{"id":22087,"date":"2025-03-26T08:58:56","date_gmt":"2025-03-26T07:58:56","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=22087"},"modified":"2025-03-26T08:58:57","modified_gmt":"2025-03-26T07:58:57","slug":"shin-da-gaske-ne-mutun-na-iya-komawa-finland-da-zama-tare-da-900-kacal-kamar-yadda-wani-mai-amfani-da-x-ke-daawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/shin-da-gaske-ne-mutun-na-iya-komawa-finland-da-zama-tare-da-900-kacal-kamar-yadda-wani-mai-amfani-da-x-ke-daawa\/","title":{"rendered":"Shin da gaske ne mutun na iya komawa Finland da zama tare da $900 kacal, Kamar yadda wani mai amfani da X ke da\u2019awa?"},"content":{"rendered":"\n<h1 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken bayani<\/strong><\/h1>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mutun mai matsakaicin karfi a Najeriya zai yi tunanin ko bayan shekaru 24 na mulkin farar hula, kasar za ta kasance cikin wani yanayi na wadata ba tare da korafe-korafe irin na rashin wutar lantarki duk da tsadarta ba, da ma rashin hanyoyin mota masu kyau, da hauhawar farashin kayayyaki da sauransu, sai dai lamura cigaba da tabarbarewa kawai su ke yi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Abun takaicin ma shi ne gazawar gwamnati wajen suaya abubuwa ya sanya \u2018yan Najeriya karkata hankulansu zuwa kasashen waje inda za su fi samun ingancin rayuwa. A wani binciken da aka yi cikin shekarar 2024, <a href=\"https:\/\/www.afrobarometer.org\/articles\/majority-of-nigerians-have-considered-emigration-in-search-of-opportunity-new-afrobarometer-survey-finds\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">kusan kashi 56 cikin 100 na wadanda suka amsa tambayoyin binciken sun nuna sha&#8217;awar barin Najeriya<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kamr dai wannan binciken, wani mai amfani da shafin X, Jesse of Ozone (<a href=\"https:\/\/x.com\/Jessseglee\/status\/1894005312828428768\">@DrJesseglee<\/a>), ya yi da\u2019awar cewa \u2018yan Najeriya na iya komawa kasar Finland su yi karatu yayin da suke aiki da dalar Amurka 900 kacal. Ya rubuta cewa:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cA matsayin \u2018yan Najeriya kada ku bari garabasar Finland ta wuce ku. Su na bukatar \u2018yan Najeriya. Ku yi karatu yayin da kuke aiki sa\u2019annan ku kai iyalinku can. Dalar Amurka 900 kadai. Bukatu: Fasfo, takardun WAEC ko NECO da kuma takardun shaidar makarantun da kuka yi.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta gano wannan da\u2019awar ne bayan da wani mai amfani da shafin X , FindingSolace (<a href=\"https:\/\/x.com\/lifeinsolace\/status\/1894144272150229327\">@lifeinsolace<\/a>), ya yi kokarin karyata wannan da\u2019awar cewa kudin makaranta kadai a kasashen da ke amfani da bisar Schengen na tsakanin euro \u20ac8,000 da \u20ac11,000.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan batun ya ja hankalin masu amfani da shafin fiye da miliyan biyu, tsokaci ya kai 1,100,. An sake wallafa labarin sau 2,700, alamar like 16,000 wasu 8,400 sun adana shi dan sake dubawa nan gaba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wasu \u2018yan shafin X din da suka yi ma\u2019amala da shi duk sun bayyana ra\u2019ayoyinsu. Wadansu sun bukaci karin bayani yayin da wasu kuma suka sanya alamar tambaya kan sahihancin bayanin<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cZan iya komawa can da miliyan 10?\u201d (<a href=\"https:\/\/x.com\/WarriWeirdo\/status\/1894050507490005431\">@WarriWeido<\/a> )ya tambaya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cDaina wannan karyar dan samun mabiya. Ba wani aiki a Finland,\u201d a cewar (<a href=\"https:\/\/x.com\/lifeinsolace\/status\/1894090274000732381\">@lifeinsolace<\/a>).<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cMazambata irin ku ke cin zarafin wadanda ba su ji ba su gani ba, kana musu tallar karya dan samun kudi,\u201dScammers like you prey on desperate people, selling them false dreams for a quick buck,\u201d (<a href=\"https:\/\/x.com\/SecretDiary\/status\/1894278092342137232\">@SecretDiary<\/a>) ya soke shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wadannan ra\u2019ayoyi mabanbantan ne suka sa DUBAWA tantance wannan bayanin.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi a Google inda ta gano wani shafi mai sun <a href=\"https:\/\/www.mastersportal.com\/articles\/2203\/student-living-costs-in-finland-norway-and-germany.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Study Portals Masters<\/a>, shafin ya kimanta yawan kudin da daliban ketare ke kashewa kowace shekara. Shafin ya bayyana cewqa dalibai na kasa da kasa na iya kashe tsakanin euro&nbsp; \u20ac4,000 zuwa \u20ac18,000 kowace shekara.&nbsp; Sai dai duk da haka ya bayyana cewa digirin digir-gir kyauta ne wa duk daliban ketare.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bugu da kari kudin kashewa dan rayuwa matsakaici a Finland din kan kasasnce tsakanin \u20ac700 da \u20ac11,100. Mafi karancin kudin da ya kamata a ce mutun na da shi kowace wata&nbsp; yayin da ya ke karatu shi ne euro&nbsp; \u20ac560 wannan ya ma danganci birnin da dalibin ke zama.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kuma bayyana yawan kudin da ya kamata a kashe kan ababen more rayuwa da ma yawan kudin da ake bukatar baki su kashe a kasar. Wadannan sun hada da Kudin mota euro 55 (\u20ac55 per month)kowace wata. Kudin gida ko daki euro 300 zuwa 600 (\u20ac300-\u20ac600 per month) kowace wata. Kudin waya\/intanet\/lantarki\/daukar shara duk a hade euro 130&nbsp; (\u20ac130 per month), da sauran abubuwan da ke da dangantaka da kiwon lafiya irin su insora da magunguna euro 36 (\u20ac36 per month) a wata.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wata kafar kuma mai suna&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.studyinfinland.fi\/funding-your-studies\/fees-and-cost-living\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Study in Finland<\/a>, ko kuma yi karatu a Finland ta yi bayanin cewa kudin makarantan ya banbanta daga jami\u2019a zuwa jami\u2019a da kuma abun da ake karantawa. Ana iya biyan daga euro \u20ac8,000 zuwa \u20ac20,000 per year. Shi ma wannan shafin ya ce ba\u2019a bukatar kudin makaranta daga wurin wadanda ke digirin digir-gir.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shafin Study in Finland ya kuma bayyana cewa hukumar kula da shige da ficcen Finland wadda aka fi sani da\u201cMigri,\u201d ta kayyade cewa mafi karancin kudin da ya kamata a ce kowani dalibi na da shi a kowace wata shi ne&nbsp; euro \u20ac800 per month, sai dai ya bayar da karfin gwiwar cewa a yi kokari a kai shi euro \u20ac900 zuwa&nbsp; \u20ac1,000 per. Wannan kudin zai je ga kayayyakin yau da kullun kamar su haya, abinci da zirga-zirga.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kuma kara da cewa dalibai kan biya wani kudi na kungiyar dalibai wanda kan kasance tsakanin euro \u20ac50 zuwa \u20ac70 kowace shekara wanda kuma ya kan taimaka mu su wajen samun rangwame a wuraren cin abinci da kuma motar haya.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shafin na study<a href=\"https:\/\/www.studyinfinland.fi\/life-finland\/working-in-finland#:~:text=Part%2Dtime%20work%20during%20your,Finland%20section%20at%20Migri.fi\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"> in Finland<\/a> ya kuma ambaci ce bacin cewa daliban ketare na iya aiki yayin da suke karatu, ba safai ne ake samun ayyukan yi ba musamman a wuraren da tilas mutun ya iya amfani da harsunan Swedanci da na \u2018yan Finland. Wannan ya sabawa abin da mai da\u2019awar ya bayyana na cewa kai tsaye duk mutumin da ke so ya yi aiki zai sami aiki a Finland.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/migri.fi\/en\/income-requirement-for-students\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Hukumar kula da shige da ficce a Finland<\/a> ta ce idan har karatun da mutun zai yi zai dauki shekara daya ko fiye, dole kana da euro \u20ac9600 a cikin banki yayin da kake sa takardun neman karatun a matsayin ka na bako. Idan kuma bai kai shekara daya ba, dole kana da hanyar samun akalla euro \u20ac800 kowace wata.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan da\u2019awar ba gaskiya ba ne. Kudin ciyar da kai na wanda ke zaman bako a kasar Finland ya wuce $900. Ma\u2019aikatu masu mahimmanci kamar na shige da ficce wadda aka fi sani da \u201cMigri,\u201d ta ce tilas mutun ya kasance da akalla \u20ac800 kowace wata idan har zai yi karatu a kasar. Wata cibiyar, Study in Finland ita ma ta ce kudin makaranta a kasar na tsakanin \u20ac8,000 zuwa&nbsp; \u20ac20,000 kowace shekara.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Cikakken bayani Mutun mai matsakaicin karfi a Najeriya zai yi tunanin ko bayan shekaru 24 na mulkin farar hula, kasar za ta kasance cikin wani yanayi na wadata ba tare da korafe-korafe irin na rashin wutar lantarki duk da tsadarta ba, da ma rashin hanyoyin mota masu kyau, da hauhawar farashin kayayyaki da sauransu, sai dai lamura cigaba da tabarbarewa kawai su ke yi. Abun takaicin ma shi ne gazawar gwamnati wajen suaya abubuwa ya sanya \u2018yan Najeriya karkata hankulansu zuwa kasashen waje inda za su fi samun ingancin rayuwa. A wani binciken da aka yi cikin shekarar 2024, kusan kashi 56 cikin 100 na wadanda suka amsa tambayoyin binciken sun nuna sha&#8217;awar barin Najeriya. Kamr dai wannan binciken, wani mai amfani da shafin X, Jesse of Ozone (@DrJesseglee), ya yi da\u2019awar cewa \u2018yan Najeriya na iya komawa kasar Finland su yi karatu yayin da suke aiki da dalar Amurka 900 kacal. Ya rubuta cewa: \u201cA matsayin \u2018yan Najeriya kada ku bari garabasar Finland ta wuce ku. Su na bukatar \u2018yan Najeriya. Ku yi karatu yayin da kuke aiki sa\u2019annan ku kai iyalinku can. Dalar Amurka 900 kadai. Bukatu: Fasfo, takardun WAEC ko NECO da kuma takardun shaidar makarantun da kuka yi.\u201d DUBAWA ta gano wannan da\u2019awar ne bayan da wani mai amfani da shafin X , FindingSolace (@lifeinsolace), ya yi kokarin karyata wannan da\u2019awar cewa kudin makaranta kadai a kasashen da ke amfani da bisar Schengen na tsakanin euro \u20ac8,000 da \u20ac11,000. Wannan batun ya ja hankalin masu amfani da shafin fiye da miliyan biyu, tsokaci ya kai 1,100,. An sake wallafa labarin sau 2,700, alamar like 16,000 wasu 8,400 sun adana shi dan sake dubawa nan gaba. Wasu \u2018yan shafin X din da suka yi ma\u2019amala da shi duk sun bayyana ra\u2019ayoyinsu. Wadansu sun bukaci karin bayani yayin da wasu kuma suka sanya alamar tambaya kan sahihancin bayanin \u201cZan iya komawa can da miliyan 10?\u201d (@WarriWeido )ya tambaya. \u201cDaina wannan karyar dan samun mabiya. Ba wani aiki a Finland,\u201d a cewar (@lifeinsolace). \u201cMazambata irin ku ke cin zarafin wadanda ba su ji ba su gani ba, kana musu tallar karya dan samun kudi,\u201dScammers like you prey on desperate people, selling them false dreams for a quick buck,\u201d (@SecretDiary) ya soke shi. Wadannan ra\u2019ayoyi mabanbantan ne suka sa DUBAWA tantance wannan bayanin. Tantancewa DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi a Google inda ta gano wani shafi mai sun Study Portals Masters, shafin ya kimanta yawan kudin da daliban ketare ke kashewa kowace shekara. Shafin ya bayyana cewqa dalibai na kasa da kasa na iya kashe tsakanin euro&nbsp; \u20ac4,000 zuwa \u20ac18,000 kowace shekara.&nbsp; Sai dai duk da haka ya bayyana cewa digirin digir-gir kyauta ne wa duk daliban ketare. Bugu da kari kudin kashewa dan rayuwa matsakaici a Finland din kan kasasnce tsakanin \u20ac700 da \u20ac11,100. Mafi karancin kudin da ya kamata a ce mutun na da shi kowace wata&nbsp; yayin da ya ke karatu shi ne euro&nbsp; \u20ac560 wannan ya ma danganci birnin da dalibin ke zama.&nbsp; Ya kuma bayyana yawan kudin da ya kamata a kashe kan ababen more rayuwa da ma yawan kudin da ake bukatar baki su kashe a kasar. Wadannan sun hada da Kudin mota euro 55 (\u20ac55 per month)kowace wata. Kudin gida ko daki euro 300 zuwa 600 (\u20ac300-\u20ac600 per month) kowace wata. Kudin waya\/intanet\/lantarki\/daukar shara duk a hade euro 130&nbsp; (\u20ac130 per month), da sauran abubuwan da ke da dangantaka da kiwon lafiya irin su insora da magunguna euro 36 (\u20ac36 per month) a wata. Wata kafar kuma mai suna&nbsp; Study in Finland, ko kuma yi karatu a Finland ta yi bayanin cewa kudin makarantan ya banbanta daga jami\u2019a zuwa jami\u2019a da kuma abun da ake karantawa. Ana iya biyan daga euro \u20ac8,000 zuwa \u20ac20,000 per year. Shi ma wannan shafin ya ce ba\u2019a bukatar kudin makaranta daga wurin wadanda ke digirin digir-gir. Shafin Study in Finland ya kuma bayyana cewa hukumar kula da shige da ficcen Finland wadda aka fi sani da\u201cMigri,\u201d ta kayyade cewa mafi karancin kudin da ya kamata a ce kowani dalibi na da shi a kowace wata shi ne&nbsp; euro \u20ac800 per month, sai dai ya bayar da karfin gwiwar cewa a yi kokari a kai shi euro \u20ac900 zuwa&nbsp; \u20ac1,000 per. Wannan kudin zai je ga kayayyakin yau da kullun kamar su haya, abinci da zirga-zirga. Ya kuma kara da cewa dalibai kan biya wani kudi na kungiyar dalibai wanda kan kasance tsakanin euro \u20ac50 zuwa \u20ac70 kowace shekara wanda kuma ya kan taimaka mu su wajen samun rangwame a wuraren cin abinci da kuma motar haya.&nbsp; Shafin na study in Finland ya kuma ambaci ce bacin cewa daliban ketare na iya aiki yayin da suke karatu, ba safai ne ake samun ayyukan yi ba musamman a wuraren da tilas mutun ya iya amfani da harsunan Swedanci da na \u2018yan Finland. Wannan ya sabawa abin da mai da\u2019awar ya bayyana na cewa kai tsaye duk mutumin da ke so ya yi aiki zai sami aiki a Finland. Hukumar kula da shige da ficce a Finland ta ce idan har karatun da mutun zai yi zai dauki shekara daya ko fiye, dole kana da euro \u20ac9600 a cikin banki yayin da kake sa takardun neman karatun a matsayin ka na bako. Idan kuma bai kai shekara daya ba, dole kana da hanyar samun akalla euro \u20ac800 kowace wata.&nbsp; A karshe Wannan da\u2019awar ba gaskiya ba ne. Kudin ciyar da kai na wanda ke zaman bako a kasar Finland ya wuce $900. Ma\u2019aikatu masu mahimmanci kamar na shige da ficce wadda aka fi sani da \u201cMigri,\u201d ta ce tilas mutun ya kasance da akalla \u20ac800 kowace wata idan har zai yi karatu a kasar. Wata cibiyar, Study in Finland ita ma ta ce kudin makaranta a kasar na tsakanin \u20ac8,000 zuwa&nbsp; \u20ac20,000 kowace shekara.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":21835,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[3699],"class_list":["post-22087","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5Kf","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":3699,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"cole-praise","display_name":"Cole Praise","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/7934b84f51e2c1f4c1e77cce93c223ac97cc2da29198aa9141fd944b0407bb2d?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Finland.png?fit=1187%2C512&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22087","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=22087"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22087\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":22088,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22087\/revisions\/22088"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/21835"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=22087"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=22087"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=22087"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=22087"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=22087"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}