{"id":22469,"date":"2025-04-27T12:22:35","date_gmt":"2025-04-27T11:22:35","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=22469"},"modified":"2025-04-27T12:22:37","modified_gmt":"2025-04-27T11:22:37","slug":"zancen-ganawar-sanata-wamakko-da-kwankwaso-da-yusuf-datti-ba-gaskiya-ne-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/zancen-ganawar-sanata-wamakko-da-kwankwaso-da-yusuf-datti-ba-gaskiya-ne-ba\/","title":{"rendered":"Zancen ganawar Sanata Wamakko da Kwankwaso da Yusuf Datti, ba gaskiya ne ba!"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa: <\/strong>Rabi\u2019u Kwankwaso na NNPP ya yi ganawar sirri da jigon APC Wamakko kan komawa jam\u2019iyyar.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"136\" height=\"59\" data-attachment-id=\"19998\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/video-of-purported-brawl-between-nigerian-ghanaian-women-in-france-misleading\/misleading-4-1-2\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/MISLEADING-4-1.png?fit=136%2C59&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"136,59\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"MISLEADING-4-1\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/MISLEADING-4-1.png?fit=136%2C59&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/MISLEADING-4-1.png?resize=136%2C59\" alt=\"\" class=\"wp-image-19998\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#7f7e0f\"><strong>Hukunci: <\/strong>Yaudara ce. Bincike Dubawa ya gano cewa Wamakko bai gana da Kwankwaso ba, tsohon hoto ne da aka yi 2020 ake yadawa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ana ci gaba da rade-radin sauya shekar madugun siyasar Kwankwasiya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin jam\u2019iyyar NNPP a zaben 2023, Rabi\u2019u Musa Kwankwaso, zuwa jam\u2019iyyar APC mai mulkin Najeriya, lamarin da jam\u2019iyyar APC ta ce <a href=\"https:\/\/thenationonlineng.net\/kano-apc-asks-kwankwaso-to-apologise-to-president-shettima-before-joining-party\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">abin farin ciki<\/a> ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai bangaren NNPP sun bayyana cewa jigon nasu, kuma tsohon gwamnan jihar Kano bai da nufin zuwa jam\u2019iyyar ta APC, kamar yadda shugaban jam\u2019iyyar na jiha <a href=\"https:\/\/www.vanguardngr.com\/2025\/04\/no-plan-by-kwankwaso-others-to-defect-to-apc-kano-nnpp-chair\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Hashimu Dungurawa<\/a> ya bayyana.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da haka wasu rahotanni na cewa ana ci gaba da <a href=\"https:\/\/tribuneonlineng.com\/disquiet-in-apc-over-tinubus-deal-with-kwankwaso\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">tattaunawa<\/a> ta karkashin kasa domin komawar Kwankwaso zuwa jam\u2019iyyar ta APC.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ana wannan sai wani labarin ya karade shafukan sada zumunta cewa, Sanata Aliyu Wamakko kuma makusancin Shugaba Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da Kwankwano da kuma wanda ya yi wa Peter Obi takarar mataimakin shugaban kasa karkashin jam\u2019iyyar LP Yusuf Datti Baba-Ahmed.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani shafin Facebook na <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/story.php?story_fbid=556497877496650&amp;id=100094093277500&amp;rdid=PcJsOjobMyrS0r9B#\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">NNPP Kwankwasiyya<\/a> ya yi da\u2019awar cewa wannan ganawar an yi ta ne a gidan Sanata Wamakko dake Asokoro a Abuja.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Zuwa ranar 25 ga watan Afrilun 2025, sama da mutum 50 ne suka yi sharhi akan labarin, inda mutum 56 suka yada shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Daga cikin masu sharhin, wani Auwalu Sabiu Nafada ya ce \u201cneman kamun kafa yaje\u201d amma Mohammed Hamza cewa ya yi \u201cwannan fa tsohon hotone tun ana covid\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Rudanin da mutane suka shiga akan wannan labarin ne ya sa DUBAWA yi bincike domin tabbatar da sahihancinsa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta saka hoton a shafin neman hotuna na Google domin gano asalin wannan hoton da ake yada wa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun gano cewa hoton an fara wallafa shi ne a ranar Talata 15 ga watan Satumban 2020, a shafin Facebook na <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/DrRabiuKwankwaso\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Rabi\u2019u Musa Kwankwaso<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kwankwaso wanda ke tare da Yusuf Datti da Wamakko a cikin hoton, ya <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/DrRabiuKwankwaso\/posts\/pfbid0L2uDKjZVNtuhHxHxa1bDibtH3DBT5gkwXYP2KoMMfCGsGMnPJ2rK7fqgA8YpMSkXl\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">wallafa<\/a> cewa ya kai \u201cziyarar ta&#8217;aziyya zuwa ga iyalan Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko bisa rasuwar diyarsu, Sadiya Wamakko\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shima Sanata Wamakko ya <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/story.php?story_fbid=2643545219294332&amp;id=1883381391977389\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">wallafa<\/a> wani hoton a shafinsa na Facebook wannan ranar, inda yake sanar da cewa ya karbi bakuncin Kwankwaso wanda ya zo domin yi masa ta\u2019aziyya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hakam mun tuntubi mataimaki na musamman ga Sanata Wamakko akan yada labarai, <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/bashar.abubakar.mc\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Bashar Abubakar<\/a> ya shaida min cewa labarin ganawar sirri tsakanin jagororin ba gaskiya ba ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cLalle ba gaskiya ne ba. Mun gode\u201d in ji&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yaudara ce, Kwankwaso bai ganawar sirri da Wamakko ba a kwanan nan.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Rabi\u2019u Kwankwaso na NNPP ya yi ganawar sirri da jigon APC Wamakko kan komawa jam\u2019iyyar. Hukunci: Yaudara ce. Bincike Dubawa ya gano cewa Wamakko bai gana da Kwankwaso ba, tsohon hoto ne da aka yi 2020 ake yadawa. Cikakken Bayani Ana ci gaba da rade-radin sauya shekar madugun siyasar Kwankwasiya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin jam\u2019iyyar NNPP a zaben 2023, Rabi\u2019u Musa Kwankwaso, zuwa jam\u2019iyyar APC mai mulkin Najeriya, lamarin da jam\u2019iyyar APC ta ce abin farin ciki ne. Sai dai bangaren NNPP sun bayyana cewa jigon nasu, kuma tsohon gwamnan jihar Kano bai da nufin zuwa jam\u2019iyyar ta APC, kamar yadda shugaban jam\u2019iyyar na jiha Hashimu Dungurawa ya bayyana. Duk da haka wasu rahotanni na cewa ana ci gaba da tattaunawa ta karkashin kasa domin komawar Kwankwaso zuwa jam\u2019iyyar ta APC. Ana wannan sai wani labarin ya karade shafukan sada zumunta cewa, Sanata Aliyu Wamakko kuma makusancin Shugaba Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da Kwankwano da kuma wanda ya yi wa Peter Obi takarar mataimakin shugaban kasa karkashin jam\u2019iyyar LP Yusuf Datti Baba-Ahmed. Wani shafin Facebook na NNPP Kwankwasiyya ya yi da\u2019awar cewa wannan ganawar an yi ta ne a gidan Sanata Wamakko dake Asokoro a Abuja. Zuwa ranar 25 ga watan Afrilun 2025, sama da mutum 50 ne suka yi sharhi akan labarin, inda mutum 56 suka yada shi. Daga cikin masu sharhin, wani Auwalu Sabiu Nafada ya ce \u201cneman kamun kafa yaje\u201d amma Mohammed Hamza cewa ya yi \u201cwannan fa tsohon hotone tun ana covid\u201d. Rudanin da mutane suka shiga akan wannan labarin ne ya sa DUBAWA yi bincike domin tabbatar da sahihancinsa. Tantancewa DUBAWA ta saka hoton a shafin neman hotuna na Google domin gano asalin wannan hoton da ake yada wa. Mun gano cewa hoton an fara wallafa shi ne a ranar Talata 15 ga watan Satumban 2020, a shafin Facebook na Rabi\u2019u Musa Kwankwaso. Kwankwaso wanda ke tare da Yusuf Datti da Wamakko a cikin hoton, ya wallafa cewa ya kai \u201cziyarar ta&#8217;aziyya zuwa ga iyalan Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko bisa rasuwar diyarsu, Sadiya Wamakko\u201d. Shima Sanata Wamakko ya wallafa wani hoton a shafinsa na Facebook wannan ranar, inda yake sanar da cewa ya karbi bakuncin Kwankwaso wanda ya zo domin yi masa ta\u2019aziyya. Hakam mun tuntubi mataimaki na musamman ga Sanata Wamakko akan yada labarai, Bashar Abubakar ya shaida min cewa labarin ganawar sirri tsakanin jagororin ba gaskiya ba ne. \u201cLalle ba gaskiya ne ba. Mun gode\u201d in ji&nbsp; A Karshe Yaudara ce, Kwankwaso bai ganawar sirri da Wamakko ba a kwanan nan.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":22470,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4439],"class_list":["post-22469","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-5Qp","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4439,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"ukashatu-wakili","display_name":"Ukashatu Wakili","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/kwankwaso.png?fit=512%2C288&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22469","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=22469"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22469\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":22471,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/22469\/revisions\/22471"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/22470"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=22469"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=22469"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=22469"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=22469"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=22469"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}