{"id":19452,"date":"2024-07-23T10:58:51","date_gmt":"2024-07-23T09:58:51","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=19452"},"modified":"2024-07-23T10:58:54","modified_gmt":"2024-07-23T09:58:54","slug":"shin-da-gaske-ne-idan-aka-jika-farar-albasa-a-ruwa-tana-kara-karfin-gani-kamar-yadda-ake-daawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/shin-da-gaske-ne-idan-aka-jika-farar-albasa-a-ruwa-tana-kara-karfin-gani-kamar-yadda-ake-daawa\/","title":{"rendered":"Shin da gaske ne idan aka jika farar albasa a ruwa tana kara karfin gani kamar yadda ake da\u2019awa?"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin\u00a0 Facebook yayi da\u2019awar cewa idan aka jika albasa a cikin ruwa tana wanke da kara karfin ganin idanu.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"136\" height=\"59\" data-attachment-id=\"17961\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/viral-footage-shows-miners-arrested-in-taraba-not-bandits-in-niger-state\/misleading-4-6\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/MISLEADING-4.png?fit=136%2C59&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"136,59\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"MISLEADING-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/MISLEADING-4.png?fit=136%2C59&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/MISLEADING-4.png?resize=136%2C59\" alt=\"\" class=\"wp-image-17961\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#7f7e07\">Hukunci: YAUDARA CE. Yayin da ake ganin albasa na dauke da wasu sinadarai da suke kara karfin idanu, idan aka jikata tsawon wasu kwanaki ba a samun abin da ake bukata a tattare da ita.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Sako<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da shafin Facebook, McMfresh, ya wallafa wani bidiyo (<a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/reel\/471943422175549\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">posted a video<\/a>) a ranar 23 ga watan Mayu, 2024 inda yayi da\u2019awar cewa idan aka yi jiko ko tsimi na albasa a ruwa ta kan kara karfin idanu. Ya bukaci masu bibiyarsa da su jika albasa ja da fara amma farar&nbsp; tafi yawa idan ta jiku a tsawon kwanaki mutum ya rika sha da safe da dare, wannan zai karfafa masa gani, zai kuma maganin matsalolin ganin kamar yanar ido da dindimi da rashin ganin abu a kusa da nesa .<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan wallafa da yayi ta samu masu martani 24,000 da masu tsokaci 1,400 da wadanda suka sake yadawa (reshares) 7,100. An samu tambaya cikin masu tsokacin inda wasu ke tambaya tsawon wane lokaci za a tsima albasar da adadi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai suna Omotayo Akinmusewe yace, \u201c Akwai matsala a abin da aka gabatar saboda babu bayanai kan yadda za a hada sinadaran dama yadda za a yi amfani da su.\u201d Wata ma mai suna Ebere Awogu tayi tambaya ne da cewa&nbsp; \u201cShin zan tace ruwan ko kuwa zan shanye komai?\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wasu masu sharhin na tambaya ne&nbsp; wanne yafi, ruwan zafi ko na sanyi, ko ma ita kanta albasar ya kamata a dafa ta kafin amfani da ita. Wannan ya sanya DUBAWA ya ga dacewar gudanar da bincike kan da\u2019awar ganin yadda ake ta bayanai.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Me ke kawo matsalolin idanu?<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Idanu wata halitta ce mai muhimmanci a jikin dan Adam wacce sai an taka tsan-tsan da ita, ido na fuskantar tarin kalubale kamar rashin gani a kusa (Myopia ) da rashin gani daga nesa (hyperopia) koma gani garara-garara (astigmatism) saboda madubin cikin idanu ya samu matsala, ana iya samun matsalar idanu dalilin yawaitar shekaru ga kuma matsalar idanu ta cataracts da&nbsp; glaucoma, wadanda ke zama sananannu ba kawai ga masu kananan shekaru ba har da masu shekaru da yawa ( <a href=\"https:\/\/completeeyecareofmedina.com\/all-about-eyes\/common-pediatric-vision-concerns-and-how-to-treat-them\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">typical eye conditions<\/a>).<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ciwon idanu dalilin gado da yawan shekaru da tsarin rayuwa duk suna tasiri ga matsalar idanu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shima muhalli na taka tasa rawar idan mutum na bayyana a inda ake samun haske mai hadari kamar (UV Light) da gurbatar muhalli duk suna taka rawa, haka nan kuma akwai ciwuka irin na suga da hawan jini duk su kan shafi idanu sannan damuwa na iya kara ta\u2019azzara lamarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Masana a fannin lafiya na ci gaba da jan hankalin al\u2019umma kan muhimmanci na idanu a cewar makarantar da ke horaswa kan idanu ta (<a href=\"https:\/\/www.aao.org\/eye-health\/anatomy\/parts-of-eye\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">American Academy of Ophthalmologists<\/a> (AAO), karamin ciwo da aka samu a idanu ko wata matsala dalilin muhalli na iya girmama daga karamin ciwo na idanu zuwa babban ciwon idanu, muddin ba a dauki matakin da ya dace ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Gano matsalar da wuri da daukar matakin kula da lafiyar muhimman abubuwa ne da za su kai ga samun lafiyayyen gani da gyara matsaloli da suka samu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Shin albasa na taimakawa?<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Albasa da a kimiyance ake kira <em>Allium Cepa, dangin kayan lambu ce<\/em> da aka tabbatar tana tallafa wa lafiya (<a href=\"https:\/\/www.healthline.com\/nutrition\/foods\/onions#nutrients\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">health properties<\/a><em>). Tana dauke da sinadaran <\/em>antioxidants da sulfur wadanda ke da tasiri ga jikin dan Adam.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sinadarin sulfur na taimakawa lafiyar idanu ta hanyar samar da sinadarin <a href=\"https:\/\/www.lybrate.com\/medicine\/glutathione\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">glutathione<\/a> protein. Wannan na taimakawa wajen kare kamuwa da <a href=\"https:\/\/www.lybrate.com\/topic\/glaucoma\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">glaucoma<\/a>, da hana&nbsp; rage karfin gani da yamushewa da kare madubin idanu da inganta gani.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kayan lambun da ke kunshe da sinadarin <a href=\"https:\/\/www.healthline.com\/nutrition\/selenium-benefits#Best-dietary-sources-of-selenium\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">selenium<\/a>, wanda ke tallafa wa vitamin E wanda ke taimaka wa kwayoyin halittar idanu, albasa na taimaka wa ci gaban fannin idanu wajen samun kyakkyawan gani.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Temiloluwa Omotosho, kwararriyar masaniya kan kayan abinci tace dangin albasar na taimakawa lafiyar jikin dan Adam.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Tace \u201calbasa na taimakawa wajen kare kwayoyin halittar jiki daga lalacewa. Nasani cewa albasa na taimakawa wajen nika abinci a ciki da lafiyar fata da lafiyar idanu.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da haka DUBAWA a binciken da ya gudanar ya gaza gano wani bincike da aka yi da ya nunar da cewa shan jiko ko tsimi da aka ayi na albasa na magani ko warkar da idanu, kwararrun lafiya da aka tuntuba sun yi watsi da wannan da\u2019awa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Abin da kwararru ke cewa&nbsp;<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ya tuntubi Jovi Boparai masanin harkar idanu a Amurka kuma babban jami\u2019i a kamfanin harkoki da suka shafi idanu na <a href=\"https:\/\/mycorneacare.com\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Corneacare<\/a> yace babu wani binciken masana da ya tabbatar da wannan da\u2019awa. Yace \u201calbasa ta yiwu tana da wasu sinadarai da ke tallafa wa &nbsp; idanu amma babu wata hujja daga binciken kwararru da ya tabbatar da samar da maganin idanu daga albasar, ni ban taba jin haka ba, kuma ba na yin amfani da wannan a matsayin ba da magani a yayin gudanar da aikina.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kuma yi gargadi ga jama\u2019a da su guji yin magani da ka, musamman ciwuka da suka shafi idanu irin su glaucoma da cataracts. \u201cMutum na iya makancewa daga (glaucoma), kada mutum yayi amfani da tsimi daga albasa ya rika shan ruwanta ya rika tunanin zai warke daga cutar glaucoma, ba haka lamarin yake ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Glaucoma da cataracts na kan gaba wajen jawo makanta a fadin duniya zai fi muhimmanci idan mutum na da larurar idanu ya je ya ga likitan idanu.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Lucy Owulo, masaniya kan harhada abinci daga ma\u2019aikatar lafiya ta kasa, tayi watsi da wannan da\u2019awa inda tace babu wata sheda ta kimiya, sai ta yi kira ga al\u2019umma da su yi watsi da duk wasu bayanai makamantan haka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ms Temiloluwa kuwa cewa tayi shan ruwan albasa yana da kyau amma baya magnin matsalar idanu, tace yana iya taimakawa wasu batutuwan na lafiyar jiki amma ba wai ace kai tsaye lafiyar idanu ba, bana ji a bangaren masana kimiya sun kai ga cimma wannan matsaya. Ba za ka ce ana amfani da albasa don kula da lafiyar idanu ba.\u201d<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da cewa albasa na kunshe da wasu sinadarai da za su iya taimakawa lafiyar gani, masana sun nunar da cewa tsimi na albasa da ake yi a sha baya magnin matsalar idanu. Wannan da\u2019awa yaudara ce.&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin\u00a0 Facebook yayi da\u2019awar cewa idan aka jika albasa a cikin ruwa tana wanke da kara karfin ganin idanu. Hukunci: YAUDARA CE. Yayin da ake ganin albasa na dauke da wasu sinadarai da suke kara karfin idanu, idan aka jikata tsawon wasu kwanaki ba a samun abin da ake bukata a tattare da ita. Cikakken Sako Wani mai amfani da shafin Facebook, McMfresh, ya wallafa wani bidiyo (posted a video) a ranar 23 ga watan Mayu, 2024 inda yayi da\u2019awar cewa idan aka yi jiko ko tsimi na albasa a ruwa ta kan kara karfin idanu. Ya bukaci masu bibiyarsa da su jika albasa ja da fara amma farar&nbsp; tafi yawa idan ta jiku a tsawon kwanaki mutum ya rika sha da safe da dare, wannan zai karfafa masa gani, zai kuma maganin matsalolin ganin kamar yanar ido da dindimi da rashin ganin abu a kusa da nesa . Wannan wallafa da yayi ta samu masu martani 24,000 da masu tsokaci 1,400 da wadanda suka sake yadawa (reshares) 7,100. An samu tambaya cikin masu tsokacin inda wasu ke tambaya tsawon wane lokaci za a tsima albasar da adadi. Wani mai suna Omotayo Akinmusewe yace, \u201c Akwai matsala a abin da aka gabatar saboda babu bayanai kan yadda za a hada sinadaran dama yadda za a yi amfani da su.\u201d Wata ma mai suna Ebere Awogu tayi tambaya ne da cewa&nbsp; \u201cShin zan tace ruwan ko kuwa zan shanye komai?\u201d Wasu masu sharhin na tambaya ne&nbsp; wanne yafi, ruwan zafi ko na sanyi, ko ma ita kanta albasar ya kamata a dafa ta kafin amfani da ita. Wannan ya sanya DUBAWA ya ga dacewar gudanar da bincike kan da\u2019awar ganin yadda ake ta bayanai. Me ke kawo matsalolin idanu? Idanu wata halitta ce mai muhimmanci a jikin dan Adam wacce sai an taka tsan-tsan da ita, ido na fuskantar tarin kalubale kamar rashin gani a kusa (Myopia ) da rashin gani daga nesa (hyperopia) koma gani garara-garara (astigmatism) saboda madubin cikin idanu ya samu matsala, ana iya samun matsalar idanu dalilin yawaitar shekaru ga kuma matsalar idanu ta cataracts da&nbsp; glaucoma, wadanda ke zama sananannu ba kawai ga masu kananan shekaru ba har da masu shekaru da yawa ( typical eye conditions). Ciwon idanu dalilin gado da yawan shekaru da tsarin rayuwa duk suna tasiri ga matsalar idanu. Shima muhalli na taka tasa rawar idan mutum na bayyana a inda ake samun haske mai hadari kamar (UV Light) da gurbatar muhalli duk suna taka rawa, haka nan kuma akwai ciwuka irin na suga da hawan jini duk su kan shafi idanu sannan damuwa na iya kara ta\u2019azzara lamarin. Masana a fannin lafiya na ci gaba da jan hankalin al\u2019umma kan muhimmanci na idanu a cewar makarantar da ke horaswa kan idanu ta (American Academy of Ophthalmologists (AAO), karamin ciwo da aka samu a idanu ko wata matsala dalilin muhalli na iya girmama daga karamin ciwo na idanu zuwa babban ciwon idanu, muddin ba a dauki matakin da ya dace ba. Gano matsalar da wuri da daukar matakin kula da lafiyar muhimman abubuwa ne da za su kai ga samun lafiyayyen gani da gyara matsaloli da suka samu. Shin albasa na taimakawa? Albasa da a kimiyance ake kira Allium Cepa, dangin kayan lambu ce da aka tabbatar tana tallafa wa lafiya (health properties). Tana dauke da sinadaran antioxidants da sulfur wadanda ke da tasiri ga jikin dan Adam. Sinadarin sulfur na taimakawa lafiyar idanu ta hanyar samar da sinadarin glutathione protein. Wannan na taimakawa wajen kare kamuwa da glaucoma, da hana&nbsp; rage karfin gani da yamushewa da kare madubin idanu da inganta gani. Kayan lambun da ke kunshe da sinadarin selenium, wanda ke tallafa wa vitamin E wanda ke taimaka wa kwayoyin halittar idanu, albasa na taimaka wa ci gaban fannin idanu wajen samun kyakkyawan gani. Temiloluwa Omotosho, kwararriyar masaniya kan kayan abinci tace dangin albasar na taimakawa lafiyar jikin dan Adam. Tace \u201calbasa na taimakawa wajen kare kwayoyin halittar jiki daga lalacewa. Nasani cewa albasa na taimakawa wajen nika abinci a ciki da lafiyar fata da lafiyar idanu.\u201d Duk da haka DUBAWA a binciken da ya gudanar ya gaza gano wani bincike da aka yi da ya nunar da cewa shan jiko ko tsimi da aka ayi na albasa na magani ko warkar da idanu, kwararrun lafiya da aka tuntuba sun yi watsi da wannan da\u2019awa. Abin da kwararru ke cewa&nbsp; DUBAWA ya tuntubi Jovi Boparai masanin harkar idanu a Amurka kuma babban jami\u2019i a kamfanin harkoki da suka shafi idanu na Corneacare yace babu wani binciken masana da ya tabbatar da wannan da\u2019awa. Yace \u201calbasa ta yiwu tana da wasu sinadarai da ke tallafa wa &nbsp; idanu amma babu wata hujja daga binciken kwararru da ya tabbatar da samar da maganin idanu daga albasar, ni ban taba jin haka ba, kuma ba na yin amfani da wannan a matsayin ba da magani a yayin gudanar da aikina.\u201d Ya kuma yi gargadi ga jama\u2019a da su guji yin magani da ka, musamman ciwuka da suka shafi idanu irin su glaucoma da cataracts. \u201cMutum na iya makancewa daga (glaucoma), kada mutum yayi amfani da tsimi daga albasa ya rika shan ruwanta ya rika tunanin zai warke daga cutar glaucoma, ba haka lamarin yake ba. Glaucoma da cataracts na kan gaba wajen jawo makanta a fadin duniya zai fi muhimmanci idan mutum na da larurar idanu ya je ya ga likitan idanu.\u201d Lucy Owulo, masaniya kan harhada abinci daga ma\u2019aikatar lafiya ta kasa, tayi watsi da wannan da\u2019awa inda tace babu wata sheda ta kimiya, sai ta yi kira ga al\u2019umma da su yi watsi da duk wasu bayanai makamantan haka. Ms Temiloluwa kuwa cewa tayi shan ruwan albasa yana da kyau amma baya magnin matsalar idanu, tace yana iya taimakawa wasu batutuwan na lafiyar jiki amma ba wai ace kai tsaye lafiyar idanu ba, bana ji a bangaren masana kimiya sun kai ga cimma wannan matsaya. Ba za ka ce ana amfani da albasa don kula<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":19330,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3263],"class_list":["post-19452","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-53K","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3263,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"phillip-anjorin","display_name":"Phillip Anjorin","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/98daaf5d9d7a2c5cd4ce1c417532d1cfa2ca293247710cf46a925146cc2e90e1?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/onion.jpg?fit=554%2C554&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19452","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=19452"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19452\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":19453,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19452\/revisions\/19453"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/19330"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=19452"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=19452"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=19452"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=19452"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=19452"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}