{"id":23907,"date":"2025-08-11T01:45:49","date_gmt":"2025-08-11T00:45:49","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=23907"},"modified":"2025-08-11T01:45:51","modified_gmt":"2025-08-11T00:45:51","slug":"babu-hujjar-kimiyya-kan-ikirarin-wani-malami-cewa-kashin-beraye-na-warkar-da-cututtuka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/babu-hujjar-kimiyya-kan-ikirarin-wani-malami-cewa-kashin-beraye-na-warkar-da-cututtuka\/","title":{"rendered":"Babu hujjar kimiyya kan ikirarin wani malami cewa kashin beraye na warkar da cututtuka"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa:<\/strong> Wani da ya bayyana kansa a matsayin <a href=\"https:\/\/archive.ph\/4ZkLG\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">malamin addini<\/a>, ya yi ikirarin cewa kashin beraye na iya warkar da appendicitis da \u0199urajen kai.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"23856\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/3bn-electric-car-sales-by-ibrahim-traore-false\/false-4-17\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-23856\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\"><strong>Hukunci:<\/strong> Karya ne. Babu wani bincike ko madogara ta kimiyya ko binciken lafiya da ya goyi bayan amfani da kashin beraye a matsayin magani.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Cikakken Bayani<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A ranar 4 ga Yuni, 2025, wani malamin addini mai suna Ibraheem Niass Kusfa, almajirin Sheikh Usman Kusfa Zaria, Kaduna \u2013 wanda aka fi sani da \u201cRigi Rigi\u201d \u2013 ya wallafa bidiyo guda biyu (mai <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/reel\/1422588778744274\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">da\u0199i\u0199u 39<\/a> da <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/reel\/2191669404590995\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">44<\/a>) a shafin Facebook yana ikirarin cewa kashin beraye na iya warkar da cutar appendicitis da kuma \u0199urajen kai.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cikin harshen Hausa, Niass Kusfa ya yi bayanin yadda ake amfani da \u0199azantar beraye wajen magance cututtuka na ciki da na jiki, yana danganta ikon warkarwar ga ikon Allah da albarkar Annabi Muhammad (SAW).<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa game da Appendix<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cKashin bera na warkar da ciwon appendix. Idan ka tara kashin beraye da yawa sai ka jika a ruwa, sai ka ba wanda ke fama da appendix, za ta narke duwatsun da ke jikinsa ta fito da su ta bayan gida. Ko yara ma da suke ci abincin da ke da duwatsu suna iya amfani da shi \u2013 da ikon Allah, da albarkar Annabi Muhammad, za ta narke.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa game da \u0199urajen kai<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cGa masu \u0199urajen kai, a tara kashin beraye a busar da shi a rana, a ni\u0199a ta ta zama gari sannan a ha\u0257a da kowace man shafawa, a shafa a kai. Da albarkar Annabi za ka warke \u2013 ko \u0199uraje ne, ko pimples, ko kowace cutar gashi.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wa\u0257annan ikirarin sun bazu sosai a kafafen sada zumunta, inda bidiyoyin suka samu sama da kallo 33,000 da 13,000 kowanne, har zuwa 4 ga Agusta, 2025.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da Facebook mai suna SafWan RidWan wanda ya yi tsokaci da gargadi cikin barkwanci ya ce: \u201cLassa fever, salamu alaikum.\u201d&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wasu kuma sun yi maraba da bayanin musamman maganin \u0199urajen kai, inda wani Imam Hussain Rigi Rigi ya gode wa malamin: \u201cAlhamdulillah Maulana, Allah ya saka maku da alkhairi.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Saboda irin wannan jan hankali da bidiyon suka yi, DUBAWA ta binciki gaskiyar lamarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/www.nhs.uk\/conditions\/appendicitis\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Apendis<\/a> ko kumburin wata cuta ce da ke faruwa yayin da wani sashe na ciki ya samu, wanda a mafi yawan lokuta ake bukatar tiyata domin a cire ta, don kauce wa fashewa. Idan ta fashe ba tare da an yi mata magani da gaggawa ba, hakan na iya haifar da mummunar illa ga rai.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXeuUCHWvMFAEfAt8Po4Z8dwDktkk4oTbJ5zZRxsgdvF1_EpqXDvNBPoSs_SmlXEaOsJA9Rxq5jSQtAXyrFWWGJ5JjqbE27jeTq1M9628pgDto-xT4Oy0Jq3gm7p2901bUuKxmxp?key=_n0MAo6kll-OY6mSls2A5w\" alt=\"\" title=\"\"><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hotun da ke nuna cutar apendis. Hakkin Mallaka: ALP<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A gefe guda kuma, <a href=\"https:\/\/www.healthline.com\/health\/scalp-acne\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">scalp acne<\/a> na nufin kuraje ko kaikayin fatar kai, wanda yawanci ke faruwa sakamakon toshewar ramukan fata, yawan maski a fata, ko kuma kamuwa da cutar \u0199wayoyin bacteria.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image\"><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/lh7-rt.googleusercontent.com\/docsz\/AD_4nXe73zMKsTYAUrCk1u6zewEU_Bb54ixnBKn1ebM2Z6YWi5Iqfgl74bkJmEjDADwmeRv_T4KHxMfbmFvO1qMhsimwsZkf9Ts2YsRgsrAf-jMZdNKVZButrGTSkkxMRmGOvmUsjEEQ?key=_n0MAo6kll-OY6mSls2A5w\" alt=\"\" title=\"\"><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hoton da ke nuna kurajen kai. Hakkin Mallaka:Tiktok<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yayin da cutar kumburin ciki ke bu\u0199atar kulawa ta gaggawa daga likita, \u0199urajen fatar kai kuwa ana iya magance shi da kayan kula da fata ko kuma magungunan rigakafi gwargwadon yadda matsalar ta tsananta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Shin najasar bera tana da amfani wajen maganin kumburin ciki ko kurajen kai ?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun gudanar da bincike ta hanyar amfani da kalmomin bincike (keyword searches) amma ba mu samu wani sahihin binciken kimiyya ba da ke goyon bayan ra\u2019ayin cewa cin najasar bera zai iya warkar da kumburin ciki.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun yi nazarin matsayar kimiyya ta yanzu daga manyan cibiyoyin binciken lafiya da tiyata, irin su <a href=\"https:\/\/www.ncbi.nlm.nih.gov\/books\/NBK580514\/?utm_source=chatgpt.com\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">StatPearls<\/a>, <a href=\"https:\/\/www.mdpi.com\/2392-7674\/11\/1\/2?\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">MDPI<\/a>, <a href=\"https:\/\/www.sages.org\/publications\/guidelines\/guideline-for-the-diagnosis-and-treatment-of-appendicitis\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">SAGES<\/a>, <a href=\"https:\/\/www.mayoclinic.org\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Mayo Clinic<\/a>\u2019, da <a href=\"https:\/\/pmc.ncbi.nlm.nih.gov\/articles\/PMC4949879\/?\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">WSES Jerusalem<\/a>, amma ba mu samu wani abu da ke tabbatar da wannan ikirarin ba. Haka kuma, mun duba wasu manyan majiyoyin lafiya, kamar <a href=\"https:\/\/medlineplus.gov\/ency\/article\/000256.htm?\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">MedlinePlus<\/a>, <a href=\"https:\/\/www.nhs.uk\/conditions\/appendicitis\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">NHS UK<\/a> da <a href=\"https:\/\/www.niddk.nih.gov\/health-information\/digestive-diseases\/appendicitis\/symptoms-causes?\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">NIDDK \u2013 NIH<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A gefe guda kuma, a cewar shafin <a href=\"https:\/\/www.webmd.com\/a-to-z-guides\/how-to-deal-with-rat-poop\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">WebMD<\/a>, kashin bera na da matu\u0199ar ha\u0257ari kuma yana \u0257auke da \u0199wayoyin cuta masu haddasa wasu manyan cututtuka, wadanda ke yaduwa ta hanyar taba kashin beraye.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Amurka (CDC) ta <a href=\"https:\/\/www.cdc.gov\/healthy-pets\/rodent-control\/index.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">tabbatar<\/a> cewa wasu cututtuka na iya ya\u0257uwa daga beraye zuwa mutane ta hanyar hul\u0257a kai tsaye da berayen da suka kamu da cuta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Ra\u2019ayin Masana<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta tuntubi <a href=\"https:\/\/www.linkedin.com\/in\/sabitu-muhammad-zainu-152b0895\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Muhammad Zainu Sabitu<\/a>, \u0199wararren likitan cututtuka a fannin \u0199wayoyin cuta a Asibitin Koyarwa na Jami\u2019ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, wanda ya karyata ikirarin yana cewa \u0199arya ne kuma abu ne mai ha\u0257ari.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cAkwai hanyoyin magani da aka tabbatar da sahihancinsu da aminci wajen magance kumburin ciki da \u0199ai\u0199ayi\/\u0199urajen fatar kai. Amma ba a ta\u0253a yin gwaji ko amincewa da kashin bera don yin magani ba.\u201d in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/afenetnigeria.net\/bio-dr-muhammad-shakir\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Muhammad Shakir Balogun<\/a>, \u0199wararren likitan \u0199wayoyin cuta kuma mai ba da shawara a cibiyar African Field Epidemiology Network (AFENET), ya gargadi cewa mutane na iya fuskantar ha\u0257arin kamuwa da \u0199wayoyin cuta masu ha\u0257ari ta hanyar ta\u0253awa, shakar \u0199amshi ko cin kashin bera.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya ce wannan kuwa sun ha\u0257a da: kwayar Hantavirus (mai jawo cututtukan numfashi da na koda), \u0199wayar Leptospira (mai lalata hanta\/koda), kwayar Lassa virus (mai haddasa mummunar zazzabin jini), Salmonella, LCM virus, da sauran su.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>A Karshe<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da\u2019awar cewa amfani da kashin bera na iya warkar da kumburin ciki (appendicitis) da \u0199ai\u0199ayi\/\u0199urajen fatar kai (scalp acne) \u0199arya ne kuma \u0199wararru sun tabbatar yana da matu\u0199ar ha\u0257ari.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani da ya bayyana kansa a matsayin malamin addini, ya yi ikirarin cewa kashin beraye na iya warkar da appendicitis da \u0199urajen kai. Hukunci: Karya ne. Babu wani bincike ko madogara ta kimiyya ko binciken lafiya da ya goyi bayan amfani da kashin beraye a matsayin magani. Cikakken Bayani A ranar 4 ga Yuni, 2025, wani malamin addini mai suna Ibraheem Niass Kusfa, almajirin Sheikh Usman Kusfa Zaria, Kaduna \u2013 wanda aka fi sani da \u201cRigi Rigi\u201d \u2013 ya wallafa bidiyo guda biyu (mai da\u0199i\u0199u 39 da 44) a shafin Facebook yana ikirarin cewa kashin beraye na iya warkar da cutar appendicitis da kuma \u0199urajen kai. A cikin harshen Hausa, Niass Kusfa ya yi bayanin yadda ake amfani da \u0199azantar beraye wajen magance cututtuka na ciki da na jiki, yana danganta ikon warkarwar ga ikon Allah da albarkar Annabi Muhammad (SAW). Da\u2019awa game da Appendix \u201cKashin bera na warkar da ciwon appendix. Idan ka tara kashin beraye da yawa sai ka jika a ruwa, sai ka ba wanda ke fama da appendix, za ta narke duwatsun da ke jikinsa ta fito da su ta bayan gida. Ko yara ma da suke ci abincin da ke da duwatsu suna iya amfani da shi \u2013 da ikon Allah, da albarkar Annabi Muhammad, za ta narke.\u201d Da\u2019awa game da \u0199urajen kai \u201cGa masu \u0199urajen kai, a tara kashin beraye a busar da shi a rana, a ni\u0199a ta ta zama gari sannan a ha\u0257a da kowace man shafawa, a shafa a kai. Da albarkar Annabi za ka warke \u2013 ko \u0199uraje ne, ko pimples, ko kowace cutar gashi.\u201d Wa\u0257annan ikirarin sun bazu sosai a kafafen sada zumunta, inda bidiyoyin suka samu sama da kallo 33,000 da 13,000 kowanne, har zuwa 4 ga Agusta, 2025. Wani mai amfani da Facebook mai suna SafWan RidWan wanda ya yi tsokaci da gargadi cikin barkwanci ya ce: \u201cLassa fever, salamu alaikum.\u201d&nbsp; Wasu kuma sun yi maraba da bayanin musamman maganin \u0199urajen kai, inda wani Imam Hussain Rigi Rigi ya gode wa malamin: \u201cAlhamdulillah Maulana, Allah ya saka maku da alkhairi.\u201d Saboda irin wannan jan hankali da bidiyon suka yi, DUBAWA ta binciki gaskiyar lamarin. Tantancewa Apendis ko kumburin wata cuta ce da ke faruwa yayin da wani sashe na ciki ya samu, wanda a mafi yawan lokuta ake bukatar tiyata domin a cire ta, don kauce wa fashewa. Idan ta fashe ba tare da an yi mata magani da gaggawa ba, hakan na iya haifar da mummunar illa ga rai. Hotun da ke nuna cutar apendis. Hakkin Mallaka: ALP A gefe guda kuma, scalp acne na nufin kuraje ko kaikayin fatar kai, wanda yawanci ke faruwa sakamakon toshewar ramukan fata, yawan maski a fata, ko kuma kamuwa da cutar \u0199wayoyin bacteria. Hoton da ke nuna kurajen kai. Hakkin Mallaka:Tiktok Yayin da cutar kumburin ciki ke bu\u0199atar kulawa ta gaggawa daga likita, \u0199urajen fatar kai kuwa ana iya magance shi da kayan kula da fata ko kuma magungunan rigakafi gwargwadon yadda matsalar ta tsananta. Shin najasar bera tana da amfani wajen maganin kumburin ciki ko kurajen kai ? Mun gudanar da bincike ta hanyar amfani da kalmomin bincike (keyword searches) amma ba mu samu wani sahihin binciken kimiyya ba da ke goyon bayan ra\u2019ayin cewa cin najasar bera zai iya warkar da kumburin ciki. Mun yi nazarin matsayar kimiyya ta yanzu daga manyan cibiyoyin binciken lafiya da tiyata, irin su StatPearls, MDPI, SAGES, Mayo Clinic\u2019, da WSES Jerusalem, amma ba mu samu wani abu da ke tabbatar da wannan ikirarin ba. Haka kuma, mun duba wasu manyan majiyoyin lafiya, kamar MedlinePlus, NHS UK da NIDDK \u2013 NIH. A gefe guda kuma, a cewar shafin WebMD, kashin bera na da matu\u0199ar ha\u0257ari kuma yana \u0257auke da \u0199wayoyin cuta masu haddasa wasu manyan cututtuka, wadanda ke yaduwa ta hanyar taba kashin beraye. Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Amurka (CDC) ta tabbatar cewa wasu cututtuka na iya ya\u0257uwa daga beraye zuwa mutane ta hanyar hul\u0257a kai tsaye da berayen da suka kamu da cuta. Ra\u2019ayin Masana DUBAWA ta tuntubi Muhammad Zainu Sabitu, \u0199wararren likitan cututtuka a fannin \u0199wayoyin cuta a Asibitin Koyarwa na Jami\u2019ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, wanda ya karyata ikirarin yana cewa \u0199arya ne kuma abu ne mai ha\u0257ari. \u201cAkwai hanyoyin magani da aka tabbatar da sahihancinsu da aminci wajen magance kumburin ciki da \u0199ai\u0199ayi\/\u0199urajen fatar kai. Amma ba a ta\u0253a yin gwaji ko amincewa da kashin bera don yin magani ba.\u201d in ji shi. Muhammad Shakir Balogun, \u0199wararren likitan \u0199wayoyin cuta kuma mai ba da shawara a cibiyar African Field Epidemiology Network (AFENET), ya gargadi cewa mutane na iya fuskantar ha\u0257arin kamuwa da \u0199wayoyin cuta masu ha\u0257ari ta hanyar ta\u0253awa, shakar \u0199amshi ko cin kashin bera. Ya ce wannan kuwa sun ha\u0257a da: kwayar Hantavirus (mai jawo cututtukan numfashi da na koda), \u0199wayar Leptospira (mai lalata hanta\/koda), kwayar Lassa virus (mai haddasa mummunar zazzabin jini), Salmonella, LCM virus, da sauran su. A Karshe Da\u2019awar cewa amfani da kashin bera na iya warkar da kumburin ciki (appendicitis) da \u0199ai\u0199ayi\/\u0199urajen fatar kai (scalp acne) \u0199arya ne kuma \u0199wararru sun tabbatar yana da matu\u0199ar ha\u0257ari.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":23908,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4439],"class_list":["post-23907","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-6dB","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4439,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"ukashatu-wakili","display_name":"Ukashatu Wakili","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Hoton-bera.jpg?fit=512%2C292&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/23907","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=23907"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/23907\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":23909,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/23907\/revisions\/23909"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/23908"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=23907"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=23907"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=23907"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=23907"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=23907"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}