{"id":21773,"date":"2025-02-27T05:38:54","date_gmt":"2025-02-27T04:38:54","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=21773"},"modified":"2025-02-27T05:39:29","modified_gmt":"2025-02-27T04:39:29","slug":"batun-wai-najeriya-ta-ficce-daga-kasuwar-hada-hadar-hannayen-jarin-najeriya-karya-ne","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/batun-wai-najeriya-ta-ficce-daga-kasuwar-hada-hadar-hannayen-jarin-najeriya-karya-ne\/","title":{"rendered":"Batun wai Najeriya ta ficce daga kasuwar hada-hadar hannayen jarin Amurka karya ne!"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Machie Johnbosce a shafin Facebook <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/groups\/PDPNNMG\/posts\/3869443036642106\/?_rdc=1&amp;_rdr#\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">na da&#8217;awar cewa<\/a> shugaba Tinubu ya janye Najeriya daga kasuwar hada-hadar hannayen jarin Amurka ya kuma hana kasar saidawa Amurka man fetur dinta.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"21052\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/liberias-finance-ministry-did-not-resubmit-the-countrys-national-budget\/false-4-2-2\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/FALSE-4-2.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4-2\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/FALSE-4-2.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/FALSE-4-2.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-21052\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Hukunci: Karya ce! Babu wata kafar yada labarai mai nagartar da ta watsa labarin. Bacin haka Najeriya ba ta ma cikin kasuwannin da ke hada-hadar hannayen jari a Amurka.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayan&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.aljazeera.com\/news\/liveblog\/2025\/1\/20\/donald-trump-inauguration-us-president-2025-live\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">rabtsuwar kama aiki<\/a> a matsayin shugaan kasa na 47 a Amurka, Donald Trump ya kaddamar da wasu sabbin matakan sauya fasalin manufofin tattalin arziki da siyasa a Amurka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ana cikin wadannan manufofin ne Machie Johnbosco, wani marubuci a shafin All Nigeria Political Parties, wani shafi a Facebook, <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/g\/14qV8tvc9F\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ya yi da&#8217;awar cewa<\/a> shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya janyue Najeriya daga kasuwar hada-hadar hannayen jarin Amurka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cikin labarin, Machie ya cet Tinubu ya kuma hana cinikin mai a Amurka sa\u2019annan ya rufe ofishin jakadancin Najeriya a Washington a matsayin wani martani ga shugaba Trump saboda hana \u2018yan Najeriya shiga kasarsa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cKowani mataki ya na da martani, kuma kowace gauta ma ja ce. Najeriya ba wata \u2018yar karamar kasa ba ce mara karfi. Idan har aka sanya mata takunkumi ita kanta za ta rama yadda ya kamata,\u201d in ji labarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da muka yi bitar labarin mun ga cewa labarin ya dauki hankalin da dama a shafin X wadanda suke so su san ko gaskiya ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da sahfin Fidelis ya yarda da labarin ya ma yaba da shi ya na cewa \u201cKyakyawar mataki\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani shi ma mai amfani da shafin, Chikira Jahari, ya nuna rashin amincewarsa ne da batun, inda ya rubuta cewa, \u201c Lallai, hakan ba zai taba faruwa ba.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">An wallafa wannan labarin a shafin Facebook a wadannan shafukan (<a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/1HAgjU1rWK\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>, <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/1HAgjU1rWK\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>, <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/1HAgjU1rWK\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>, <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/19wAfrgJLM\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>, da <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/1HAgjU1rWK\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>).&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ganin wannan ne ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiya.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa&nbsp;<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta fara da gudanar da bincike cikin Google dan ganin ko kafofin yda labarai masu nagarta sun wallafa labari dangane da wannan batun. Sai dai babu wani labarin hannayen jari bare ma hana saida wa Amurka man fetur.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Shin ana iya sa Najeriya cikin kasuwannin hada-hadar hannayen jarin Amurka?<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A kasuwar&nbsp; hada-hadar hannayen jarin New York wanda aka fi sani da&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.nyse.com\/index\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">New York Stock Exchange<\/a> babu Najeriya. Dan haka, ba ma za\u2019a iya cewa an \u201ccire\u201d Najeriya daga ciki ba hukumance, domin tun can dama ba ya ciki bare&nbsp; ce an cire.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Haka nan kuma Najeriya ba ta cikin na <a href=\"https:\/\/www.investopedia.com\/terms\/n\/nasdaq.asp\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">National Association of Securities Dealers Automated Quotation System<\/a> (NASDAQ, nan ma ba za\u2019a iya cewa an cire ta ba.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">To sai dai ana iya sanya kamfanonin da ke da asalin Najeriya a ciki, kuma akwai abubuwa da dama da za su iya yin tasiri kan kasancewa masu zuba jari daga Najeriya a kasuwannin Amurka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta tuntubi mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, dangane da sahihancin wannan batun amma ba ta sami wani martani daga wurin shi ba.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Zargin cewa Tinubu ya cifre Najeriya daga kasuwar hada-hadar hannayen jarin Amurka ta kuma hana Najeriyar saida wa Amurka mai ba gaskiya ba ne domin Najeriya ma ba ta a cikin jerin masu zuba jarin da ke da hannayen jari a kasuwannin ma baki daya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Machie Johnbosce a shafin Facebook na da&#8217;awar cewa shugaba Tinubu ya janye Najeriya daga kasuwar hada-hadar hannayen jarin Amurka ya kuma hana kasar saidawa Amurka man fetur dinta. Hukunci: Karya ce! Babu wata kafar yada labarai mai nagartar da ta watsa labarin. Bacin haka Najeriya ba ta ma cikin kasuwannin da ke hada-hadar hannayen jari a Amurka. Cikakken bayani Bayan&nbsp; rabtsuwar kama aiki a matsayin shugaan kasa na 47 a Amurka, Donald Trump ya kaddamar da wasu sabbin matakan sauya fasalin manufofin tattalin arziki da siyasa a Amurka. Ana cikin wadannan manufofin ne Machie Johnbosco, wani marubuci a shafin All Nigeria Political Parties, wani shafi a Facebook, ya yi da&#8217;awar cewa shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya janyue Najeriya daga kasuwar hada-hadar hannayen jarin Amurka. A cikin labarin, Machie ya cet Tinubu ya kuma hana cinikin mai a Amurka sa\u2019annan ya rufe ofishin jakadancin Najeriya a Washington a matsayin wani martani ga shugaba Trump saboda hana \u2018yan Najeriya shiga kasarsa. \u201cKowani mataki ya na da martani, kuma kowace gauta ma ja ce. Najeriya ba wata \u2018yar karamar kasa ba ce mara karfi. Idan har aka sanya mata takunkumi ita kanta za ta rama yadda ya kamata,\u201d in ji labarin. Da muka yi bitar labarin mun ga cewa labarin ya dauki hankalin da dama a shafin X wadanda suke so su san ko gaskiya ne. Wani mai amfani da sahfin Fidelis ya yarda da labarin ya ma yaba da shi ya na cewa \u201cKyakyawar mataki\u201d Wani shi ma mai amfani da shafin, Chikira Jahari, ya nuna rashin amincewarsa ne da batun, inda ya rubuta cewa, \u201c Lallai, hakan ba zai taba faruwa ba.\u201d An wallafa wannan labarin a shafin Facebook a wadannan shafukan (nan, nan, nan, nan, da nan).&nbsp; Ganin wannan ne ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiya. Tantancewa&nbsp; DUBAWA ta fara da gudanar da bincike cikin Google dan ganin ko kafofin yda labarai masu nagarta sun wallafa labari dangane da wannan batun. Sai dai babu wani labarin hannayen jari bare ma hana saida wa Amurka man fetur. Shin ana iya sa Najeriya cikin kasuwannin hada-hadar hannayen jarin Amurka? A kasuwar&nbsp; hada-hadar hannayen jarin New York wanda aka fi sani da&nbsp; New York Stock Exchange babu Najeriya. Dan haka, ba ma za\u2019a iya cewa an \u201ccire\u201d Najeriya daga ciki ba hukumance, domin tun can dama ba ya ciki bare&nbsp; ce an cire. Haka nan kuma Najeriya ba ta cikin na National Association of Securities Dealers Automated Quotation System (NASDAQ, nan ma ba za\u2019a iya cewa an cire ta ba.&nbsp; To sai dai ana iya sanya kamfanonin da ke da asalin Najeriya a ciki, kuma akwai abubuwa da dama da za su iya yin tasiri kan kasancewa masu zuba jari daga Najeriya a kasuwannin Amurka. DUBAWA ta tuntubi mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, dangane da sahihancin wannan batun amma ba ta sami wani martani daga wurin shi ba. A karshe Zargin cewa Tinubu ya cifre Najeriya daga kasuwar hada-hadar hannayen jarin Amurka ta kuma hana Najeriyar saida wa Amurka mai ba gaskiya ba ne domin Najeriya ma ba ta a cikin jerin masu zuba jarin da ke da hannayen jari a kasuwannin ma baki daya.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":21504,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3793],"class_list":["post-21773","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5Fb","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3793,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"lademi-aborisade","display_name":"Lademi Aborisade","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/stock-image.jpg?fit=259%2C194&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21773","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=21773"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21773\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":21775,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21773\/revisions\/21775"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/21504"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=21773"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=21773"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=21773"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=21773"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=21773"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}