{"id":22366,"date":"2025-04-21T13:09:16","date_gmt":"2025-04-21T12:09:16","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=22366"},"modified":"2025-04-23T03:34:18","modified_gmt":"2025-04-23T02:34:18","slug":"shin-da-gaske-ne-ali-ndume-ya-shafe-shekaru-21-ya-na-wakiltar-kudancin-borno-a-majalisar-dattawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/shin-da-gaske-ne-ali-ndume-ya-shafe-shekaru-21-ya-na-wakiltar-kudancin-borno-a-majalisar-dattawa\/","title":{"rendered":"Shin da gaske ne Ali Ndume ya shafe shekaru 21 ya na wakiltar kudancin Borno a majalisar dattawa?"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Mai amfani da shafin X, @Onsogbu, <a href=\"https:\/\/x.com\/onsogbu\/status\/1910950954276434052?s=48\">na da&#8217;awar cewa<\/a> sanataAli Ndume ya shafe shekaru 21 a majalisar dattawa ba tare da ya tabuka komai ba<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hukunci: Yaudara ce. Binciken mahimman kalmomin da DUBAWA ta gudanar ya tabbar cewa an zabi sanatan ne shekaru 14 da suka wuce.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ali Ndume na kan gaba cikin masu sukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu. Kakkausar sukar da ya yi kan mukaman da shugaban ya bayar a&nbsp; <a href=\"https:\/\/youtu.be\/R9GQw2RRcmk?si=jfuMMiZ2ZJGe6w7s\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Arise TV<\/strong><\/a> ya janyo martanoni masu kaifi daga magoya bayan jam\u2019iyya mai mulki ta APC.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da shafin wanda ma har ya tantance shafinsa Pastor Okezie J. Atani (@Onsogbu)da mabiya h 47,700, ya yi da\u2019awar cewa Ali Ndume ya yi shekaru 21 a majalisar dattawa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cShin Sanata&nbsp; Ali Ndume ya shafe shekaru 21 a majalisar dattawa? Akwai wanda zai iya nuna mun abin da ya yi wa mutanensa?\u201d ya <a href=\"https:\/\/x.com\/onsogbu\/status\/1910950954276434052?s=48\"><strong>rubuta<\/strong><\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya zuwa ranat 14 ga watan Afrilun 2025, wannan da\u2019awar ya dauki hankalin mutane sama da 38,000, akwai tsokaci 144, an sake rabawa sau 111, wasu 496 sun yi ma\u2019amala da batun ya yin da wasu biyu kuma suka adana shafin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shafin tsokacin ko kuma kwament na dauke da ra\u2019ayoyi mabanbanta. Yayin da wasu ke kira da a bayyana nasarorin gwamnatin Tinubu tun bayan da ya kama aiki, wasu kuma na da\u2019awar cewa shekaru 14 kadai Ndume ya yi a majalisar dattawan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani wanda shi ma ya tantance shafinsa da alamar nagarta,\u200b\u200b Adetunji Adewolu (@AsetunjiAdewolu), <a href=\"https:\/\/x.com\/adetunjiadewolu\/status\/1910974361823039641?s=46\"><strong>cewa ya yi<\/strong><\/a>, \u201cshekaru 21 a majalisar dattawa amma duk da haka Borno na fama da rashin tsaro. Ina nasarori na gaske masu dorewa wadanda mutane za su mora? Lokaci ne na yanke hukunci kan ayyukan tasiri ba tsawon wa\u2019adi ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201c Shekaru biyar a majalisar wakilai da shekaru 14 a majalisar dattawa. Hasali dai shekari 21 a majalisar dokoki ba majalisar dattawa ba.\u201d&nbsp; bisa bayanan Prince De Lagos (@TheKayodeBadmus) <a href=\"https:\/\/x.com\/thekayodebadmus\/status\/1911449166934384642?s=46\"><strong>a wannan shafin<\/strong><\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da shafin X din shi ma, Jbj001 (@JaybeeJay001), <a href=\"https:\/\/x.com\/jaybeejay001\/status\/1911225776315211996?s=46\"><strong>ya rubuta cewa<\/strong><\/a>, \u201cYawan shekarun da ya yi a majalisar ne nasarorin, duk da cewa dai ban tabbatar da shekaru ashirin da dayan nan dai ba.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Saboda wadannan ra\u2019ayoyi mabanbantan ne, DUBAWA ta dauki nauyin tantance wannan da\u2019awar.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa\u00a0<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Najeriya na amfani da tsarin da ke da majalisu biyu ne a majalisar <a href=\"https:\/\/nass.gov.ng\/about\/item\/1548#:~:text=The%20country%20operates%20a%20Bi,36%20States%20of%20the%20Federation.\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>dokoki<\/strong><\/a>, wanda ya hada da majalisar dattawa da ta wakilai.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi dan gano ko shekaru nawa sanata Ali Ndume ya shafe a a majalisa ya na wakiltar yankin kudancin Borno.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011, Ali Ndume ya kasance&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/news\/top-news\/334522-profile-ali-ndume-former-marketing-teacher-who-tried-to-be-senate-president.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>mamba ne a majalisar wakilai<\/strong><\/a>,&nbsp; a karkashin inuwar jam\u2019iyyar ANPP. Daga nan ne ya suaya sheka zuwa jam\u2019iyyar PDP a shekarar 2010 ya tsaya takarar zuwa majalisar dattawa a shekarar 2011.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA <a href=\"https:\/\/en.wikipedia.org\/wiki\/Mohammed_Ali_Ndume\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>ta binciki<\/strong><\/a> gajeren bayani dangane da rayuwarsa a shafin wikipedia inda ta gano cewa Ali Ndume ya fara aiki ne ranar 6 ga watan Yunin 2011, bayan da ya karbi mulki daga wurin Omar Hambagda wanda ke zaman sanatan da ke wakiltar yankin kudancin Borno.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Binciken DUBAWA na nuna cewa sanatan ya shafe shekaru 14 ne a majalisar dattawan kasar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ga wasu daga cikin wadanda suka kasance a mukamin kafin Ali Ndume: <a href=\"https:\/\/en.wikipedia.org\/wiki\/Abubakar_Mahdi\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Abubakar Mahdi<\/strong><\/a>\u2014&nbsp; uku ga watan Yunin, 1999,zuwa uku ga watan Yunin&nbsp; 2003, a karkashin inuwar PDP, da <a href=\"https:\/\/en.wikipedia.org\/wiki\/Omar_Hambagda\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Omar Abubakar Hamgagba<\/strong><\/a>\u2014Uku ga watan, 2003, zuwa shida ga watan Yunin, 2011, a karkashin jam\u2019iyyar ANPP.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan da\u2019awar yaudara ce don Ali Ndume bai yi shekaru 21 a majalisar dattawa ba. Shekaru 14 ya yi a majalisar dattawan tun bayan da ya karbi mulki daga wurin Hambagada a shekarar 2011.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Mai amfani da shafin X, @Onsogbu, na da&#8217;awar cewa sanataAli Ndume ya shafe shekaru 21 a majalisar dattawa ba tare da ya tabuka komai ba Hukunci: Yaudara ce. Binciken mahimman kalmomin da DUBAWA ta gudanar ya tabbar cewa an zabi sanatan ne shekaru 14 da suka wuce. Cikakken bayani Ali Ndume na kan gaba cikin masu sukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu. Kakkausar sukar da ya yi kan mukaman da shugaban ya bayar a&nbsp; Arise TV ya janyo martanoni masu kaifi daga magoya bayan jam\u2019iyya mai mulki ta APC. Wani mai amfani da shafin wanda ma har ya tantance shafinsa Pastor Okezie J. Atani (@Onsogbu)da mabiya h 47,700, ya yi da\u2019awar cewa Ali Ndume ya yi shekaru 21 a majalisar dattawa. \u201cShin Sanata&nbsp; Ali Ndume ya shafe shekaru 21 a majalisar dattawa? Akwai wanda zai iya nuna mun abin da ya yi wa mutanensa?\u201d ya rubuta. Ya zuwa ranat 14 ga watan Afrilun 2025, wannan da\u2019awar ya dauki hankalin mutane sama da 38,000, akwai tsokaci 144, an sake rabawa sau 111, wasu 496 sun yi ma\u2019amala da batun ya yin da wasu biyu kuma suka adana shafin. Shafin tsokacin ko kuma kwament na dauke da ra\u2019ayoyi mabanbanta. Yayin da wasu ke kira da a bayyana nasarorin gwamnatin Tinubu tun bayan da ya kama aiki, wasu kuma na da\u2019awar cewa shekaru 14 kadai Ndume ya yi a majalisar dattawan. Wani wanda shi ma ya tantance shafinsa da alamar nagarta,\u200b\u200b Adetunji Adewolu (@AsetunjiAdewolu), cewa ya yi, \u201cshekaru 21 a majalisar dattawa amma duk da haka Borno na fama da rashin tsaro. Ina nasarori na gaske masu dorewa wadanda mutane za su mora? Lokaci ne na yanke hukunci kan ayyukan tasiri ba tsawon wa\u2019adi ba. \u201c Shekaru biyar a majalisar wakilai da shekaru 14 a majalisar dattawa. Hasali dai shekari 21 a majalisar dokoki ba majalisar dattawa ba.\u201d&nbsp; bisa bayanan Prince De Lagos (@TheKayodeBadmus) a wannan shafin. Wani mai amfani da shafin X din shi ma, Jbj001 (@JaybeeJay001), ya rubuta cewa, \u201cYawan shekarun da ya yi a majalisar ne nasarorin, duk da cewa dai ban tabbatar da shekaru ashirin da dayan nan dai ba.\u201d Saboda wadannan ra\u2019ayoyi mabanbantan ne, DUBAWA ta dauki nauyin tantance wannan da\u2019awar. Tantancewa\u00a0 Najeriya na amfani da tsarin da ke da majalisu biyu ne a majalisar dokoki, wanda ya hada da majalisar dattawa da ta wakilai. DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi dan gano ko shekaru nawa sanata Ali Ndume ya shafe a a majalisa ya na wakiltar yankin kudancin Borno. Tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011, Ali Ndume ya kasance&nbsp; mamba ne a majalisar wakilai,&nbsp; a karkashin inuwar jam\u2019iyyar ANPP. Daga nan ne ya suaya sheka zuwa jam\u2019iyyar PDP a shekarar 2010 ya tsaya takarar zuwa majalisar dattawa a shekarar 2011. DUBAWA ta binciki gajeren bayani dangane da rayuwarsa a shafin wikipedia inda ta gano cewa Ali Ndume ya fara aiki ne ranar 6 ga watan Yunin 2011, bayan da ya karbi mulki daga wurin Omar Hambagda wanda ke zaman sanatan da ke wakiltar yankin kudancin Borno. Binciken DUBAWA na nuna cewa sanatan ya shafe shekaru 14 ne a majalisar dattawan kasar. Ga wasu daga cikin wadanda suka kasance a mukamin kafin Ali Ndume: Abubakar Mahdi\u2014&nbsp; uku ga watan Yunin, 1999,zuwa uku ga watan Yunin&nbsp; 2003, a karkashin inuwar PDP, da Omar Abubakar Hamgagba\u2014Uku ga watan, 2003, zuwa shida ga watan Yunin, 2011, a karkashin jam\u2019iyyar ANPP. A karshe Wannan da\u2019awar yaudara ce don Ali Ndume bai yi shekaru 21 a majalisar dattawa ba. Shekaru 14 ya yi a majalisar dattawan tun bayan da ya karbi mulki daga wurin Hambagada a shekarar 2011.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":22356,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,1571,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4450],"class_list":["post-22366","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-fact-check","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5OK","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4450,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"yunusa-umar","display_name":"Yunusa Umar","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/Ali-Ndume.jpg?fit=956%2C1024&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22366","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=22366"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22366\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":22400,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22366\/revisions\/22400"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/22356"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=22366"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=22366"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=22366"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=22366"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=22366"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}