{"id":19454,"date":"2024-07-23T12:03:11","date_gmt":"2024-07-23T11:03:11","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=19454"},"modified":"2024-07-23T12:49:59","modified_gmt":"2024-07-23T11:49:59","slug":"karya-ce-tinubu-bai-yi-murabus-daga-mukaminsa-na-shugaban-ecowas-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/karya-ce-tinubu-bai-yi-murabus-daga-mukaminsa-na-shugaban-ecowas-ba\/","title":{"rendered":"Karya ce! Tinubu bai yi murabus daga mukaminsa na shugaban ECOWAS ba"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Wani bidiyo da ya shuhura <a href=\"https:\/\/twitter.com\/Naija_PR\/status\/1809941860833480819?t=2ott1pxcdtEKN-dstyxNmQ&amp;s=19\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">a shafukan soshiyal mediya<\/a> na da\u2019awar cewa shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa na shugaba a Kungiyar Raya Tattalin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS).\u00a0<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"17979\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/false-nokia-3310-does-not-contain-gold\/false-4-16\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/FALSE-4.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-17979\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Hukunci: Karya! Tinubu bai yi murabus daga kujerar shugabancin ECOWAS ba. Bisa bayanan wata sanarwar da ECOWAS ta fitar, wa\u2019adinsa ya cika ne ranar tara ga watan Yulin 2024 amma an sake zabensa a wannan ranan. Kafofin yada labarai masu nagarta duk sun dauki labarin, kuma sun yi bayani makamancin wannan.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bola Tinubu, shi ne shugaban kasa mai ci yanzu a Najeriya, kuma shi ne ke <a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/news\/top-news\/608892-tinubu-emerges-as-new-ecowas-chair-calls-for-regional-security.html?tztc=1\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">jagorantar<\/a> ECOWAS tun watan Yulin shekarar 2023, bayan da ya karbi shugabancin daga hannun shugaban kasar Jamhuriyar Guinea Bissau, Umaro Embalo.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da shafin X, <a href=\"https:\/\/twitter.com\/Naija_PR\/status\/1809941860833480819?t=2ott1pxcdtEKN-dstyxNmQ&amp;s=19\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">@Naija_PR<\/a>, ya yi da\u2019awar cewa Tinubu ya yi murabus bayan da ya shafe shekara daya yana shugabancin kungiyar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya wallafa wannan bayanin da hoton Tinubun da tsokacin da ke cewa: \u201cLabari da dumi-dumi: Shugaba Tinubu ya sauka daga mukaminsa na shugaban ECOWAS.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ana iya ganin wannan da\u2019aawar a shafukan X da na Facebook, a <a href=\"https:\/\/x.com\/instablog9ja\/status\/1809915972741902796\">nan<\/a> da <a href=\"https:\/\/m.facebook.com\/groups\/mysoundmind\/posts\/breaking-president-tinubu-has-stepped-aside-as-ecowas-chairman\/1872667033295916\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Tun ranar 7 ga watan Yulin 2024 aka wallafa labarin kuma an kalla sau 131,000, an sake wallafawa a wasu shafukan sau 180 sa\u2019annan ya sami alamar like 1,000.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bisa la\u2019akari da shuhurar da wannan batun ya yi da ma yadda zai iya tasiri, DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiya a matsayin gangamin da ta take yi na yaki da bayanan karya a yankin Yammacin Afirka.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewaa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta fara da gudanar da binciken mahimman kalmomi. Sakamakon ya nuna mana cewa an <a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/news\/top-news\/609471-senate-congratulates-tinubu-on-emergence-as-ecowas-chairman.html?tztc=1\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">zabi <\/a>Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS din ne ranar tara ga watan Yulin 2023.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Dan tantance tsawon wa\u2019adin da mukamin ke da shi, mun duba babban shafin ECOWAS, (<a href=\"https:\/\/www.ecowas.int\/authority-of-heads-of-states\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ECOWAS\u2019s official website<\/a>) inda muka gano wani sakin layin da ke bayanin cewa \u201cMukamin shugaban kungiyar na yawo ne tsakanin kasashe mambobi kuma ana gudanar da zaben ne bayan kowace shekara.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Dan haka, tsawon lokacin da kowani zababben shugaba ke yi a kan kujerar mulkin ba ya taba wuce shekara daya. Bisa la\u2019akari da haka, ya kamata a ce da Mr Tinubu ya kammala wa\u2019adinsa ranar tara ga watan Yulin 2024 \u2014 sadda ya cika shekara daya a mukamin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta sake gano wata <a href=\"https:\/\/www.ecowas.int\/ecowas-heads-of-state-and-government-holds-65th-ordinary-session-in-abuja\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">sanarwar <\/a>da ECOWAS ta fitar da kanta ta na sanar da cewa ta sake zaben Mr Tinubu dan ya yi tazarce a mukamin na wani karin shekara dayan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan ya faru ne sadda suka gudanar da babban taron shugabannim kasashe da gwamnatocin&nbsp; ECOWAS karo na 65 wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa a ABuja.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bacin haka, kafofin yada labarai masu nagarta irin su <a href=\"https:\/\/www.channelstv.com\/2024\/07\/07\/just-in-tinubu-re-elected-as-ecowas-chairman\/#:~:text=President%20Bola%20Tinubu%20has%20been,Bissau%20on%20July%209,%202023\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Channels<\/a> da <a href=\"https:\/\/punchng.com\/breaking-tinubu-re-elected-ecowas-chairman\/?amp\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Punch<\/a> duk sun dauki labarin.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bincikenmu ya nuna mana cewa Tinubu bai yi murabus daga mukaminsa na shugaban ECOWAS ba. Ya kamata a ce ya kammala wa\u2019adinsa ne ranar tara ga watan Yulin 2024, kafin aka sake zaben shi.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani bidiyo da ya shuhura a shafukan soshiyal mediya na da\u2019awar cewa shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa na shugaba a Kungiyar Raya Tattalin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS).\u00a0 Hukunci: Karya! Tinubu bai yi murabus daga kujerar shugabancin ECOWAS ba. Bisa bayanan wata sanarwar da ECOWAS ta fitar, wa\u2019adinsa ya cika ne ranar tara ga watan Yulin 2024 amma an sake zabensa a wannan ranan. Kafofin yada labarai masu nagarta duk sun dauki labarin, kuma sun yi bayani makamancin wannan. Cikakken bayani Bola Tinubu, shi ne shugaban kasa mai ci yanzu a Najeriya, kuma shi ne ke jagorantar ECOWAS tun watan Yulin shekarar 2023, bayan da ya karbi shugabancin daga hannun shugaban kasar Jamhuriyar Guinea Bissau, Umaro Embalo. Wani mai amfani da shafin X, @Naija_PR, ya yi da\u2019awar cewa Tinubu ya yi murabus bayan da ya shafe shekara daya yana shugabancin kungiyar. Ya wallafa wannan bayanin da hoton Tinubun da tsokacin da ke cewa: \u201cLabari da dumi-dumi: Shugaba Tinubu ya sauka daga mukaminsa na shugaban ECOWAS.\u201d Ana iya ganin wannan da\u2019aawar a shafukan X da na Facebook, a nan da nan.&nbsp; Tun ranar 7 ga watan Yulin 2024 aka wallafa labarin kuma an kalla sau 131,000, an sake wallafawa a wasu shafukan sau 180 sa\u2019annan ya sami alamar like 1,000. Bisa la\u2019akari da shuhurar da wannan batun ya yi da ma yadda zai iya tasiri, DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiya a matsayin gangamin da ta take yi na yaki da bayanan karya a yankin Yammacin Afirka. Tantancewaa DUBAWA ta fara da gudanar da binciken mahimman kalmomi. Sakamakon ya nuna mana cewa an zabi Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS din ne ranar tara ga watan Yulin 2023. Dan tantance tsawon wa\u2019adin da mukamin ke da shi, mun duba babban shafin ECOWAS, (ECOWAS\u2019s official website) inda muka gano wani sakin layin da ke bayanin cewa \u201cMukamin shugaban kungiyar na yawo ne tsakanin kasashe mambobi kuma ana gudanar da zaben ne bayan kowace shekara.\u201d Dan haka, tsawon lokacin da kowani zababben shugaba ke yi a kan kujerar mulkin ba ya taba wuce shekara daya. Bisa la\u2019akari da haka, ya kamata a ce da Mr Tinubu ya kammala wa\u2019adinsa ranar tara ga watan Yulin 2024 \u2014 sadda ya cika shekara daya a mukamin. DUBAWA ta sake gano wata sanarwar da ECOWAS ta fitar da kanta ta na sanar da cewa ta sake zaben Mr Tinubu dan ya yi tazarce a mukamin na wani karin shekara dayan. Wannan ya faru ne sadda suka gudanar da babban taron shugabannim kasashe da gwamnatocin&nbsp; ECOWAS karo na 65 wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa a ABuja. Bacin haka, kafofin yada labarai masu nagarta irin su Channels da Punch duk sun dauki labarin.&nbsp; A Karshe Bincikenmu ya nuna mana cewa Tinubu bai yi murabus daga mukaminsa na shugaban ECOWAS ba. Ya kamata a ce ya kammala wa\u2019adinsa ne ranar tara ga watan Yulin 2024, kafin aka sake zaben shi.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":19413,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3803],"class_list":["post-19454","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-53M","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3803,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"mohammed-taoheed","display_name":"Mohammed Taoheed","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/ECOWAS-Chairperson.jpg?fit=1536%2C1016&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19454","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=19454"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19454\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":19455,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19454\/revisions\/19455"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/19413"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=19454"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=19454"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=19454"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=19454"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=19454"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}