{"id":25498,"date":"2025-10-29T12:30:27","date_gmt":"2025-10-29T11:30:27","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=25498"},"modified":"2025-10-29T12:30:30","modified_gmt":"2025-10-29T11:30:30","slug":"babu-sheda-cewa-zamafara-ta-tura-askarawa-500-don-yakar-yanfashin-daji-su-kadai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/babu-sheda-cewa-zamafara-ta-tura-askarawa-500-don-yakar-yanfashin-daji-su-kadai\/","title":{"rendered":"Babu sheda cewa Zamafara ta tura Askarawa 500 don yakar \u2018yanfashin daji su kadai"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Wata wallafa a shafin Facebook (<a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/v\/1HuNvDQPXn\/?mibextid=wwXIfr\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>claims<\/strong><\/a>) ta yi da\u2019awar cewa gwamnan\u00a0 Zamfara ya tura \u2018yanbijilanti da aka fi sani da Askarawa 500 don shawo kan matsalar tsaro ta hanyar \u201c shiga yaki da \u2018yanfashin daji ko \u2018yanbindiga maimakon jira sai sun kawo hari.\u2019\u2019<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"56\" data-attachment-id=\"20029\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/did-uba-fraudulently-move-n1-9-billion-belonging-to-pension-fund-administrator\/insufficient-evidence-1-8\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/INSUFFICIENT-EVIDENCE-1.png?fit=132%2C56&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,56\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"INSUFFICIENT-EVIDENCE-1\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/INSUFFICIENT-EVIDENCE-1.png?fit=132%2C56&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/INSUFFICIENT-EVIDENCE-1.png?resize=132%2C56\" alt=\"\" class=\"wp-image-20029\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#db850a\">Hukunci: Babu isassun shedu, duk da cewa gaskiya ne an kaddamar da Askarawan a watan Janairu, 2024 a matsayin dakaru daga bangaren gwamnatin jiha wadanda za su mara baya ga sojoji da \u2018yansanda, babu wata sheda da ta nuna gwamnan Zamfara\u00a0 ya tura \u2018yan bijilanti 500 da za su je yakar \u2018yan fashin daji su kadai.\u00a0<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Sako<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Jihar Zamfara Arewa maso Yammacin Najeriya ta kswashe kimanin shekaru 10 tana fama da hare-hare (<a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/regional\/nwest\/755538-terrorists-attack-zamfara-community-kill-five-burn-houses.html?tztc=1\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>ruthless armed attacks<\/strong><\/a>) dalilin ayyukan \u2018yanbindiga wadanda ayyukansu ya bunkasa ya zama na \u2018yanta\u2019adda. Guggun \u2018yanbindiga kan afkawa gari ko su tare hanya ko su kama mutane su nemi kudaden fansa. Tun daga shekarar 2011 tarin&nbsp; (<a href=\"https:\/\/www.vanguardngr.com\/2021\/04\/banditry-its-hausa-fulani-war-zamfara-traces-origin-of-hostilities\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>waves<\/strong><\/a>)&nbsp; hare-hare irin wadannan sun sanya mutane da dama sun kauracewa muhallansu wasu kuma da dama an halaka su.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hukumomin jinkai sun yi kiyasi (<a href=\"https:\/\/reliefweb.int\/report\/nigeria\/voices-internally-displaced-persons-zamfara-state-nigeria-intention-survey-august-2024\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>estimate<\/strong><\/a>) cewa akwai dubban al\u2019umma da aka raba su da muhallansu(<a href=\"https:\/\/www.msf.org\/run-violence-nigeria\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>displaced<\/strong><\/a>) a sassa daban-daban na jihar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da shafin Facebook <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/Denglish88?__tn__=-UC\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>@D English Alhaji<\/strong><\/a>, yayi da\u2019awar cewa gwamnatin jihar <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/v\/1Gmyeduegr\/?mibextid=wwXIfr\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>&nbsp;(Zamfara State) <\/strong><\/a>ta amince da tura \u2018yan bijilanti&nbsp; ko \u2018yankato da gora 500 da za su tunkari \u2018yanfashin daji.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A wani bidiyo ya nuna wani mutum na cewa \u201cGwamnatin Zamfara ta yi nata bangare a kokari na tunkarar matsalar tsaro da jihar ke fuskanta. Ana kiransu da suna Askarawa, ko kuma masu yaki da matsalar tsaro a jihar inda suke gudanar da aikinsu a jihar ta Zamfara. Ba suna jira ba ne a kawo hari kafin su yi abin da ya dace, yanzu suna tunkarar \u2018yanbindigar ne.\u201d Ya yaba da kokarin da suke yi inda yace dama Najeriya irin wannan kokari take fatan gani.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&nbsp;Bidiyon na nuna mutane&nbsp; akan babura wadanda mai bayanin yace su kusan 500 ne wadanda gwamnatin ta basu ababen hawan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya zuwa ranar 25 ga Satumba,2025 wannan bidiyo ya samu wadanda suka kalla 69,000 (views), da wadanda suka sake yadawa 155 (shares) da wadanda suka yi tsokaci 4,300 (comments).<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun duba tattaunawa da masu amfani da shafin na Facebook ke yi kan wannan batu ga kuma abin da wasu daga cikinsu ke cewa:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/king.bass.52?comment_id=Y29tbWVudDoxNDYzMTkyNjkyMDc2NzcyXzc5MTc1MDY2MzgxMzQwMA%3D%3D&amp;__tn__=R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>@Kingston Samuel <\/strong><\/a>ya rubuta cewa , \u201c Idan lamura suka kwanta, suka kuma tarwatsa gungun, ina fatan gwamnatin jihar Zamafara za ta ba da bayani na dukkanin kayan aiki da aka ba wa \u2018yanbijilantin.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/chibuzor.patrick.586352?comment_id=Y29tbWVudDoxNDYzMTkyNjkyMDc2NzcyXzgwNDUxMTkzNTM0OTcyNQ%3D%3D&amp;__tn__=R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>@Chibuzor Patrick<\/strong><\/a> yace, \u201c\u2018Yansiyasa marasa amfani nan ba da dadewa ba za su bayyana bukatar ganin gwamnatin Zamafara ta janye mutanenta suna da\u2019awar cewa \u2018yanbindigar sun tuba.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/moor.moor.900014?comment_id=Y29tbWVudDoxNDYzMTkyNjkyMDc2NzcyXzE5MDY3NDc4NzY1NTg4NjM%3D&amp;__tn__=R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>@Moor Moor<\/strong><\/a> yayi tsokaci da cewa \u201cBa da wata-wata ba za su mika wadannan babura ga \u2018yanbindigar.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/ralo.ralo.1671?comment_id=Y29tbWVudDoxNDYzMTkyNjkyMDc2NzcyXzc5MzE1MDUyOTc2NjAyOQ%3D%3D&amp;__tn__=R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>@Brazy Slime <\/strong><\/a>na mai ra\u2019ayin\u201c Su tabbatar da ganin cewa babu \u2018yanfulani a cikin mayakan, idan ba haka ba za a yi nasara a kansu, zai zama kunar bakin wake idan ya kasance akwai Fulani a wannan tafiya, suna nan a cikin sojoji ma na kasa da na sama da na ruwa suna kawo cikas.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wasu da dama cikin masu tsokaci na nuna shakkunsu a dangane wannan da\u2019awa. Destiny Charles yace shin kana Zamafara ne ka tabbatar da wannan da\u2019awa ko dai kawai kana zuba surutu ne mara amfani. Shi kuwa <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/nonso.ogbonna.2025?comment_id=Y29tbWVudDoxNDYzMTkyNjkyMDc2NzcyXzc1MjMzNTg2Nzc5ODIwMw%3D%3D&amp;__tn__=R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>@Nonso Ogbonna<\/strong><\/a> yace \u201cdan\u2019uwa a ina kake samu wadannan bayanai?&nbsp; Ni ina zaune ne a Gusau jihar Zamfara. \u201c&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ganin irin wannan da\u2019awa da irin tsokaci da mutane ke yi hakan ya sanya DUBAWA ganin wajibcin nitsawa da bincike don tantance wannan da\u2019awa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta fara gudanar da bincikenta ta hanayar amfani da wasu kalmomi&nbsp; daga abin da aka wallafa a shafin na Facebook alal misali \u201cGwamnan Zamfara\u201d da \u201cmasu yakar \u2018yanbindiga\u201d da \u201cdakarun Askarawa\u201d abin da binciken Google ya gano ya hadar da wasu da\u2019awowin irin wannan a shafukan X da Facebook.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani a shafin X, <a href=\"https:\/\/x.com\/futurepotn\/status\/1966812698970034405?s=46\"><strong>@Future President<\/strong><\/a>, a ranar 13 gacwatan Satumba,2025 ya yada cewa \u201cGwamna Dauda Lawal ya fara lugude kan \u2018yanbindiga inda ake amfdani da dakarun da jihar ta samar na Askarawa da \u2018yankato da gora CJTF.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A shafin&nbsp; Facebook ma, (<a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/profile.php?id=100000709738705&amp;sk=reels_tab&amp;__cft__[0]=AZX0xq3xCqFIflZUj4yUbYXJAEKDufOEoaqpGhnvax3q5zd52kGwzUrDePk8uAtI0SinStZv5k4pJeaEUuLdCbNNZZo7HGdpRPcWU5Obhj5V2ZRzms_JNxrQ97NP4WdEoPKbd3n-VuwUPRHLPsIJmqnURLsuuLn_mN5kZqexNxaXGg&amp;__tn__=-]F\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>@Shehu Umar<\/strong><\/a>) ya yada labarin irin wannan (<a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/share\/v\/17dmAK3LSY\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>similar<\/strong><\/a>) a dai wannan rana.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Domin tantance bidiyon ta hanayar amfani da dabarun gano asalin bidiyo a Google da Yandex , babu wata kafa da za a ce ga asalin inda aka samo bidiyon, abin da kawai ake gani shine wannan dai bidiyo da aka wallafa a shafin na Facebook ko na X, kamar dai yadda aka gani a bincike ta hanayar amfani da muhimman kalmomi da aka yi a Google tun da fari, duka dai abu guda ake gani da taken labarin iri daya. Wannan ya nuna cewa wannan bidiyo tun da fari da aka gani a kafafan sada zumuntar guda biyu su kenan babu wata kafa a hukumance ko wata kafar yada labarai sahihiya da ta yi labarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da muka kara bincikawa sai muka ga cewa akwai kafa ta hukuma da ta nuna yadda a ranar 31 ga Janairu,2024 Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar (<a href=\"https:\/\/zamfara.gov.ng\/2024\/06\/15\/gov-lawal-decorates-20-gallants-zamfara-community-protection-guards-pledges-full-support\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>launched<\/strong><\/a>) da rundunar ba da kariya ga al\u2019umma ta Community Protection Guards (CPG), wadanda aka fi sani da Askarawa, Kafafan yada labaran sun bayyana CPG&nbsp; a matasayin rundunar tsaron da ta samu goyo bayan gwamnatin jiha da nufin tallafawa jami\u2019ai na gwamnatin tarayya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Karin bayani a yayin kaddamarwar jami\u2019an su 2,645 ne da suka kammala (<a href=\"https:\/\/www.vanguardngr.com\/2024\/02\/banditry-in-zamfara-gov-lawal-launches-community-protection-guards-to-fight-terrorism\/amp\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>completed<\/strong><\/a>) samun horo na farko&nbsp; inda aka bayyana za a samar da karin wasu inda ake sa ran samar da mambobi 5,200, wanda yawansu ma yafi adadin da aka bayyana a wallafar ta Facebook.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wasu rahotannin kuma sun bayyana cewa gwamnan jihar ta Zamfara Dauda Lawal ya bada motoci da babura ga jami\u2019an tsaro na cikin gida, A ranar 16 ga Agusta,2022 jami\u2019an gwamnatin jihar sun raba ( <a href=\"https:\/\/www.tvcnews.tv\/zamfara-govt-donates-20-patrol-vehicles-1500-motorcycles-others-to-security-guards\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>distributed<\/strong><\/a>) babura 1,500 da motocin sintiri 20 don samar da tsaro a yankunan al\u2019umma, haka kuma a ranar 13 ga watan Mayu,2025&nbsp; gwamnan jihar ya mika (<a href=\"https:\/\/punchng.com\/zamfara-gov-donates-vehicles-to-security-agencies-unveils-mass-transit\/?amp\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>handed<\/strong><\/a>) sama da motoci 140 zuwa ga huumomin tsaro.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Duk da cewa wannan na nuna irin kokarin gwamnati na bunkasa tsaro, babu wata sheda da ta nuna cewa an yi wanann rarrabawa a baya-bayan nan, kamar yadda masu amfani da shafukan na sada zumunta suka nunar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A karshe mun gano cewa su jami\u2019an na CPG suna aiki ne (<a href=\"https:\/\/www.thisdaylive.com\/2024\/02\/07\/cooperate-with-cpg-personnel-zamfara-gov-urges-heads-of-security-agencies\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>works<\/strong><\/a>) tare da sojoji da \u2018yansanda a wurare da ke da wahalar sha\u2019ani, wannan yasa suke aiki tare a wurare irin su dajin Sunke inda aka ga dakarun&nbsp; na CPG suna gudanar da ayyukansu a wuraren da \u2018yanbindigar (<a href=\"https:\/\/zagazola.org\/index.php\/breaking-news\/bandits-kill-one-cpg-member-two-hunters-in-zamfara-village-ambush\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>bandits<\/strong><\/a>) ke buya. Kamar yadda me fadin ke cewa gwamnati ke nuna yadda za su yi aiki wato cewa \u201cku karbi aikin ku danna cikin dajin\u201d wato su kadai ba haka bane.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\"><strong>Bayanin Mahukunta<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta tuntubi gwamnatin jihar Zamafara ta hanyar adireshinta na e-mail wato&nbsp; (<a href=\"mailto:zitda@zamfara.gov.ng\">zitda@zamfara.gov.ng<\/a>) amma har zuwa lokacin kammala wannan aikin gano bayanan gaskiya babu wata amsa daga bangaren na gwamnati.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Haka kuma ita ma lambar da ke kan shafin intanet na gwamnatin mun tuntuba babu amsa, sai kuma a karshe muka tuntubi jami\u2019in hulda da jama\u2019a a rundunar \u2018yansanda ta jihar Zamfara don neman karin bayani, shima ana tsaka da tattaunawa da shi ya katse tattaunawar, kuma duk yunkuri na sake kiransa babu amsa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">A <strong>Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Binciken DUBAWA ya tabbatar da cewa akwai dakarun na Askarawa ko CPG wadanda aka kafa su a watan Janairu,2024 a kokarin gwamnatin jihar ta Zamafa na tallafawa ayyukan tsaro na jami\u2019an soja da \u2018yansanda, sai dai babu wata sheda da ta nuna cewa gwamnati ta ba su umarni su je su kai wa \u2018yanbindiga hari su kadai ba tare da soja ko \u2018yan sanda ba.\u00a0\u00a0<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wata wallafa a shafin Facebook (claims) ta yi da\u2019awar cewa gwamnan\u00a0 Zamfara ya tura \u2018yanbijilanti da aka fi sani da Askarawa 500 don shawo kan matsalar tsaro ta hanyar \u201c shiga yaki da \u2018yanfashin daji ko \u2018yanbindiga maimakon jira sai sun kawo hari.\u2019\u2019 Hukunci: Babu isassun shedu, duk da cewa gaskiya ne an kaddamar da Askarawan a watan Janairu, 2024 a matsayin dakaru daga bangaren gwamnatin jiha wadanda za su mara baya ga sojoji da \u2018yansanda, babu wata sheda da ta nuna gwamnan Zamfara\u00a0 ya tura \u2018yan bijilanti 500 da za su je yakar \u2018yan fashin daji su kadai.\u00a0 Cikakken Sako Jihar Zamfara Arewa maso Yammacin Najeriya ta kswashe kimanin shekaru 10 tana fama da hare-hare (ruthless armed attacks) dalilin ayyukan \u2018yanbindiga wadanda ayyukansu ya bunkasa ya zama na \u2018yanta\u2019adda. Guggun \u2018yanbindiga kan afkawa gari ko su tare hanya ko su kama mutane su nemi kudaden fansa. Tun daga shekarar 2011 tarin&nbsp; (waves)&nbsp; hare-hare irin wadannan sun sanya mutane da dama sun kauracewa muhallansu wasu kuma da dama an halaka su. Hukumomin jinkai sun yi kiyasi (estimate) cewa akwai dubban al\u2019umma da aka raba su da muhallansu(displaced) a sassa daban-daban na jihar. Wani mai amfani da shafin Facebook @D English Alhaji, yayi da\u2019awar cewa gwamnatin jihar &nbsp;(Zamfara State) ta amince da tura \u2018yan bijilanti&nbsp; ko \u2018yankato da gora 500 da za su tunkari \u2018yanfashin daji. A wani bidiyo ya nuna wani mutum na cewa \u201cGwamnatin Zamfara ta yi nata bangare a kokari na tunkarar matsalar tsaro da jihar ke fuskanta. Ana kiransu da suna Askarawa, ko kuma masu yaki da matsalar tsaro a jihar inda suke gudanar da aikinsu a jihar ta Zamfara. Ba suna jira ba ne a kawo hari kafin su yi abin da ya dace, yanzu suna tunkarar \u2018yanbindigar ne.\u201d Ya yaba da kokarin da suke yi inda yace dama Najeriya irin wannan kokari take fatan gani. &nbsp;Bidiyon na nuna mutane&nbsp; akan babura wadanda mai bayanin yace su kusan 500 ne wadanda gwamnatin ta basu ababen hawan. Ya zuwa ranar 25 ga Satumba,2025 wannan bidiyo ya samu wadanda suka kalla 69,000 (views), da wadanda suka sake yadawa 155 (shares) da wadanda suka yi tsokaci 4,300 (comments). Mun duba tattaunawa da masu amfani da shafin na Facebook ke yi kan wannan batu ga kuma abin da wasu daga cikinsu ke cewa: @Kingston Samuel ya rubuta cewa , \u201c Idan lamura suka kwanta, suka kuma tarwatsa gungun, ina fatan gwamnatin jihar Zamafara za ta ba da bayani na dukkanin kayan aiki da aka ba wa \u2018yanbijilantin.\u201d @Chibuzor Patrick yace, \u201c\u2018Yansiyasa marasa amfani nan ba da dadewa ba za su bayyana bukatar ganin gwamnatin Zamafara ta janye mutanenta suna da\u2019awar cewa \u2018yanbindigar sun tuba.\u201d @Moor Moor yayi tsokaci da cewa \u201cBa da wata-wata ba za su mika wadannan babura ga \u2018yanbindigar.\u201d @Brazy Slime na mai ra\u2019ayin\u201c Su tabbatar da ganin cewa babu \u2018yanfulani a cikin mayakan, idan ba haka ba za a yi nasara a kansu, zai zama kunar bakin wake idan ya kasance akwai Fulani a wannan tafiya, suna nan a cikin sojoji ma na kasa da na sama da na ruwa suna kawo cikas.\u201d Wasu da dama cikin masu tsokaci na nuna shakkunsu a dangane wannan da\u2019awa. Destiny Charles yace shin kana Zamafara ne ka tabbatar da wannan da\u2019awa ko dai kawai kana zuba surutu ne mara amfani. Shi kuwa @Nonso Ogbonna yace \u201cdan\u2019uwa a ina kake samu wadannan bayanai?&nbsp; Ni ina zaune ne a Gusau jihar Zamfara. \u201c&nbsp; Ganin irin wannan da\u2019awa da irin tsokaci da mutane ke yi hakan ya sanya DUBAWA ganin wajibcin nitsawa da bincike don tantance wannan da\u2019awa. Tantancewa DUBAWA ta fara gudanar da bincikenta ta hanayar amfani da wasu kalmomi&nbsp; daga abin da aka wallafa a shafin na Facebook alal misali \u201cGwamnan Zamfara\u201d da \u201cmasu yakar \u2018yanbindiga\u201d da \u201cdakarun Askarawa\u201d abin da binciken Google ya gano ya hadar da wasu da\u2019awowin irin wannan a shafukan X da Facebook. Wani a shafin X, @Future President, a ranar 13 gacwatan Satumba,2025 ya yada cewa \u201cGwamna Dauda Lawal ya fara lugude kan \u2018yanbindiga inda ake amfdani da dakarun da jihar ta samar na Askarawa da \u2018yankato da gora CJTF.\u201d A shafin&nbsp; Facebook ma, (@Shehu Umar) ya yada labarin irin wannan (similar) a dai wannan rana. Domin tantance bidiyon ta hanayar amfani da dabarun gano asalin bidiyo a Google da Yandex , babu wata kafa da za a ce ga asalin inda aka samo bidiyon, abin da kawai ake gani shine wannan dai bidiyo da aka wallafa a shafin na Facebook ko na X, kamar dai yadda aka gani a bincike ta hanayar amfani da muhimman kalmomi da aka yi a Google tun da fari, duka dai abu guda ake gani da taken labarin iri daya. Wannan ya nuna cewa wannan bidiyo tun da fari da aka gani a kafafan sada zumuntar guda biyu su kenan babu wata kafa a hukumance ko wata kafar yada labarai sahihiya da ta yi labarin. Da muka kara bincikawa sai muka ga cewa akwai kafa ta hukuma da ta nuna yadda a ranar 31 ga Janairu,2024 Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar (launched) da rundunar ba da kariya ga al\u2019umma ta Community Protection Guards (CPG), wadanda aka fi sani da Askarawa, Kafafan yada labaran sun bayyana CPG&nbsp; a matasayin rundunar tsaron da ta samu goyo bayan gwamnatin jiha da nufin tallafawa jami\u2019ai na gwamnatin tarayya. Karin bayani a yayin kaddamarwar jami\u2019an su 2,645 ne da suka kammala (completed) samun horo na farko&nbsp; inda aka bayyana za a samar da karin wasu inda ake sa ran samar da mambobi 5,200, wanda yawansu ma yafi adadin da aka bayyana a wallafar ta Facebook. Wasu rahotannin kuma sun bayyana cewa gwamnan jihar ta Zamfara Dauda Lawal ya bada motoci da babura ga jami\u2019an tsaro na cikin gida, A ranar 16 ga Agusta,2022 jami\u2019an gwamnatin jihar sun raba ( distributed) babura 1,500 da motocin sintiri 20 don samar da tsaro a yankunan al\u2019umma, haka kuma a ranar 13 ga watan Mayu,2025&nbsp; gwamnan jihar ya mika (handed) sama da motoci 140 zuwa ga huumomin<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":22818,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"default","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4069],"class_list":["post-25498","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-6Dg","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4069,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"rejoice-taddy","display_name":"Rejoice Taddy","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/05\/Zamfara-state-map.jpg?fit=653%2C365&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/25498","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=25498"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/25498\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":25499,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/25498\/revisions\/25499"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/22818"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=25498"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=25498"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=25498"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=25498"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=25498"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}