{"id":23230,"date":"2025-06-19T03:56:43","date_gmt":"2025-06-19T02:56:43","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=23230"},"modified":"2025-06-19T04:02:54","modified_gmt":"2025-06-19T03:02:54","slug":"shin-da-gaske-ne-an-jefi-sarkin-kano-sanusi-ii-a-gidan-gwamnatin-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/shin-da-gaske-ne-an-jefi-sarkin-kano-sanusi-ii-a-gidan-gwamnatin-kano\/","title":{"rendered":"Shin da gaske ne an jefi sarkin Kano Sanusi II a gidan gwamnatin Kano?"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\"><strong>DA\u2019AWA:<\/strong>  Wasu sun jefi sarkin Kano Sanusi na biyu yayin da ya ke jawabi a gidan gwamnatin Kano<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"136\" height=\"59\" data-attachment-id=\"20177\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/post-edo-election-fact-checks-edo-2024-governorship-election\/misleading-4-1-2-2\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/MISLEADING-4-1-2.png?fit=136%2C59&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"136,59\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"MISLEADING-4-1-2\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/MISLEADING-4-1-2.png?fit=136%2C59&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/MISLEADING-4-1-2.png?resize=136%2C59\" alt=\"\" class=\"wp-image-20177\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#7f7e07\"><strong>HUKUNCI:<\/strong> Yaudara ce! Babu wata sheda da ta tabbatar da cewa an jefi sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu a fadar gwamnatin jihar Kano.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>CIKAKKEN SAKO<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;\u201cYau din nan muna cike da farinciki\u201d a cewar Junaidu Aminu Kilishi wani mai amfani da shafin <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/reel\/704996228788376\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Facebook<\/a>. Kilishi ya bayyana haka ne ya na da\u2019awar jewa an jefi sarkin Kano Sanusi na biyu yayin da ya ke jawabi a gidan gwamnatin Kano<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Haka nan ita ma@Gambizatv <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/mujallartauraruwa24\/videos\/684487604396807\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Facebook<\/a> a shafin na Facebook ta yi irin wannan wallafa, inda a bidiyonta ya nunar da cewa bayan jifan sarkin a gidan gwamnati an kuma jefe shi a unguwar Fagge cikin birnin na Kano. Wadannan kenan baya ga wasu shafukan.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXdkzc_vjn_Bbg29PxsYwl78RIGwLI26MokV_Jtzy4Us4chUlSKO4J4Sa0poy6wt-tvKm7thcV718Gz7WdFfrIDwwiTcN9wD5hI66gcrsUqK_a5oeIBc72gs9rgKRVNDIJrpLuG0?key=R-6kpLnZ6X9JZLGWzVxNMw\" alt=\"\" title=\"\"><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Hoton shafin Junaidu Aminu Kilishi&nbsp;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan wallafa da ta bayyana a yayin bukukuwan babbar sallah a jihar Kano na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takkadama kan batun wa ke zama halastaccen Sarkin Kano, Sarki Muhammmadu Sunusi na biyu wato sarki na 14 ko kuwa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero sarki na 15.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu dai wanda shine gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam\u2019iyyar NNPP ta amince da zama sarki, ya kai ziyara a gidan gwamnati a ranar biyu ga sallah da ake kira ranar Hawan Nasarawa kamar yadda aka saba gani a duk shekara,don zuwa kai gaisuwar sallah ga gwamna.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A bana dai sarkin ya kai ziyarar gaisuwar Babbar Sallah a ranar 8 ga watan Yuni,2025 inda ya samu tarbar mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo saboda Gwamna Yusuf na halartar aikin Hajji a kasar Saudiya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXeg2rMJIUuvqb3smOvnZsCuPAjIgaGOvlQZKmi-GDfQIL9Yuzrl3r5Pb-1MSn0pj70169zGR9EE1lbQGv26kHtt_E-v-Q6PfSozAceeHw3sZbNm3oQTJzbooOXM7Kv79O3upFxmOg?key=R-6kpLnZ6X9JZLGWzVxNMw\" width=\"577\" height=\"384\" alt=\"\" title=\"\"><em>Sarki Muhammadu Sunusi na biyu tare da mataimakin gwamna Aminu Abdussalam a ranar hawan Nasarawa a gidan gwamnati: Hoto daga gidan gwamnatin Kano<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A yayin da sarkin ke bayani a wajen taron hawan a gidan sarki sai wani bangare na na\u2019urar daukar hoto da ake kira (drone) ta fado ta shafi hular sarkin wanda da wannan ne mai da\u2019awar a shafin na <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/reel\/704996228788376\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">&nbsp;Facebook<\/a> ke cewa an jefi sarkin.&nbsp;&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha\u2019awarsu wato<strong> likes<\/strong> sama da 1300&nbsp; da masu sharhi <strong>comments<\/strong> 106 da wadanda suka sake wallafawa wato <strong>shares <\/strong>su 70. Duba da yadda wannan wallafa da ma makamantanta suka karade shafukan sada zumunta musamman shafukan da ke zama na masu yada farfaganda ta adawa da sarkin ya sanya<strong> DUBAWA <\/strong>ganin wajibcin nazartar wannan wallafa don tantancewa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>TANTANCEWA:&nbsp;<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Dubawa ta bibiyi kafafan yada labarai da dama don gano gaskiyar labarin cewa an jefi sarkin na Kano Muhammadu Sunusi na biyu a fadar gwamnati a ranar ta 8 ga watan na Yuni, 2025, sai dai duk kafafan yada labarai da ke zama sahihai babu wacce ta wallafa wannan labari inda ta nuna cewa an jefi sarkin a wannan rana a irin labaran da suka buga.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/von.gov.ng\/sallah-kano-governor-urges-residents-to-embrace-peace-good-governance\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Sallah: Kano Governor Urges Residents to Embrace Peace, Good Governance &#8211; Voice of Nigeria Broadcasting Service<\/a>&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/www.thecable.ng\/kano-demands-compensation-from-fg-over-durbar-cancellations\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Kano demands compensation from FG over durbar cancellation | TheCable<\/a><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ko a bidiyon <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/reel\/704996228788376\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Facebook<\/a>@JunaiduAminuKilishi babu inda hoton bidiyon ya nuna cewa ga inda aka jefo wani abin jifa har yazo ya samu sarkin.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXdKsSz9BqJI3bI5YRyH0NX63Ot4doDgfN-7Vz8twmUTxuWuHLPizGLeXkTI888za-PQAEURtxI4Bh81g3CUBc1ieenof6-QqwhoRGej3IPvV7BGHXqlxZslvy4CUQAQqWNFkfUjxg?key=R-6kpLnZ6X9JZLGWzVxNMw\" alt=\"\" title=\"\"><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Irin na\u2019urar daukar hoto da ake kira drone-Hoto daga News Central TV<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayanan da <strong>DUBAWA<\/strong> ta samu daga fadar gwamnatin jihar ta Kano sun nunar da cewa a lokacin da Sarki Muhammadu Sunusi na biyu ke tsaka da jawabi a zauran taron da aka tanada a wannan rana ta Hawan Nasarawa a fadar gwamnati, na\u2019urar daukar hoto da ake kira (drone) itace cajinta ya kare sai ta fado gefenta ya shafi kadan na grfen malafar sarki da ke kansa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Har ila yau wasu hotuna na bidiyo sahihai sun nuna yadda na\u2019\u2019urar ta fado ba tare da ta tsayar da duk wani abu da ake yi a wajen ba, kuma sarkin ya ci gaba da bayanansa, nan da nan fadawa suka dauke na\u2019urar ba tare da wata alama ta cewa jefota aka yi ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>A KARSHE<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bincike da shedu sun tabbatar da cewa babu inda aka jefi Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu a gidan gwamnatin Kano lokacin da ya je gaisuwar Sallah wajen Gwamna Abba Kabir Yusuf. Wanda ya wallafa labarin yaudara ce da tsabar karya ya wallafa a shafinsa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>DA\u2019AWA: Wasu sun jefi sarkin Kano Sanusi na biyu yayin da ya ke jawabi a gidan gwamnatin Kano HUKUNCI: Yaudara ce! Babu wata sheda da ta tabbatar da cewa an jefi sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu a fadar gwamnatin jihar Kano. CIKAKKEN SAKO &nbsp;\u201cYau din nan muna cike da farinciki\u201d a cewar Junaidu Aminu Kilishi wani mai amfani da shafin Facebook. Kilishi ya bayyana haka ne ya na da\u2019awar jewa an jefi sarkin Kano Sanusi na biyu yayin da ya ke jawabi a gidan gwamnatin Kano Haka nan ita ma@Gambizatv Facebook a shafin na Facebook ta yi irin wannan wallafa, inda a bidiyonta ya nunar da cewa bayan jifan sarkin a gidan gwamnati an kuma jefe shi a unguwar Fagge cikin birnin na Kano. Wadannan kenan baya ga wasu shafukan. Hoton shafin Junaidu Aminu Kilishi&nbsp; Wannan wallafa da ta bayyana a yayin bukukuwan babbar sallah a jihar Kano na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takkadama kan batun wa ke zama halastaccen Sarkin Kano, Sarki Muhammmadu Sunusi na biyu wato sarki na 14 ko kuwa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero sarki na 15. Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu dai wanda shine gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam\u2019iyyar NNPP ta amince da zama sarki, ya kai ziyara a gidan gwamnati a ranar biyu ga sallah da ake kira ranar Hawan Nasarawa kamar yadda aka saba gani a duk shekara,don zuwa kai gaisuwar sallah ga gwamna. A bana dai sarkin ya kai ziyarar gaisuwar Babbar Sallah a ranar 8 ga watan Yuni,2025 inda ya samu tarbar mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo saboda Gwamna Yusuf na halartar aikin Hajji a kasar Saudiya. Sarki Muhammadu Sunusi na biyu tare da mataimakin gwamna Aminu Abdussalam a ranar hawan Nasarawa a gidan gwamnati: Hoto daga gidan gwamnatin Kano A yayin da sarkin ke bayani a wajen taron hawan a gidan sarki sai wani bangare na na\u2019urar daukar hoto da ake kira (drone) ta fado ta shafi hular sarkin wanda da wannan ne mai da\u2019awar a shafin na &nbsp;Facebook ke cewa an jefi sarkin.&nbsp;&nbsp; Wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha\u2019awarsu wato likes sama da 1300&nbsp; da masu sharhi comments 106 da wadanda suka sake wallafawa wato shares su 70. Duba da yadda wannan wallafa da ma makamantanta suka karade shafukan sada zumunta musamman shafukan da ke zama na masu yada farfaganda ta adawa da sarkin ya sanya DUBAWA ganin wajibcin nazartar wannan wallafa don tantancewa. TANTANCEWA:&nbsp; Dubawa ta bibiyi kafafan yada labarai da dama don gano gaskiyar labarin cewa an jefi sarkin na Kano Muhammadu Sunusi na biyu a fadar gwamnati a ranar ta 8 ga watan na Yuni, 2025, sai dai duk kafafan yada labarai da ke zama sahihai babu wacce ta wallafa wannan labari inda ta nuna cewa an jefi sarkin a wannan rana a irin labaran da suka buga. Sallah: Kano Governor Urges Residents to Embrace Peace, Good Governance &#8211; Voice of Nigeria Broadcasting Service&nbsp; Kano demands compensation from FG over durbar cancellation | TheCable Ko a bidiyon Facebook@JunaiduAminuKilishi babu inda hoton bidiyon ya nuna cewa ga inda aka jefo wani abin jifa har yazo ya samu sarkin. Irin na\u2019urar daukar hoto da ake kira drone-Hoto daga News Central TV Bayanan da DUBAWA ta samu daga fadar gwamnatin jihar ta Kano sun nunar da cewa a lokacin da Sarki Muhammadu Sunusi na biyu ke tsaka da jawabi a zauran taron da aka tanada a wannan rana ta Hawan Nasarawa a fadar gwamnati, na\u2019urar daukar hoto da ake kira (drone) itace cajinta ya kare sai ta fado gefenta ya shafi kadan na grfen malafar sarki da ke kansa. Har ila yau wasu hotuna na bidiyo sahihai sun nuna yadda na\u2019\u2019urar ta fado ba tare da ta tsayar da duk wani abu da ake yi a wajen ba, kuma sarkin ya ci gaba da bayanansa, nan da nan fadawa suka dauke na\u2019urar ba tare da wata alama ta cewa jefota aka yi ba. A KARSHE Bincike da shedu sun tabbatar da cewa babu inda aka jefi Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu a gidan gwamnatin Kano lokacin da ya je gaisuwar Sallah wajen Gwamna Abba Kabir Yusuf. Wanda ya wallafa labarin yaudara ce da tsabar karya ya wallafa a shafinsa.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":23231,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4445],"class_list":["post-23230","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-62G","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4445,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"yusuf-nayaya","display_name":"Yusuf Nayaya","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/Sarki-Sanusi-na-biyu.-Hoto-daga-shafin-masarautar-Kano.jpg?fit=448%2C512&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/23230","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=23230"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/23230\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":23234,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/23230\/revisions\/23234"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/23231"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=23230"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=23230"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=23230"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=23230"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=23230"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}