{"id":19298,"date":"2024-07-08T12:23:05","date_gmt":"2024-07-08T11:23:05","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=19298"},"modified":"2024-07-08T12:23:09","modified_gmt":"2024-07-08T11:23:09","slug":"yancin-aikin-jarida-ba-koina-a-najeriya-ne-ake-da-yancin-walwala-na-aikin-jarida-ba-kamar-yadda-minista-ke-daawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/yancin-aikin-jarida-ba-koina-a-najeriya-ne-ake-da-yancin-walwala-na-aikin-jarida-ba-kamar-yadda-minista-ke-daawa\/","title":{"rendered":"\u2018Yancin aikin jarida: Ba ko\u2019ina a Najeriya ne ake da \u2018yancin walwala na aikin jarida ba kamar yadda minista ke da\u2019awa"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2018Yancin aikin jarida na da mahimmanci ga mulkin dimokiradiyya. A tsarin mulkin dimokiradiyya irin na Najeriya, wajibi ne kafafen yada labarai su kasance masu \u2018yancin walwala, ta yadda \u2018yan jarida za su yi aiki ba tare da fargabar wani hari ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Babu al\u2019ummar zamanin da za ta iya rayuwa ba tare da kafafen yada labarai ba kuma babu wanda zai iya sakewa yadda ya kamata idan har kafafen yada labarai ba su da \u2018yancin walwala. Wannan \u2018yancin walwalar \u2018yan jaridan da na kafafen yada labarai ne zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu ba tare da barazana ko kutse ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bisa bayanan kundin da ke nazarin yanayin \u2018yancin walwalar \u2018yan jarida a duniya na 2023 wanda da turanci aka fi sani da World Press Freedom Index, Najeriya ta kasance kasar da ta fi <a href=\"https:\/\/rsf.org\/en\/country\/nigeria\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">hadari<\/a> da wahala wa \u2018yan jarida, wadanda kusan kowani lokaci ana sanya mu su ido, ana kai my si hari, sa\u2019annan a kan kama su ba tare da kwararan dalilai ba kamar yadda aka gani lokacin zaben 2023.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da ma dai akwai abubuwa da dama da kan kasance kalubale ga samar da \u2018yancin \u2018yan jarida a Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Dan haka abun mamaki ne a ce Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama\u2019a, Mohammed Idris ya fadi cewa akwai \u2018yancin aikin jarida a mafi yawancin yankunan Najeriya kuma ma ba\u2019a taba kama dan jarida ba tun bayan da gwamnatin Tinubu ta fara aiki.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ministan ya <a href=\"https:\/\/punchng.com\/no-journalist-jailed-under-tinubu-minister\/#:~:text=The%20Minister%20of%20Information%20and,administration%20for%20practising%20responsible%20journalism\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">bayyana hakan ne<\/a> lokacin wata ganawar da ma\u2019aikatar ta sa ta shirya tare da hadin gwiwar Ma\u2019aikatar Muhalli da UNESCO dan gudanar da bukin \u2018Yancin Walwalar Kafafen Yada Labarai na Duniya 2024 ranar uku ga watan Mayu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cewar ministan, \u201cNi ban taba ganin wani, tun bayan da wannan gwamnatin ta fara aiki, alal misali, wanda aka taba kulle shi a gidan kaso ko kuma ya shiga buya saboda \u2018yancin aikin jarida ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cMun san cewa hakan ya taba faruwa a wannan kasar a baya. Wasu shekaru gommai da suka wuce, mun san cewa lokacin kafin ka yi rahoto sai ka bar kasar. Zan iya fada muku cewa \u2018yan jarida a Najeriya yawanci suna da \u2018yanci, amma wannan \u2018yancin zai fi karfi ne idan har ana kamanta gaskiya ana kuma gudanar a abubuwa a bayyane, a yanayin da muke rahotanni\u2026.\u201d<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Lokutan da aka musgunawa \u2018yan jarida a karkashin jagorancin gwamnatin Tinubu<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A \u2018yan shekarun baya-bayan nan, \u2018yan jarida a Najeriya baki daya sun fuskanc kame-kame, dauri, kotu, muzgunawa, zargin kotu da duka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kafin uku ga watan Mayun 2024, sadda ministan ya yi wannan furucin, an dauki rahotannin lokutan da aka kama \u2018yan jarida ba tare da kwararan dalilai ko ma la\u2019akari da tanadin doka ba. Misali, ranar 21 ga watan Fabrairun 2024, Kasarahchi Aniagolu, wani dan jaridan da ke aiki da jaridar The Whistler, ya shiga hannun \u2018yan sanda wadanda suka kama shi, suka yi masa duka sa\u2019annan suka kulle bisa zarginsa da daukar rahoto ba tare da izininsu ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Haka nan kuma ranar 115 ga watan Maris 2024, Segun Olatunji, Eduta da FirstNews, shi ma <a href=\"https:\/\/cpj.org\/2024\/03\/armed-men-take-nigerian-journalist-segun-olatunji-from-lagos-home\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">jami&#8217;an sojoji sun kama shi sun kulle<\/a>. Ya shiga hannun sojojin ne saboda wani rahotan da ya wallafa dangane da wani jami\u2019i daga Hukumar Leken Asirin Ma\u2019aikatar Tsaro (DIA) wanda ke karkashin ma\u2019aikatar tsaron Najeriya, wanda ake zargi da bayar da kwangiloli ba tare da bin ka\u2019ida ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bacin haka, Daniel Ojukwu, wani dan jaridan da ke aiki da Gidauniyar Bincike Mai Zurfi Na Aikin Jarida shi ma an <a href=\"https:\/\/cpj.org\/2024\/05\/nigerian-police-secretly-arrest-journalist-daniel-ojukwu-over-critical-report\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">kama <\/a>&nbsp;shi ranar daya ga watan Mayun 2024, kwanaki biyu kafin ministan ya yi wannan furucin na cewa ba\u2019a taba kama dan jarida ba tun bayan da Tinubu ya karbi madafun iko.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ranar ce kuma ranar \u2018Yancin Aikin Jarida na Dunya, sadda al\u2019ummar kasa da kasa ta taro dan yin bukin \u2018yancin walwalar \u2018yan jarida ko\u2019ina a duniya. Sa\u2019annan rana ce da ke wa jama\u2019a tuni dangane da mahimmancin kare hakkin \u2018yan jarida da tabbatar da cewa suna da zarafin dauko rahotanni ba tare da tsoron danniya ko tashin hankali ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Tsakanin 29 ga watan Mayun 2023, sadda Tinubu ya dare karagar mulki, da Mayun 2024, an sami rahotanni da yawa na lokutan da aka tsare \u2018yan jarida ba bisa ka\u2019ida ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cikin wannan lokacin <a href=\"https:\/\/fij.ng\/article\/bold-minister-said-no-journalist-has-been-put-in-jail-under-tinubu-here-are-11-cases-he-forgot\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">&#8216;yan jarida fiye da 12<\/a> wadanda aka sani, jami\u2019an tsaro ko sun kama su, ko sun tsare su ko kuma dai sun ci zarafinsu yayin da suke gudanar da aikinsu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A wani lokacin ma, an kama ainihin shugaban kamfanin wallafa jaridan ne Precious Eze Chukwunonso, ranar 27 ga watan Mayun 2024. An kama Chukwunonso na kusan <a href=\"https:\/\/cpj.org\/2024\/06\/nigerian-authorities-detain-journalist-precious-eze-chukwunonso-for-18-days\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">makwanni uku<\/a>&nbsp; bayan da aka yi korafin rahoton da aka wallafa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>\u2018Yancin aikin jarida a Najeriya da kundin nazarin yanayin aikin jarida a duniya<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cewar kundin nazarin \u2018yancin&nbsp; aikin jarida na World Press Freedom Index 2024, \u2018yancin aikin jarida shi ne damar da \u2018yan jarida da ma a al\u2019umma baki daya ke da shi na zaba da, hadawa da yada labaran da ke da mahimmanci ga al\u2019umma wanda ba ruwan shi da siyasa, tattalin arziki, shari\u2019a ko zamantakewa, ba tare da barazana ga lafiyarsu ta jiki da ta kwakwalwa ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Walwalar gudanar da aikin jarida a Najeriya ya kara lalacewa a \u2018yan shekarun da suka gabata. Makin da aka baiwa aikin jarida cikin walwala a kasar ya sauka daga 65.9 cikin 100 a shekarar 2013 zuwa 51.03 cikin 100 a shekarar 2024 (Inda 0 ke nufin tabarbarewa 100 kuma nasara)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Makin da Najeriya ta samu tsakanin 40-55 na nuna cewa aikin jarida na da sarkakiya.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-us.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXcL4FsRiJhUFME8y0AvPmbDStmoyE-iQdlQyx8Yl4lieV17RQ_WgVu4XUeV4O6khCg-x65ivVGubHDbBIO-41LfYl9I1FvsY0QqbBT-9G5DY6ZzEhsiHAOr-htH_KdAqJa7vazFDDlzAImYn46zZUEAaPAk?key=2AHlc4Slv_LfMELk2e6gqw\" alt=\"Press freedom: Nigeria not \u201clargely free\u201d as claimed by minister\" title=\"Chart\"\/><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Idan ana la\u2019akari da kasar a matakin yanki, Najeriya na daga cikin kasashen da ke baya a wajen walwalar aikin jarida a yankin yammacin Afirka. A cikin kasashen, wani sakamakon binciken da aka yi na nuna cewa Najeriya na zaman kasa ta 14 cikin 16.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-us.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXecoaiu_T2sf37Ijxe9cr84AhZIoTfAkp2OVksvrZn9amNSIVpoj-dQbGXbN4YdQBrlZ8cqV0rz8o_A4Rci9czgc_1id1vMaY4wY3JuQXbFQEw7jzm_mR9Lu5g47Ek3PzfL9lfxk0z1zAqWoa4v2Z8igI1U?key=2AHlc4Slv_LfMELk2e6gqw\" alt=\"Press freedom: Nigeria not \u201clargely free\u201d as claimed by minister\" title=\"Chart\"\/><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bisa bayanan <a href=\"https:\/\/rsf.org\/en\/country\/nigeria\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nazarin <\/a>da kungiyar \u2018Yan Jarida Mara Iyaka wato Reporters Without Borders a turance, yawancin hare-hare, da tsare mutane ba tare da wani dalili mai kwari ba, da kuma harbin da aka yi a kan \u2018yan jarida kwanan nan a yankin Yammacin Afirka a Najeriya suka faru, musamman a lokutan zabe. Kusan \u2018yan jarida 20 da kafofin yada labarai ne aka kai wa hari lokacin zabukan da aka yi a watannin Fabrairu da Maris na 2023.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Laifuffukan da aka yi a kan \u2018yan jarida yawanci ba\u2019a hukuntawa, ko da kuwa an gane wadanda suka aikata an kama su. Babu wani tsari na kasa da ke tabbatar da kariyar \u2018yan jarida. Mahukunta na yawan sa musu ido kuma nan da nan sun yi musu barazana.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bisa la\u2019akari da wannan ne, za\u2019a iya cewa yanayin \u2018yancin walwalar aikin jarida a Najeriya ya yi kasa sosai.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da cewa babu kasar da za\u2019a ce ba ta da na ta matsalar idan ya zo batun \u2018yancin walwalar aikin jarida, muna fatan ganin Najeriya ta dauki mahimman matakai wajen inganta kariyar \u2018yan jarida ta yadda za su yi aikinsu yadda ya kamata \u2014 ba sani ba sabo.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Abin da kwararru ke cewa kan \u2018yancin walwalar \u2018yan jarida a Najeriya<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta yi magana da Busola Ajibola, kwararriya kan bunkasa kafofin yada labarai kuma mataimakiyar darektan Cibiyar \u2018Yan Jarida, Sabbin Dabaru da Cigaba (CJID) dangane da \u2018yancin walwalar \u2018yan jarida a Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ta bayyana cewa da ma Najeriya na da tarihin muzgunawar da \u2018yan sanda ke wa \u2018yan jarida da kuma kama su ba tare da kwararan dalilai ba. Wannan yanayin ne ke yawan sa tsoro, abin da kuma ke hana su fitowa su kalubalanci abubuwan da ya kamata a ce sun kalubalanta, wanda kuma ya kai ga koma baya a yanayin walwalar gudanar da aikin jarida.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cewar madam Ajibola, \u201cAkwai wadansu tanade-tanaden doka da ba\u2019a fayyace sosai ba, wadanda kuma \u2018yan sanda ke yawan amfani da shi su ci mutuncin \u2018yan jarida. Misali shi ne dokar laifin yanar gozo wanda ake kira Cybercrime Act. Duk da cewa an kwaskware wannan dokar, \u2018yan sanda na cigaba da amfani da shi su zalunci \u2018yan jarida.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cAkwai kuma batun bata suna, inda dan jarida zai rubuta labarin da ke da mahimmanci sosai saboda tasirin da ya ke da shi a akn al\u2019umma ko kuma dai wani jami\u2019in gwamnati, sai \u2018yan sanda su juyya su kira shi bata suna. Wadannan dokoki ne da aka san \u2018yan sanda na amfani da su wajen cin zarafin \u2018yan jarida.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cDangane da dokar intanet, a wannan shekarar kadai, Press Attack Tracker na CJID, wanda ke bin diddigin hare-haren da ake wa \u2018yan jarida ya yi rahotanni kan lokuta 11 da \u2018yan sanda suka gayyaci \u2018yan jarida ko kuma suka zarge su da bin mutane a shafukan intanet ko kuma dai suka kama su suka kulle babu gaira ba dalili. Sun yi nasarar kama Daniel Ojukwu, wani dan jarida tare da Gidauniyar Bincike Mai Zurfi a Aikin Jarida (FIJ), kuma sun tsare shi na kusan kwanaki 10. Sun yi kokarin kama Nurudeen Akewusola na ICIR, amma ayyukan kungiyoyin farar hula sun hana hakan faruwa. Wadannan ne abubuwan da mek fuskanta a Najeriya,\u201d a cewar Madam Ajibola.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A karshe&nbsp;<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sabanin abin da ministan ya bayyana, akwai \u2018yan jarida da dama wadanda ko an kama su, ko an tsare su, ko kuma dai an ci zarafinsu tun bayan da shugaba Tinubu ya fara mulki. Baki daya dai \u2018yancin walwala na aikin jarida na tabarbarewa, kuma aikin jarida na kara wahaka sakamakon thare-haren da ake kai wa kan \u2018yan jarida, kutse na harkokin siyasa da barazana.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Wannan rahoto an fitar da shi ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararrun masu gano gaskiya labari na Kwame Karikari da hadin giwar Dataphyte a kokarin da ake yi na mutunta fadin gaskiya a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a Najeriya.&nbsp;<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u2018Yancin aikin jarida na da mahimmanci ga mulkin dimokiradiyya. A tsarin mulkin dimokiradiyya irin na Najeriya, wajibi ne kafafen yada labarai su kasance masu \u2018yancin walwala, ta yadda \u2018yan jarida za su yi aiki ba tare da fargabar wani hari ba. Babu al\u2019ummar zamanin da za ta iya rayuwa ba tare da kafafen yada labarai ba kuma babu wanda zai iya sakewa yadda ya kamata idan har kafafen yada labarai ba su da \u2018yancin walwala. Wannan \u2018yancin walwalar \u2018yan jaridan da na kafafen yada labarai ne zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu ba tare da barazana ko kutse ba. Bisa bayanan kundin da ke nazarin yanayin \u2018yancin walwalar \u2018yan jarida a duniya na 2023 wanda da turanci aka fi sani da World Press Freedom Index, Najeriya ta kasance kasar da ta fi hadari da wahala wa \u2018yan jarida, wadanda kusan kowani lokaci ana sanya mu su ido, ana kai my si hari, sa\u2019annan a kan kama su ba tare da kwararan dalilai ba kamar yadda aka gani lokacin zaben 2023. Da ma dai akwai abubuwa da dama da kan kasance kalubale ga samar da \u2018yancin \u2018yan jarida a Najeriya. Dan haka abun mamaki ne a ce Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama\u2019a, Mohammed Idris ya fadi cewa akwai \u2018yancin aikin jarida a mafi yawancin yankunan Najeriya kuma ma ba\u2019a taba kama dan jarida ba tun bayan da gwamnatin Tinubu ta fara aiki. Ministan ya bayyana hakan ne lokacin wata ganawar da ma\u2019aikatar ta sa ta shirya tare da hadin gwiwar Ma\u2019aikatar Muhalli da UNESCO dan gudanar da bukin \u2018Yancin Walwalar Kafafen Yada Labarai na Duniya 2024 ranar uku ga watan Mayu. A cewar ministan, \u201cNi ban taba ganin wani, tun bayan da wannan gwamnatin ta fara aiki, alal misali, wanda aka taba kulle shi a gidan kaso ko kuma ya shiga buya saboda \u2018yancin aikin jarida ba. \u201cMun san cewa hakan ya taba faruwa a wannan kasar a baya. Wasu shekaru gommai da suka wuce, mun san cewa lokacin kafin ka yi rahoto sai ka bar kasar. Zan iya fada muku cewa \u2018yan jarida a Najeriya yawanci suna da \u2018yanci, amma wannan \u2018yancin zai fi karfi ne idan har ana kamanta gaskiya ana kuma gudanar a abubuwa a bayyane, a yanayin da muke rahotanni\u2026.\u201d Lokutan da aka musgunawa \u2018yan jarida a karkashin jagorancin gwamnatin Tinubu A \u2018yan shekarun baya-bayan nan, \u2018yan jarida a Najeriya baki daya sun fuskanc kame-kame, dauri, kotu, muzgunawa, zargin kotu da duka. Kafin uku ga watan Mayun 2024, sadda ministan ya yi wannan furucin, an dauki rahotannin lokutan da aka kama \u2018yan jarida ba tare da kwararan dalilai ko ma la\u2019akari da tanadin doka ba. Misali, ranar 21 ga watan Fabrairun 2024, Kasarahchi Aniagolu, wani dan jaridan da ke aiki da jaridar The Whistler, ya shiga hannun \u2018yan sanda wadanda suka kama shi, suka yi masa duka sa\u2019annan suka kulle bisa zarginsa da daukar rahoto ba tare da izininsu ba. Haka nan kuma ranar 115 ga watan Maris 2024, Segun Olatunji, Eduta da FirstNews, shi ma jami&#8217;an sojoji sun kama shi sun kulle. Ya shiga hannun sojojin ne saboda wani rahotan da ya wallafa dangane da wani jami\u2019i daga Hukumar Leken Asirin Ma\u2019aikatar Tsaro (DIA) wanda ke karkashin ma\u2019aikatar tsaron Najeriya, wanda ake zargi da bayar da kwangiloli ba tare da bin ka\u2019ida ba. Bacin haka, Daniel Ojukwu, wani dan jaridan da ke aiki da Gidauniyar Bincike Mai Zurfi Na Aikin Jarida shi ma an kama &nbsp;shi ranar daya ga watan Mayun 2024, kwanaki biyu kafin ministan ya yi wannan furucin na cewa ba\u2019a taba kama dan jarida ba tun bayan da Tinubu ya karbi madafun iko. Ranar ce kuma ranar \u2018Yancin Aikin Jarida na Dunya, sadda al\u2019ummar kasa da kasa ta taro dan yin bukin \u2018yancin walwalar \u2018yan jarida ko\u2019ina a duniya. Sa\u2019annan rana ce da ke wa jama\u2019a tuni dangane da mahimmancin kare hakkin \u2018yan jarida da tabbatar da cewa suna da zarafin dauko rahotanni ba tare da tsoron danniya ko tashin hankali ba. Tsakanin 29 ga watan Mayun 2023, sadda Tinubu ya dare karagar mulki, da Mayun 2024, an sami rahotanni da yawa na lokutan da aka tsare \u2018yan jarida ba bisa ka\u2019ida ba. A cikin wannan lokacin &#8216;yan jarida fiye da 12 wadanda aka sani, jami\u2019an tsaro ko sun kama su, ko sun tsare su ko kuma dai sun ci zarafinsu yayin da suke gudanar da aikinsu. A wani lokacin ma, an kama ainihin shugaban kamfanin wallafa jaridan ne Precious Eze Chukwunonso, ranar 27 ga watan Mayun 2024. An kama Chukwunonso na kusan makwanni uku&nbsp; bayan da aka yi korafin rahoton da aka wallafa. \u2018Yancin aikin jarida a Najeriya da kundin nazarin yanayin aikin jarida a duniya A cewar kundin nazarin \u2018yancin&nbsp; aikin jarida na World Press Freedom Index 2024, \u2018yancin aikin jarida shi ne damar da \u2018yan jarida da ma a al\u2019umma baki daya ke da shi na zaba da, hadawa da yada labaran da ke da mahimmanci ga al\u2019umma wanda ba ruwan shi da siyasa, tattalin arziki, shari\u2019a ko zamantakewa, ba tare da barazana ga lafiyarsu ta jiki da ta kwakwalwa ba. Walwalar gudanar da aikin jarida a Najeriya ya kara lalacewa a \u2018yan shekarun da suka gabata. Makin da aka baiwa aikin jarida cikin walwala a kasar ya sauka daga 65.9 cikin 100 a shekarar 2013 zuwa 51.03 cikin 100 a shekarar 2024 (Inda 0 ke nufin tabarbarewa 100 kuma nasara) Makin da Najeriya ta samu tsakanin 40-55 na nuna cewa aikin jarida na da sarkakiya. Idan ana la\u2019akari da kasar a matakin yanki, Najeriya na daga cikin kasashen da ke baya a wajen walwalar aikin jarida a yankin yammacin Afirka. A cikin kasashen, wani sakamakon binciken da aka yi na nuna cewa Najeriya na zaman kasa ta 14 cikin 16. Bisa bayanan nazarin da kungiyar \u2018Yan Jarida Mara Iyaka wato Reporters Without Borders a turance, yawancin hare-hare, da tsare mutane ba tare da wani dalili mai kwari ba, da kuma harbin da aka yi a kan \u2018yan jarida kwanan nan a yankin Yammacin Afirka<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":19213,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4070],"class_list":["post-19298","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-51g","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4070,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"funmilayo-babatunde","display_name":"Funmilayo Babatunde","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/Press-Freedom.png?fit=900%2C600&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19298","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=19298"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19298\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":19299,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19298\/revisions\/19299"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/19213"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=19298"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=19298"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=19298"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=19298"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=19298"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}