{"id":25035,"date":"2025-10-14T08:56:18","date_gmt":"2025-10-14T07:56:18","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=25035"},"modified":"2025-10-14T08:56:20","modified_gmt":"2025-10-14T07:56:20","slug":"shin-da-gaske-ne-wai-ilimin-boko-kyauta-ne-a-makarantu-mallakar-gwamnati-a-najeriya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/shin-da-gaske-ne-wai-ilimin-boko-kyauta-ne-a-makarantu-mallakar-gwamnati-a-najeriya\/","title":{"rendered":"Shin Da gaske ne wai ilimin boko kyauta ne a makarantu mallakar gwamnati a Najeriya?\u00a0"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin X @TemidayoOniosun, kwananan nan ya yi\u00a0 <a href=\"https:\/\/x.com\/temidayooniosun\/status\/1973280497133576464?s=46\"><strong>da&#8217;awar cewa<\/strong><\/a> makarantun firamare, sakandare da jami\u2019a duk kyauta ne idan dai na gwamnati ne.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"23856\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/3bn-electric-car-sales-by-ibrahim-traore-false\/false-4-17\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-23856\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Hukunci: Yaudara ce! Yayin da makarantun firamare, sakandare da ma wasu jami\u2019o\u2019in da ke karkashin gwamnati ba su bukatar kudin makaranta, akwai wadansu kudaden da tilas ne kowani dalubi ya biya kuma idan ba haka ba a hana su karbar darassi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ranar 15 ga watan Satumba makarantun firamare da sakandare a Najeriya suka dawo makaranta daga dogon hutu. Bayan nan ne wasu iyaye suka shiga kafofin sada zumunta suna korafin tsadar farashin kudin makaranta, takardu da dai sauran abubuwna da ake bukata dan zuwa makarantar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan kuma ya biyo bayan korafe-korafen da dama can daliban jami\u2019o\u2019i su ma suka yi a kafofin sada zumunta su ma kan tsadar farashin kudin makaranta, wasu daga cikin masu amfani da shafukan ma har sun yi magana taka mai mai a kan Jami\u2019ar Ilori wadda ita ma ta kara kudin makaranta na sabuwar shekarar ta 2025\/2026 da za\u2019a shiga yanzu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan mai amfani da shafin @<a href=\"https:\/\/x.com\/theiyanuoluwa__\/status\/1973113316605304876?s=46\"><strong>theiyanuoluwa<\/strong><\/a> cewa ya yi, \u201cJami\u2019ar Ilori ta fara zama jami\u2019a mai zaman kanta. Kudin makarantar ya karu sosai irin na fitan hankali.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani shi ma mai amfani da shafin da sunan @Uilgist <a href=\"https:\/\/x.com\/uil_gists\/status\/1973098559646978305?s=46\"><strong>cewa ya yi<\/strong><\/a>, \u201cLABARI DA DUMI-DUMI! Daliban jami\u2019ar Ilori sun fashe da kuka ganin yadda wasu tilsa su daina zuwa makaranta saboda farashin da aka kara. Daliban da ke dawowa zasu biya sama da dubu 200 ya yin da wadanda ke shekara ta karshe kuma za\u2019a caje su su kuma sama da dubu 100.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A wani&nbsp; <a href=\"https:\/\/x.com\/uniben_sug\/status\/1972389464380170409?s=46\"><strong>cigaban kuma<\/strong><\/a>, Kungiyar dalibai na Student Union a jami\u2019ar Benin ta fitar da sanarwar da ke karyata da\u2019awar cewa akwai dalibai 5,000 din da ba su biya kudin makaranta ba wadanda za\u2019a hana su rubuta jarabawa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yayin da ya ke tsokaci kan fannin ilimi a Najeriya, mai amfani da shafin X @TemidayoOniosun <a href=\"https:\/\/x.com\/temidayooniosun\/status\/1973280497133576464?s=46\"><strong>ya yi zargin cewa<\/strong><\/a> ilimin firamare da sakandare a makarantun gwamnati kyauta ne, ya kuma kara wa iyaye karfin gwiwa da su sa yaransu a makarantun gwamnati idan har ba za su iya biyan na kudin ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan tsokacin na sa martani ne ga wani&nbsp; <a href=\"https:\/\/x.com\/_debbieoa\/status\/1972354284865101942?s=46\"><strong>batun da <\/strong><\/a>&nbsp;@DebbieOA ta wallafa, wadda ta ce yawancin iyalai da kyar su ke iya biyan kudin makarantar yaransu, sa\u2019annan dan jaddada wannan ra\u2019ayin na ta ta yi amfani da wani labarin da ya dauki hankali na wasu wasu masu yara biyar wadanda suka gaza biya musu kudin makaranta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bisa la\u2019akari da wannan batun ne, Temidayo <a href=\"https:\/\/x.com\/temidayooniosun\/status\/1973280497133576464?s=46\"><strong>ya yi bayanin cewa <\/strong><\/a>, \u201cmakarantun firamare, sakandare da jami\u2019a duk kyauta ne a Najeriya. Duk wanda ba zai iya biyan na kudin ba ya je na gwamnati.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">To sai dai da yawa daga cikin masu amfani da shafin ba su amince da wannan tsokacin na shi ba kums su ma sun bayyana ra\u2019ayoyinsu dangane da abubuwan da suka faru da su a makarantun gwamnati.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Samun ilimin boko na cigaba da kasancewa batu mai daukar hankali tsakanin masu ruwa da tsaki a \u2018yan shekarun baya-bayan nan, musamman bayan wani rahoton da ya nuna cewa a Najeriya kusan yara&nbsp; <a href=\"https:\/\/tribuneonlineng.com\/nigerias-out-of-school-children-hit-18-95-million-unicef\/amp\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>miliyan 18 ba su zuwa makaranta<\/strong><\/a>.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ganin mahimmancin da batun ke da shi ne ya s, DUBAWA tantance wannan bayani na mai amfani da shafin X dan gano gaskiyar lamarin.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Binciken da muka yi da muhimman kalmomi ya bayyana mana wani rahoton da fadar shugaban kasa ta&nbsp; wallafa a shekarar 2023 wanda ya <a href=\"https:\/\/www.icirnigeria.org\/federal-universities-still-tuition-free-presidency\/#:~:text=July%2026,%202023,by%20students%20on%20sundry%20charges\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>tabbatar<\/strong><\/a> mana cewa karatu kyauta ne a duka jami\u2019o\u2019in tarayya. A ciki ne ma gwamnatin ta bayyana cewa abin da ake kira kudin makaranta yawanci kudi ne da ba dole ne a biya ba,&nbsp; ita kanta jami\u2019ar ke caja bisa la\u2019akari da irin bukatun da za ta cimma wajen gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, kamar kudin mafani da dakunan gwaji, yin rajista da dakunan kwana.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta ce kudaden ba dole ba ne, jami\u2019o\u2019in tarayyar kan <a href=\"https:\/\/unilag.edu.ng\/adjusted-obligatory-fees-for-new-and-returning-undergraduate-students\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>kira su dole<\/strong><\/a> ta kuma ce tilas ne kowa ya biya wannan adadin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kamata a jaddada cewa gwamnatin Najeriya ta yi magana a kan jami\u2019o\u2019i mallakar gwamnatin tarayya ne kadai a matsayin wadanda ba\u2019a biya, ba ta hada da makarantun da ke karkashin jihohi ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bincike ya nuna cewa daliban da ke makarantun jihohi na biyan kudade daban-daban wadanda tilas ne kuma dan haka ya sabawa bayanin da aka yi na cewa kyauta ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Alal misali, Makarantun sakandare na gwamnatin tarayya wadanda ake kira Federal Government Colleges da turanci, bai kamata ana biya ba. AMma shi ma duk da haka <a href=\"https:\/\/drive.google.com\/file\/d\/1mC_YqyXJupUMKJDR3kwyztTKTKK8fuZ6\/view?usp=drivesdk\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>a kan bukaci<\/strong><\/a> a biya kudin rigunan makaranta (na sabbin dalibai) litattafai da takardu, da kudaden magunguna da na wutar lantarki da sauransu. Kudin da daliban&nbsp; <a href=\"https:\/\/radionigeria.gov.ng\/2023\/07\/21\/fg-increases-unity-schools-tuition-to-n100000\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>da ke yin na kwana<\/strong><\/a> a ire-iren wadannan makarantun ya ma karu daga&nbsp; N45,000 zuwa&nbsp; N100,000 a shekarar&nbsp; 2023.&nbsp;&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A waje guda kuma,&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.pulse.ng\/articles\/lifestyle\/tuition-free-federal-technical-colleges-nigeria-2025092820195421976\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>ba da dadewan nan ba ne<\/strong><\/a> gwamnatin Najeriya ta sanar cewa Kwalejojin Fasaha na Tarayyar da ke kasar ba kyauta ne kadai su ke ba, gwamnatin za ta ma kara da biyan duk wani karin kudin da za\u2019a bukaci iyaye su biya. Sai dai wadanda ke yin na kwana tilas ne su kawo kayayyakin da suke bukata dan tsayawa a makarantar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A fanin makarantun firamare kuma, binciken ya nuna cewa makarantun baki daya kyauta ne, sai dai akwai wadansu <a href=\"https:\/\/www.icirnigeria.org\/how-hidden-fees-contribute-to-out-of-school-children-in-fct\/?tztc=1\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>kudaden<\/strong><\/a> wadanad suka hada da kudin PTA, kudin bunkasa makaranta, rigunan makaranta da sauran wasu makamantan wadannan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wadannan kudaden ne ake kira kudin makaranta tare da wani dan wanda ake caja dan kula da abubuwan more rayuwa a makarantar. Duk wani kudin makaranta a makarantun sakandare da jami\u2019i\u2019o\u2019i ne ke biya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yayin da makarantun tarayya na firamare da sakandare da na jami\u2019a kyauta ne su ma akwai \u2018yan wadansu kudaden da ake bukatansu su biya wadanda idan har ba su biya ma za su fiskanci matsala.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Alal misali, daliban da ke&nbsp; <a href=\"https:\/\/uniben.edu\/admissionrequirements.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Jami&#8217;o&#8217;in Tarayya<\/strong><\/a> dole su biya kudin samun damar shiga kafin a amince da su a matsayin daliban makarantar. Wadanda <a href=\"https:\/\/guardian.ng\/features\/debate-intensifies-over-acceptance-fees-in-varsities\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>suka gaza biya <\/strong><\/a>kafin ranar da aka sa, ko a kara musu yawan kudin da za su biya ko kuma su rasa gurbinsu a makarantar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da cewa idan har aka kwatanta yawan kudin makarantun jami\u2019a a Najeriya da sa\u2019o\u2019insu na kasashen waje na Najeriyar ya fi rangwame, makarantun jami\u2019a a Najeriya ba su samun irin tallafin da suke bukata.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A shekarar 2025, kasafin kudin Najeriyar da akaware wa fannin ilimi ya kasance kashi 6.4 cikin 100 na jimilar nera&nbsp; <a href=\"https:\/\/niser.gov.ng\/v2\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/2025-FGN-PROPOSED-BUDGET-NISER-BRIEF.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>tiriliyan<\/strong><\/a> din da aka yi. Wannan na nuna cewa kudin ya ragu daga kashi 8.21 cikin 100n da aka ware a shekarar 2024.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/eksu.edu.ng\/wp-content\/uploads\/2021\/08\/PAYABLE-FOR-2020-2021.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Jami&#8217;o&#8217;in Jihohi<\/strong><\/a>, Makarantun Foliteknik da kwalejojin ilimi duk suna cajan kudi&nbsp; amma <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/1BSutAkRZX\/?mibextid=wwXIfr\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>salon biyan kan banbanta<\/strong><\/a> wa mazauna jihohin da baki, kamar yadda muka gani a <a href=\"http:\/\/odlri.lasu.edu.ng\/home\/wp-content\/uploads\/2019\/04\/odlri_schedule_of_fees.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>nan<\/strong><\/a>, <a href=\"https:\/\/edocoe.edu.ng\/fees-schedule\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>nan<\/strong><\/a>, <a href=\"https:\/\/kwasued.edu.ng\/tuition\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>nan<\/strong><\/a> da <a href=\"https:\/\/www.bsum.edu.ng\/w3\/dwnloads\/pgUserCharges.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>nan<\/strong><\/a>.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" alt=\"Is education entirely free in government-owned schools in Nigeria?\" src=\"blob:http:\/\/dubawa.org\/dir\/d7f779c6-8a46-4768-a3f5-899f652299b0\" width=\"602\" height=\"476\" title=\"\"><img decoding=\"async\" alt=\"Is education entirely free in government-owned schools in Nigeria?\" src=\"blob:http:\/\/dubawa.org\/dir\/3bc67def-d044-4493-ba63-ff78df64d6c5\" width=\"602\" height=\"428\" title=\"\">hoton kudin makarantar da aka biya a <em>ABSU&nbsp;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>A Karshe<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da\u2019awar cewa makarantun gwamnati a kowani mataki kyauta ne a Najeriya yaudara ce! An dai rage yawan kudin makaranta a na gwamnati amma duk da haka akwai wani kudin da ake karba wadanda dole ne sai an biya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin X @TemidayoOniosun, kwananan nan ya yi\u00a0 da&#8217;awar cewa makarantun firamare, sakandare da jami\u2019a duk kyauta ne idan dai na gwamnati ne. Hukunci: Yaudara ce! Yayin da makarantun firamare, sakandare da ma wasu jami\u2019o\u2019in da ke karkashin gwamnati ba su bukatar kudin makaranta, akwai wadansu kudaden da tilas ne kowani dalubi ya biya kuma idan ba haka ba a hana su karbar darassi. Cikakken bayani Ranar 15 ga watan Satumba makarantun firamare da sakandare a Najeriya suka dawo makaranta daga dogon hutu. Bayan nan ne wasu iyaye suka shiga kafofin sada zumunta suna korafin tsadar farashin kudin makaranta, takardu da dai sauran abubuwna da ake bukata dan zuwa makarantar. Wannan kuma ya biyo bayan korafe-korafen da dama can daliban jami\u2019o\u2019i su ma suka yi a kafofin sada zumunta su ma kan tsadar farashin kudin makaranta, wasu daga cikin masu amfani da shafukan ma har sun yi magana taka mai mai a kan Jami\u2019ar Ilori wadda ita ma ta kara kudin makaranta na sabuwar shekarar ta 2025\/2026 da za\u2019a shiga yanzu. Wannan mai amfani da shafin @theiyanuoluwa cewa ya yi, \u201cJami\u2019ar Ilori ta fara zama jami\u2019a mai zaman kanta. Kudin makarantar ya karu sosai irin na fitan hankali.\u201d Wani shi ma mai amfani da shafin da sunan @Uilgist cewa ya yi, \u201cLABARI DA DUMI-DUMI! Daliban jami\u2019ar Ilori sun fashe da kuka ganin yadda wasu tilsa su daina zuwa makaranta saboda farashin da aka kara. Daliban da ke dawowa zasu biya sama da dubu 200 ya yin da wadanda ke shekara ta karshe kuma za\u2019a caje su su kuma sama da dubu 100.\u201d A wani&nbsp; cigaban kuma, Kungiyar dalibai na Student Union a jami\u2019ar Benin ta fitar da sanarwar da ke karyata da\u2019awar cewa akwai dalibai 5,000 din da ba su biya kudin makaranta ba wadanda za\u2019a hana su rubuta jarabawa. Yayin da ya ke tsokaci kan fannin ilimi a Najeriya, mai amfani da shafin X @TemidayoOniosun ya yi zargin cewa ilimin firamare da sakandare a makarantun gwamnati kyauta ne, ya kuma kara wa iyaye karfin gwiwa da su sa yaransu a makarantun gwamnati idan har ba za su iya biyan na kudin ba. Wannan tsokacin na sa martani ne ga wani&nbsp; batun da &nbsp;@DebbieOA ta wallafa, wadda ta ce yawancin iyalai da kyar su ke iya biyan kudin makarantar yaransu, sa\u2019annan dan jaddada wannan ra\u2019ayin na ta ta yi amfani da wani labarin da ya dauki hankali na wasu wasu masu yara biyar wadanda suka gaza biya musu kudin makaranta. Bisa la\u2019akari da wannan batun ne, Temidayo ya yi bayanin cewa , \u201cmakarantun firamare, sakandare da jami\u2019a duk kyauta ne a Najeriya. Duk wanda ba zai iya biyan na kudin ba ya je na gwamnati.\u201d To sai dai da yawa daga cikin masu amfani da shafin ba su amince da wannan tsokacin na shi ba kums su ma sun bayyana ra\u2019ayoyinsu dangane da abubuwan da suka faru da su a makarantun gwamnati. Samun ilimin boko na cigaba da kasancewa batu mai daukar hankali tsakanin masu ruwa da tsaki a \u2018yan shekarun baya-bayan nan, musamman bayan wani rahoton da ya nuna cewa a Najeriya kusan yara&nbsp; miliyan 18 ba su zuwa makaranta.&nbsp; Ganin mahimmancin da batun ke da shi ne ya s, DUBAWA tantance wannan bayani na mai amfani da shafin X dan gano gaskiyar lamarin. Tantancewa Binciken da muka yi da muhimman kalmomi ya bayyana mana wani rahoton da fadar shugaban kasa ta&nbsp; wallafa a shekarar 2023 wanda ya tabbatar mana cewa karatu kyauta ne a duka jami\u2019o\u2019in tarayya. A ciki ne ma gwamnatin ta bayyana cewa abin da ake kira kudin makaranta yawanci kudi ne da ba dole ne a biya ba,&nbsp; ita kanta jami\u2019ar ke caja bisa la\u2019akari da irin bukatun da za ta cimma wajen gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, kamar kudin mafani da dakunan gwaji, yin rajista da dakunan kwana. Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta ce kudaden ba dole ba ne, jami\u2019o\u2019in tarayyar kan kira su dole ta kuma ce tilas ne kowa ya biya wannan adadin. Ya kamata a jaddada cewa gwamnatin Najeriya ta yi magana a kan jami\u2019o\u2019i mallakar gwamnatin tarayya ne kadai a matsayin wadanda ba\u2019a biya, ba ta hada da makarantun da ke karkashin jihohi ba. Bincike ya nuna cewa daliban da ke makarantun jihohi na biyan kudade daban-daban wadanda tilas ne kuma dan haka ya sabawa bayanin da aka yi na cewa kyauta ne. Alal misali, Makarantun sakandare na gwamnatin tarayya wadanda ake kira Federal Government Colleges da turanci, bai kamata ana biya ba. AMma shi ma duk da haka a kan bukaci a biya kudin rigunan makaranta (na sabbin dalibai) litattafai da takardu, da kudaden magunguna da na wutar lantarki da sauransu. Kudin da daliban&nbsp; da ke yin na kwana a ire-iren wadannan makarantun ya ma karu daga&nbsp; N45,000 zuwa&nbsp; N100,000 a shekarar&nbsp; 2023.&nbsp;&nbsp; A waje guda kuma,&nbsp; ba da dadewan nan ba ne gwamnatin Najeriya ta sanar cewa Kwalejojin Fasaha na Tarayyar da ke kasar ba kyauta ne kadai su ke ba, gwamnatin za ta ma kara da biyan duk wani karin kudin da za\u2019a bukaci iyaye su biya. Sai dai wadanda ke yin na kwana tilas ne su kawo kayayyakin da suke bukata dan tsayawa a makarantar. A fanin makarantun firamare kuma, binciken ya nuna cewa makarantun baki daya kyauta ne, sai dai akwai wadansu kudaden wadanad suka hada da kudin PTA, kudin bunkasa makaranta, rigunan makaranta da sauran wasu makamantan wadannan. Wadannan kudaden ne ake kira kudin makaranta tare da wani dan wanda ake caja dan kula da abubuwan more rayuwa a makarantar. Duk wani kudin makaranta a makarantun sakandare da jami\u2019i\u2019o\u2019i ne ke biya. Yayin da makarantun tarayya na firamare da sakandare da na jami\u2019a kyauta ne su ma akwai \u2018yan wadansu kudaden da ake bukatansu su biya wadanda idan har ba su biya ma za su fiskanci matsala. Alal misali, daliban da ke&nbsp; Jami&#8217;o&#8217;in Tarayya dole su biya kudin samun damar shiga kafin a amince da su a matsayin daliban makarantar. Wadanda suka gaza biya kafin ranar da<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":24927,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"default","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[1920],"class_list":["post-25035","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-6vN","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":1920,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"elizabeth-ogunbamowo","display_name":"Elizabeth Ogunbamowo","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/7043a07f4ff292637cb75d13c8340fa9afb2ec87eceec4eedd980077c8bfd304?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/10\/Screenshot-2025-10-10-at-2.56.55-PM.png?fit=391%2C260&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/25035","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=25035"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/25035\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":25036,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/25035\/revisions\/25036"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/24927"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=25035"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=25035"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=25035"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=25035"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=25035"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}