{"id":22006,"date":"2025-03-21T03:07:24","date_gmt":"2025-03-21T02:07:24","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=22006"},"modified":"2025-03-21T03:11:15","modified_gmt":"2025-03-21T02:11:15","slug":"ana-zazza%c9%93i-a-%c6%99asashen-turai-kuwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/ana-zazza%c9%93i-a-%c6%99asashen-turai-kuwa\/","title":{"rendered":"Ana Zazza\u0253i a \u0198asashen Turai Kuwa?"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A \u0199asashen Turai, ana zazza\u0253i, amma ba irin zazza\u0253in da muke fama da shi ba ne a Najeriya, da wasu sassa na \u0199asashen Afirka ba. A Najeriya, sauro tana \u0257auke da sinadarin da yake sanya zazza\u0253i, bayan ya ciji mutum. Amma a Turai, akwai sauro, wa\u0257anda suka fi namu girma ka\u0257an a idanu. Amma, abin tambayar a nan shi ne, a yaushe ake ganin su? Suna cizo kuwa? Suna sanya zazza\u0253i?<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u0198asashen Turai wuri ne da suke da yanayi, wanda akasari, akwai sanyi sosai, yawancin lokuta. A lokacin sanyi, wanda yakan fara ne daga watan Disamba zuwa Watan Faburairu (wasu wurare ma, tun watan Nuwamba zuwa watan Maris), akan samu, sanyi ya yi tsanani sosai. Sanyi ya fi tsanani a ta gabashin \u0199asashen Turai, kamar su Rahsa, Iceland, da dai sauransu. A \u0199asar Jamus, ana sanyi sosai, kuma yakan kai daga digiri 4 zuwa 0, da kuma \u0199asa da 0. Idan ya yi \u0199asa da 0, akan ji sanyi mai tsanani. A irin wannan lokaci na sanyi, babu sauro, babu kuma hanyar ma da sauro za su iya rayuwa a irin wannan yanayi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Amma a lokacin zafi a Jamus, wanda yakan fara tun daga watannin Yuli zuwa Agusta, akan samu \u0253ulluwar sauro, musamman a wasu wurare, kuma sukan yi cizo. Yawancin sauro, an fi artabu da su ne a jeji, ko kuma inda akwai lambuna, ko wajen sha\u0199atawa. Idan muka \u0257auki Jamus alal misali, Jamusawa suna son shawagi a lambuna da kuma zuwa yawo cikin jejinsu. Ta haka ne, a wajen shan iska, musamman da yamma, akan samu sauro su yi cizo. Idan har hakan ya faru, waurin yakan \u0257an yi fushi, wato ya \u0257an kumbura na alamar cizon sauro, kuma kafin \u0257an wani lokaci \u0199alilan, wajen yakan baje. Duk da haka, sauronsu a nan, ba sa sanya zazza\u0253i.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai kuma, akwai zazza\u0253i da ake fama da shi a nan, mai kama da na cizon sauro. Jamusawa suna kiran wannan zazza\u0253i da suna \u201cGrippe.\u201d Wato, duk wanda ya ta\u0253a kamuwa da zazza\u0253i na malariya, kuma ya zauna a Jamus, ko wasu sassa na \u0199asashen Turai, kuma ya yi zazza\u0253i na \u201cGrippe\u201d, zai ji shi ne, kamar irin na cizon sauro, wato cutar malariya. Dukkan ilahirin jikin mutum zai \u0257au zafi, ciwon kai, da dai sauransu da duk mai malariya yake ji a lokacin fama da rashin lafiyar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da haka, a wajen Turawa, akwai banbanci. Dalilin kuwa shi ne, zazza\u0253i mai \u0257auke da sinadarin cutar sauro yana da illa matu\u0199a, tun da yana kisa. Kamar yadda aka \u0199iyasta, kowace shekara, mutane sama da 500,000 suna mutuwa a ta dalilin sauro. Hakazalika, idan mutum ya shigo Jamus daga nahiyar Afirka, ko inda ya kamu da cutar cizon sauro, kuma ta bayyana cewa, yana \u0257auke da zazza\u0253in malariya, kuma aka kai shi asibiti, to akan killace mutum ne a wani \u0257aki. Likitoci, idan za su shiga wannan \u0257aki, sai sun yi shiga irin na lokacin Korona, wato dukkan jiki, daga kai har zuwa sawu, sai an sanya tufafin-kariya. Mai jinya kuwa, ba zai bar wannan \u0257akin ba, sai ya sha magunguna da tasa-tasai, an kuma tabbatar babu wannan cutar ta malariya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A ta\u0199aice dai, duk da babu zazza\u0253in malariya, akwai zazza\u0253i mai suna \u201cGrippe\u201d, mai kuma jikkata mutum, idan mutum ya kamu da shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Umma Aliyu Musa Malama ce a jami&#8217;ar Hamburg da ke Jamus, kuma daga can Jamus din ne ta turo mana wannan gudunmawar<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A \u0199asashen Turai, ana zazza\u0253i, amma ba irin zazza\u0253in da muke fama da shi ba ne a Najeriya, da wasu sassa na \u0199asashen Afirka ba. A Najeriya, sauro tana \u0257auke da sinadarin da yake sanya zazza\u0253i, bayan ya ciji mutum. Amma a Turai, akwai sauro, wa\u0257anda suka fi namu girma ka\u0257an a idanu. Amma, abin tambayar a nan shi ne, a yaushe ake ganin su? Suna cizo kuwa? Suna sanya zazza\u0253i? \u0198asashen Turai wuri ne da suke da yanayi, wanda akasari, akwai sanyi sosai, yawancin lokuta. A lokacin sanyi, wanda yakan fara ne daga watan Disamba zuwa Watan Faburairu (wasu wurare ma, tun watan Nuwamba zuwa watan Maris), akan samu, sanyi ya yi tsanani sosai. Sanyi ya fi tsanani a ta gabashin \u0199asashen Turai, kamar su Rahsa, Iceland, da dai sauransu. A \u0199asar Jamus, ana sanyi sosai, kuma yakan kai daga digiri 4 zuwa 0, da kuma \u0199asa da 0. Idan ya yi \u0199asa da 0, akan ji sanyi mai tsanani. A irin wannan lokaci na sanyi, babu sauro, babu kuma hanyar ma da sauro za su iya rayuwa a irin wannan yanayi. Amma a lokacin zafi a Jamus, wanda yakan fara tun daga watannin Yuli zuwa Agusta, akan samu \u0253ulluwar sauro, musamman a wasu wurare, kuma sukan yi cizo. Yawancin sauro, an fi artabu da su ne a jeji, ko kuma inda akwai lambuna, ko wajen sha\u0199atawa. Idan muka \u0257auki Jamus alal misali, Jamusawa suna son shawagi a lambuna da kuma zuwa yawo cikin jejinsu. Ta haka ne, a wajen shan iska, musamman da yamma, akan samu sauro su yi cizo. Idan har hakan ya faru, waurin yakan \u0257an yi fushi, wato ya \u0257an kumbura na alamar cizon sauro, kuma kafin \u0257an wani lokaci \u0199alilan, wajen yakan baje. Duk da haka, sauronsu a nan, ba sa sanya zazza\u0253i. Sai dai kuma, akwai zazza\u0253i da ake fama da shi a nan, mai kama da na cizon sauro. Jamusawa suna kiran wannan zazza\u0253i da suna \u201cGrippe.\u201d Wato, duk wanda ya ta\u0253a kamuwa da zazza\u0253i na malariya, kuma ya zauna a Jamus, ko wasu sassa na \u0199asashen Turai, kuma ya yi zazza\u0253i na \u201cGrippe\u201d, zai ji shi ne, kamar irin na cizon sauro, wato cutar malariya. Dukkan ilahirin jikin mutum zai \u0257au zafi, ciwon kai, da dai sauransu da duk mai malariya yake ji a lokacin fama da rashin lafiyar. Duk da haka, a wajen Turawa, akwai banbanci. Dalilin kuwa shi ne, zazza\u0253i mai \u0257auke da sinadarin cutar sauro yana da illa matu\u0199a, tun da yana kisa. Kamar yadda aka \u0199iyasta, kowace shekara, mutane sama da 500,000 suna mutuwa a ta dalilin sauro. Hakazalika, idan mutum ya shigo Jamus daga nahiyar Afirka, ko inda ya kamu da cutar cizon sauro, kuma ta bayyana cewa, yana \u0257auke da zazza\u0253in malariya, kuma aka kai shi asibiti, to akan killace mutum ne a wani \u0257aki. Likitoci, idan za su shiga wannan \u0257aki, sai sun yi shiga irin na lokacin Korona, wato dukkan jiki, daga kai har zuwa sawu, sai an sanya tufafin-kariya. Mai jinya kuwa, ba zai bar wannan \u0257akin ba, sai ya sha magunguna da tasa-tasai, an kuma tabbatar babu wannan cutar ta malariya. A ta\u0199aice dai, duk da babu zazza\u0253in malariya, akwai zazza\u0253i mai suna \u201cGrippe\u201d, mai kuma jikkata mutum, idan mutum ya kamu da shi. Umma Aliyu Musa Malama ce a jami&#8217;ar Hamburg da ke Jamus, kuma daga can Jamus din ne ta turo mana wannan gudunmawar<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":22007,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,435,4,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4448],"class_list":["post-22006","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-article","category-featured","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5IW","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4448,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"umma-aliyu","display_name":"Umma Aliyu","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Hoton-sauro-daga-shafin-cdc.png?fit=881%2C620&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22006","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=22006"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22006\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":22010,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22006\/revisions\/22010"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/22007"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=22006"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=22006"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=22006"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=22006"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=22006"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}