{"id":20559,"date":"2024-10-25T23:41:01","date_gmt":"2024-10-25T22:41:01","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=20559"},"modified":"2024-10-25T23:41:04","modified_gmt":"2024-10-25T22:41:04","slug":"ayyukan-da-yar-majalisa-ireti-kingibe-ta-birnin-tarayya-abuja-tayi-daawar-aikatawa-karya-ta-jagoranci-gaskiya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/ayyukan-da-yar-majalisa-ireti-kingibe-ta-birnin-tarayya-abuja-tayi-daawar-aikatawa-karya-ta-jagoranci-gaskiya\/","title":{"rendered":"Ayyukan da \u2018yar majalisa Ireti Kingibe ta Birnin Tarayya Abuja tayi da\u2019awar aikatawa Karya ta jagoranci Gaskiya"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ireti Kingibe, \u2018yar majalisa daga jam\u2019iyyar Labour Party da ta cika shekara guda akan kujerarta a majalisa a ranar 12 ga watan Yuni, 2024. Makonni kadan da suka gabata ta gudanar da bikin cika shekara guda a kan kujera inda anan ta gabatar da abubuwan da ta cimma da suka hadar da kudirai da ta gabatar a majalisa da ayyuka da ta gabatar a mazabarta kamar yadda ta wallafa a shafinta na <a href=\"https:\/\/x.com\/IretiKingibe\/status\/1811808006696239584\">X account<\/a> (<a href=\"https:\/\/perma.cc\/HY5B-5SLL\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">archived<\/a>).<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Cikin ayyukan da ta ce ta aiwatar sun hadar da aikin gina hanya a Kpaduma, da Karu da Gwagwalada. Haka kuma ta lisafo aikin samar da hasken lantarki a tituna a Karamajiji da Mpape da Kwali da Jikwoyi da aikin samar asibiti mai gadaje 50 a Dobi da gina dakin kwanciya a asibitin Abuja da ke a Gwagwalada kamar yadda ta zayyano cikin abubuwan da ta cimma.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Cikin abubuwa da DUBAWA ta lura da su ta gano cewa \u2018yar majalisar ta zayyano ayyuka 29 baki daya, mafi akasari ba ta bayyana inda aka yi ayyukan ba, amma DUBAWA ta gudanar da bincike kan ayyuka guda tara da ke zama sanannu.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXcgUjFkgr4D5y8yIuPJWVXE-APORB80-mcF48rK3HXkVJmyDIpJG80BG4mZRrVxqh-k68wnco4l-ZJM4sFslmDuCWWpNlTgH6jC5cdFTz2SBWW18jeTxm2SZK0fm_c_dmsJU422L17FatJzjX3DYt7rxiwD?key=ClppMBS_SAkQzbdJfqpnhw\" alt=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts\" title=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts 2\"\/><\/figure>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Da\u2019awa da ke zama ta gaskiya<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><br><\/strong>Daga cikin ayyuka guda tara DUBAWA ta gano ayyuka guda uku da ke zama na gaskiya. Mun fara da aikin gina asibiti mai gadaje 50 a Dobi da Gwagwalada wadanda sanatar ta ce&nbsp; aikin ana ci gaba da \u201cgudanar da shi.\u201d A farkon watan Agusta mai dauko rahoto ya je wurin da ake aikin inda ya ga cewa ana kan aikin ba a kammala ba. Inda ake aikin ba shi da nisa da wata cibiyar kula da lafiya a yankin.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" alt=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXfABkkhTFgIZgWhWM7CtbRGdz1YUBil_u9dVrg_mP9Zv5gFZxhWDAgCsM3LNwTuBr0fVNIOSUjJTvgfP85KAP46XPCbL7YOaX98sXS50D1WBIsnJSgrccl_9GKrWVGZDumKy4zo6D8VNmdf76VJwB_n47fM?key=ClppMBS_SAkQzbdJfqpnhw\" width=\"602\" height=\"451\" title=\"\"><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Aikin gina asibiti mai gadaje 50. Wanda ya dauki hoto: Phillip Anjorin<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A aiki na biyu da aka tabbatar. mun je aikin gina hanya ta&nbsp; Ishan Road a Karu sannan an tabbatar da rahotanni (<a href=\"https:\/\/leadership.ng\/sen-kingibe-commissions-road-project\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">reports<\/a>) na gina hanya mai kwalta mai nisan kilomita 6, daga nan sai muka nufi yankin Karamajiji inda tayi da\u2019awar cewa ta samar da fitulu 23 wanda ke zama na uku cikin ayyukan da muka tabbatar.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta ga fitila ta farko a hanyar shiga yankin al\u2019ummar wacce aka bata lamba ta 12, wadannan fitulu na jere kusa da juna.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><img decoding=\"async\" alt=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXdDnGxgGxvCEXCf5SIZ4RI8ZkQitJd39VCgFpqfdro8PyRgbjE7ZET8gKfqCuRp81rVNxAFQh1bJSAfpWtEZ-s7kgkO1IYC9D23p-YIEEESW1RSTLCOwfsy5tYwtIQYsclHDegIrSueAjZTKv6yucHei6OB?key=ClppMBS_SAkQzbdJfqpnhw\" width=\"602\" height=\"504\" title=\"\"><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Fitilun titi a Karamajiji. Wanda ya dau hoto: Phillip Anjorin<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ta bayyana cewa an sanya fitilun titi 23 a Anagie da Sangaruwa da Ajegunle da Gbagi village da&nbsp; Mashapa. DUBAWA ta tabbatar da ganin fitilu hudu a Gbagi village, yayin da a sauran wuraren babu labarin ganin wata fitialar titin a bangaren, al\u2019ummar yankin ma sun tabbatar da cewa basu ga wani aiki ba mai kama da wannan.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Wurin da aka ga wallenta<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Anthony Udeh, mai tuka babur na haya a yankin Jikwoyi da ke a wajen Abuja, yayi gatsine ne lokacin da mai aiko mana da rahoto ya bayyana cewa ai \u2018yar majalisa daga yankin ta gina hanya mai nisan kilomita 1.5 a Phase 1. A lokacin da yake tafiya a wannan yanki da ake fadi, yayi da\u2019awar cewa shekara guda da ta gabata yayi hadari akan wannan hanya sai da aka garzaya da shi zuwa asibiti ya kwashe watanni uku. Bayan da muka isa hanyar, ya bayyana cewa tituna a wasu rukunan na Jikwoyi an masu kwalta shekaru biyu da suka gabata , amma a rukunin farko phase 1&nbsp; an dai kawo mota ta share titun don kaucewa zaizayar kasa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cA tsawon sama da shekara guda ban taba ganin wani babban inji wanda zai yi aiki a kan gyara wannan titi ba, ballantana ayi maganar gina titi sai dai idan share titi na nufin an gina titi kenan.\u201d kamar yadda ya fada a turancin pidgin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hanya kuwa a Jikwoyi Phase 1 ta zaizaye babu wata alama da ta nuna cewa ana aikin gina hanya, a tsawon shekara guda da ta gabata ko ya zuwa watan Agusta 2024. Sai dai abin da ke a zahiri DUBAWA ta lura da cewa an kafa alama ko allo a kan hanyar: Da suna&nbsp; \u201c Aikin kare zaizayar kasa a hanyar God of Elijah, Jikwoyi a Abuja Fadar Gwamnatin Tarayya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><img decoding=\"async\" alt=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXcb24kuIpUoasqWWyn3Y-QBqflsfF7hXO8sVCSb3px--MG721ZwuiCvUvGoHs_vfLJFhJiKd7p27tk_dBo9YKKQUCa4TDB2e354bVUAG_bwNjzDZp2RQu4jbSh2OHL9ulQm9tkOqY-vRHT1aTUXBQLGtxM?key=ClppMBS_SAkQzbdJfqpnhw\" width=\"602\" height=\"504\" title=\"\"><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Jikwoyi Phase 1. Wanda ya dauki hoto: Phillip Anjorin<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta tabbatar da cewa hanyoyin da ta fada dama anyi masu kwalta tun tuni idan aka cire ta Jikwoyi Phase 1. Har ila yau wanda ta gada Philip Aduda na jam\u2019iyyar PDP shi ya tabbatar da ganin ayi su a kudurin kasafin kudi na 2023 wanda aka sawa hannu ya zama doka a ranar 3 ga watan Janairu,2023. Mun samu bayanai daga <a href=\"https:\/\/www.tracka.ng\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Tracka<\/a>, wata kafa da ke bibiyar ayyukan da ake yi a cikin al\u2019umma don tabbatar da ganin an yi su.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A 2023 ayyukan gwamnatin tarayya na yankunan al\u2019umma da kudaden da aka ware don aiwatarwa (<a href=\"https:\/\/s3.eu-west-2.amazonaws.com\/tracka-mobile-images\/assets\/uploads\/documents\/trackadocOeYOeB3zPr92huJ.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">consolidated capital projects<\/a>) a birnin tarayya an warewa aikin gina hanya ta Jikwoyi Phase 1 Naira miliyan 90 da lambar aikin ERGP202301237 a lokacin Aduda. Hukumar da ke lura aikin itace ta raya kogin Niger (Upper Niger River Basin Development Authority (RBDA), an ba da N7,616,744.18 a ranar 14 ga watan Agusta,2023, don fara aikin gina hanyar mai kwalta kamar yadda yake a <a href=\"https:\/\/www.govspend.ng\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">GovSpend<\/a>, wata kafa da ke ba da bayanai kan yadda gwamnatin tarayya ke kashe kudadenta.KO da yake a lokacin Kingibe tana sanata, a lokacin Aduda ne ya sanya aikin a kasafin kudi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Haka nan shima hanyoyi da kwalbati a Kpaduma 1 da 3,&nbsp; wanda shima tayi da\u2019awar aiwatarwa. Naira miliyan 100 aka ware don ginin hanyoyin a 2023 da lambar ZIP20231339 kuma ana ci gaba da wannan aiki tun a ranar 29 ga watan Dismba, 2022, inda aka saki kudade N45,469,767.45.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta je wurin sai ta gano cewa an yi wani bangare na aikin. Shi kansa wannan fara aikin bai nuna alamar na baya-bayan nan ba ne. Haka allo da ke nuna shedar wanda yayi aiki ya nuna cewa Mista Aduda ne yayi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" alt=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXduKpdoHTO6DpO4XreH0UGFD1HTFk11x-FhtUPz23aTelFYK8Xq4HItoNOHICJGO7geo9nlVrF6t7nci7luKVnFR-HKzpqDDCXx7Mbk5M_pQ7lJUDWp637_BpD6x_7louPd403lldvcT2128uHiSiDIQPYh?key=ClppMBS_SAkQzbdJfqpnhw\" width=\"602\" height=\"504\" title=\"\"><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Allo da aka kafa a Kpaduma 1 &amp; 3. Wanda ya dauki hoton: Phillip Anjorin<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ko da yake bamu samu shedu ba kan kudade da aka ware don aikin Pai a Kwali daga kafar samun bayanan ta GovSpend, mun gano cewa an ware Naira miliyan 100 don aikin gina hanya da hanyoyin ruwa ko kwalbati a ayyukan da za a yi a 2023 inda aka ba wa aikin lamba ERGP202301236 kamar yadda yake a bayanan Tracka, a wannan lokaci Aduda ne sanata an kuma bayyana shi a matsayin \u201caikin da ake tsaka da yinsa\u201d lokacin da muka je wajen mun gano cewa an yi rabin aikin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" alt=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXdEYstNMMK3BVHnr2SEPJZ5Rdhftd1kCSGSAsAEEMWjuOOhBsnVBNqW9O4Odj0IdVlV58WdnoK4Xp_LR5vtjVnZJ2mgAI8pTMMtmxHsXC4ZfbbNJBB-__yaZWA3trL4MP-UmufYOPT7zSpvbvLiExLJ3pd3?key=ClppMBS_SAkQzbdJfqpnhw\" width=\"602\" height=\"803\" title=\"\"><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Allo da ke nuna aikin gina hanya a Pai, Kwali. Wanda ya dauki hoto: Phillip Anjorin<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Ms Kingibe ta yi da\u2019awar gina ofishin kwararun likitoci a asibitin koyarwa na Abuja da ke Gwagwalada, amma ba ta bayyana cewa ana yin aikin bane.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Har ila yau bayanai da aka tattara sun nunar da cewa Mista Aduda ne ya jagoranci wannan aiki kamar yadda aka gani a Tracka. Ga ma lambar aikin ERGP202301233, an kuma ware masa Naira miliyan 100.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;A ranar 3 ga Disamba, 2023 GovSpend ta bayyana cewa an ware kudi N72,159,994.5&nbsp; don wannan aiki, abin da ya hadar da harajin aikin, da tsarin zanensa da ginawa, watanni shida daga bisani kuma aka sake biyan N18,893,874.92 don ci gaba da aikin. Baki daya abin da aka kashe N91,053,869.42. Kamar yadda aka fadi a baya wannan ya sa aka ga rashin gaskiyar da\u2019awar sanatar na bayyanar aikin cikin nasarar da ta cimma.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" alt=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXegUT9_wsYlc0Oc-2Os1JdaNWKOIn-anNEaufl1aLoq8PYYckGZthLXHfoQwk0CVzSgvivXXWsQvI0hkjpwFYtukG7Oozq7NoNGOeTqXoMn0aqatMXNSsNKPQVshCSPPjR57LDgWrEmfj55AQQr7kZdnPpk?key=ClppMBS_SAkQzbdJfqpnhw\" width=\"602\" height=\"451\" title=\"\"><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Ofishin kwararru a Asibitin Koyarwa na Jami\u2019ar Abuja. Mai hoto : Phillip Anjorin<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;Haka zalika sanatar ta yi da\u2019awar kammala aikin hanyar Angwan Dodo, amma DUBAWA ta gano yadda aka kammala aikin. Amma kafin ta zama sanata an ware miliyan N150, ga ma lambar aikin ERGP202301239 kamar yadda yake a kan Tracka.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" alt=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXfL-LxT7fzL6IS5W9kuxsfRpSxL4u1zNhUIgeVyAr_FXw_zrxr1S--2gHEqFjpFFRwNfmn3sSm7lnC6VlCFSjpKdZvuGod20KHKKnCF-tfKkNMyGEnPifnwu67jGnXEQwsHUInvhSUSortcHMWQf6cnBID_?key=ClppMBS_SAkQzbdJfqpnhw\" width=\"602\" height=\"389\" title=\"\"><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Jadawali da ke nuna yadda ake tsara kudade da ake kashewa da yadda ake sakin kudaden don aikin kammala hanyar\u00a0 Angwan Dodo. Wanda ya tsara Phillip Anjorin<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayanai da aka tattaro daga GovSpend sun nunar da cewa an fara biyan kudaden aikin tun 12 ga Disamba,2020 lokacin da aka ba da kudi N27,065,861.61 don aikin gina hanya mai tsawon kilomita 1.3km. Domin aiwatar da aikin mai tsawon kilomita 1.3km a 2021. Gwamnatin Tarayya ta saki kudi N38,649,234.10 a ranar 25 ga watan Maris sai ta sake sakin N31,544,509.22 a ranar 4 ga Oktoba sai kuma N29,935,452.07 a ranar 29 ga Fabrairu, 2022. Ya zuwa 14 ga Agusta, 2023 gwamnatin Tarayya ta fara aikin sakin kudade don tsara kammala ayyukan, wanda aka kashe N8,030,697.69. An saki kudade sama da miliyan N127 don kammala aikin ya zuwa 20 ga Maris,2024 ga ma lambar aikin kwantiragin ERGP202301239.&nbsp;&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" alt=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXexxU8NDrlGw2oen-5ZBSWbYffR4c1CB0rBnecJ51CK4NOOoafm6BE4Pwv9y7F0s1uicCeoJ_NEk1JzL_pZIF4rpj_0ldhESHR9d-DCjkWDNs6aNRqlH-hlD9z2WVhlOqRHsLDJVEHXAp5h938MJF6LFrQ9?key=ClppMBS_SAkQzbdJfqpnhw\" width=\"602\" height=\"539\" title=\"\"><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Kasafi-kasafi na ayyukan mazaba da aka gudanar da binciken gaskiya a kansu. Wanda ya tsara Phillip Anjorin<\/strong><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Bayani kan ayyukan mazabu<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Ayyukan mazabu a Najeriya, ayyuka ne da gwamnatin tarayya ke daukar nauyinsu&nbsp; wadanda kan inganta rayuwar al\u2019umma da suka fito daga mazabun \u2018yanmajalisar tarayya. Tun bayan da aka dawo tafarkin dimukuradiyya a 1999, an ware miliyoyi dubbai na naira ta yadda za a tabbatar da ganin al\u2019umma sun amfana kai tsaye daga kudaden da gwamnati ke kashewa.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Babbar manufar irin wadannan ayyuka shine a tabbatar da ganin al\u2019umma sun amfana da ayyuka na gwamnati kamar a fannoni irin su samar da ababen more rayuwa da fannin lafiya da ilimi da tallafin ayyukan gona wadanda \u2018yanmajalisa kan gabatarwa wasu ma\u2019aikatu don tabbatar da ganin an aiwatar.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Duk da cewa wasu rahotanni sun yi nuni da cewa an ware tsabar kudade tiriliyan 2 don gudanar da irin wadannan ayyuka (<\/strong><a href=\"https:\/\/www.vanguardngr.com\/2024\/03\/constituency-project-stink-how-lawmakers-pad-budgets-make-billions\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>constituency projects<\/strong><\/a><strong>) tun daga 2003 zuwa yau, inda aka ware ayyuka sama da 18,000 a fadin Najeriya, da dama irin wadannan ayyuka ba a yi su ba, koma an yi almundahna wajen aiwatarwa (<\/strong><a href=\"https:\/\/www.thisdaylive.com\/index.php\/2022\/08\/08\/lack-of-awareness-corruption-responsible-for-poor-execution-of-constituency-projects-says-budget-expert\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>poorly implemented<\/strong><\/a><strong>,). Abin da ya jawo lalata dukiyar al\u2019umma.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Dukkanin shugabannin Najeriya da suka gabata in ban da Umaru Yar\u2019adua sun soki wannan tsari har wanda ke a gaba wato <\/strong><a href=\"https:\/\/www.thisdaylive.com\/index.php\/2017\/08\/14\/obasanjo-lawmakers-constituency-project-is-corruption\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Olusegun Obasanjo<\/strong><\/a><strong>.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Har ila yau Lukman Raji wani lauya kuma darakta a fannin shari\u2019a a cibiyar Elites Network for Sustainable Development (ENetSuD), ya bayyana cewa aikin wanda ake kira Zonal Intervention Project (ZIP)-ba aiki bane da \u2018yanmajalisa suka kirkira, amma aiki ne na hadin gwiwa tsakanin majalisar zartarwa da majalisar dokoki.\u201dTsari ne da aka fito da shi don a tabbatar da ganin cewa al\u2019umma sun sharbi roman dimukuradiyya a mazabunsa.\u201d<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Ko da yake a tsarin kundin mulkin kasa babu wani aiki wai shi na mazabu, Mista Raji yace \u2018yanmalisa na gabatar da shi kamar wasu nasarori da suka cimma, wannan na iya zama yaudara.\u201dYanmajalisa na gabatar da su ga al\u2019umma a matsayin su suka yi su, har wasu lokutan suna alfahari wanda ba haka lamarin&nbsp; yake ba, burin da ake da shi shine a kai aiki ga al\u2019umma na mazabu ba wai danmajalisa ya rika nuna cewa shi yayi ba, wannan ne&nbsp; ya sanya ake ganin ayyukan da ake a mazabu a matsayin wani makami ga dan siyasa sabanin ace ana yinsu ne don samar da ci gaba a yankunan na mazabu.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>&nbsp;A cewar Ijeoma Okereke, manaja a cibiyar bibiyar ayyuka ta UDEME Africa da ke duba ayyuka karkashin CJID, ta kara da ba da bayani kan aiwatar da ayyuka, tace ko da danmajalisa ya kammala wa\u2019adin mulkinsa ayyukan da suke lura da su za su ci gaba da bibiya muddin an ba da kudaden aiwatarwa.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Ta kara da cewa \u201cIdan dan majalisa ya kammala wa\u2019adin mulkinsa, irin wadannan ayyuka za su ci gaba saboda ai dama an riga an saki kudade don gudanar da ayyukan daga ma\u2019aikatar kudi da kasafi zuwa ga ma\u2019aikatu da hukumomi da aka dorawa alhakin gudanar da ayyukan.\u201d<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Kazalika tace&nbsp; danmajalisa da ya gaji wani zai ci gaba da lura da irin wadannan ayyuka yayin da a bangare guda kuma dan majalisar shi ma zai gabatar da nasa aikin idan ya lura da akwai bukatar yin hakan.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>\u201cMuna bukatarsu\u201d- Mazauna yankuna&nbsp;<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Yankunan al\u2019ummar guda biyar da Ms Kingibe ta bayyana a Mpape basu da hanyoyi masu kyau da masu amfani da babura za su yi amfani da su musamman da dare,ba gaskiya ba ne an sanya fitilun titi, Eunice Adelabu mai sana\u2019ar POS a Ajegunle tace ta daina kasuwanci da dare tun bayan da aka yi mata fashi a watan Afrilu, watan da ya gabata ne ta dawo bakin aiki.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Ta kara da cewa \u201dMasu sana\u2019ar tukin babur sun dena shigowa wannan hanya da daddare saboda munin hanyar, idan da a ce an samar da haske a hanyar da za su rika iya bin hanyar suna kaucewa ramuka, rashin masu baburan ya sanya har aka yi min fashi, ai da na bar hanyar da wuri.\u201d<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" alt=\"Ireti Kingibe\u2019s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXeiKoDS2k-vD_AR0G-FNCgyI__dGDdVPdUc9LhCiIbyhBR3dWVicMl0DpDQN-_sIq6UK8plWAaO7wAJPNcFwu5CQhjcZidPmOK079q5frWLSBuVP-zzCJX80lPlc8W76on-65sSyX9ibm0hR8OaTA962YxW?key=ClppMBS_SAkQzbdJfqpnhw\" width=\"602\" height=\"253\" title=\"\"><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Yadda hanyoyi suke a yankunan al\u2019ummar Mpape. Wanda ya dauki hotunan Phillip Anjorin.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Yakubu Aliu, manomi ne a Ledi, ya ce idan aka kammala aikin gina asibitin Dobi cikin gaggawa zai taimaka mana wajen kula da lafiyarmu.\u201d Idan aka samar da isassun ma\u2019aikatan lafiya sabon asibitin zai taimaka ganin yadda ake samun cikowa a cibiyar kula da lafiya ta Dobi, musamman ga al\u2019umma da ke zama makota za su fi amfana da wannan asibiti sabanin suce sai sun je Asibitin Gwagwalada.\u201d<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Duk da abin da ya fada tun da fari Mista Udeh yace yana fatan ganin an kammala aikin hanyar ta Jikwoyi Phase 1 don samun saukin zirga-zirga.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Aduda ya ciri tuta, Kingibe ta kwashi kunya<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>An yi kokari a lokuta da dama don yin magana da Ms Kingibe ta kiran wayar hannu da WhatsApp amma bata dauki wayar ba. Mun kuma aika mata da sako ta Twitter da e-mail amma babu wata amsa da ta bayar har lokacin hada wannan rahoto. Da muka tuntubi mai taimaka mata kan harkokin yada labarai Kennedy Nwankwo, yace zai tuntube mu bayan tuntubar mai kula da aikin a ranar 2 ga Oktoba,2024, shima babu abin da muka ji daga gare shi lokacin kammala wannan rahoto.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>A tattaunawa ta wayar hannu da DUBAWA tayi da Mista Aduda yace ayyukan da ake da\u2019awa sun kasance wani bangare ne na ayyukan da shi da abokin aikinsa a majalisa suka amince da su .\u201dKasafin 2023 an amince da shi kafin ma sabuwar gwamnati ta zo a watan Yuni. A lokacin da ni\u00a0 nake kan kujerar, ina tabbatar da cewa an fara aiwatar da kasafin kafin ma wa\u2019adin mulkinta ya fara.\u201d A cewarsa.<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ireti Kingibe, \u2018yar majalisa daga jam\u2019iyyar Labour Party da ta cika shekara guda akan kujerarta a majalisa a ranar 12 ga watan Yuni, 2024. Makonni kadan da suka gabata ta gudanar da bikin cika shekara guda a kan kujera inda anan ta gabatar da abubuwan da ta cimma da suka hadar da kudirai da ta gabatar a majalisa da ayyuka da ta gabatar a mazabarta kamar yadda ta wallafa a shafinta na X account (archived). Cikin ayyukan da ta ce ta aiwatar sun hadar da aikin gina hanya a Kpaduma, da Karu da Gwagwalada. Haka kuma ta lisafo aikin samar da hasken lantarki a tituna a Karamajiji da Mpape da Kwali da Jikwoyi da aikin samar asibiti mai gadaje 50 a Dobi da gina dakin kwanciya a asibitin Abuja da ke a Gwagwalada kamar yadda ta zayyano cikin abubuwan da ta cimma. Cikin abubuwa da DUBAWA ta lura da su ta gano cewa \u2018yar majalisar ta zayyano ayyuka 29 baki daya, mafi akasari ba ta bayyana inda aka yi ayyukan ba, amma DUBAWA ta gudanar da bincike kan ayyuka guda tara da ke zama sanannu.&nbsp; Da\u2019awa da ke zama ta gaskiya Daga cikin ayyuka guda tara DUBAWA ta gano ayyuka guda uku da ke zama na gaskiya. Mun fara da aikin gina asibiti mai gadaje 50 a Dobi da Gwagwalada wadanda sanatar ta ce&nbsp; aikin ana ci gaba da \u201cgudanar da shi.\u201d A farkon watan Agusta mai dauko rahoto ya je wurin da ake aikin inda ya ga cewa ana kan aikin ba a kammala ba. Inda ake aikin ba shi da nisa da wata cibiyar kula da lafiya a yankin.&nbsp; Aikin gina asibiti mai gadaje 50. Wanda ya dauki hoto: Phillip Anjorin A aiki na biyu da aka tabbatar. mun je aikin gina hanya ta&nbsp; Ishan Road a Karu sannan an tabbatar da rahotanni (reports) na gina hanya mai kwalta mai nisan kilomita 6, daga nan sai muka nufi yankin Karamajiji inda tayi da\u2019awar cewa ta samar da fitulu 23 wanda ke zama na uku cikin ayyukan da muka tabbatar.&nbsp; DUBAWA ta ga fitila ta farko a hanyar shiga yankin al\u2019ummar wacce aka bata lamba ta 12, wadannan fitulu na jere kusa da juna. Fitilun titi a Karamajiji. Wanda ya dau hoto: Phillip Anjorin Ta bayyana cewa an sanya fitilun titi 23 a Anagie da Sangaruwa da Ajegunle da Gbagi village da&nbsp; Mashapa. DUBAWA ta tabbatar da ganin fitilu hudu a Gbagi village, yayin da a sauran wuraren babu labarin ganin wata fitialar titin a bangaren, al\u2019ummar yankin ma sun tabbatar da cewa basu ga wani aiki ba mai kama da wannan. Wurin da aka ga wallenta Anthony Udeh, mai tuka babur na haya a yankin Jikwoyi da ke a wajen Abuja, yayi gatsine ne lokacin da mai aiko mana da rahoto ya bayyana cewa ai \u2018yar majalisa daga yankin ta gina hanya mai nisan kilomita 1.5 a Phase 1. A lokacin da yake tafiya a wannan yanki da ake fadi, yayi da\u2019awar cewa shekara guda da ta gabata yayi hadari akan wannan hanya sai da aka garzaya da shi zuwa asibiti ya kwashe watanni uku. Bayan da muka isa hanyar, ya bayyana cewa tituna a wasu rukunan na Jikwoyi an masu kwalta shekaru biyu da suka gabata , amma a rukunin farko phase 1&nbsp; an dai kawo mota ta share titun don kaucewa zaizayar kasa. \u201cA tsawon sama da shekara guda ban taba ganin wani babban inji wanda zai yi aiki a kan gyara wannan titi ba, ballantana ayi maganar gina titi sai dai idan share titi na nufin an gina titi kenan.\u201d kamar yadda ya fada a turancin pidgin. Hanya kuwa a Jikwoyi Phase 1 ta zaizaye babu wata alama da ta nuna cewa ana aikin gina hanya, a tsawon shekara guda da ta gabata ko ya zuwa watan Agusta 2024. Sai dai abin da ke a zahiri DUBAWA ta lura da cewa an kafa alama ko allo a kan hanyar: Da suna&nbsp; \u201c Aikin kare zaizayar kasa a hanyar God of Elijah, Jikwoyi a Abuja Fadar Gwamnatin Tarayya. Jikwoyi Phase 1. Wanda ya dauki hoto: Phillip Anjorin DUBAWA ta tabbatar da cewa hanyoyin da ta fada dama anyi masu kwalta tun tuni idan aka cire ta Jikwoyi Phase 1. Har ila yau wanda ta gada Philip Aduda na jam\u2019iyyar PDP shi ya tabbatar da ganin ayi su a kudurin kasafin kudi na 2023 wanda aka sawa hannu ya zama doka a ranar 3 ga watan Janairu,2023. Mun samu bayanai daga Tracka, wata kafa da ke bibiyar ayyukan da ake yi a cikin al\u2019umma don tabbatar da ganin an yi su. A 2023 ayyukan gwamnatin tarayya na yankunan al\u2019umma da kudaden da aka ware don aiwatarwa (consolidated capital projects) a birnin tarayya an warewa aikin gina hanya ta Jikwoyi Phase 1 Naira miliyan 90 da lambar aikin ERGP202301237 a lokacin Aduda. Hukumar da ke lura aikin itace ta raya kogin Niger (Upper Niger River Basin Development Authority (RBDA), an ba da N7,616,744.18 a ranar 14 ga watan Agusta,2023, don fara aikin gina hanyar mai kwalta kamar yadda yake a GovSpend, wata kafa da ke ba da bayanai kan yadda gwamnatin tarayya ke kashe kudadenta.KO da yake a lokacin Kingibe tana sanata, a lokacin Aduda ne ya sanya aikin a kasafin kudi. Haka nan shima hanyoyi da kwalbati a Kpaduma 1 da 3,&nbsp; wanda shima tayi da\u2019awar aiwatarwa. Naira miliyan 100 aka ware don ginin hanyoyin a 2023 da lambar ZIP20231339 kuma ana ci gaba da wannan aiki tun a ranar 29 ga watan Dismba, 2022, inda aka saki kudade N45,469,767.45.&nbsp; DUBAWA ta je wurin sai ta gano cewa an yi wani bangare na aikin. Shi kansa wannan fara aikin bai nuna alamar na baya-bayan nan ba ne. Haka allo da ke nuna shedar wanda yayi aiki ya nuna cewa Mista Aduda ne yayi. Allo da aka kafa a Kpaduma 1 &amp; 3. Wanda ya dauki hoton: Phillip Anjorin Ko da yake bamu samu shedu ba kan kudade da aka ware don aikin Pai a Kwali daga<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":20423,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3263],"class_list":["post-20559","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5lB","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3263,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"phillip-anjorin","display_name":"Phillip Anjorin","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/98daaf5d9d7a2c5cd4ce1c417532d1cfa2ca293247710cf46a925146cc2e90e1?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/Ireti.png?fit=1200%2C719&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/20559","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=20559"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/20559\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":20560,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/20559\/revisions\/20560"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/20423"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=20559"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=20559"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=20559"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=20559"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=20559"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}