{"id":21022,"date":"2024-12-16T10:31:50","date_gmt":"2024-12-16T09:31:50","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=21022"},"modified":"2024-12-16T10:31:53","modified_gmt":"2024-12-16T09:31:53","slug":"yadda-kwararru-ke-kallon-rikice-rikice-a-yankin-sahel","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/yadda-kwararru-ke-kallon-rikice-rikice-a-yankin-sahel\/","title":{"rendered":"Yadda kwararru ke kallon rikice-rikice a yankin Sahel"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Manaja a harkokin gudanar da bincike ta fasahar zamani a Cibiyar Fasahar Kirkire-kirkire da Sharhi kan Bayanai da ake yada wa barkatai (DAIDAC) Silas Jonathan, ya bayyana cewa kungiyoyin \u2018yanta\u2019adda na amfani sosai da bayanan karya da ake yadawa da gangan don su yada manufarsu a yankin Tafkin Chadi me fama da rikici.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya bayyana haka ne a makalar da ya gabatar a lokacin da yake bayani ga \u2018yanjarida lokacin taron \u2018yanjarida masu samun horo kan gudanar da bincike a aikin jarida na kwanaki uku, (AIJC2024) wanda aka yi tsakanin 30 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba, 2024 a birnin Johannesburg na Afurka ta Kudu.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yayin da yake bayani kan manufar \u201cYaki da \u2018yanta\u2019adda a yankin Sahel\u201dya bayyana muhimmanci da ke akwai na tuntubar al\u2019umma wajen tattara bayanai da ake yawan tattaunawa a rikicin. \u201cDuk lokacin da irin wannan tattaunawa ta taso, ba kawai tunanin ba, ku yi tunani ya za ta kasance idan kuka samu kanku a yanki da ake fama da rikice-rikice.\u201da cewarsa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;A matsayinsa na mai bincike a aikin jarida mai kuma nazari, Mista Jonathan ya mayar da hankali kan yadda bayanai suke taka rawa a rikicin yankin na Tafkin Chadi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yace, \u201cdaya daga cikin abubuwa da na gano shine ribatar tattalin arziki daga rikici da ma ba wa rikicin fifiko.\u2019<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yace bangaren gwamnati da masu tada kayar baya na samun riba daga wannan rikici inda ya ba da misali da yadda dakarun soja ke hada rikici don samun abin duniya ko kudade a wajensu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201dAkwai kuma karin samun mutane da ke hijira yayin da mutane ke neman rayuwa mai inganci.\u201d a cewarsa. Yace wannan ya zama silar tattalin arziki ya karkata ga masu fataucin mutane.\u201d&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Har ila yau ya sake haskaka raunin mulkin dimukuradiya a yankin na Sahel, abin da ya kara ta\u2019azzara rashin zaman lafiya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cA tarihance, dimukuradiyya ana sa mata ayar tambaya kan ingancinta wajen yakar ta\u2019addanci.\u201d a cewar Jonathan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kuma nuna yadda \u2018yankasashen waje suka kara ta\u2019azzara tashin hankalin da ke faruwa, musamman daga kungiyoyi kamar na kasar Rasha Wagner Group, wadanda suka kara dagula lamarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A bincikensa kan bayanan da ake yadawa barkatai wadanda ba haka suke ba, Jonathan yace bayanai na da tasiri ne wanda ke karuwa idan ana yada labaran karya ga al\u2019umma. Wadanda ke tafiya kafada da kafada kamar yadda tarihi ya nuna a yakin basasar Rwanda da farfaganda ta \u2018yanNazi, ya kuma yi bayani kan yadda masu tsatstsauran ra\u2019ayi ke amfani da kafafan sada zumunta wajen daukar sabbin mambobi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cA shafin Facebook da TikTok akwai shafukan da kungiyoyin na masu tsatstsauran ra\u2019ayi ke kula da su inda suke wa mabiyan albishir na samun kyakykyawar rayuwa a agare su muddin suka mika wuya. \u201dA cewarsa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kara da cewa akwai nazari ko bincike da dama fiye ma da na cibiyarsa wadanda suka tabbatar da cewa labaran karya kan haddasa shigar al\u2019umma masu rauni cikin rudani.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mista Jonathan ya kuma tattauna batun yanayi na al\u2019umma da suka fi amfani da shafukan na sada zumunta inda yace \u2018yanta\u2019addar na amfani da wannan dama ma su sake mamaya. \u201cMutane sun fi so su rika baza labarai da ke sanya tsoro a zukatan al\u2019umma.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya bayyana cewa al\u2019umma su kan shiga yanayi na rashin karsashi ko kwarin gwiwa yayin da suka ji karar bindiga ko aka watsa wani labari mai firgitarwa a shafukan sada zumunta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kara da cewa safarar mutane wani babban lamari ne, idan ana maganar wannan rikici. Jonathan ya ba da labarin yadda wani dan Najeriya ya dena jin duriyar dan\u2019uwansa tsawon shekaru shida tun bayan da ya kudiri aniyar zuwa Turai don neman rayuwa mai inganci.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yace \u201cKo da yake wannan labarin na wani mutum ne daya, amma ya bayyana yadda za a iya samun labaran wasu da ke zama cikin rudani a kokari na ficewa daga yankin.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mista Jonathan yayi kira ga \u2018yanjarida su yaki labaran karya, su kuma sa ido da bibiyar irin wadannan labarai.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yace \u201cWannan rikici na sauyawa daga wanda ake gani a zahiri zuwa wanda ake a shafukan intanet na zamani.\u201dA nan sai yayi gargadi da ma kira ga \u2018yanjarida su sake duba sabbin hanyoyi na samar da waraka ga wannan kalubale.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kuma sake nuni da cewa a zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan a Najeriya, an ga yadda wasu masu zanga-zangar suka rika daga tutar kasar Rasha, kana suna kira da cewa sojoji su zo su karbi mulkin Najeriya, wadannan alamu ne na kira ko jawo masu mulkin kama karya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A karshe Mista Jonathan yace \u201cTalauci shine babban sanadi da ke kara zafin rikici a yankin Sahel.\u201d Sai ya jaddada bukatar da ke akwai ta kawar da talauci a yankin.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Manaja a harkokin gudanar da bincike ta fasahar zamani a Cibiyar Fasahar Kirkire-kirkire da Sharhi kan Bayanai da ake yada wa barkatai (DAIDAC) Silas Jonathan, ya bayyana cewa kungiyoyin \u2018yanta\u2019adda na amfani sosai da bayanan karya da ake yadawa da gangan don su yada manufarsu a yankin Tafkin Chadi me fama da rikici. Ya bayyana haka ne a makalar da ya gabatar a lokacin da yake bayani ga \u2018yanjarida lokacin taron \u2018yanjarida masu samun horo kan gudanar da bincike a aikin jarida na kwanaki uku, (AIJC2024) wanda aka yi tsakanin 30 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba, 2024 a birnin Johannesburg na Afurka ta Kudu.&nbsp; Yayin da yake bayani kan manufar \u201cYaki da \u2018yanta\u2019adda a yankin Sahel\u201dya bayyana muhimmanci da ke akwai na tuntubar al\u2019umma wajen tattara bayanai da ake yawan tattaunawa a rikicin. \u201cDuk lokacin da irin wannan tattaunawa ta taso, ba kawai tunanin ba, ku yi tunani ya za ta kasance idan kuka samu kanku a yanki da ake fama da rikice-rikice.\u201da cewarsa. &nbsp;A matsayinsa na mai bincike a aikin jarida mai kuma nazari, Mista Jonathan ya mayar da hankali kan yadda bayanai suke taka rawa a rikicin yankin na Tafkin Chadi. Yace, \u201cdaya daga cikin abubuwa da na gano shine ribatar tattalin arziki daga rikici da ma ba wa rikicin fifiko.\u2019 Yace bangaren gwamnati da masu tada kayar baya na samun riba daga wannan rikici inda ya ba da misali da yadda dakarun soja ke hada rikici don samun abin duniya ko kudade a wajensu. \u201dAkwai kuma karin samun mutane da ke hijira yayin da mutane ke neman rayuwa mai inganci.\u201d a cewarsa. Yace wannan ya zama silar tattalin arziki ya karkata ga masu fataucin mutane.\u201d&nbsp; Har ila yau ya sake haskaka raunin mulkin dimukuradiya a yankin na Sahel, abin da ya kara ta\u2019azzara rashin zaman lafiya. \u201cA tarihance, dimukuradiyya ana sa mata ayar tambaya kan ingancinta wajen yakar ta\u2019addanci.\u201d a cewar Jonathan. Ya kuma nuna yadda \u2018yankasashen waje suka kara ta\u2019azzara tashin hankalin da ke faruwa, musamman daga kungiyoyi kamar na kasar Rasha Wagner Group, wadanda suka kara dagula lamarin. A bincikensa kan bayanan da ake yadawa barkatai wadanda ba haka suke ba, Jonathan yace bayanai na da tasiri ne wanda ke karuwa idan ana yada labaran karya ga al\u2019umma. Wadanda ke tafiya kafada da kafada kamar yadda tarihi ya nuna a yakin basasar Rwanda da farfaganda ta \u2018yanNazi, ya kuma yi bayani kan yadda masu tsatstsauran ra\u2019ayi ke amfani da kafafan sada zumunta wajen daukar sabbin mambobi. \u201cA shafin Facebook da TikTok akwai shafukan da kungiyoyin na masu tsatstsauran ra\u2019ayi ke kula da su inda suke wa mabiyan albishir na samun kyakykyawar rayuwa a agare su muddin suka mika wuya. \u201dA cewarsa. Ya kara da cewa akwai nazari ko bincike da dama fiye ma da na cibiyarsa wadanda suka tabbatar da cewa labaran karya kan haddasa shigar al\u2019umma masu rauni cikin rudani.&nbsp; Mista Jonathan ya kuma tattauna batun yanayi na al\u2019umma da suka fi amfani da shafukan na sada zumunta inda yace \u2018yanta\u2019addar na amfani da wannan dama ma su sake mamaya. \u201cMutane sun fi so su rika baza labarai da ke sanya tsoro a zukatan al\u2019umma.\u201d Ya bayyana cewa al\u2019umma su kan shiga yanayi na rashin karsashi ko kwarin gwiwa yayin da suka ji karar bindiga ko aka watsa wani labari mai firgitarwa a shafukan sada zumunta. Ya kara da cewa safarar mutane wani babban lamari ne, idan ana maganar wannan rikici. Jonathan ya ba da labarin yadda wani dan Najeriya ya dena jin duriyar dan\u2019uwansa tsawon shekaru shida tun bayan da ya kudiri aniyar zuwa Turai don neman rayuwa mai inganci. Yace \u201cKo da yake wannan labarin na wani mutum ne daya, amma ya bayyana yadda za a iya samun labaran wasu da ke zama cikin rudani a kokari na ficewa daga yankin.\u201d Mista Jonathan yayi kira ga \u2018yanjarida su yaki labaran karya, su kuma sa ido da bibiyar irin wadannan labarai. Yace \u201cWannan rikici na sauyawa daga wanda ake gani a zahiri zuwa wanda ake a shafukan intanet na zamani.\u201dA nan sai yayi gargadi da ma kira ga \u2018yanjarida su sake duba sabbin hanyoyi na samar da waraka ga wannan kalubale. Ya kuma sake nuni da cewa a zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan a Najeriya, an ga yadda wasu masu zanga-zangar suka rika daga tutar kasar Rasha, kana suna kira da cewa sojoji su zo su karbi mulkin Najeriya, wadannan alamu ne na kira ko jawo masu mulkin kama karya. A karshe Mista Jonathan yace \u201cTalauci shine babban sanadi da ke kara zafin rikici a yankin Sahel.\u201d Sai ya jaddada bukatar da ke akwai ta kawar da talauci a yankin.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":20643,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3263],"class_list":["post-21022","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5t4","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3263,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"phillip-anjorin","display_name":"Phillip Anjorin","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/98daaf5d9d7a2c5cd4ce1c417532d1cfa2ca293247710cf46a925146cc2e90e1?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/img_3_1730453204127.webp?fit=1070%2C713&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21022","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=21022"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21022\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":21023,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21022\/revisions\/21023"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/20643"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=21022"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=21022"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=21022"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=21022"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=21022"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}