{"id":19825,"date":"2024-08-27T11:12:07","date_gmt":"2024-08-27T10:12:07","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=19825"},"modified":"2024-08-27T11:12:11","modified_gmt":"2024-08-27T10:12:11","slug":"bidiyo-da-ya-nuna-trump-na-caccakar-tinubu-yana-kuma-yaba-wa-obi-hadawa-aka-yi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/bidiyo-da-ya-nuna-trump-na-caccakar-tinubu-yana-kuma-yaba-wa-obi-hadawa-aka-yi\/","title":{"rendered":"Bidiyo da ya nuna Trump na caccakar Tinubu yana kuma yaba wa Obi, hadawa aka yi"},"content":{"rendered":"\n<ol class=\"wp-block-list\"><\/ol>\n\n\n\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: A wani bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna yadda tsohon Shugaba Donald Trump na Amurka ke caccakar Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yana kuma yaba wa tsohon dantakarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam\u2019iyyar Labour, Peter Obi.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"18035\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/x-user-shares-a-false-claim-about-ovarian-disorder\/false-4-1\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/FALSE-4-1.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4-1\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/FALSE-4-1.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/FALSE-4-1.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-18035\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Hukunci: Karya ne! Wannan bidiyo da ya shahara a shafukan sada zumunta harhada shi kawai aka yi, asalin bidiyon ya kasance wani bangare ne na tattaunawar da aka yi da Shugaba Donald Trump a lokacin da ya cika kwanaki 100 a gadan mulkin Amurka a watan Afrilu na 2017.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Sakon<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A baya-bayan nan an samu wani bidiyo (video) a shafukan sada zumunta (platforms) inda aka nuna tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump yana kushe&nbsp; Mista Tinubu tare da yaba wa Mista Obi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A bidiyon Mista Trump na cewa tsohon gwamnan na Anambra ya fahimci me ake nufi da shugabanci fiye da shugaban Najeriya. A bidiyon an kuma nuna Mista Trump&nbsp; na cewa tsohon gwamnan Anambra ya fahimci shugabanci fiye da shugaban na Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cTinubu shine shugaba mafi rashin kan gado da Najeriya ta taba yi, idan Najeriya na son ci gaba dole ta nemo mutane masu hazaka da basira masu jini a jika irin Peter Obi wanda ya fahimci yaya tattalin arziki ke tafiya a gwamnatance da ma huldodin diflomasiya. \u201d A cewarsa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cBa tsofaffi ba wadanda basa iya tsayawa da kafarsu, wadanda ke bacci a lokacin taro , Najeriya na bukatar wani kamar Peter Obi muddin kasar na son ta ci gaba.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bidiyon ya kare da tafi daga \u2018yankallo.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mista <a href=\"https:\/\/www.bbc.com\/news\/world-africa-61865502\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Obi<\/a> shine dantakarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023 karkashin inuwar jam\u2019iyyar Labour. Ya samu goyon bayan matasa wadanda ake kiransu da sunan <a href=\"https:\/\/www.dw.com\/en\/peter-obis-obidient-movement-ignites-nigerias-youth\/a-63375362\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Obidients<\/a>, sun yi masa yakin neman zabe babu kakkautawa a zaben da ya gabata.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mista <a href=\"https:\/\/punchng.com\/inec-declares-tinubu-winner-of-presidential-election\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Tinubu<\/a> yayi yakin neman zabe karkashin inuwar jam\u2019iyyar APC a 2023 inda kuma yayi nasara kamar yadda Hukumar Zabe mai Zaman Kanta INEC ta bayyana.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan sakamako shine abin da ya fuskanci suka da kalubalanta a kotun koli&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.aljazeera.com\/news\/2023\/10\/26\/nigerias-supreme-court-affirms-tinubus-presidential-victory\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Court<\/a>, anan ne kuma aka jaddada masa nasarar zaben.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai kasa da shekaru biyu Mista Tinubu ya fuskanci kalubale da suka ta fuskoki da dama inda al\u2019ummar kasar ke sukar gwamnatinsa saboda sanadi na tsadar rayuwa da hauhawar farashi (<a href=\"https:\/\/nigerianstat.gov.ng\/elibrary\/read\/1241533\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">inflation<\/a>,) wadanda ake alakantawa da cire tallafin manfetir (<a href=\"https:\/\/www.bbc.com\/news\/world-africa-65737846\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">petrol subsidy<\/a>) da kyale Naira ta sama wa kanta daraja.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ganin yadda al\u2019umma ke ji a jika saboda matsi na tattalin arziki, wasu \u2018yan Najeriya sun shiga zanga-zanga (<a href=\"https:\/\/www.thisdaylive.com\/index.php\/2024\/07\/30\/august-1-protest-and-nigerian-youths-defiance-in-quest-for-equitable-society-effective-leadership\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">protest<\/a>) daga ranar 1 ga watan Agusta don jan hankalin gwamnati kan halin matsin rayuwa da suke ciki.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da dama cikin masu zanga-zangar sun bayyana gwamnatin ta Tinubu a matsayin mara kan gado inda suka bukaci (<a href=\"https:\/\/www.thecable.ng\/protest-may-go-beyond-10-days-if-demands-arent-addressed-say-organisers\/amp\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">demanded<\/a>) a ci gaba da biyan kudaden tallafin manfetir.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ana tsaka da wannan zanga-zanga ce kwatsam sai ga bidiyon Mista Trump na kushe gwamnatin Tinubu abin da ya dauki hankali musamman ga wadanda dama ke adawa da shugaban na Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Amma abin tambaya a nan shine, shin wannan bidiyo na gaskiya ne? Ganin irin tasirinsa ya sa DUBAWA ganin dacewar gudanar da bincike a kansa don tabbatar da sahihancinsa.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ya lura cewa yadda maganar ke fita ta sha banban da yadda leben Trump ke motsi, wannan ya nuna an samar da maganar&nbsp; ne aka cusa a bidiyon, abin da ya tabbatar da cewa bidiyon da aka yada hada shi aka yi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA har ila yau ya gudanar da bincike ta hanyar amfani da dabarun gano asalin hoto na Google inda anan aka gano cewa asalin bidiyon an samo shi ne daga wata tattaunawa da aka yi da Trump&nbsp; (<a href=\"https:\/\/www.today.com\/video\/trump-talks-about-north-korea-afghanistan-health-care-i-love-governing-942347331837\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">exclusive interviews<\/a>,) inda kai tsaye ake tattaunawa da shi kan kamun ludayin gwamnatinsa a watan Mayu,2017.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">An yada wannan tattaunawa a kafar yada labarai ta NBC kamfanin yada labarai na talabijin da rediyo a kasar ta Amurka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;Da aka ci gaba da bincike kuma an gano cewa babu inda Mista Trump yayi wata magana kan gwamnatin ta Shugaba Tinubu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">A <strong>Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;Bidiyo da aka yada da ya nuna Mista Trump na caccakar Tinubu hadawa aka yi don haka karya ce, asalin bidiyon an fito da shi ne daga wata tattaunawa da aka yi da Trump a 2017 lokacin da ya cika kwanaki 100 a gadon mulkin Amurka.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: A wani bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna yadda tsohon Shugaba Donald Trump na Amurka ke caccakar Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yana kuma yaba wa tsohon dantakarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam\u2019iyyar Labour, Peter Obi. Hukunci: Karya ne! Wannan bidiyo da ya shahara a shafukan sada zumunta harhada shi kawai aka yi, asalin bidiyon ya kasance wani bangare ne na tattaunawar da aka yi da Shugaba Donald Trump a lokacin da ya cika kwanaki 100 a gadan mulkin Amurka a watan Afrilu na 2017. Cikakken Sakon A baya-bayan nan an samu wani bidiyo (video) a shafukan sada zumunta (platforms) inda aka nuna tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump yana kushe&nbsp; Mista Tinubu tare da yaba wa Mista Obi. A bidiyon Mista Trump na cewa tsohon gwamnan na Anambra ya fahimci me ake nufi da shugabanci fiye da shugaban Najeriya. A bidiyon an kuma nuna Mista Trump&nbsp; na cewa tsohon gwamnan Anambra ya fahimci shugabanci fiye da shugaban na Najeriya. \u201cTinubu shine shugaba mafi rashin kan gado da Najeriya ta taba yi, idan Najeriya na son ci gaba dole ta nemo mutane masu hazaka da basira masu jini a jika irin Peter Obi wanda ya fahimci yaya tattalin arziki ke tafiya a gwamnatance da ma huldodin diflomasiya. \u201d A cewarsa. \u201cBa tsofaffi ba wadanda basa iya tsayawa da kafarsu, wadanda ke bacci a lokacin taro , Najeriya na bukatar wani kamar Peter Obi muddin kasar na son ta ci gaba.\u201d Bidiyon ya kare da tafi daga \u2018yankallo. Mista Obi shine dantakarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023 karkashin inuwar jam\u2019iyyar Labour. Ya samu goyon bayan matasa wadanda ake kiransu da sunan Obidients, sun yi masa yakin neman zabe babu kakkautawa a zaben da ya gabata. Mista Tinubu yayi yakin neman zabe karkashin inuwar jam\u2019iyyar APC a 2023 inda kuma yayi nasara kamar yadda Hukumar Zabe mai Zaman Kanta INEC ta bayyana.&nbsp; Wannan sakamako shine abin da ya fuskanci suka da kalubalanta a kotun koli&nbsp; Court, anan ne kuma aka jaddada masa nasarar zaben. Sai dai kasa da shekaru biyu Mista Tinubu ya fuskanci kalubale da suka ta fuskoki da dama inda al\u2019ummar kasar ke sukar gwamnatinsa saboda sanadi na tsadar rayuwa da hauhawar farashi (inflation,) wadanda ake alakantawa da cire tallafin manfetir (petrol subsidy) da kyale Naira ta sama wa kanta daraja. Ganin yadda al\u2019umma ke ji a jika saboda matsi na tattalin arziki, wasu \u2018yan Najeriya sun shiga zanga-zanga (protest) daga ranar 1 ga watan Agusta don jan hankalin gwamnati kan halin matsin rayuwa da suke ciki. Da dama cikin masu zanga-zangar sun bayyana gwamnatin ta Tinubu a matsayin mara kan gado inda suka bukaci (demanded) a ci gaba da biyan kudaden tallafin manfetir. Ana tsaka da wannan zanga-zanga ce kwatsam sai ga bidiyon Mista Trump na kushe gwamnatin Tinubu abin da ya dauki hankali musamman ga wadanda dama ke adawa da shugaban na Najeriya. Amma abin tambaya a nan shine, shin wannan bidiyo na gaskiya ne? Ganin irin tasirinsa ya sa DUBAWA ganin dacewar gudanar da bincike a kansa don tabbatar da sahihancinsa.&nbsp; Tantancewa DUBAWA ya lura cewa yadda maganar ke fita ta sha banban da yadda leben Trump ke motsi, wannan ya nuna an samar da maganar&nbsp; ne aka cusa a bidiyon, abin da ya tabbatar da cewa bidiyon da aka yada hada shi aka yi. DUBAWA har ila yau ya gudanar da bincike ta hanyar amfani da dabarun gano asalin hoto na Google inda anan aka gano cewa asalin bidiyon an samo shi ne daga wata tattaunawa da aka yi da Trump&nbsp; (exclusive interviews,) inda kai tsaye ake tattaunawa da shi kan kamun ludayin gwamnatinsa a watan Mayu,2017. An yada wannan tattaunawa a kafar yada labarai ta NBC kamfanin yada labarai na talabijin da rediyo a kasar ta Amurka. &nbsp;Da aka ci gaba da bincike kuma an gano cewa babu inda Mista Trump yayi wata magana kan gwamnatin ta Shugaba Tinubu. A Karshe &nbsp;Bidiyo da aka yada da ya nuna Mista Trump na caccakar Tinubu hadawa aka yi don haka karya ce, asalin bidiyon an fito da shi ne daga wata tattaunawa da aka yi da Trump a 2017 lokacin da ya cika kwanaki 100 a gadon mulkin Amurka.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":19629,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4142],"class_list":["post-19825","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-59L","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4142,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"taiwo-adeyemi","display_name":"T\u00e1\u00edw\u00f2 Ad\u00e9y\u1eb9m\u00ed","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/08\/Donald-pres.jpg?fit=874%2C949&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19825","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=19825"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19825\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":19826,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/19825\/revisions\/19826"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/19629"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=19825"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=19825"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=19825"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=19825"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=19825"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}