{"id":24096,"date":"2025-08-23T04:20:57","date_gmt":"2025-08-23T03:20:57","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=24096"},"modified":"2025-08-23T04:20:59","modified_gmt":"2025-08-23T03:20:59","slug":"yaudara-ce-sojan-da-aka-kama-ya-na-baiwa-yan-taadda-makamai-ba-tsohon-dan-taadda-ba-ne","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/yaudara-ce-sojan-da-aka-kama-ya-na-baiwa-yan-taadda-makamai-ba-tsohon-dan-taadda-ba-ne\/","title":{"rendered":"Yaudara ce! Sojan da aka kama ya na baiwa \u2018yan ta\u2019adda makamai ba tsohon dan ta\u2019adda ba ne"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin X ya wallafa&nbsp; <a href=\"https:\/\/x.com\/chude__\/status\/1954279794675442111?t=xdOzUeRh92um16azceTqKQ&amp;s=19\">bidiyon<\/a> da ke da\u2019awar cewa wani tsohon mamban kumgiyar Boko Haram ya shigo hannun mahukunta bayan da aka kama shi ya na saidawa \u2018yan ta\u2019addan makamai.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"136\" height=\"59\" data-attachment-id=\"21059\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/national-elections-commission-did-not-dismiss-over-sixty-employees\/misleading-29\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/MISLEADING.png?fit=136%2C59&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"136,59\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"MISLEADING\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/MISLEADING.png?fit=136%2C59&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/MISLEADING.png?resize=136%2C59\" alt=\"\" class=\"wp-image-21059\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#7f7e07\">Hukunci: Yaudara ce! Rahotannin kafafen yada labarai sun bayyana wanda aka kama a sunan yana saidawa \u2018yan ta\u2019adda makamai a matsayin soja, sai dai, babu wata hujjar da ta nuna cewa tsohon mamban Boko Haram din ya shiga soja bayan da ya fita daga kungiyar. Bacin hakan, a shekarar 2022 ne aka nadi bidiyon ba kwanan nan ne ba kamar yadda ake fadi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A shekarar 2022, gwamnatin jihar Borno ta sanar cewa ta yi <a href=\"https:\/\/www.dw.com\/en\/nigeria-ex-boko-haram-fighters-face-tough-path-to-reintegration\/a-61169893\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>nasarar mayar da tsoffin mambobin kungiyar Boko Haram cikin al&#8217;umma<\/strong><\/a>. Shekaru uku bayan nan a watan Afrilun 2025 tsoffin mambobin kungiyar fiye da 390 suka yi bukin <a href=\"https:\/\/punchng.com\/390-ex-insurgents-graduate-from-de-radicalisation-programme-in-gombe\/?amp=\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>kammala karatu<\/strong><\/a> a shirin gwamnatin na sauya akidu masu kaifi da sake maido da su cikin al\u2019ummar bayan da suka shafe watanni suna horaswa a jihar Gombe.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shugaban hafsar sojoji, Christopher Musa, <a href=\"https:\/\/nannews.ng\/2025\/04\/17\/390-ex-insurgents-graduate-from-de-radicalisation-programme-in-gombe\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>ya kwantanta<\/strong><\/a> shirin matsayin wata dabara ta sojoji wajen rage rashin tsaro a kasar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Daga baya wani mai amfani da shafin X&nbsp; <a href=\"https:\/\/x.com\/chude__\/status\/1954279794675442111?t=xdOzUeRh92um16azceTqKQ&amp;s=19\"><strong>@Chude<\/strong><\/a> ya wallafa wani <a href=\"https:\/\/x.com\/chude__\/status\/1954279794675442111?t=xdOzUeRh92um16azceTqKQ&amp;s=19\"><strong>bidiyon<\/strong><\/a> da ke da\u2019awar wai sojojin Najeriyar ne ke neman wani tsohon mamban kungiyar Boko Haram&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ana iya gani wadansu labaran makamantan wannan a wadannan shafukan na Facebook, a <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/v\/1AarVzdWgt\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>nan<\/strong><\/a>, <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/r\/1C9t14BbLg\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>nan<\/strong><\/a>, da <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/p\/171NcXwo4x\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>nan<\/strong><\/a>.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A ranar Alhamis 14 ga watan Agustan 2025 mutane sama da 54,000 sun kalla bidiyon, wasu sama da 1,300 sun latsa alaman like sa\u2019annan wasu 950 sun yi amfani da labarin, 173 sun adana wasu 81 sun yi amfani da labarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cikin wurin tsokaci ko wato kwament section, yawancin wadanda suka tofa albarkacin bankinsu sun gaskata da da\u2019awan sun kuma soki shawarar gwamnati na sake maido su cikin al\u2019umma su zauna kafada da kafada da wadanda suka muzgunawa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cAbun takaici ne, domin daga karshe, sojojin da suka kama shi ne za su fiskanci hukunci da wulakanci a wajen mahukunta,\u201d a cewar&nbsp; <a href=\"https:\/\/x.com\/afrisagacity\/status\/1954284433248297278?t=hoPcUbEboXO8XmKzTIBrRA&amp;s=19\"><strong>@Afrisagacity<\/strong><\/a> .<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cTa yaya za\u2019a ce wai kasa ta yafewa \u2018yan ta\u2019adda ta kuma sanya su cikin rundunar sojojin Najeriya?\u201d<a href=\"https:\/\/x.com\/henriobi\/status\/1954291262367977855?t=xckcdcY1tnNMqAsFULu1_g&amp;s=19\"><strong>@Henryobi<\/strong><\/a> ya tambaya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cGwamnatin Najeriya ce babbar matsalar Najeriya. Wannan guntun wai shi ma na daya daga cikin tsoffin \u2018yan boko haram din da aka yafewa,\u201d in ji <a href=\"https:\/\/x.com\/Forsby31\/status\/1954320115270365689?t=SavgJ2JuRFPvtp08T-9eFw&amp;s=19\"><strong>@Forsby31<\/strong><\/a> .<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Domin irin sarkakiyar da ke tattare da wannan batun da ma yadda gwamnatin Najeriya ta fi muradin sauya akidun tsoffin \u2018yan Boko Harama a maimakon hukunta su, DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar wannan bidiyon.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa&nbsp;<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta yi amfani da manhajar tantance asalin bidiyoyi da hotuna na Google wato Google Reverse Image Search. Nan da nan ya hada mu da wani rahoton da aka wallafa a shafin <a href=\"https:\/\/ceoafrica.com\/newsdetails.php?tabnews=90339\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>CEOAfrica<\/strong><\/a> a watan Oktoban 2022.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Rahoton ya bayyana cewa abokan aikin tohon sojan a rundunar sojojin Najeriya suka kama shi yayin da ya ke sace makaman da ya ke saidawa kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka da \u2018yan ta\u2019adda. A cewar shafin, sunan tsohon sojan&nbsp; Iorliam Emmanuel.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayan haka DUBAWAta gudanar da wani karin binciken ta yin amfani da mahimman kalmomi dan gano sauran rahotanni makamantan wannan. Jaridar&nbsp; <a href=\"https:\/\/punchng.com\/soldier-accused-of-selling-ammunition-to-terrorists-arrested\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Punch<\/strong><\/a> ma ta dauki rahoton ranar 13 ga watan Oktoba 2022 inda su ma suka ce an kama Emmanuel ne sadda ya ke kokarin kai bindigogi da makaman da ya sace zuwa wurin \u2018yan ta\u2019addan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Haka nan ita ma jaridar <a href=\"https:\/\/www.thecable.ng\/soldier-nabbed-in-borno-for-stealing-and-supplying-ammunition-to-bandits\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Cable<\/strong><\/a> ta dauki labarin a shekarar 2022, inda ta kara da cewa tsohon dan asalin jihar Binuwai ne, kuma na mika shi ga sashen kula da leken asiri na sojoji dan gudanar da bincike mai zurfi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wasu karin rahotanni makamantan wannan wadanda kafofin yada labaran suka dauka a cikin watan Oktoban 2022 sun hada da wadannan biyun&nbsp; <a href=\"https:\/\/thestreetjournal.org\/army-arrests-soldier-who-steals-supplies-ammunition-to-terrorists-video\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>wannan<\/strong><\/a> da <a href=\"https:\/\/barristerng.com\/video-soldier-arrested-for-stealing-selling-ammunition-to-terrorists\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>wannan<\/strong><\/a>. A cikin irin wadannan rahotannin, babu inda aka kwatanta Emmanuel a matsayin mamban Boko Haram.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan da\u2019awar yaudara ce kawai kuma bidiyon na cikin shafukan yanar gizo-gizo tun watan oktoban 2022.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin X ya wallafa&nbsp; bidiyon da ke da\u2019awar cewa wani tsohon mamban kumgiyar Boko Haram ya shigo hannun mahukunta bayan da aka kama shi ya na saidawa \u2018yan ta\u2019addan makamai. Hukunci: Yaudara ce! Rahotannin kafafen yada labarai sun bayyana wanda aka kama a sunan yana saidawa \u2018yan ta\u2019adda makamai a matsayin soja, sai dai, babu wata hujjar da ta nuna cewa tsohon mamban Boko Haram din ya shiga soja bayan da ya fita daga kungiyar. Bacin hakan, a shekarar 2022 ne aka nadi bidiyon ba kwanan nan ne ba kamar yadda ake fadi. Cikakken bayani A shekarar 2022, gwamnatin jihar Borno ta sanar cewa ta yi nasarar mayar da tsoffin mambobin kungiyar Boko Haram cikin al&#8217;umma. Shekaru uku bayan nan a watan Afrilun 2025 tsoffin mambobin kungiyar fiye da 390 suka yi bukin kammala karatu a shirin gwamnatin na sauya akidu masu kaifi da sake maido da su cikin al\u2019ummar bayan da suka shafe watanni suna horaswa a jihar Gombe. Shugaban hafsar sojoji, Christopher Musa, ya kwantanta shirin matsayin wata dabara ta sojoji wajen rage rashin tsaro a kasar. Daga baya wani mai amfani da shafin X&nbsp; @Chude ya wallafa wani bidiyon da ke da\u2019awar wai sojojin Najeriyar ne ke neman wani tsohon mamban kungiyar Boko Haram&nbsp; Ana iya gani wadansu labaran makamantan wannan a wadannan shafukan na Facebook, a nan, nan, da nan.&nbsp; A ranar Alhamis 14 ga watan Agustan 2025 mutane sama da 54,000 sun kalla bidiyon, wasu sama da 1,300 sun latsa alaman like sa\u2019annan wasu 950 sun yi amfani da labarin, 173 sun adana wasu 81 sun yi amfani da labarin. A cikin wurin tsokaci ko wato kwament section, yawancin wadanda suka tofa albarkacin bankinsu sun gaskata da da\u2019awan sun kuma soki shawarar gwamnati na sake maido su cikin al\u2019umma su zauna kafada da kafada da wadanda suka muzgunawa. \u201cAbun takaici ne, domin daga karshe, sojojin da suka kama shi ne za su fiskanci hukunci da wulakanci a wajen mahukunta,\u201d a cewar&nbsp; @Afrisagacity . \u201cTa yaya za\u2019a ce wai kasa ta yafewa \u2018yan ta\u2019adda ta kuma sanya su cikin rundunar sojojin Najeriya?\u201d@Henryobi ya tambaya. \u201cGwamnatin Najeriya ce babbar matsalar Najeriya. Wannan guntun wai shi ma na daya daga cikin tsoffin \u2018yan boko haram din da aka yafewa,\u201d in ji @Forsby31 . Domin irin sarkakiyar da ke tattare da wannan batun da ma yadda gwamnatin Najeriya ta fi muradin sauya akidun tsoffin \u2018yan Boko Harama a maimakon hukunta su, DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar wannan bidiyon. Tantancewa&nbsp; DUBAWA ta yi amfani da manhajar tantance asalin bidiyoyi da hotuna na Google wato Google Reverse Image Search. Nan da nan ya hada mu da wani rahoton da aka wallafa a shafin CEOAfrica a watan Oktoban 2022.&nbsp; Rahoton ya bayyana cewa abokan aikin tohon sojan a rundunar sojojin Najeriya suka kama shi yayin da ya ke sace makaman da ya ke saidawa kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka da \u2018yan ta\u2019adda. A cewar shafin, sunan tsohon sojan&nbsp; Iorliam Emmanuel. Bayan haka DUBAWAta gudanar da wani karin binciken ta yin amfani da mahimman kalmomi dan gano sauran rahotanni makamantan wannan. Jaridar&nbsp; Punch ma ta dauki rahoton ranar 13 ga watan Oktoba 2022 inda su ma suka ce an kama Emmanuel ne sadda ya ke kokarin kai bindigogi da makaman da ya sace zuwa wurin \u2018yan ta\u2019addan. Haka nan ita ma jaridar Cable ta dauki labarin a shekarar 2022, inda ta kara da cewa tsohon dan asalin jihar Binuwai ne, kuma na mika shi ga sashen kula da leken asiri na sojoji dan gudanar da bincike mai zurfi. Wasu karin rahotanni makamantan wannan wadanda kafofin yada labaran suka dauka a cikin watan Oktoban 2022 sun hada da wadannan biyun&nbsp; wannan da wannan. A cikin irin wadannan rahotannin, babu inda aka kwatanta Emmanuel a matsayin mamban Boko Haram. A Karshe Wannan da\u2019awar yaudara ce kawai kuma bidiyon na cikin shafukan yanar gizo-gizo tun watan oktoban 2022.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":24088,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4055],"class_list":["post-24096","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-6gE","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4055,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"miracle-akubuo","display_name":"Miracle Akubuo","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/terrorist.png?fit=1024%2C576&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/24096","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=24096"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/24096\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":24097,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/24096\/revisions\/24097"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/24088"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=24096"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=24096"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=24096"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=24096"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=24096"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}