{"id":22080,"date":"2025-03-26T06:59:58","date_gmt":"2025-03-26T05:59:58","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=22080"},"modified":"2025-03-26T07:00:01","modified_gmt":"2025-03-26T06:00:01","slug":"labari-na-musamman-jamiar-texas-ta-nisanta-kanta-daga-wanda-ke-kiran-kansa-karamin-likita-inibehe-okon-shi-kuma-ya-mayar-da-martani","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/labari-na-musamman-jamiar-texas-ta-nisanta-kanta-daga-wanda-ke-kiran-kansa-karamin-likita-inibehe-okon-shi-kuma-ya-mayar-da-martani\/","title":{"rendered":"Labari na musamman: Jami\u2019ar Texas ta nisanta kanta daga wanda ke kiran kansa\u00a0 \u2018karamin likita\u2019 Inibehe Okon; Shi kuma ya mayar da martani"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Inibehe Okon, wanda ke ikirarin cewa shi kwararren likitan kwakwalwa ne ya shiga matsala inda ake zarginsa da zamba a harkokin iilimi, tare da tabbatar da cewa shi ba dalibin jami\u2019ar Texas da ke Austin ba ne kamar yadda ya ke zargi, DUBAWA na da tabbacin hakan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ranar Talata 25 ga watan maris na shekarar 2025, <a href=\"https:\/\/www.utexas.edu\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Jami&#8217;ar Texas da ke Austin<\/strong><\/a> ta nisanta kanta daga Okon wanda ke zargin ya na da alaka da ita da wasu cibiyoyin ilimi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kwanan nan ne Okon ya yi suna bayan da hotunan da ke dauke da shi suka bayyana wajen kwatanta tsarin yadda ake daukar dalibai likitoci a Amurka a sunan wau shi ma likita ne a jami\u2019ar Johns Hopkins.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXfT5kMpHaQLtqDul2ixmPTLncs4N_p7-WNEg1PyRUmneg0hl88-l4Mv6r0IgjEfAxzVPghcJBS24G0QKpUZg3Rm3ncAUuIW9Wwrqv7QdvAHegXtg6ITNt5_0fhHAMjcbArPMxQD6w?key=7O9vvmm7h9JDpNLPzwSR_DPS\" alt=\"EXCLUSIVE: University of Texas dissociates self from viral \u2018resident doctor\u2019 Inibehe Okon; he reacts\" title=\"EXCLUSIVE: University of Texas dissociates self from viral \u2018resident doctor\u2019 Inibehe Okon; he reacts 2\"\/><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Hoton Okon ya na dauke kasidar cewa shi ma dalibi ne. Asalin hoton: Chriseny on X.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan hoton ya ja hankalin jama\u2019a da yawa kuma suka rika sha\u2019awarsa suna bayyana hakan a shafukan soshiyal mediya, wadansu masu amfani da shafin X sun sun wallafa hotunan irin bayanan da jama\u2019a suka rika yi, inda har ma wasu ke tabbatar da cewa shi dalibi ne tun 2029.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Okon,&nbsp; wanda <a href=\"https:\/\/www.researchgate.net\/profile\/Inibehe-Okon\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>shafinsa <\/strong><\/a>&nbsp;a babban shafin masu bincike na ResearchGate ya bayyana sa a matsayin kwararren likitan kwakwalwa wanda ke da dangantaka da Jami\u2019ar Texas na fuskantar zargin satar bayanan wani. Shafinsa na da\u2019awar cewa ya wallafa kasidu 65. Sai dai <a href=\"https:\/\/x.com\/Ahnie_Etesin\/status\/1903561125582799001\"><strong>bayanan <\/strong><\/a>da ake samu daga masu amfani da shafukan sada zaumunta, a ciki har da tsoffin daliban likita daga jami\u2019ar Uyom inda ya ke da\u2019awar cewa a can ma ya yi karatu, sun sanya alamar tambaya a kan sahihancin takardun kammala karatun da ya ke takamar ya samu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta tuntubi jami\u2019ar Texas dan tantance sahihancin takardun na sa. Inda ta ce babu wani mai suna kamar nasa a jami\u2019ar da ma sauran cibiyoyin da ke da alaka da ita.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cJami\u2019ar Texas ba ta da wani dalibi tsoho ko sabo wanda ke da wannan sunan da kuke neman karin bayani a kai,\u201d Mike ROsen, mataimakin shugaban sahin hulda da kafofin yada labaran jami\u2019ar ya bayyana wa DUBAWA.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DA DUBAWA ta tuntubi Okon a shafin WhatsApp, ya kaucewa tambayar ko ya taba halartar jami\u2019ar ko bai halarta ba. A maimakon hakan sai dai ya kada baki ya ce ya riga ya tanadi daftarin da zai yi amfani da shi wajen sanar da na sa barayin labarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cA sane na ke da ko na yi ko ban yi ba. Zan yafe musu. Na shirya sanarwar da zan gabatar. Zan fito in bayyana cikakkiyar gaskiyar ba zan boye komai ba,\u201d ya rubuta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ko daya bai amsa sauran tambayoyin da muka yi masa ba sadda muka bukaci karin bayani. Da muka yi kokarin kiransa a waya sai muka ga layin a kulle.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun kuma tuntubi jami\u2019ar Johns Hopkins da Jami\u2019ar Uyo dan tantance sauran zarge-zargen mu kuma sami karin bayani dangane da sahihanci ko nagartar takardun kammala makarantar na sa. Sai dai har zuwa sadda muka hada wannan rahoton ba mu sami amsa daga jami\u2019o\u2019in ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Tun bayan da aka fara zarginsa da aikata zambar, Okon ya rufe shafukansa na sada zumunta ya rage yawan mutanen da za su iya ganin shafin bare ma su yi ma\u2019amala da shi.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Inibehe Okon, wanda ke ikirarin cewa shi kwararren likitan kwakwalwa ne ya shiga matsala inda ake zarginsa da zamba a harkokin iilimi, tare da tabbatar da cewa shi ba dalibin jami\u2019ar Texas da ke Austin ba ne kamar yadda ya ke zargi, DUBAWA na da tabbacin hakan. Ranar Talata 25 ga watan maris na shekarar 2025, Jami&#8217;ar Texas da ke Austin ta nisanta kanta daga Okon wanda ke zargin ya na da alaka da ita da wasu cibiyoyin ilimi. Kwanan nan ne Okon ya yi suna bayan da hotunan da ke dauke da shi suka bayyana wajen kwatanta tsarin yadda ake daukar dalibai likitoci a Amurka a sunan wau shi ma likita ne a jami\u2019ar Johns Hopkins. Hoton Okon ya na dauke kasidar cewa shi ma dalibi ne. Asalin hoton: Chriseny on X. Wannan hoton ya ja hankalin jama\u2019a da yawa kuma suka rika sha\u2019awarsa suna bayyana hakan a shafukan soshiyal mediya, wadansu masu amfani da shafin X sun sun wallafa hotunan irin bayanan da jama\u2019a suka rika yi, inda har ma wasu ke tabbatar da cewa shi dalibi ne tun 2029. Okon,&nbsp; wanda shafinsa &nbsp;a babban shafin masu bincike na ResearchGate ya bayyana sa a matsayin kwararren likitan kwakwalwa wanda ke da dangantaka da Jami\u2019ar Texas na fuskantar zargin satar bayanan wani. Shafinsa na da\u2019awar cewa ya wallafa kasidu 65. Sai dai bayanan da ake samu daga masu amfani da shafukan sada zaumunta, a ciki har da tsoffin daliban likita daga jami\u2019ar Uyom inda ya ke da\u2019awar cewa a can ma ya yi karatu, sun sanya alamar tambaya a kan sahihancin takardun kammala karatun da ya ke takamar ya samu. DUBAWA ta tuntubi jami\u2019ar Texas dan tantance sahihancin takardun na sa. Inda ta ce babu wani mai suna kamar nasa a jami\u2019ar da ma sauran cibiyoyin da ke da alaka da ita. \u201cJami\u2019ar Texas ba ta da wani dalibi tsoho ko sabo wanda ke da wannan sunan da kuke neman karin bayani a kai,\u201d Mike ROsen, mataimakin shugaban sahin hulda da kafofin yada labaran jami\u2019ar ya bayyana wa DUBAWA. DA DUBAWA ta tuntubi Okon a shafin WhatsApp, ya kaucewa tambayar ko ya taba halartar jami\u2019ar ko bai halarta ba. A maimakon hakan sai dai ya kada baki ya ce ya riga ya tanadi daftarin da zai yi amfani da shi wajen sanar da na sa barayin labarin. \u201cA sane na ke da ko na yi ko ban yi ba. Zan yafe musu. Na shirya sanarwar da zan gabatar. Zan fito in bayyana cikakkiyar gaskiyar ba zan boye komai ba,\u201d ya rubuta. Ko daya bai amsa sauran tambayoyin da muka yi masa ba sadda muka bukaci karin bayani. Da muka yi kokarin kiransa a waya sai muka ga layin a kulle. Mun kuma tuntubi jami\u2019ar Johns Hopkins da Jami\u2019ar Uyo dan tantance sauran zarge-zargen mu kuma sami karin bayani dangane da sahihanci ko nagartar takardun kammala makarantar na sa. Sai dai har zuwa sadda muka hada wannan rahoton ba mu sami amsa daga jami\u2019o\u2019in ba. Tun bayan da aka fara zarginsa da aikata zambar, Okon ya rufe shafukansa na sada zumunta ya rage yawan mutanen da za su iya ganin shafin bare ma su yi ma\u2019amala da shi.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":22067,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3793],"class_list":["post-22080","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5K8","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3793,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"lademi-aborisade","display_name":"Lademi Aborisade","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Okon.jpg?fit=613%2C680&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22080","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=22080"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22080\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":22081,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22080\/revisions\/22081"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/22067"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=22080"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=22080"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=22080"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=22080"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=22080"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}