{"id":23564,"date":"2025-07-13T07:58:27","date_gmt":"2025-07-13T06:58:27","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=23564"},"modified":"2025-07-13T07:58:29","modified_gmt":"2025-07-13T06:58:29","slug":"da-gaske-an-yi-karin-kudin-rajistar-bvn-da-nin-da-kuma-sauya-layin-da-ya-bata","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/da-gaske-an-yi-karin-kudin-rajistar-bvn-da-nin-da-kuma-sauya-layin-da-ya-bata\/","title":{"rendered":"Da gaske an yi karin kudin rajistar BVN da NIN da kuma sauya layin da ya bata?"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa:<\/strong> Wasu sa\u0199onni da ke yawo a dandalin sada zumunta suna i\u0199irarin cewa an kara kudin yin rajistar BVN a banki zuwa \u20a680,000, yin NIN ya koma \u20a630,000, sai kuma dawo da layin waya da ya \u0253ata wato \u201cWelcome Back\u201d zuwa&nbsp; \u20a650,000.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"21052\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/liberias-finance-ministry-did-not-resubmit-the-countrys-national-budget\/false-4-2-2\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/FALSE-4-2.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4-2\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/FALSE-4-2.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/FALSE-4-2.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-21052\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\"><strong>Hukunci:<\/strong> Dukkanin i\u0199irarin da ke cikin sa\u0199on da ke yawo ba gaskiya ne ba. babu wani tabbaci daga hukumomi ko kamfanoni cewa an yi wannan kari.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Cikakken Bayani<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A watannin da suka gabata ne <a href=\"https:\/\/guardian.ng\/business-services\/business\/fg-approves-50-telecoms-tariff-hike\/#:~:text=The%20Federal%20Government%2C%20on%20Monday,of%20Public%20Affairs%2C%20Reuben%20Muoka.\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">gwamantin Najeriya<\/a> ta amince kamfanonin sadarwa su yi karin kudin sadarwa da kashi 50 ga abokan huldarsu a Najeriya, to sai dai a \u2018yan kwanakin nan wani sa\u0199on da ke \u0199unshe da da\u2019awa uku ya fara yawo sosai a dandalin WhatsApp da Facebook.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sa\u0199on ya bayyana cewa an kara kudin wasu muhimman ayyukan gwamnati da sadarwa da suka hada da BVN da NIN da kuma welcome back.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sa\u0199on kamar yadda wani shafi na <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/story.php?story_fbid=122139853508405094&amp;id=61562152837595&amp;rdid=DhTPYsojOD0PpZNG#\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ALIB Hausa<\/a> ya wallafa a Facebook na cewa:&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cYanzu idan zaka yi BVN a banki, sai ka biya \u20a680,000.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Idan zaka yi NIN sai ka biya \u20a630,000.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Idan ka \u0253atar da layin wayarka, sai ka biya \u20a650,000 domin welcome back.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ganin cewa i\u0199irarin zai iya jawo ce-ce-ku-ce da damuwa, musamman a tsakanin matasa da masu kananan sana\u2019o\u2019i da ke bu\u0199atar amfani da wayar hannu da asusun banki kullum, DUBAWA ta yi bincike domin tabbatar da sahihancin labarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Tantancewa:<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa 1: An kara kudin BVN zuwa \u20a680,000<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Binciken da DUBAWA ta gudanar ya nuna cewa har yanzu yin rajistar BVN yana nan kyauta ga masu bu\u0199ata \u2018yan Najeriya, kuma babu wata sanarwa daga babban bankin kasar CBN da bankunan \u0199asa da suka tabbatar da cewa an yi karin kudin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Amma ga \u2018yan Najeriya dake zaune a kasashen waje, akwai bu\u0199atar biyan $50 (kimanin \u20a680,000) domin yin Non-Resident Bank Verification Number (NRBVN).&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan tsarin na musamman ne ga masu asusu daga \u0199etare, kamar yadda <a href=\"https:\/\/www.thecable.ng\/work-permit-valid-passport-n80k-fee-how-nigerians-in-diaspora-can-apply-for-bvn\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">CBN ya sanar<\/a> a watan Mayun 2025.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa 2: Za a rika biyan \u20a630,000 a matsayin kudin rajistar NIN<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shafin hukumar NIMC ya bayyana cewa yin rijistar NIN na farko da samun slip \u0257in farko yana nan kyauta ga \u2018yan Nijeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai DUBAWA ta gano cewa hukumar yin rajistar katin zama dan kasa ta <a href=\"https:\/\/punchng.com\/nimc-raises-fees-for-nin-data-modification-services\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">kara kudin<\/a> yin wasu ayyuka kamar gyara suna, gyara ranar haihuwa ko sake jinsi, wadanda farashinsu ya karu matuka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Babu wata sanarwa daga NIMC da ta ce ana biyan \u20a630,000 don yin NIN daga farko.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa 3: SIM Welcome Back \u2013 \u20a650,000<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kamfanonin sadarwa kamar MTN, Airtel, GLO da 9Mobile ba su fitar da wata sanarwa da ke nuna cewa dawo da SIM (welcome back) yana bukatar \u20a650,000.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta tattauna da wani dillalin layukan MTN a jihar Sokoto, Usamatu Hussaini, wanda ya ce:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cYin welcome back yawanci bai fi \u20a61,500 zuwa \u20a63,000 ba, sai dai idan mutum ya rasa katin rijista ko kuma yana son yin sa da gaggawa.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bugu da \u0199ari, hukumar NCC mai kula da sadarwa ta Najeriya ba ta fitar da wani \u0199a\u2019ida da ke nuna sabon farashin nan ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>A Karshe<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayanin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kara kudin yin rajistar BVN da yin NIN yda kuma dawo da layin waya da ya \u0253ata wato \u201cWelcome Backd\u201d bai da tushe ko makama daga hukumomin da abin ya shafa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wasu sa\u0199onni da ke yawo a dandalin sada zumunta suna i\u0199irarin cewa an kara kudin yin rajistar BVN a banki zuwa \u20a680,000, yin NIN ya koma \u20a630,000, sai kuma dawo da layin waya da ya \u0253ata wato \u201cWelcome Back\u201d zuwa&nbsp; \u20a650,000. Hukunci: Dukkanin i\u0199irarin da ke cikin sa\u0199on da ke yawo ba gaskiya ne ba. babu wani tabbaci daga hukumomi ko kamfanoni cewa an yi wannan kari. Cikakken Bayani A watannin da suka gabata ne gwamantin Najeriya ta amince kamfanonin sadarwa su yi karin kudin sadarwa da kashi 50 ga abokan huldarsu a Najeriya, to sai dai a \u2018yan kwanakin nan wani sa\u0199on da ke \u0199unshe da da\u2019awa uku ya fara yawo sosai a dandalin WhatsApp da Facebook.&nbsp; Sa\u0199on ya bayyana cewa an kara kudin wasu muhimman ayyukan gwamnati da sadarwa da suka hada da BVN da NIN da kuma welcome back.&nbsp; Sa\u0199on kamar yadda wani shafi na ALIB Hausa ya wallafa a Facebook na cewa:&nbsp; \u201cYanzu idan zaka yi BVN a banki, sai ka biya \u20a680,000. Idan zaka yi NIN sai ka biya \u20a630,000. Idan ka \u0253atar da layin wayarka, sai ka biya \u20a650,000 domin welcome back.\u201d Ganin cewa i\u0199irarin zai iya jawo ce-ce-ku-ce da damuwa, musamman a tsakanin matasa da masu kananan sana\u2019o\u2019i da ke bu\u0199atar amfani da wayar hannu da asusun banki kullum, DUBAWA ta yi bincike domin tabbatar da sahihancin labarin. Tantancewa: Da\u2019awa 1: An kara kudin BVN zuwa \u20a680,000 Binciken da DUBAWA ta gudanar ya nuna cewa har yanzu yin rajistar BVN yana nan kyauta ga masu bu\u0199ata \u2018yan Najeriya, kuma babu wata sanarwa daga babban bankin kasar CBN da bankunan \u0199asa da suka tabbatar da cewa an yi karin kudin. Amma ga \u2018yan Najeriya dake zaune a kasashen waje, akwai bu\u0199atar biyan $50 (kimanin \u20a680,000) domin yin Non-Resident Bank Verification Number (NRBVN).&nbsp; Wannan tsarin na musamman ne ga masu asusu daga \u0199etare, kamar yadda CBN ya sanar a watan Mayun 2025. Da\u2019awa 2: Za a rika biyan \u20a630,000 a matsayin kudin rajistar NIN Shafin hukumar NIMC ya bayyana cewa yin rijistar NIN na farko da samun slip \u0257in farko yana nan kyauta ga \u2018yan Nijeriya. Sai dai DUBAWA ta gano cewa hukumar yin rajistar katin zama dan kasa ta kara kudin yin wasu ayyuka kamar gyara suna, gyara ranar haihuwa ko sake jinsi, wadanda farashinsu ya karu matuka. Babu wata sanarwa daga NIMC da ta ce ana biyan \u20a630,000 don yin NIN daga farko. Da\u2019awa 3: SIM Welcome Back \u2013 \u20a650,000 Kamfanonin sadarwa kamar MTN, Airtel, GLO da 9Mobile ba su fitar da wata sanarwa da ke nuna cewa dawo da SIM (welcome back) yana bukatar \u20a650,000. DUBAWA ta tattauna da wani dillalin layukan MTN a jihar Sokoto, Usamatu Hussaini, wanda ya ce: \u201cYin welcome back yawanci bai fi \u20a61,500 zuwa \u20a63,000 ba, sai dai idan mutum ya rasa katin rijista ko kuma yana son yin sa da gaggawa.\u201d Bugu da \u0199ari, hukumar NCC mai kula da sadarwa ta Najeriya ba ta fitar da wani \u0199a\u2019ida da ke nuna sabon farashin nan ba. A Karshe Bayanin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kara kudin yin rajistar BVN da yin NIN yda kuma dawo da layin waya da ya \u0253ata wato \u201cWelcome Backd\u201d bai da tushe ko makama daga hukumomin da abin ya shafa.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":23566,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4439],"class_list":["post-23564","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-684","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4439,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"ukashatu-wakili","display_name":"Ukashatu Wakili","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/hoton-layuka.png?fit=512%2C256&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/23564","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=23564"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/23564\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":23567,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/23564\/revisions\/23567"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/23566"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=23564"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=23564"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=23564"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=23564"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=23564"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}