{"id":20689,"date":"2024-11-12T03:41:20","date_gmt":"2024-11-12T02:41:20","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=20689"},"modified":"2024-11-12T03:45:30","modified_gmt":"2024-11-12T02:45:30","slug":"aladu-da-zamantakewa-kaciyar-mata-da-matsayinta-a-wajen-hausawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/aladu-da-zamantakewa-kaciyar-mata-da-matsayinta-a-wajen-hausawa\/","title":{"rendered":"Al&#8217;adu da zamantakewa: Kaciyar mata da matsayinta a wajen Hausawa"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kaciya wata hanya ce da al\u2019ummomi daban-daban a cikin wannan duniya suke bi wajen cire fatar da ta rufe kan azzakarin namiji don yin biyayya ga dokokin al\u2019ada ko addini. A al\u2019adance tun kafin zuwan addinin Musulunci \u0199asar Hausa da kuma kar\u0253ar sa da Hausawa suka yi, al\u2019ummar Hausawa na yi wa \u2018ya\u2019yansu maza kaciya. Kar\u0253ar addinin Musulunci a wajen Hausawa, ya \u0199ara masu \u0199arfin gwiwa wajen \u0199ara ri\u0199o da yi wa \u2018ya\u2019yansu maza kaciya. Wannan kuwa ya faru ne saboda samuwar wasu Hadisai na Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su \u0199ara tabbata a gare shi, wa\u0257anda suka bayyana alfanu da muhimmancin yi wa maza kaciya, a matsayin hanyar kula da lafiya da kuma yin koyi da Annabi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayan kaciyar maza, akwai wasu al\u2019ummomi da suke yi wa mata kaciya inda suke cire dukkan tsokar belun da take cikin farjin mace. Ita ma wannan \u0257abi\u2019a, ana yin ta don yin biyayya ga dokokin al\u2019ada da na addini. A al\u2019adance, al\u2019ummar Hausawa ba sa yi wa \u2018ya\u2019yansu mata kaciya, amma akwai wasu ayyuka da ake yi wa wasu mata a farjinsu, kuma ba kowace mace ake yi wa wa\u0257annan ayyuka ba, sai wa\u0257anda ake haifa ko kuma suka sami matsalar bayan sun girma. Daga cikin ire-iren wa\u0257annan matsaloli akwai angurya ko belun-mata da sadadda. Wanzaman gargajiya na Hausawa ne suke yin ire-iren wa\u0257annan ayyuka a \u0199asar Hausa. Ga bayanin yadda wa\u0257annan matsaloli suke da kuma yadda ake magance su a tsakanin matan Hausawa a \u0199asar Hausa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Angurya ko Belun-Mata<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Angurya ko belun-mata wani tantanin nama ne wanda yake kamanni da \u2018ya\u2019yan auduga bayan an cire ka\u0257ar auduga wadda ake sarrafawa don yin ka\u0257i da sa\u0199a. Saboda yadda ya yi kamanni da \u2018ya\u2019yan auduga wa\u0257anda ake kira gurya, shi ya sa ake kiran lalurar da angurya. Ana haihuwar wasu mata da wannan lalura a cikin farjinsu, wasu kuma sai sun girma yake fito masu. Idan ba a cire shi ba yana iya hana mace saduwa da namiji idan ta girma. Wanzamai na gane mata masu fama da angurya a lokacin da suka zo cire beli ko hakin-wuya. A nan ne idan budurwa ce, sai su binciki farjinta su ga idan tana da angurya, sai su cire shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wasu wanzamai na yin amfani da yatsa domin cire angurya. Suna sa babban yatsansu ne su tallabo shi daga tushensa sai su sa \u2018yar tsaga su cire shi. Wasu na amfani da allura da zare domin cire shi. Ana tsiro shi da allurar ne da zaren sai a \u0257aga sama a sanya askar aski a yanke shi. Wasu wanzaman kuma suna amfani da hantsaki domin cire shi, ana sanya hantsakin a kamo tushensa sai a sa askar aski a yanke shi.Wasu kuma na amfani da akaifar babban yatsansu su kama shi daga tushensa su sa askar aski su yanke shi. Bayan an cire shi sai wanzamin ya tauna \u2018ya\u2019yan bagaruwa ya furza a wurin, daga nan kuma, sai ya barba\u0257a maganin da zai tsayar da jini da wanda zai hana shi sake tu\u0199owa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Sadadda<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mace mai lalurar sadadda ana haihuwar ta ne da wannan laluri, domin ana samun \u0199ofar farjinta \u2018yar \u0199arama ce wadda fitsari ne kawai ke iya fita ta wurin ta, amma can daga cikin farjinta lafiya lau yake. Matsalar wurin \u0199ofar farjin take. Wasu kuma ana haihuwar su lafiya lau, amma saboda rashin tsabta da rashin kula daga wurin iyayensu ko masu ri\u0199on su, sai \u0199ofar ta sake toshewa. Matan da suke da irin wannan matsala idan za su yi fitsari sai ya ri\u0199a fita kamar na namiji. Idan iyaye sun fahimci haka, sai su sanar da wanzamin gidansu domin ya binciki yarinyar don ya gyara ta. Ana yin irin wannan gyara ne ta yadda aka fahimci matsala. Ga wa\u0257anda aka haifa da matsalar sai an sanya askar aski an \u0199ara bu\u0257a \u0199ofar farjin, daga nan sai a barba\u0257a maganin da zai tsayar da jini da wanda zai sa wurin ya yi saurin warkewa. Ga kuma wa\u0257anda suka sami matsalar sakamakon rashin kula ko rashin tsabta, ana amfani da hannu ne a sake bu\u0257a \u0199ofar, daga nan sai wanzamin ya garga\u0257i iyayen yarinyar ko masu kula da ita da su ri\u0199a tsabtace farjin yarinyar ta hanyar wanke mata a duk lokacin da ta yi fitsari ko ta tashi daga barci.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bisa la\u2019akari da yadda Allah, Maigirma da \u018aaukaka ya halicci mutane, jikin mutum ba shi da wata cikakkiyar kariya daga kamuwa daga wasu cututtuka. Allah Maigirma da \u018aaukaka, cikin ikonSa, sai ya sauko da wasu cututtuka da kuma magungunansu. A fafitikar mutum wajen samo magungunan cututtukan da suke matsa masa, sai Allah Maigirma da \u018aaukaka ya sanar da wasu manazarta da masana kiwon lafiya na gargajiya da na zamani fahimtar cewa, cuta na iya kama kowane \u0253angare na jikin mutum. Domin magance cutar ana bin hanyoyi daban-daban wa\u0257anda suka ha\u0257a da shan magani ko shafawa wurin da cuta take, ko kuma cire wurin da cuta ta kama. Dangane da haka, a iya cewa, al\u2019ummar Hausawa suna bin hanyoyin gargajiya daban-daban wajen magance cututtukan da suke addabar al\u2019ummarsu. Daga cikin su, akwai wa\u0257anda ake samu a cikin farjin mata, amma al\u2019ummar Hausawa ba sa yi wa \u2018ya\u2019yansu mata kaciya, sai dai suna gyara wasu matsaloli da ake haihuwar wasu mata da su, ko kuma suka sami matsalar bayan sun girma.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Farfesa Bashir Aliyu Sallau shi ne Sarkin Askar Yariman Katsina kuma ya turo mana wannan bayani na musamman ne daga Sashen Koyar da Hausa Tsangayar Fasaha a Jami\u2019iar Gwamnatin Tarayya Dutsin-Ma inda ya ke koyarwa.<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kaciya wata hanya ce da al\u2019ummomi daban-daban a cikin wannan duniya suke bi wajen cire fatar da ta rufe kan azzakarin namiji don yin biyayya ga dokokin al\u2019ada ko addini. A al\u2019adance tun kafin zuwan addinin Musulunci \u0199asar Hausa da kuma kar\u0253ar sa da Hausawa suka yi, al\u2019ummar Hausawa na yi wa \u2018ya\u2019yansu maza kaciya. Kar\u0253ar addinin Musulunci a wajen Hausawa, ya \u0199ara masu \u0199arfin gwiwa wajen \u0199ara ri\u0199o da yi wa \u2018ya\u2019yansu maza kaciya. Wannan kuwa ya faru ne saboda samuwar wasu Hadisai na Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su \u0199ara tabbata a gare shi, wa\u0257anda suka bayyana alfanu da muhimmancin yi wa maza kaciya, a matsayin hanyar kula da lafiya da kuma yin koyi da Annabi. Bayan kaciyar maza, akwai wasu al\u2019ummomi da suke yi wa mata kaciya inda suke cire dukkan tsokar belun da take cikin farjin mace. Ita ma wannan \u0257abi\u2019a, ana yin ta don yin biyayya ga dokokin al\u2019ada da na addini. A al\u2019adance, al\u2019ummar Hausawa ba sa yi wa \u2018ya\u2019yansu mata kaciya, amma akwai wasu ayyuka da ake yi wa wasu mata a farjinsu, kuma ba kowace mace ake yi wa wa\u0257annan ayyuka ba, sai wa\u0257anda ake haifa ko kuma suka sami matsalar bayan sun girma. Daga cikin ire-iren wa\u0257annan matsaloli akwai angurya ko belun-mata da sadadda. Wanzaman gargajiya na Hausawa ne suke yin ire-iren wa\u0257annan ayyuka a \u0199asar Hausa. Ga bayanin yadda wa\u0257annan matsaloli suke da kuma yadda ake magance su a tsakanin matan Hausawa a \u0199asar Hausa. Angurya ko Belun-Mata Angurya ko belun-mata wani tantanin nama ne wanda yake kamanni da \u2018ya\u2019yan auduga bayan an cire ka\u0257ar auduga wadda ake sarrafawa don yin ka\u0257i da sa\u0199a. Saboda yadda ya yi kamanni da \u2018ya\u2019yan auduga wa\u0257anda ake kira gurya, shi ya sa ake kiran lalurar da angurya. Ana haihuwar wasu mata da wannan lalura a cikin farjinsu, wasu kuma sai sun girma yake fito masu. Idan ba a cire shi ba yana iya hana mace saduwa da namiji idan ta girma. Wanzamai na gane mata masu fama da angurya a lokacin da suka zo cire beli ko hakin-wuya. A nan ne idan budurwa ce, sai su binciki farjinta su ga idan tana da angurya, sai su cire shi. Wasu wanzamai na yin amfani da yatsa domin cire angurya. Suna sa babban yatsansu ne su tallabo shi daga tushensa sai su sa \u2018yar tsaga su cire shi. Wasu na amfani da allura da zare domin cire shi. Ana tsiro shi da allurar ne da zaren sai a \u0257aga sama a sanya askar aski a yanke shi. Wasu wanzaman kuma suna amfani da hantsaki domin cire shi, ana sanya hantsakin a kamo tushensa sai a sa askar aski a yanke shi.Wasu kuma na amfani da akaifar babban yatsansu su kama shi daga tushensa su sa askar aski su yanke shi. Bayan an cire shi sai wanzamin ya tauna \u2018ya\u2019yan bagaruwa ya furza a wurin, daga nan kuma, sai ya barba\u0257a maganin da zai tsayar da jini da wanda zai hana shi sake tu\u0199owa. Sadadda Mace mai lalurar sadadda ana haihuwar ta ne da wannan laluri, domin ana samun \u0199ofar farjinta \u2018yar \u0199arama ce wadda fitsari ne kawai ke iya fita ta wurin ta, amma can daga cikin farjinta lafiya lau yake. Matsalar wurin \u0199ofar farjin take. Wasu kuma ana haihuwar su lafiya lau, amma saboda rashin tsabta da rashin kula daga wurin iyayensu ko masu ri\u0199on su, sai \u0199ofar ta sake toshewa. Matan da suke da irin wannan matsala idan za su yi fitsari sai ya ri\u0199a fita kamar na namiji. Idan iyaye sun fahimci haka, sai su sanar da wanzamin gidansu domin ya binciki yarinyar don ya gyara ta. Ana yin irin wannan gyara ne ta yadda aka fahimci matsala. Ga wa\u0257anda aka haifa da matsalar sai an sanya askar aski an \u0199ara bu\u0257a \u0199ofar farjin, daga nan sai a barba\u0257a maganin da zai tsayar da jini da wanda zai sa wurin ya yi saurin warkewa. Ga kuma wa\u0257anda suka sami matsalar sakamakon rashin kula ko rashin tsabta, ana amfani da hannu ne a sake bu\u0257a \u0199ofar, daga nan sai wanzamin ya garga\u0257i iyayen yarinyar ko masu kula da ita da su ri\u0199a tsabtace farjin yarinyar ta hanyar wanke mata a duk lokacin da ta yi fitsari ko ta tashi daga barci. Bisa la\u2019akari da yadda Allah, Maigirma da \u018aaukaka ya halicci mutane, jikin mutum ba shi da wata cikakkiyar kariya daga kamuwa daga wasu cututtuka. Allah Maigirma da \u018aaukaka, cikin ikonSa, sai ya sauko da wasu cututtuka da kuma magungunansu. A fafitikar mutum wajen samo magungunan cututtukan da suke matsa masa, sai Allah Maigirma da \u018aaukaka ya sanar da wasu manazarta da masana kiwon lafiya na gargajiya da na zamani fahimtar cewa, cuta na iya kama kowane \u0253angare na jikin mutum. Domin magance cutar ana bin hanyoyi daban-daban wa\u0257anda suka ha\u0257a da shan magani ko shafawa wurin da cuta take, ko kuma cire wurin da cuta ta kama. Dangane da haka, a iya cewa, al\u2019ummar Hausawa suna bin hanyoyin gargajiya daban-daban wajen magance cututtukan da suke addabar al\u2019ummarsu. Daga cikin su, akwai wa\u0257anda ake samu a cikin farjin mata, amma al\u2019ummar Hausawa ba sa yi wa \u2018ya\u2019yansu mata kaciya, sai dai suna gyara wasu matsaloli da ake haihuwar wasu mata da su, ko kuma suka sami matsalar bayan sun girma. Farfesa Bashir Aliyu Sallau shi ne Sarkin Askar Yariman Katsina kuma ya turo mana wannan bayani na musamman ne daga Sashen Koyar da Hausa Tsangayar Fasaha a Jami\u2019iar Gwamnatin Tarayya Dutsin-Ma inda ya ke koyarwa.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":13472,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,1572,4,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4417],"class_list":["post-20689","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-explainers","category-featured","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5nH","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4417,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"bashir-sallau","display_name":"Bashir Sallau","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2023\/02\/FGM.png?fit=976%2C549&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/20689","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=20689"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/20689\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":20691,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/20689\/revisions\/20691"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/13472"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=20689"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=20689"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=20689"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=20689"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=20689"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}