{"id":24781,"date":"2025-09-28T11:52:10","date_gmt":"2025-09-28T10:52:10","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=24781"},"modified":"2025-09-28T11:52:12","modified_gmt":"2025-09-28T10:52:12","slug":"shin-gaskiya-ne-matan-shugabannin-kananan-hukumomin-adamawa-sun-tafi-turkiyya-dan-samun-horo","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/shin-gaskiya-ne-matan-shugabannin-kananan-hukumomin-adamawa-sun-tafi-turkiyya-dan-samun-horo\/","title":{"rendered":"Shin gaskiya ne matan shugabannin kananan hukumomin Adamawa sun tafi Turkiyya dan samun horo?"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa:<\/strong> Wasu <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/search\/top\/?q=matan%20shugabannin%20kananan%20hukumomi%20adamawa\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">hotuna<\/a> sun karade shafukan sada zumunta da ke nuna cewa matan shugabannin kananan hukumomin jihar Adamawa sun je Turkiyya domin samun horo kan jagoranci da ci gaban al\u2019umma.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"135\" height=\"57\" data-attachment-id=\"20095\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/live-fact-check-dubawa-nfc-monitor-mis-disinformation-on-edo-governorship-election\/true-1-1-2\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/TRUE-1-1.png?fit=135%2C57&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"135,57\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"TRUE-1-1\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/TRUE-1-1.png?fit=135%2C57&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/TRUE-1-1.png?resize=135%2C57\" alt=\"\" class=\"wp-image-20095\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#0aa403\"><strong>Hukunci:<\/strong> Gaskiya ne. Binciken DUBAWA ya gano cewa matan shugabannin \u0199ananan hukumomin Adamawa sun tafi horo a Istanbul, Turkiyya, kamar yadda rahotanni masu inganci suka tabbatar.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A ranar 22 ga Satumba, 2025, hotuna da labarai sun karade shafukan Facebook da WhatsApp inda aka bayyana cewa matan shugabannin kananan hukumomin jihar Adamawa sun isa birnin Istanbul na \u0199asar Turkiyya domin halartar taron horaswa na mako guda kan jagoranci da ci gaban al\u2019umma.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Rahoton (kamar yadda muka zakulo a <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/1Jfp3mx2ed\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>, <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/p\/1LrM1GD6Yy\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a> da <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/Dandalinlabarai\/posts\/pfbid02QG46C392dzAzREjMMC3xNvQqp5uxBGMk4aaKNZZcDVCrB814UuzHn8a4kQrqbmtvl\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>) ya ce tawagar ta \u0199unshi matan shugabannin guda 21, kuma gwamnatin jihar Adamawa ce ta \u0257auki nauyin tafiyar, tare da ha\u0257in gwiwa da kungiyar shugabannin \u0199ananan hukumomi ta kasa, wato ALGON.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan batu ya haddasa cece-kuce tsakanin jama\u2019a musamman a arewacin Najeriya. Wasu na ganin an kashe ku\u0257in jama\u2019a ba tare da bu\u0199ata ba, yayin da wasu ke tambayar ko labarin gaskiya ne ko kuma sharri ne kawai.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da Facebook, Abubakar Al Ameen, ya yi rubutu cewa: \u201cDan Allah, tayaya za ayi wa talakan Arewa adalci idan ku\u0257insa ake kashewa wajen yawon bude ido?\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wadannan martani sun nuna yadda jama\u2019a ke kallon irin wannan tafiya a matsayin almubazzaranci, musamman a yanayi da talauci da hauhawar farashin kaya ke addabar jama\u2019a.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai a gefe guda, wasu na shakku kan gaskiyar labarin, kamar wani Usman Ibrahim Tanko, ya yi tambaya cewa: \u201cYawon bude ido da ku\u0257in talakawa? Wannan abin ba gaskiya ne ba.\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Saboda yadda labarin da ra\u2019ayoyi mabanbanta suka karade kafafen sada zumunta, DUBAWA ta gudanar da bincike domin tabbatar da sahihancin ikirarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta bincika a shafin nema na Google inda muka gano cewa labarin gaskiya ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Suleiman Toungo, shugaban karamar hukumar Toungo kuma shugaban \u0199ungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Adamawa, ya tabbatar da tafiyar a tattaunawa da <a href=\"https:\/\/punchng.com\/adamawa-retirees-question-turkey-training-for-lg-chairmens-wives\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">jaridar Punch<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya ce: \u201cMun yi irin wannan horo a watanni biyu da suka gabata, don haka ba na ganin wani abu da ba daidai ba a cikin tafiyar matanmu zuwa wajen horo. Su matanmu ne kuma muna bukatar shawararsu. Muna kallon muhimmancin horar da su kan jagoranci, ba kudin da za a kashe a tafiyar ba.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Jaridar <a href=\"https:\/\/dailytrust.com\/reactions-trail-training-of-adamawa-lg-chairmens-wives-in-turkey\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Daily Trust<\/a> ma ta ruwaito wannan batu, inda ta nuna yadda martani daban-daban suka biyo bayan tafiyar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan ya tabbatar da cewa hotunan da ake yadawa na tafiyar sun yi daidai da gaskiya, ba kirkirarrun hotuna ba ne ko labaran \u0199arya da aka shirya don bata suna.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ikirarin cewa matan shugabannin \u0199ananan hukumomi na jihar Adamawa sun tafi Turkiyya domin shirin horo kan jagoranci gaskiya ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wasu hotuna sun karade shafukan sada zumunta da ke nuna cewa matan shugabannin kananan hukumomin jihar Adamawa sun je Turkiyya domin samun horo kan jagoranci da ci gaban al\u2019umma. Hukunci: Gaskiya ne. Binciken DUBAWA ya gano cewa matan shugabannin \u0199ananan hukumomin Adamawa sun tafi horo a Istanbul, Turkiyya, kamar yadda rahotanni masu inganci suka tabbatar. Cikakken Bayani A ranar 22 ga Satumba, 2025, hotuna da labarai sun karade shafukan Facebook da WhatsApp inda aka bayyana cewa matan shugabannin kananan hukumomin jihar Adamawa sun isa birnin Istanbul na \u0199asar Turkiyya domin halartar taron horaswa na mako guda kan jagoranci da ci gaban al\u2019umma. Rahoton (kamar yadda muka zakulo a nan, nan da nan) ya ce tawagar ta \u0199unshi matan shugabannin guda 21, kuma gwamnatin jihar Adamawa ce ta \u0257auki nauyin tafiyar, tare da ha\u0257in gwiwa da kungiyar shugabannin \u0199ananan hukumomi ta kasa, wato ALGON. Wannan batu ya haddasa cece-kuce tsakanin jama\u2019a musamman a arewacin Najeriya. Wasu na ganin an kashe ku\u0257in jama\u2019a ba tare da bu\u0199ata ba, yayin da wasu ke tambayar ko labarin gaskiya ne ko kuma sharri ne kawai. Wani mai amfani da Facebook, Abubakar Al Ameen, ya yi rubutu cewa: \u201cDan Allah, tayaya za ayi wa talakan Arewa adalci idan ku\u0257insa ake kashewa wajen yawon bude ido?\u201d Wadannan martani sun nuna yadda jama\u2019a ke kallon irin wannan tafiya a matsayin almubazzaranci, musamman a yanayi da talauci da hauhawar farashin kaya ke addabar jama\u2019a. Sai dai a gefe guda, wasu na shakku kan gaskiyar labarin, kamar wani Usman Ibrahim Tanko, ya yi tambaya cewa: \u201cYawon bude ido da ku\u0257in talakawa? Wannan abin ba gaskiya ne ba.\u201d. Saboda yadda labarin da ra\u2019ayoyi mabanbanta suka karade kafafen sada zumunta, DUBAWA ta gudanar da bincike domin tabbatar da sahihancin ikirarin. Tantancewa DUBAWA ta bincika a shafin nema na Google inda muka gano cewa labarin gaskiya ne. Suleiman Toungo, shugaban karamar hukumar Toungo kuma shugaban \u0199ungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Adamawa, ya tabbatar da tafiyar a tattaunawa da jaridar Punch. Ya ce: \u201cMun yi irin wannan horo a watanni biyu da suka gabata, don haka ba na ganin wani abu da ba daidai ba a cikin tafiyar matanmu zuwa wajen horo. Su matanmu ne kuma muna bukatar shawararsu. Muna kallon muhimmancin horar da su kan jagoranci, ba kudin da za a kashe a tafiyar ba.\u201d Jaridar Daily Trust ma ta ruwaito wannan batu, inda ta nuna yadda martani daban-daban suka biyo bayan tafiyar. Wannan ya tabbatar da cewa hotunan da ake yadawa na tafiyar sun yi daidai da gaskiya, ba kirkirarrun hotuna ba ne ko labaran \u0199arya da aka shirya don bata suna. A Karshe Ikirarin cewa matan shugabannin \u0199ananan hukumomi na jihar Adamawa sun tafi Turkiyya domin shirin horo kan jagoranci gaskiya ne.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":24782,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"default","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4439],"class_list":["post-24781","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-6rH","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4439,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"ukashatu-wakili","display_name":"Ukashatu Wakili","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/Matan-Ciyamomi.jpg?fit=512%2C363&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/24781","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=24781"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/24781\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":24783,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/24781\/revisions\/24783"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/24782"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=24781"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=24781"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=24781"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=24781"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=24781"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}