan ma ba mu sami wani labari makamancin hakan ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Daga nan ne DUBAWA ta tuntubi ofishin hulda da manema labarai na hukumar NYSC dangane da wannan da\u2019awar. Ofishin ya tabbatar mana cewa zai gudanar da bincike. Ba da dadewa ba bayan nan, NYSC ta fitar da sanarwar da ke karyata labarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sanarwar ta ce duk abubuwan da ake rabawa masu yi wa kasa hidima a lokutan da suka je NYSC na nan yadda suke babu abin da aka canza. Sun kuma yi kira ga al\u2019umma da su yi watsi da duk wani bayanin da aka yi dangane da sabbin kayayyakin a shafin TikiTok, kuma suna cigaba da yunkurin rarrabawa kayayyakin da ake bukata a duka sansanonin 37 da aka saba taron farko na yin NYSC din, a shirye-shiryen da ake yi na karbar rukunin B na shekarar 2024.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cWannan gargadi ne ga infuluwensas na soshiyal mediya da su daina amfani da tambarin NYSC a kan shafukansu dan suna iya bata wa hukumar suna ta yin hakan, kuma buga da kara duk wadanda aka kama za su fiskanci sharia,\u201d a cewar <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/100066436096498\/posts\/pfbid02kpaxLEoTuudoqSkoDXub2kJBkqNyVGbSVWeBAivQs2cqNtZicT8t6ZYL91ePAfE6l\/?_rdc=1&amp;_rdr\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">sanarwar<\/a>.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da\u2019awar cewa hukumar NYSC ta canza inifam ba gaskiya ba ne. Sanarwar da jami\u2019in hulda da kafafen yada labarai ya fitar ua nna cewa hukumar ba ta da niyyar sauya kayan NYSC din.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: wani mai amfani da shafin Facebook na da&#8217;awar cewa Hukumar NYSC na so ta dinkawa masu yi wa kasa hidima sabbin inifam Hukunci: Karya ce! Shafin da hukumar ke amfani da shi a hukumance bai yi wani bayani kamar haka ba. Sa\u2019annan binciken mahimman kalmomin dada muka yi bai nuna mana labarin a shafukan kafofin yada labarai masu sahihanci ba. Cikakken bayani Hukumar Kula da Masu yi wa kasa hidima (NYSC) shiri ne da gwamnatin Najeriya ta samar a zamanin mulkin sojoji dan damawa da matasan Najeriyar da suka kammala karatun jami\u2019a da sauran makarantun da akan kammala bayan sakandare wajen gina al\u2019umma da bunkasa kasa. Wani mai amfani da Tiktok Classy Pee ya wallafa a shafinsa cewa hukumar na so ta dinka sabbin inifam ma masu yi wa kasa hidimar. Hoton da ya hada da labarin ya nuna wani mutun ya na sanye da sabbin kayayyakin da ake da\u2019awar za\u2019a fara amfani da su, wanda kuma ya nuna irin banbance-banbancen da ke tsakanin tsohon da sabon. Wannan hoton bidiyon da aka yi wa taken \u201cproposed new NYSC kits\u201d ya sami alamar likes gida 2,543 an yi tsokaci 504 yayin da aka kuma sake raba labarin sau 134 tun bayan da aka wallafa labarin ranar daya ga watan Yunin 2024. Wannan bidiyon dai ya shuhura a shafukan Facebook da TikTok.&nbsp; @Lola___, yayin da take mayar da martani dangane da hoton da ta gani a TikTok cewa ta yi, \u201cYanzu da ya kai lokaci na na yin NYSC inifam din ya zama irin na \u2018yan banga. Wani mai amfani da shafin kuma @bignelly, ya bayyana rashin gamsuwarsa ya rubuta cewa, \u201cNi dai gara in sa tsohon in gama kafin a canza. Ba na son wannan.\u201d Mutane da dama kuma sun yi tambaya ne kan sahihancin wannan bayanin baki daya a wurin tsokacin.&nbsp; Yadda wannan labarin ya shiga ko\u2019ina ne da ma hukumar da ake magana a kai ya sa muka dauki nauyin tantance batun. Tantancewa Shafin NYSC na da wani gefe inda ake iya ganin duka sabbin abubuwan da hukumar ke yi, amma da muka duba wurin babu wani abun da ke bayani kan rigunan na NYSC wanda ya fara sa mu shakkar sahihancin wannan bayanin. Haka nan kuma mun lura cewa rigunan da aka nuna kamar an yi amfani da manhajar AI ne wanda ke kwaikwayon dabi\u2019un dan adam. Dan haka kusan kowa zai iya yin wannan zanen ko kirkiro irin wannan hoton dan ya yaudari jama\u2019a&nbsp; DUBAWA ta kuma yi binciken mahimman kalmomi dan ganin ko za ta sami karin bayani daga dangane da batun, musamman a sauran kafafen yada labarai masu sahihanci, amma ba mu sami komai ba, wanda ya kara sa mu shakka. Daga nan mun kuma duba shafin hukumar ta NYSC a X da sauran shafukan da ta mallaka a sochiyal mediya dan ganin ko ita da kanta ta yi labari kan sabbin kayayyakin, inda a nan ma ba mu sami wani labari makamancin hakan ba. Daga nan ne DUBAWA ta tuntubi ofishin hulda da manema labarai na hukumar NYSC dangane da wannan da\u2019awar. Ofishin ya tabbatar mana cewa zai gudanar da bincike. Ba da dadewa ba bayan nan, NYSC ta fitar da sanarwar da ke karyata labarin. Sanarwar ta ce duk abubuwan da ake rabawa masu yi wa kasa hidima a lokutan da suka je NYSC na nan yadda suke babu abin da aka canza. Sun kuma yi kira ga al\u2019umma da su yi watsi da duk wani bayanin da aka yi dangane da sabbin kayayyakin a shafin TikiTok, kuma suna cigaba da yunkurin rarrabawa kayayyakin da ake bukata a duka sansanonin 37 da aka saba taron farko na yin NYSC din, a shirye-shiryen da ake yi na karbar rukunin B na shekarar 2024. \u201cWannan gargadi ne ga infuluwensas na soshiyal mediya da su daina amfani da tambarin NYSC a kan shafukansu dan suna iya bata wa hukumar suna ta yin hakan, kuma buga da kara duk wadanda aka kama za su fiskanci sharia,\u201d a cewar sanarwar.&nbsp; A Karshe Da\u2019awar cewa hukumar NYSC ta canza inifam ba gaskiya ba ne. Sanarwar da jami\u2019in hulda da kafafen yada labarai ya fitar ua nna cewa hukumar ba ta da niyyar sauya kayan NYSC din.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":19153,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3793],"class_list":["post-19205","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-4ZL","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3793,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"lademi-aborisade","display_name":"Lademi Aborisade","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/NYSC-636x357-1.jpg?fit=636%2C357&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19205","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=19205"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19205\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":19206,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19205\/revisions\/19206"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/19153"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=19205"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=19205"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=19205"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=19205"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=19205"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}