{"id":21837,"date":"2025-03-07T12:12:04","date_gmt":"2025-03-07T11:12:04","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=21837"},"modified":"2025-03-07T12:12:06","modified_gmt":"2025-03-07T11:12:06","slug":"yadda-yancin-mata-ya-canza-a-jihar-kano-kalubale-nasarori-da-tafiyar-da-ke-gaba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/yadda-yancin-mata-ya-canza-a-jihar-kano-kalubale-nasarori-da-tafiyar-da-ke-gaba\/","title":{"rendered":"Yadda \u2018yancin mata ya canza a jihar Kano: Kalubale, nasarori da tafiyar da ke gaba"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Yayin da ake bukin ranar mata ta duniya Mariya Shu\u2019aibu ta yi ma nazarin rayuwar mata a Kano \u2013 waiwaye da hanyoyin da suke bi wajen inganta rayuwarsu<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shekaru 30 da sanya hannu kan yarjejeniyar Beijing wadda ta fadada hakkokin mata da sauran harkokin da suka shafi mata da \u2018yan mata ana iya cewa an sami sauyi a jihar Kano. A shekarun baya, jin ra\u2019ayin mace ko a ce mace na samun albarka a kasuwancinta, tana tsayawa takara ko ma wadda ke da da iko a kan rayuwarta abu ne mai wahala sai dai watakila a mafarki.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Al\u2019adun gargajiya, rashin samun ilimi, da kalubalen da ke tattare da irin tsarin rayuwar da ta ke gudanarwa sun hana mata damar taka rawa a wuraren daukar matakai. Amma yanzu akwai sauyi, ko da yake a hankali yak e zuwa, ana iya ganin wasu alamu a bayyane. Yanzu haka \u2018yan mata da dama na makaranta, mata da yawa sun samu \u2018yancin neman kudi, kuma kariya ta shari\u2019a akan cin zarafi ya karu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai duk da haka, tafiyar ba ta kare ba. Har yanzu akwai mata da dama da ke fama da irin kalubalen da iyayensu da kakanninsu suka fuskanta\u2014cin zarafi, rashin wakilci a siyasa, da kuma al\u2019adun da ke hana ci gaba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yayin da duniya ke bikin Ranar Mata ta Duniya ta 2025, lokaci ya yi da za a yi nazari: Har yaushe matan Kano suka zo matakin da ake a yau? Wadanne gwagwarmaya aka yi wajen samun nasara? Kuma menene ke ci gaba da hana a samu daidaito na gaskiya?<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"614\" height=\"499\" data-attachment-id=\"21845\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/yadda-yancin-mata-ya-canza-a-jihar-kano-kalubale-nasarori-da-tafiyar-da-ke-gaba\/photo-2025-03-04-08-16-57\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-08-16-57.jpg?fit=614%2C499&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"614,499\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"PHOTO-2025-03-04-08-16-57\" data-image-description=\"&lt;p&gt;Farida Kallah&lt;\/p&gt;\n\" data-image-caption=\"&lt;p&gt;Farida Kallah&lt;\/p&gt;\n\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-08-16-57.jpg?fit=614%2C499&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-08-16-57.jpg?resize=614%2C499\" alt=\"Farida Kallah\" class=\"wp-image-21845\" title=\"\" srcset=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-08-16-57.jpg?w=614&amp;ssl=1 614w, https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-08-16-57.jpg?resize=300%2C244&amp;ssl=1 300w\" sizes=\"(max-width: 614px) 100vw, 614px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\">Farida Kallah<\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Ilimi: Warware Sarkar Auren Wuri<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A baya, ilimin \u2018yan mata a Kano an rika masa kallon gata \u2014 wato wani abun da za a iya sadaukarwa don auren wuri ko ayyukan gida. Amma a cikin \u2018yan shekarun nan, sauyi ya fara shiga. Iyaye, suna samun kwarin gwiwa daga labarun nasara da kuma manufofin gwamnati da ke karfafa ilimin \u2018yan mata, suna fahimtar amfanin barin \u2018ya\u2019yansu mata su kammala karatu ko da kuwa zai dauki lokaci.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yau, matasa mata a Kano sun daina kammala daga sakandare; suna zama likitoci, injiniyoyi, da lauyoyi. Sai dai wannan ci gaban bai kai ko\u2019ina ba. A karkara, talauci da takunkumin al\u2019ada har yanzu suna hana \u2018yan mata damar karatu. Dan haka, yaki da jahilci bai kare ba, amma nasarorin da aka samu sun sauya rayuwa kuma suna cigaba da yin hakan.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Daga Kasuwanni zuwa Ofisoshin Manyan Hukumomi<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mata sun shafe shekaru yanzu suna sauya dabarun kasuwanci, kuma matan Kano su ne ginshikin kasuwanci na gargajiya \u2014 suna sayar da abinci, zane, da kayan gida a kasuwanni masu cike da hayaniya. Amma samun rancen kudi, jagoranci, da kuma hanyar shiga hanyoyin kasuwanci ya kan kasance da wahala. Wannan abu ne da ke sauyawa sannu a hankali.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Daya daga cikin manyan labarun nasara ita ce ta Farida Musa Kalla, wacce ta kafa FMK Clothing, daya daga cikin manyan kamfanonin kaya a Kano. Farida ta fara daga tushe (da N600,000 da mahaifiyarta ta bata domin ta sayi mota, amma ta ajiye kudin a banki kuma ta fara sayen kayan sawa don siyarwa) tun tana daliba ta na sayar da kayan zanen gida a makaranta har zuwa lokacin yi wa kasa hidima (NYSC) Ta yi fuskantar matsin kudi da kalubalen al\u2019ummar da ke hana mata tafiyar da manyan kasuwanci, amma da hakuri da kwazo, ta gina FMK Clothing zuwa wani babban suna a Kano, kuma da haka tana tabbatar da cewa mata na iya cin nasara a harkar kasuwanci.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Labarai irin na Farida hujjoji ne na juriya da kwazon matan Kano, wadanda da dama yanzu suna amfani da shirin microfinance, horon sana\u2019a, da kuma dandalin sada zumunta don habaka kasuwancinsu. Sai dai har yanzu matsaloli na nan \u2014 samun rance babbar matsala ce, kuma ra\u2019ayin al\u2019umma yana ci gaba da rage girman kasuwancin da mata ke iya yi.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"768\" data-attachment-id=\"21838\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/yadda-yancin-mata-ya-canza-a-jihar-kano-kalubale-nasarori-da-tafiyar-da-ke-gaba\/photo-2025-03-04-15-34-39\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-34-39.jpg?fit=1080%2C810&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"1080,810\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"Mariya Shu&amp;#8217;aibu lokacin gangamin fadakarwa kan cin zarafin mata\" data-image-description=\"&lt;p&gt;Mariya Shu&amp;#8217;aibu lokacin gangamin fadakarwa kan cin zarafin mata&lt;\/p&gt;\n\" data-image-caption=\"&lt;p&gt;Mariya Shu&amp;#8217;aibu lokacin gangamin fadakarwa kan cin zarafin mata&lt;\/p&gt;\n\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-34-39.jpg?fit=1024%2C768&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-34-39.jpg?resize=1024%2C768\" alt=\"Mariya Shu&#039;aibu lokacin gangamin fadakarwa kan cin zarafin mata\" class=\"wp-image-21838\" title=\"\" srcset=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-34-39.jpg?resize=1024%2C768&amp;ssl=1 1024w, https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-34-39.jpg?resize=300%2C225&amp;ssl=1 300w, https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-34-39.jpg?resize=768%2C576&amp;ssl=1 768w, https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-34-39.jpg?w=1080&amp;ssl=1 1080w\" sizes=\"(max-width: 1000px) 100vw, 1000px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\">Mariya Shu&#8217;aibu lokacin gangamin fadakarwa kan cin zarafin mata<\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Yaki da Cin Zarafin Mata<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u00a0Yanzu ba\u2019a yin shiru ko jin nauyin magana dangane da cin zarafin mata a Kano, a baya ya kasance sirrin da akan boye, sa\u2019annan yawanci wadanda aka ci zarafinsu bas u da wurin kai kuka, kuma masu laifi suna yawo da \u2018yanci ba tare da hukunci ba. Amma yau, abubuwa sun sauya. Kungiyoyi kamar Ma\u2019aikatar Kula da Harkokin Mata, FIDA (Kungiyar Lauyoyin Mata), da CITAD (Cibiyar Fasaha da Cigaban Al\u2019umma) sun shiga gaba wajen yaki da cin zarafi a Kano. Ta hanyar bayar da taimakon shari\u2019a, wayar da kai, da amfani da fasaha, suna tabbatar da cewa wanda aka ci wa zarafi yana samun adalci. Cibiyar Waraka Sexual Referral Centre ita ma ta zama haske ga wadanda aka ci zarafi, tana bayar da kula ta lafiya, taimakon shari\u2019a, da shawarwari. A waje guda kuma, CITAD ta kirkiri hanyoyin fasaha da ke ba mutane damar kai rahoton cin zarafi cikin sirri da kwanciyar hankali.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da haka, tsoro da kunya har yanzu suna hana mutane da yawa magana, kuma jami\u2019an tsaro da yawa ba sa daukar mataki da sauri. Yakin neman adalci bai kare ba, amma ci gaban da aka samu yana bayyane.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Mata a Siyasa: Har yanzu suna neman kujerun mukamai<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A shekarar 1995, ra\u2019ayin mace tana rike da mukamin siyasa a Kano abu ne mai wahala. Yau, mata da dama suna shiga siyasa, amma adadinsu har yanzu kadan ne sosai. Ra\u2019ayoyi na gargajiya, matsalar kudi, da siyasar da maza suka mamaye na hana mata shiga mukaman shugabanci. Wadanda suka samu nasara sun yi hakan ne da matsanancin gwagwarmaya. Amma nasararsu ta bude kofar dama ga matan da ke tasowa masu sha\u2019awar siyasa. Kalubalen yanzu ba karfafa mata su tsaya takara ne kadai ba \u2014 amma tabbatar da cewa suna da kayan aiki da goyon baya don su samu nasara da jagoranci mai nagarta.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"540\" data-attachment-id=\"21839\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/yadda-yancin-mata-ya-canza-a-jihar-kano-kalubale-nasarori-da-tafiyar-da-ke-gaba\/photo-2025-03-04-15-30-56\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-30-56.jpg?fit=720%2C540&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"720,540\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"Hoto daga shafin ma&amp;#8217;aikatar kula da harkokin mata a Kano\" data-image-description=\"&lt;p&gt;Hoto daga shafin ma&amp;#8217;aikatar kula da harkokin mata a Kano&lt;\/p&gt;\n\" data-image-caption=\"&lt;p&gt;Hoto daga shafin ma&amp;#8217;aikatar kula da harkokin mata a Kano&lt;\/p&gt;\n\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-30-56.jpg?fit=720%2C540&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-30-56.jpg?resize=720%2C540\" alt=\"Hoto daga shafin ma&#039;aikatar kula da harkokin mata a Kano\" class=\"wp-image-21839\" title=\"\" srcset=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-30-56.jpg?w=720&amp;ssl=1 720w, https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/PHOTO-2025-03-04-15-30-56.jpg?resize=300%2C225&amp;ssl=1 300w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\">Hoto daga shafin ma&#8217;aikatar kula da harkokin mata a Kano<\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Mene Ne Na Gaba? Hanyar samun daidaito na gaskiya<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da ci gaban da aka samu, aikin bai kare ba. Yakin kare \u2018yancin mata a Kano dole ne ya ci gaba da sabon kuzari da jajircewa. Ga abubuwan da suka kamata a yi gaba:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Karfin Aiwatar da Dokoki: Dole a tabbatar dokokin kare hakkin mata suna aiki, ba wai  a rubuce kawai za su cigaba da kasnacewa ba a tabbatar an aiwatar.<\/li>\n\n\n\n<li>Sauya Al\u2019adu: Dole ne a jawo malamai da shugabannin gargajiya domin canza al\u2019adun da ke hana ci gaba.<\/li>\n\n\n\n<li>\u2018Yancin Tattalin Arziki: A samar da karin kudade, jagoranci, da horo ga mata \u2018yan kasuwa.<\/li>\n\n\n\n<li>Karin Wakilci a Siyasa: A samar da jagoranci da tallafi domin mata su shiga siyasa kuma su yi nasara.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;Lallai matan Kano sun yi nisa, amma hanyar zuwa daidaito har yanzu tana kan gina ta. Shekaru talatin da suka wuce sun tabbatar da cewa sauyi yana yiwuwa \u2014 amma sai da jajircewa, fafutuka, da aiki. Yayin da muke bikin Ranar Mata ta Duniya ta 2025, muna girmama matan da suka fafata don ci gaba da wadanda har yanzu ke ci gaba da gwagwarmaya, suna kin amincewa da takura. Gobe na wadanda suka shirya kalubalantar al\u2019ada ne \u2014 kuma matan Kano suna tabbatar da cewa sun shirya karbe wannan dama.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Yayin da ake bukin ranar mata ta duniya Mariya Shu\u2019aibu ta yi ma nazarin rayuwar mata a Kano \u2013 waiwaye da hanyoyin da suke bi wajen inganta rayuwarsu Shekaru 30 da sanya hannu kan yarjejeniyar Beijing wadda ta fadada hakkokin mata da sauran harkokin da suka shafi mata da \u2018yan mata ana iya cewa an sami sauyi a jihar Kano. A shekarun baya, jin ra\u2019ayin mace ko a ce mace na samun albarka a kasuwancinta, tana tsayawa takara ko ma wadda ke da da iko a kan rayuwarta abu ne mai wahala sai dai watakila a mafarki. Al\u2019adun gargajiya, rashin samun ilimi, da kalubalen da ke tattare da irin tsarin rayuwar da ta ke gudanarwa sun hana mata damar taka rawa a wuraren daukar matakai. Amma yanzu akwai sauyi, ko da yake a hankali yak e zuwa, ana iya ganin wasu alamu a bayyane. Yanzu haka \u2018yan mata da dama na makaranta, mata da yawa sun samu \u2018yancin neman kudi, kuma kariya ta shari\u2019a akan cin zarafi ya karu. Sai dai duk da haka, tafiyar ba ta kare ba. Har yanzu akwai mata da dama da ke fama da irin kalubalen da iyayensu da kakanninsu suka fuskanta\u2014cin zarafi, rashin wakilci a siyasa, da kuma al\u2019adun da ke hana ci gaba. Yayin da duniya ke bikin Ranar Mata ta Duniya ta 2025, lokaci ya yi da za a yi nazari: Har yaushe matan Kano suka zo matakin da ake a yau? Wadanne gwagwarmaya aka yi wajen samun nasara? Kuma menene ke ci gaba da hana a samu daidaito na gaskiya? Ilimi: Warware Sarkar Auren Wuri A baya, ilimin \u2018yan mata a Kano an rika masa kallon gata \u2014 wato wani abun da za a iya sadaukarwa don auren wuri ko ayyukan gida. Amma a cikin \u2018yan shekarun nan, sauyi ya fara shiga. Iyaye, suna samun kwarin gwiwa daga labarun nasara da kuma manufofin gwamnati da ke karfafa ilimin \u2018yan mata, suna fahimtar amfanin barin \u2018ya\u2019yansu mata su kammala karatu ko da kuwa zai dauki lokaci. Yau, matasa mata a Kano sun daina kammala daga sakandare; suna zama likitoci, injiniyoyi, da lauyoyi. Sai dai wannan ci gaban bai kai ko\u2019ina ba. A karkara, talauci da takunkumin al\u2019ada har yanzu suna hana \u2018yan mata damar karatu. Dan haka, yaki da jahilci bai kare ba, amma nasarorin da aka samu sun sauya rayuwa kuma suna cigaba da yin hakan. Daga Kasuwanni zuwa Ofisoshin Manyan Hukumomi Mata sun shafe shekaru yanzu suna sauya dabarun kasuwanci, kuma matan Kano su ne ginshikin kasuwanci na gargajiya \u2014 suna sayar da abinci, zane, da kayan gida a kasuwanni masu cike da hayaniya. Amma samun rancen kudi, jagoranci, da kuma hanyar shiga hanyoyin kasuwanci ya kan kasance da wahala. Wannan abu ne da ke sauyawa sannu a hankali. Daya daga cikin manyan labarun nasara ita ce ta Farida Musa Kalla, wacce ta kafa FMK Clothing, daya daga cikin manyan kamfanonin kaya a Kano. Farida ta fara daga tushe (da N600,000 da mahaifiyarta ta bata domin ta sayi mota, amma ta ajiye kudin a banki kuma ta fara sayen kayan sawa don siyarwa) tun tana daliba ta na sayar da kayan zanen gida a makaranta har zuwa lokacin yi wa kasa hidima (NYSC) Ta yi fuskantar matsin kudi da kalubalen al\u2019ummar da ke hana mata tafiyar da manyan kasuwanci, amma da hakuri da kwazo, ta gina FMK Clothing zuwa wani babban suna a Kano, kuma da haka tana tabbatar da cewa mata na iya cin nasara a harkar kasuwanci. Labarai irin na Farida hujjoji ne na juriya da kwazon matan Kano, wadanda da dama yanzu suna amfani da shirin microfinance, horon sana\u2019a, da kuma dandalin sada zumunta don habaka kasuwancinsu. Sai dai har yanzu matsaloli na nan \u2014 samun rance babbar matsala ce, kuma ra\u2019ayin al\u2019umma yana ci gaba da rage girman kasuwancin da mata ke iya yi. Yaki da Cin Zarafin Mata \u00a0Yanzu ba\u2019a yin shiru ko jin nauyin magana dangane da cin zarafin mata a Kano, a baya ya kasance sirrin da akan boye, sa\u2019annan yawanci wadanda aka ci zarafinsu bas u da wurin kai kuka, kuma masu laifi suna yawo da \u2018yanci ba tare da hukunci ba. Amma yau, abubuwa sun sauya. Kungiyoyi kamar Ma\u2019aikatar Kula da Harkokin Mata, FIDA (Kungiyar Lauyoyin Mata), da CITAD (Cibiyar Fasaha da Cigaban Al\u2019umma) sun shiga gaba wajen yaki da cin zarafi a Kano. Ta hanyar bayar da taimakon shari\u2019a, wayar da kai, da amfani da fasaha, suna tabbatar da cewa wanda aka ci wa zarafi yana samun adalci. Cibiyar Waraka Sexual Referral Centre ita ma ta zama haske ga wadanda aka ci zarafi, tana bayar da kula ta lafiya, taimakon shari\u2019a, da shawarwari. A waje guda kuma, CITAD ta kirkiri hanyoyin fasaha da ke ba mutane damar kai rahoton cin zarafi cikin sirri da kwanciyar hankali. Duk da haka, tsoro da kunya har yanzu suna hana mutane da yawa magana, kuma jami\u2019an tsaro da yawa ba sa daukar mataki da sauri. Yakin neman adalci bai kare ba, amma ci gaban da aka samu yana bayyane. Mata a Siyasa: Har yanzu suna neman kujerun mukamai A shekarar 1995, ra\u2019ayin mace tana rike da mukamin siyasa a Kano abu ne mai wahala. Yau, mata da dama suna shiga siyasa, amma adadinsu har yanzu kadan ne sosai. Ra\u2019ayoyi na gargajiya, matsalar kudi, da siyasar da maza suka mamaye na hana mata shiga mukaman shugabanci. Wadanda suka samu nasara sun yi hakan ne da matsanancin gwagwarmaya. Amma nasararsu ta bude kofar dama ga matan da ke tasowa masu sha\u2019awar siyasa. Kalubalen yanzu ba karfafa mata su tsaya takara ne kadai ba \u2014 amma tabbatar da cewa suna da kayan aiki da goyon baya don su samu nasara da jagoranci mai nagarta. Mene Ne Na Gaba? Hanyar samun daidaito na gaskiya Duk da ci gaban da aka samu, aikin bai kare ba. Yakin kare \u2018yancin mata a Kano dole ne ya ci gaba da sabon kuzari da jajircewa. Ga abubuwan da suka kamata a yi gaba: &nbsp;Lallai matan Kano sun yi nisa, amma hanyar<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":21840,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,4,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4444],"class_list":["post-21837","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-featured","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5Gd","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4444,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"mariya-shuaibu","display_name":"Mariya Shu'aibu","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/small-business-inghts.png?fit=1049%2C589&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21837","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=21837"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21837\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":21846,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/21837\/revisions\/21846"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/21840"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=21837"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=21837"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=21837"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=21837"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=21837"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}