{"id":21515,"date":"2025-02-08T05:06:57","date_gmt":"2025-02-08T04:06:57","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=21515"},"modified":"2025-02-08T05:07:00","modified_gmt":"2025-02-08T04:07:00","slug":"shin-haramun-ne-limancin-yarubawa-a-arewacin-najeriya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/shin-haramun-ne-limancin-yarubawa-a-arewacin-najeriya\/","title":{"rendered":"Shin haramun ne limancin Yarubawa a Arewacin Najeriya ?"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin X yayi da\u2019awar (<a href=\"https:\/\/x.com\/yomiable\/status\/1871177441286271110?t=sGo90Gq4ZQRYqHrmsbZyvQ&amp;s=08\">claimed<\/a>) cewa an haramtawa Yarubawa Musulmai damar yin limanci a Arewacin Najeriya.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"21052\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/liberias-finance-ministry-did-not-resubmit-the-countrys-national-budget\/false-4-2-2\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/FALSE-4-2.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4-2\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/FALSE-4-2.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/FALSE-4-2.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-21052\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Hukunci: Karya ce, Al\u2019Kur\u2019ani yayi tanadin cewa wanda zai jagoranci Musulmi a wajen Sallah ya kasance shi ya fi ilimi na addini da kamewa a cikinsu. Kuma malamai sun yi wa mai wannan da\u2019awa raddi da cewa jagoranci na sallah ba shi da alaka da kabilanci.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Sako<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Addini da kabilanci suna taka muhimmiyar rawa (<a href=\"https:\/\/punchng.com\/why-nigerians-shouldnt-vote-along-ethnic-religious-lines\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">integral role<\/a>) a zamantakewa da siyasar Najeriya. Haduwar wadanan abubuwa biyu kuma ana ganin tasirinsu a zahiri a yankunan kasar da siyasarta. Akwai dai mabanbantan addini da kabila a zamantakewar \u2018yan Najeriya, abin da ke kawo tarnaki a zamantakewa (<a href=\"https:\/\/punchng.com\/addressing-ethnic-religious-divisions-among-nigerians\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">social rift<\/a>) da rashin fahimta a tsakanin \u2018yan kasar, kasancewar kowanne na ikirarin cewa nasa addini ko kabila shine ke kan gaba da na dan\u2019uwansa. Abu mafi muni shine yadda wasu ke ganin su suka fi cancanta su samu wata moriya da suka hadar da ganin cewa su ke jagoranci, da basu wasu mukamai da ma basu wata dama ta kasa da sauransu saboda matsayinsu a cikin al\u2019ummar kasar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A kan wannan ne mai amfani da shafin na X Omo Oodua (<a href=\"https:\/\/x.com\/yomiable\/status\/1871177441286271110?t=sGo90Gq4ZQRYqHrmsbZyvQ&amp;s=08\">@yomiable<\/a>) ke kafa tasa da\u2019awa da cewa Yarubawa da ke zama Musulmai ba a basu damar su jagoranci sallah a arewacin Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya rubata ne cewa, \u201cYorubawa&nbsp; Musulmai an haramta masu jagorancin sallah a Arewacin Najeriya.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kara da cewa (<a href=\"https:\/\/x.com\/yomiable\/status\/1871207889588887824\">mentioned<\/a>) wannan na faruwa ne saboda koyarwar Shehu Usman Danfodio.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan wallafa dai a shafin na X ta tada kura inda masu amfani da shafin suka yi ta mayar da martani, an samu masu tsokaci 716 da masu sake yadawa 903 da masu nuna sha\u2019awarsu 1,500 da masu nuna za su sake nazarta 90, wannan ya zuwa ranar 22 ga Janairun,2025 kenan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta nazarci sashin yin tsokaci na wannan wallafa, inda anan ne ta lura da cewa wasu sun aminta da abin da mai da\u2019awar ke fadi har suna cewa ai haka lamarin yake a Najeriya&nbsp; yayin da wasu kuma ke ganin ba haka lamarin yake ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cAbun takaici ne ganin yadda wasu al\u2019ummar Yarubawa Musulmai suke yin duk abin da za su iya a mayar da su baya ko da kuwa a yankinsu ne\u2026Anawa ra\u2019ayin kada su bari a mayar da yankin mu Arewa maso Gabas,\u201d a cewar Asiwaju of Owoland (<a href=\"https:\/\/x.com\/egtapere\/status\/1871190637854560708\">@egtapere<\/a>).<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cAmma za su zo nan ma suce za su yi yadda suka ga dama,\u201d Akintayo (<a href=\"https:\/\/x.com\/Morre24\/status\/1871185694141370648\">@Morre<\/a>) shima yayi nasa martani.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cBana jin hakan gaskiya ne,\u201d Ismail Asiemu (<a href=\"https:\/\/x.com\/ismailaniemu\/status\/1871248299732164844\">@ismailaniemu<\/a>) ya banbanta da su a nasa tsokaci.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ganin yadda irin wannan wallafa ke iya kawo nakasu da ma jawo tashin hankali ga kuma yadda ake ta cece-ku-ce , DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike don tabbatar da gaskiya kan da\u2019awar.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta gudanar da bincike cikin ayoyin Al-Kur\u2019ani mai girma (<a href=\"https:\/\/www.iium.edu.my\/deed\/lawbase\/risalah_maliki\/book11.html#:~:text=The%20man%20who%20should%20lead,is%20entitled%20to%20be%20Imam\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Iium.edu.my<\/a>) inda a sura ta 11 aya ta farko ta nunar da cewa mutum (Namiji) wanda ya kamata ya jagoranci sallah shine ya zama mafi ilimi da kamala. Ta kara da cewa mafi tsantseni ya jagoranci sallah.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cMutum da zai jagoranci sallah cikin mutane shine mafi ilimin addini da tsoron Allah a cikin al\u2019umma.\u201d kamar yadda Al-Kur\u2019ani ya nunar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shafin <a href=\"https:\/\/islamqa.info\/en\/answers\/20219\/who-should-lead-the-prayer\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">IslamQA<\/a> shima ya bayyana cewa mafi dacewa cikin al\u2019umma Musulmi shine wanda ya kasance mai ilimi da ya fahimci abubuwan da Al-Kur\u2019ani mai girma ya koyar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cWanda ya cancanci yayi limanci shine wanda yake da ilimi kan abubuwan da aka tanada a cikin Sallah wanda kuma yafi haddar Al\u2019Kur\u2019ani\u201d kamar yadda kafar ta wallafa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Me masana a ilimin addinin Islama ke fadi:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta tuntubi wasu daga cikin malaman addinin Islama a Arewacin Najeriya don ji daga gare su ko Musulmi Bayerabe ba shi da dama ta jagorantar sallah&nbsp; a Arewacin Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun tuntubi Aminu Numan, wani masanin ilimin addinin Islama a jihar Adamawa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya don jin karin bayani game da wannan da\u2019awa. Sai ya ce cikin al\u2019umma Musulmi muddin mutum na da ilimin Al\u2019Kur\u2019ani mai girma ya canci ya jagoranci mutane su yi sallah.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201c A duk lokacin da muka samu kanmu za a yi sallah to wanda yafi ilimi na addini da iya karatun Al-Kur\u2019ani a cikinmu shine yafi cancanta yayi jagorancin sallah, haka Annabinmu&nbsp; Sallallahu Alaihu Wa Sallam ya nunar mana.\u201d A cewar Malam Aminu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kara da cewa ya ziyarci jihohi da dama a Najeriya musamman a arewacin kasar bai taba ganin abin da mai da\u2019awar a shafin na X ke fadi ba. Ya kara da cewa abin da mai da\u2019awar ke fadi ma \u201cya sabawa koyarwar addinin Islama\u201d irin wadannan kalamai ba za su fito ba a bakin wanda ya san addinin Islama.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani malamin addinin a jihar ta Adamawa Haruna Yawale, shima a nasa tsokaci a dangane da wannan da\u2019awa yace ya zauna a wurare da dama a Arewacin Najeriya inda Yarubawa ke jagorantar sallah a lokuta da dama.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cBa da\u2019awa ce mai kyau ba, na zauna a wurare da dama a arewacin na Najeriya inda na yi mu\u2019amala da Yarubawa da dama wadanda suke jan mu sallah sau tari, wasu daga cikinsu ma sune limaman masallatan\u201d kamar yadda Malam Haruna ya fadawa DUBAWA.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cGa misali anan masallacin asibitin koyarwa na Moddibo Adama Teaching Hospital, Yola, shugaban kwamitin Musulmi ne Bayerabe. Ya kasance guda daga cikin limaman masallacin,\u201d&nbsp; kamar yadda Haruna yayi karin haske.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Awwal Salusu malami ne a jami\u2019ar Tarayya ta Gashua jihar Yobe, yayi fatali da wannan da\u2019awa da yace karya ce, ya kara da cewa sharadi na yin limanci shine mutum ya kasance wanda ya mika kansa wajen gudanar da addinin Musulinci ya kuma zamana zai iya karanta Suratul Fatiha da wasu surori na Al\u2019Kur\u2019ani.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cWannan da\u2019awa ba gaskiya ba ce , baki daya ma yaudara ce, sharadi guda da zai sa mutim ya zama limami anan arewaci shine mutum ya zama mai kama kai Musulmi yana iya karanta suratul Fatiha da wasu ayoyi daga cikin Al\u2019Kur\u2019ani mai girma, dole ,mutum ya zama yana da ilimi kan yadda ake sallah da sharudanta , ba magana ba ce ta kabila ko jiha ko ma wane launin fata mutum ke da shi.\u201dkamar yadda Awwal ya jaddada.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta sake tambayar malamin jami\u2019ar ko ya taba gani, ko jin wasu Musulmi na tattaunawa wa zai jagoranci sallah, sai ya mayar da martani da cewa kwamitin masallaci na iya yin hakan a wasu lokutan, abu ne sananne cewa babban limami ko mai taimakamasa su ake bawa wannan jagoranci na sallah a masallatai.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cIdan kuma kana nufin duk wata sallah, ba haka lamarin yake ba, amma idan kana nufin kwamitin masallaci haka ne, a wasu lokutan yana zabar wanda zai jagoranci sallah.\u201d A cewarsa<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cSaboda batu na wa zai jagoranci sallah a masallaci wani abu ne sananne ga kowa a masallaci, akwai limami na farko da mataimakinsa na farko da na biyu, idan basa nan ne sai a samu wani ya jagoranci sallah wannan abune sananne kamar yadda Awwal ya bayyana.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ibrahim Damare, shugaban sashen koyar da addinin Islama a kwalejin fasaha ta jihar Adamawa ya fadawa DUBAWA cewa wannan da\u2019awa bata da tushe, baki daya babu wani banbanci a tsakanin masu yin bautar Allah a addinin Islama, kuma akwai sharuda da za a cika kafin mutum ya zama limami, kuma wadannan sharuda haka aka gindaya su ga duk wani mabiyin addinin Islama a fadin duniya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201dAbin da zan fada maka shine wannan kawai zargi ne. Ina fada maka cewa a addinin Islama ba kawai maganar arewacin Najeriya ba, ko wani bangare na Najeriya, ana magana ne a baki daya, duk sanda mutum ya zama Musulmi babu wani banbanci da kake da shi da wanda yake cikin masallaci, sharadin zama limami addini ne yake gindayawa babu banbanci na kabila ko wani jinsi,\u201d kamar yadda Ibrahim ya bayyana.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun kuma tambaya don jin matsayar da Al-Kur\u2019ani ya bayyana a dangane da limancin, sai Awwal yace ai duk dan Adam iri daya ne, ya kara da cewa duk mai son yin limanci zai zamana yana da ilimi na addini da cikar kamala ta addini.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cKu saurara ya ku al\u2019umma; mun halicce ku daga uwa da uba guda daya, sai muka raba ku a kasashe da kabilu don ku san junan ku.\u201d Ayar Kur\u2019ani da ya karanto.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cWannan ya sanya na fada maku babu wasu sharuda da aka gindaya, sharadi kawai shine mutum ya zama Musulmi, na biyu ya zama mutum na da ilimin&nbsp; Al\u2019Kur\u2019ani na uku mutum ya zama yana da kamala.\u201d kamar yadda masanin na addinin Islama ya kara bayani.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shedu da aka samu daga Al\u2019Kur\u2019ani mai girma da bayanan malamai sun tabbatar da cewa wanda zai jagoranci sallah a cikin al\u2019umma sai ya kasance mai ilimin addini kuma yana da sanin Al\u2019Kur\u2019ani.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin X yayi da\u2019awar (claimed) cewa an haramtawa Yarubawa Musulmai damar yin limanci a Arewacin Najeriya. Hukunci: Karya ce, Al\u2019Kur\u2019ani yayi tanadin cewa wanda zai jagoranci Musulmi a wajen Sallah ya kasance shi ya fi ilimi na addini da kamewa a cikinsu. Kuma malamai sun yi wa mai wannan da\u2019awa raddi da cewa jagoranci na sallah ba shi da alaka da kabilanci. Cikakken Sako Addini da kabilanci suna taka muhimmiyar rawa (integral role) a zamantakewa da siyasar Najeriya. Haduwar wadanan abubuwa biyu kuma ana ganin tasirinsu a zahiri a yankunan kasar da siyasarta. Akwai dai mabanbantan addini da kabila a zamantakewar \u2018yan Najeriya, abin da ke kawo tarnaki a zamantakewa (social rift) da rashin fahimta a tsakanin \u2018yan kasar, kasancewar kowanne na ikirarin cewa nasa addini ko kabila shine ke kan gaba da na dan\u2019uwansa. Abu mafi muni shine yadda wasu ke ganin su suka fi cancanta su samu wata moriya da suka hadar da ganin cewa su ke jagoranci, da basu wasu mukamai da ma basu wata dama ta kasa da sauransu saboda matsayinsu a cikin al\u2019ummar kasar. A kan wannan ne mai amfani da shafin na X Omo Oodua (@yomiable) ke kafa tasa da\u2019awa da cewa Yarubawa da ke zama Musulmai ba a basu damar su jagoranci sallah a arewacin Najeriya. Ya rubata ne cewa, \u201cYorubawa&nbsp; Musulmai an haramta masu jagorancin sallah a Arewacin Najeriya.\u201d Ya kara da cewa (mentioned) wannan na faruwa ne saboda koyarwar Shehu Usman Danfodio.&nbsp; Wannan wallafa dai a shafin na X ta tada kura inda masu amfani da shafin suka yi ta mayar da martani, an samu masu tsokaci 716 da masu sake yadawa 903 da masu nuna sha\u2019awarsu 1,500 da masu nuna za su sake nazarta 90, wannan ya zuwa ranar 22 ga Janairun,2025 kenan. DUBAWA ta nazarci sashin yin tsokaci na wannan wallafa, inda anan ne ta lura da cewa wasu sun aminta da abin da mai da\u2019awar ke fadi har suna cewa ai haka lamarin yake a Najeriya&nbsp; yayin da wasu kuma ke ganin ba haka lamarin yake ba. \u201cAbun takaici ne ganin yadda wasu al\u2019ummar Yarubawa Musulmai suke yin duk abin da za su iya a mayar da su baya ko da kuwa a yankinsu ne\u2026Anawa ra\u2019ayin kada su bari a mayar da yankin mu Arewa maso Gabas,\u201d a cewar Asiwaju of Owoland (@egtapere). \u201cAmma za su zo nan ma suce za su yi yadda suka ga dama,\u201d Akintayo (@Morre) shima yayi nasa martani. \u201cBana jin hakan gaskiya ne,\u201d Ismail Asiemu (@ismailaniemu) ya banbanta da su a nasa tsokaci.&nbsp; Ganin yadda irin wannan wallafa ke iya kawo nakasu da ma jawo tashin hankali ga kuma yadda ake ta cece-ku-ce , DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike don tabbatar da gaskiya kan da\u2019awar. Tantancewa DUBAWA ta gudanar da bincike cikin ayoyin Al-Kur\u2019ani mai girma (Iium.edu.my) inda a sura ta 11 aya ta farko ta nunar da cewa mutum (Namiji) wanda ya kamata ya jagoranci sallah shine ya zama mafi ilimi da kamala. Ta kara da cewa mafi tsantseni ya jagoranci sallah. \u201cMutum da zai jagoranci sallah cikin mutane shine mafi ilimin addini da tsoron Allah a cikin al\u2019umma.\u201d kamar yadda Al-Kur\u2019ani ya nunar. . Shafin IslamQA shima ya bayyana cewa mafi dacewa cikin al\u2019umma Musulmi shine wanda ya kasance mai ilimi da ya fahimci abubuwan da Al-Kur\u2019ani mai girma ya koyar. \u201cWanda ya cancanci yayi limanci shine wanda yake da ilimi kan abubuwan da aka tanada a cikin Sallah wanda kuma yafi haddar Al\u2019Kur\u2019ani\u201d kamar yadda kafar ta wallafa. Me masana a ilimin addinin Islama ke fadi: DUBAWA ta tuntubi wasu daga cikin malaman addinin Islama a Arewacin Najeriya don ji daga gare su ko Musulmi Bayerabe ba shi da dama ta jagorantar sallah&nbsp; a Arewacin Najeriya. Mun tuntubi Aminu Numan, wani masanin ilimin addinin Islama a jihar Adamawa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya don jin karin bayani game da wannan da\u2019awa. Sai ya ce cikin al\u2019umma Musulmi muddin mutum na da ilimin Al\u2019Kur\u2019ani mai girma ya canci ya jagoranci mutane su yi sallah. \u201c A duk lokacin da muka samu kanmu za a yi sallah to wanda yafi ilimi na addini da iya karatun Al-Kur\u2019ani a cikinmu shine yafi cancanta yayi jagorancin sallah, haka Annabinmu&nbsp; Sallallahu Alaihu Wa Sallam ya nunar mana.\u201d A cewar Malam Aminu. Ya kara da cewa ya ziyarci jihohi da dama a Najeriya musamman a arewacin kasar bai taba ganin abin da mai da\u2019awar a shafin na X ke fadi ba. Ya kara da cewa abin da mai da\u2019awar ke fadi ma \u201cya sabawa koyarwar addinin Islama\u201d irin wadannan kalamai ba za su fito ba a bakin wanda ya san addinin Islama. Wani malamin addinin a jihar ta Adamawa Haruna Yawale, shima a nasa tsokaci a dangane da wannan da\u2019awa yace ya zauna a wurare da dama a Arewacin Najeriya inda Yarubawa ke jagorantar sallah a lokuta da dama. \u201cBa da\u2019awa ce mai kyau ba, na zauna a wurare da dama a arewacin na Najeriya inda na yi mu\u2019amala da Yarubawa da dama wadanda suke jan mu sallah sau tari, wasu daga cikinsu ma sune limaman masallatan\u201d kamar yadda Malam Haruna ya fadawa DUBAWA. \u201cGa misali anan masallacin asibitin koyarwa na Moddibo Adama Teaching Hospital, Yola, shugaban kwamitin Musulmi ne Bayerabe. Ya kasance guda daga cikin limaman masallacin,\u201d&nbsp; kamar yadda Haruna yayi karin haske. Awwal Salusu malami ne a jami\u2019ar Tarayya ta Gashua jihar Yobe, yayi fatali da wannan da\u2019awa da yace karya ce, ya kara da cewa sharadi na yin limanci shine mutum ya kasance wanda ya mika kansa wajen gudanar da addinin Musulinci ya kuma zamana zai iya karanta Suratul Fatiha da wasu surori na Al\u2019Kur\u2019ani. \u201cWannan da\u2019awa ba gaskiya ba ce , baki daya ma yaudara ce, sharadi guda da zai sa mutim ya zama limami anan arewaci shine mutum ya zama mai kama kai Musulmi yana iya karanta suratul Fatiha da wasu ayoyi daga cikin Al\u2019Kur\u2019ani mai girma, dole ,mutum ya zama yana da ilimi kan yadda ake sallah da sharudanta , ba<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":21440,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3699],"class_list":["post-21515","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5B1","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3699,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"cole-praise","display_name":"Cole Praise","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/7934b84f51e2c1f4c1e77cce93c223ac97cc2da29198aa9141fd944b0407bb2d?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/Yoruba.png?fit=643%2C336&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21515","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=21515"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21515\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":21516,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21515\/revisions\/21516"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/21440"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=21515"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=21515"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=21515"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=21515"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=21515"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}