{"id":22011,"date":"2025-03-21T03:29:06","date_gmt":"2025-03-21T02:29:06","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=22011"},"modified":"2025-03-21T03:29:07","modified_gmt":"2025-03-21T02:29:07","slug":"ba-gidan-wike-ne-ya-kama-da-wuta-ba-hotunan-kikirarriyar-basira-ne-wato-ai-ake-yadawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/ba-gidan-wike-ne-ya-kama-da-wuta-ba-hotunan-kikirarriyar-basira-ne-wato-ai-ake-yadawa\/","title":{"rendered":"Ba gidan Wike ne ya kama da wuta ba hotunan kikirarriyar basira ne wato AI ake yadawa"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Wani mai amfani da <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/19LdGEL6GL\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Facebook<\/a> ya yada labarin da ke cewa matasa sun kone gidan Nyesom Wike dake jihar Rivers.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"20176\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/post-edo-election-fact-checks-edo-2024-governorship-election\/false-4-1-11\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/FALSE-4-1-11.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4-1-11\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/FALSE-4-1-11.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/FALSE-4-1-11.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-20176\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\"><strong>Hukunci: <\/strong>Karya ce! Binciken Dubawa ya gano cewa hotunan da ake yadawa fasahar AI wato kirkirarriyar basira ce<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/www.bbc.com\/hausa\/articles\/c89lqj7kyeno\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Rikicin siyasar jihar Rivers<\/a> na kara zafafa, sakamakon \u0199o\u0199arin fa\u0257a\u0257a ikon da Gwamna Siminalayi Fubara ya yi a jihar, ta hanyar shiga takun saka da tsohon ubangidansa kuma ministan Abuja Nyesom Wike.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Rikcin nasu ya kai ga tarwatsa kan majalisar dokokin jihar tsakanin magoya bayansu. inda har aka samu kakakin majalisa biyu kafin daga baya shugaban kasa ya ayyana <a href=\"https:\/\/aminiya.ng\/tinubu-ya-sanya-dokar-ta-baci-a-ribas\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">dokar ta baci<\/a> a jihar da kuma nada gwamnan rikon kwarya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ana cikin haka ne wani labari da wani <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/16AF5JMnFd\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">mai amfani da Facebook<\/a> ya wallafa ya karade shafukan sada zumunta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Labarin na cewa fusatattun matasa a jihar Ribas sun \u0199one gidan Ministan Abuja Wike yayin da Wike ya kama hanyar zuwa mahaifar sa jihar Ribas.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXeQ3YsSmSqfok4C7XKAN35tVFI4D_FAh81psaJteZwG03GILaa2_5wi7niL2btPvMJn1Uh2UoGmebdyamD1BsPV9e9sC_ftPxwNC2aeoZ2S_cSp3Y24cQkCmhQQaIvT00A1swKsZg?key=2DjlGv9_29NlxcCvBFAgiX68\" alt=\"\" title=\"\"><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Hoton da aka zakulo a Facebook<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan labarin da aka sake wallafawa ya dauki hankalin masu amfani da shafin Facebook, zuwa ranar 20 ga watan Maris na 2025 sama da mutane 640 ne suka yi sharhi (comments) a kan labarin yayin da mutane 160 suka yada shi (share).<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Dubawa ta yi bincike domin tabbatar da sahihancin labarin, ganin cewa labarin na iya haddasa hargitsi da tashin hankali.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun yi binciken hotunan da ake yadawa cewa na gidan ministan Abuja ne dake jihar Rivers, inda muka gano cewa an hada su ne ta hanyar amfani da kirkirarriyar basira.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXfHzwpzWj3UY_4RyFs9hF9P3ZSkY4j7UsfymjZ5IyZNSEcWtnHe6FuBQHqMz19yCjC90lQG38_EwgRCxYsvn0Rb6u38TPhRXLJeVfogPrMkmqRXvF_OxDc45hF22Ue_sRbWDpaZBQ?key=2DjlGv9_29NlxcCvBFAgiX68\" alt=\"\" title=\"\"><\/figure>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXc7TzT-87H3xMUImJcWCdfwcgUo_V0vKWj7eIklny9HeRrWzDogngqUNd0YdAIpG8jAQuk7frU3kCUK2wctTlkg4e71t3nDAeoRntX-15rZkEUYTuvgt6TWw3nwjLCMdDgd64f_hg?key=2DjlGv9_29NlxcCvBFAgiX68\" alt=\"\" title=\"\"><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong><em>Sakamakon binciken da muka yi da manhajar <\/em><\/strong><a href=\"https:\/\/sightengine.com\/detect-ai-generated-images\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><em><strong>sight engine<\/strong><\/em><\/a><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Binciken tsanaki da muka yi mun gano cewa mutanen da ke cikin wadannan hotunan ba su yi kama da mutanen gaskiya ba, domin irin wannan wutar da aka nuna cewa ta kama babban gida zai yi wuya mutane su kusance a yadda aka nuna a hotunan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hakama Dubawa ta ga wata sanarwa da rundunar \u2018yan sandan jihar Ribas ta fitar, inda ta yi <a href=\"https:\/\/www.vanguardngr.com\/2025\/03\/wikes-house-not-attacked-or-burnt-police\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">watsi<\/a> da rahotannin da ke cewa wasu \u2018yan daba ne sun kai hari a gidan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike tare da kone shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Jami\u2019ar hulda da jama\u2019a ta \u2018yan sandan, Sufeto Grace Iringe-Koko, ta bayyana labarin a matsayin karya da yaudara da kuma yun\u0199urin tada tarzoma da kuma sanya tsoro ga al\u2019ummar jihar..<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Karya ce! Binciken Dubawa ya gano cewa hotunan da ake yadawa fasahar AI wato kirkirarriyar basira ce aka hada su kuma rundunar \u2018yan sandan Ribas ta karyata labarin cinna wa gidan Wike wuta.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani mai amfani da Facebook ya yada labarin da ke cewa matasa sun kone gidan Nyesom Wike dake jihar Rivers. Hukunci: Karya ce! Binciken Dubawa ya gano cewa hotunan da ake yadawa fasahar AI wato kirkirarriyar basira ce Cikakken Bayani Rikicin siyasar jihar Rivers na kara zafafa, sakamakon \u0199o\u0199arin fa\u0257a\u0257a ikon da Gwamna Siminalayi Fubara ya yi a jihar, ta hanyar shiga takun saka da tsohon ubangidansa kuma ministan Abuja Nyesom Wike. Rikcin nasu ya kai ga tarwatsa kan majalisar dokokin jihar tsakanin magoya bayansu. inda har aka samu kakakin majalisa biyu kafin daga baya shugaban kasa ya ayyana dokar ta baci a jihar da kuma nada gwamnan rikon kwarya. Ana cikin haka ne wani labari da wani mai amfani da Facebook ya wallafa ya karade shafukan sada zumunta. Labarin na cewa fusatattun matasa a jihar Ribas sun \u0199one gidan Ministan Abuja Wike yayin da Wike ya kama hanyar zuwa mahaifar sa jihar Ribas. Hoton da aka zakulo a Facebook Wannan labarin da aka sake wallafawa ya dauki hankalin masu amfani da shafin Facebook, zuwa ranar 20 ga watan Maris na 2025 sama da mutane 640 ne suka yi sharhi (comments) a kan labarin yayin da mutane 160 suka yada shi (share). Dubawa ta yi bincike domin tabbatar da sahihancin labarin, ganin cewa labarin na iya haddasa hargitsi da tashin hankali. Tantancewa Mun yi binciken hotunan da ake yadawa cewa na gidan ministan Abuja ne dake jihar Rivers, inda muka gano cewa an hada su ne ta hanyar amfani da kirkirarriyar basira. Sakamakon binciken da muka yi da manhajar sight engine Binciken tsanaki da muka yi mun gano cewa mutanen da ke cikin wadannan hotunan ba su yi kama da mutanen gaskiya ba, domin irin wannan wutar da aka nuna cewa ta kama babban gida zai yi wuya mutane su kusance a yadda aka nuna a hotunan. Hakama Dubawa ta ga wata sanarwa da rundunar \u2018yan sandan jihar Ribas ta fitar, inda ta yi watsi da rahotannin da ke cewa wasu \u2018yan daba ne sun kai hari a gidan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike tare da kone shi. Jami\u2019ar hulda da jama\u2019a ta \u2018yan sandan, Sufeto Grace Iringe-Koko, ta bayyana labarin a matsayin karya da yaudara da kuma yun\u0199urin tada tarzoma da kuma sanya tsoro ga al\u2019ummar jihar.. A Karshe Karya ce! Binciken Dubawa ya gano cewa hotunan da ake yadawa fasahar AI wato kirkirarriyar basira ce aka hada su kuma rundunar \u2018yan sandan Ribas ta karyata labarin cinna wa gidan Wike wuta.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":22012,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4139],"class_list":["post-22011","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5J1","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4139,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"ukashatu-ibrahim-wakili","display_name":"Ukashatu Ibrahim Wakili","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Wike.jpg?fit=512%2C276&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22011","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=22011"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22011\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":22013,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22011\/revisions\/22013"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/22012"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=22011"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=22011"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=22011"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=22011"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=22011"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}