{"id":21331,"date":"2025-01-20T12:13:32","date_gmt":"2025-01-20T11:13:32","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=21331"},"modified":"2025-01-20T12:25:56","modified_gmt":"2025-01-20T11:25:56","slug":"daawowi-biyar-masu-daure-kai-da-muka-bincika-a-2024","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/daawowi-biyar-masu-daure-kai-da-muka-bincika-a-2024\/","title":{"rendered":"Da\u2019awowi biyar masu daure kai dangane da cutar daji da muka bincika a 2024"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da kasancewarsa wani dandali da ake samun bayanai na karya, kafafan sadarwar zamani sun kasance wata kafa da mutane da dama ke ziyarta don neman bayanai da ke da alaka da lafiya, yayin da a hannu guda masu aikin gano gaskiyar bayanai suke aiki shekara bayan shekara a kokari na tsaftace dandalin sadarwar ta zamani.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Cutar daji ko kansa ta kasance a kan gaba wajen sanadi na rayukan al\u2019umma a duniya, abin takaici masu yada labaran karya na amfani da wannan dama wajen ba da bayanai na yaudara ga al\u2019umma ba tare da la\u2019akari da illar hakan ba. A matsayinta na zama dandali da ke ba wa al\u2019umma bayanai masu inganci jaridar DUBAWA&nbsp; ta duba wasu da\u2019awowi da dama kan batun da ya shafi cutar ta daji ko kansa, ga wasu daga cikinsu:&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li>Wasu nau\u2019ikan abinci na maganin cutar kansa<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A watan Fabrairu, 2024 wani mai amfani da shafin Facebook yayi da\u2019awar cewa cin wake da miyar da aka yi da wake da lemon tumatir suna warkar da cutar daji ko kansar mafitsara ko ta nono ko wacce kan shafi yankin kwanciyar da a cikin mace ko ma girman tsiro a jikin dan Adam.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai binciken masana ya nunar da cewa duk da cewa wannan nau\u2019ikan kayan abinci na da alfanu ga jikin dan Adam akwai bukatar binciken kimiya kafin tabbatar da hakan, musamman a wannan fanni.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kwarraru sun bayyana wannan wallafa a matsayin mai hadari wajen ba da bayanan karya, inda suka yi gargadin cewa masu cutar kansa da suka yarda da wannan da\u2019awa za su iya ci gaba da zama a yanayi na yunwa, suna ma iya ajiye rigakafin da suke yi a game da cutar. Za a iya karatu idan aka duba wannan link <a href=\"http:\/\/dubawa.org\/dir\/two-weeks-cancer-remedy-by-social-media-user-false\/\">Read more<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\" start=\"2\">\n<li>Jijiyar fulawar ko furen nan Dandelion na maganin cutar daji cikin sa\u2019oi 48\u00a0<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A shekarar ta 2024 ce wani mai amfani da shafin sadarwar yayi da\u2019awa cewa jijiyar wannana fulawar ko fure ta Dandelion na maganin cutar daji da kaso 98 cikin dari cikin kwanaki biyu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Amma bincike ya&nbsp; nunar da cewa akwai yiwuwar cewa jijiyar ta fulawar ko furen Dandelion na dakile bazuwar kwayoyin halittar kansar nono a jikin bera, wannan bincike bai kai ga yi a jikin dan Adam ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Har ila yau wasu ayyukan bincike sun nunar da cewa dandelion na iya taimakawa yaki da cutittika, masana sun yi gargadi cewa&nbsp; akwai bukatar neman shawarar kwararru kafin shan shayi na furannin dandelion, wanda hakan na iya jawo cutika a jikin dan Adam&nbsp; idan ba a lura ba. Akwai karin bayani a nan ( <a href=\"http:\/\/dubawa.org\/dir\/medical-experts-say-dandelion-cannot-cure-cancer-cells-in-humans-as-claimed\/\">here<\/a>).&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\" start=\"3\">\n<li>Amfani da karamar lasifika ta kunne tsawon lokaci na iya jawo cutar kansar kwakwalwa<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wata da\u2019awar da ke da alaka da cutar kansa da DUBAWA ta yi nazari a kanta a 2024 ita ce yadda wani bidiyo da aka yada a shafin Instagram wanda aka fi sani da Instablog wannan bidiyo da aka yada ya nuna yadda wata mata ta yi da\u2019awar cewa wani mutum ya ja hankalinta da cewa idan mutum ya dauki lokaci mai tsawo yana amfani da wannan karamar lasifikar ta kunne yana iya fuskantar hadarin kamuwa da cutar kansar kwakwalwa.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Har kawo yanzu babu wata sheda a kimiyance da ta goyi bayan wannan da\u2019awa, sai dai kwararru na ba da shawara da a rika rage karfin lasifikar idan an zo likawa ko amfani da ita a kunne, saboda suna cewa idan sautin yayi karfi yana iya illa ga jin mutum, ba wai ya haifar da cutar kansa ba. Za a iya kara nazari idan an bi wannan link <a href=\"http:\/\/dubawa.org\/dir\/no-scientific-evidence-to-prove-airpods-cause-brain-cancer\/\">More details<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\" start=\"4\">\n<li>Man shafawa na Vaseline na jawo cutar kansa\u00a0<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A wani labarin kuma wani mai amfani da shafin X yayi da\u2019awar cewa amfani da man Vasiline na da hadari, inda yayi kira ga jama\u2019a da su rika amfani da Mankadanya na asali ko Sheabutter a Turance maimakon Vaseline.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan mai amfani da shafin na X yayi da\u2019awar cewa Vaseline na dauke da wasu sinadarai wadanda za su iya jawo cutar dajin mama ko nono da jawo tsufan fata da wuri da rikita kwayoyin halitta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai bincike ya nunar da cewa ana iya fuskantar hadari ne idan ana amfani da Vaseline wanda ba a tace ba. Wata makala da kamfanin Unilever yayi bayani a cikinta yayi bayani cewa ana tace abin da ake yin Vaseline akalla sau uku a tabbatar da an cire duk wasu abubuwa masu hadari.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wasu nazarce-nazarcen da aka yi kuma sun nunar da cewa babu alaka tsakanin Vaseline da cutar ta kansa. Zaa iya zurfafa bincike idan aka duba wannan link (<a href=\"http:\/\/dubawa.org\/dir\/can-vaseline-cause-breast-cancer-as-posited-by-x-user\/\">Read more here<\/a>).<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\" start=\"5\">\n<li>Turiri daga na\u2019urar dumama abinci na jawo cutar kansa<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan&nbsp; da\u2019awa ta karshe an samo ta ne daga wani mai amfani da shafin Facebook wanda ya sake yada labarin da mutane suka dade suna ji wanda ke nuna cewa amfani da na\u2019urar dumama abinci na jawo cutar daji ko kansa a jikin dan Adam. Ko da dai wannan na\u2019ura na fitar da wani tururi kadan saboda lantarki da karafan da ke jikinta kamar yadda ake samun irinsu a samaniya da suke fesawa duniya, kamar ita ma na\u2019urar da ke ba da intanet Wi-Fi da sautin rediyo, da dama sun aminta da samun cutar daga wadannan sabubba musamman na\u2019urar ta dumama abinci ana alakantata da jawo cutar ta daji ko kansa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai bincike da aka yi sun nunar da cewa amfani da na\u2019urar dumama abinci baya lalata abinci sanadin tururin da ke fita.Ko da yake mai da\u2019awar yace tsayawa kusa da na\u2019urar dumama abincin na iya jawo cutar daji, wani bincike ya nunar da cewa cibiyoyi na gwamnati sun ba da shawarwari cewa a guji tsayawa kai tsaye kusa da na\u2019urar a lokacin da take aiki, ba kawai saboda cutar kansa ba don gudun iya samun wasu raunika da ka iya shafar fatar jikin mutum ko ma idanuwansa. Za a iya samun karin bayani idan aka bi wannan link (<a href=\"http:\/\/dubawa.org\/dir\/does-standing-before-microwave-oven-cause-cancer\/\">information here<\/a>).<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Duk da kasancewarsa wani dandali da ake samun bayanai na karya, kafafan sadarwar zamani sun kasance wata kafa da mutane da dama ke ziyarta don neman bayanai da ke da alaka da lafiya, yayin da a hannu guda masu aikin gano gaskiyar bayanai suke aiki shekara bayan shekara a kokari na tsaftace dandalin sadarwar ta zamani. Cutar daji ko kansa ta kasance a kan gaba wajen sanadi na rayukan al\u2019umma a duniya, abin takaici masu yada labaran karya na amfani da wannan dama wajen ba da bayanai na yaudara ga al\u2019umma ba tare da la\u2019akari da illar hakan ba. A matsayinta na zama dandali da ke ba wa al\u2019umma bayanai masu inganci jaridar DUBAWA&nbsp; ta duba wasu da\u2019awowi da dama kan batun da ya shafi cutar ta daji ko kansa, ga wasu daga cikinsu:&nbsp; A watan Fabrairu, 2024 wani mai amfani da shafin Facebook yayi da\u2019awar cewa cin wake da miyar da aka yi da wake da lemon tumatir suna warkar da cutar daji ko kansar mafitsara ko ta nono ko wacce kan shafi yankin kwanciyar da a cikin mace ko ma girman tsiro a jikin dan Adam. Sai dai binciken masana ya nunar da cewa duk da cewa wannan nau\u2019ikan kayan abinci na da alfanu ga jikin dan Adam akwai bukatar binciken kimiya kafin tabbatar da hakan, musamman a wannan fanni.&nbsp; Kwarraru sun bayyana wannan wallafa a matsayin mai hadari wajen ba da bayanan karya, inda suka yi gargadin cewa masu cutar kansa da suka yarda da wannan da\u2019awa za su iya ci gaba da zama a yanayi na yunwa, suna ma iya ajiye rigakafin da suke yi a game da cutar. Za a iya karatu idan aka duba wannan link Read more. A shekarar ta 2024 ce wani mai amfani da shafin sadarwar yayi da\u2019awa cewa jijiyar wannana fulawar ko fure ta Dandelion na maganin cutar daji da kaso 98 cikin dari cikin kwanaki biyu. Amma bincike ya&nbsp; nunar da cewa akwai yiwuwar cewa jijiyar ta fulawar ko furen Dandelion na dakile bazuwar kwayoyin halittar kansar nono a jikin bera, wannan bincike bai kai ga yi a jikin dan Adam ba. Har ila yau wasu ayyukan bincike sun nunar da cewa dandelion na iya taimakawa yaki da cutittika, masana sun yi gargadi cewa&nbsp; akwai bukatar neman shawarar kwararru kafin shan shayi na furannin dandelion, wanda hakan na iya jawo cutika a jikin dan Adam&nbsp; idan ba a lura ba. Akwai karin bayani a nan ( here).&nbsp; Wata da\u2019awar da ke da alaka da cutar kansa da DUBAWA ta yi nazari a kanta a 2024 ita ce yadda wani bidiyo da aka yada a shafin Instagram wanda aka fi sani da Instablog wannan bidiyo da aka yada ya nuna yadda wata mata ta yi da\u2019awar cewa wani mutum ya ja hankalinta da cewa idan mutum ya dauki lokaci mai tsawo yana amfani da wannan karamar lasifikar ta kunne yana iya fuskantar hadarin kamuwa da cutar kansar kwakwalwa.&nbsp; Har kawo yanzu babu wata sheda a kimiyance da ta goyi bayan wannan da\u2019awa, sai dai kwararru na ba da shawara da a rika rage karfin lasifikar idan an zo likawa ko amfani da ita a kunne, saboda suna cewa idan sautin yayi karfi yana iya illa ga jin mutum, ba wai ya haifar da cutar kansa ba. Za a iya kara nazari idan an bi wannan link More details. A wani labarin kuma wani mai amfani da shafin X yayi da\u2019awar cewa amfani da man Vasiline na da hadari, inda yayi kira ga jama\u2019a da su rika amfani da Mankadanya na asali ko Sheabutter a Turance maimakon Vaseline.&nbsp; Wannan mai amfani da shafin na X yayi da\u2019awar cewa Vaseline na dauke da wasu sinadarai wadanda za su iya jawo cutar dajin mama ko nono da jawo tsufan fata da wuri da rikita kwayoyin halitta. Sai dai bincike ya nunar da cewa ana iya fuskantar hadari ne idan ana amfani da Vaseline wanda ba a tace ba. Wata makala da kamfanin Unilever yayi bayani a cikinta yayi bayani cewa ana tace abin da ake yin Vaseline akalla sau uku a tabbatar da an cire duk wasu abubuwa masu hadari.&nbsp; Wasu nazarce-nazarcen da aka yi kuma sun nunar da cewa babu alaka tsakanin Vaseline da cutar ta kansa. Zaa iya zurfafa bincike idan aka duba wannan link (Read more here). Wannan&nbsp; da\u2019awa ta karshe an samo ta ne daga wani mai amfani da shafin Facebook wanda ya sake yada labarin da mutane suka dade suna ji wanda ke nuna cewa amfani da na\u2019urar dumama abinci na jawo cutar daji ko kansa a jikin dan Adam. Ko da dai wannan na\u2019ura na fitar da wani tururi kadan saboda lantarki da karafan da ke jikinta kamar yadda ake samun irinsu a samaniya da suke fesawa duniya, kamar ita ma na\u2019urar da ke ba da intanet Wi-Fi da sautin rediyo, da dama sun aminta da samun cutar daga wadannan sabubba musamman na\u2019urar ta dumama abinci ana alakantata da jawo cutar ta daji ko kansa. Sai dai bincike da aka yi sun nunar da cewa amfani da na\u2019urar dumama abinci baya lalata abinci sanadin tururin da ke fita.Ko da yake mai da\u2019awar yace tsayawa kusa da na\u2019urar dumama abincin na iya jawo cutar daji, wani bincike ya nunar da cewa cibiyoyi na gwamnati sun ba da shawarwari cewa a guji tsayawa kai tsaye kusa da na\u2019urar a lokacin da take aiki, ba kawai saboda cutar kansa ba don gudun iya samun wasu raunika da ka iya shafar fatar jikin mutum ko ma idanuwansa. Za a iya samun karin bayani idan aka bi wannan link (information here).<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":21198,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,1571,2451,121],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[1920],"class_list":["post-21331","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-fact-check","category-hausa","category-health"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5y3","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":1920,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"elizabeth-ogunbamowo","display_name":"Elizabeth Ogunbamowo","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/7043a07f4ff292637cb75d13c8340fa9afb2ec87eceec4eedd980077c8bfd304?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/Cancer-image.jpg?fit=390%2C351&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21331","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=21331"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21331\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":21336,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21331\/revisions\/21336"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/21198"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=21331"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=21331"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=21331"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=21331"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=21331"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}