{"id":25722,"date":"2025-11-08T03:06:13","date_gmt":"2025-11-08T02:06:13","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=25722"},"modified":"2025-11-08T03:10:00","modified_gmt":"2025-11-08T02:10:00","slug":"anambra2025-yadda-masu-jefa-kuria-za-su-iya-kaucewa-bayanan-karya-a-rumfunan-zabe","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/anambra2025-yadda-masu-jefa-kuria-za-su-iya-kaucewa-bayanan-karya-a-rumfunan-zabe\/","title":{"rendered":"#Anambra2025: Yadda masu jefa kuri\u2019a za su iya kaucewa bayanan karya a rumfunan zabe"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wayewan garin 8 ga watan Nuwamba ne masu jefa kuri\u2019a a jihar Anambara za su nufi rumfunan zabe dan zaban sabon gwamnan.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A lokutan zabe a Najeriya da sauran kasashen duniya, akwai <a href=\"http:\/\/dubawa.org\/dir\/viral-election-related-disinformation-across-west-africa-in-2023\/\"><strong>salon<\/strong><\/a> yaudarar jama\u2019a da bayanann karyar da ya bulla. A zabukan baya, DUBAWA ta sanya ido wajen ganin yadda ake yada bayanan a yanar gizo-gizo dangane da yadda ma aka taba yin da\u2019awar wai wasu \u2018yan takara sun janye sa\u2019o\u2019i kadan kafin kaddamar da zaben.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sauran nau\u2019o\u2019in raba&nbsp; ire-iren wadannan bayanan sun hada da yada bayanan karya dangane da tashe-tashen hankula, wadanda burin kirkiro su shi ne yaudarar jama\u2019a wajen fargabar cewa akwai rashin daidaito a wasu yankunan. A wasu lokutan kuma, bayanan su kan yi kokarin rage<a href=\"http:\/\/dubawa.org\/dir\/2024ondoelection-understanding-disinformation-trends-and-targets-ahead-of-the-election\/\"><strong>kimar<\/strong><\/a> \u2018yan takara ne ko kuma hukumar zabe a idon jama\u2019a.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yayin da masu tantance gaskiyar bayanai ke iya karyata wadannan labaran,&nbsp; <a href=\"https:\/\/akademie.dw.com\/en\/is-fact-checking-effective-a-critical-review-of-what-works-and-what-doesnt\/a-55248257\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>tasirin<\/strong><\/a> tantance bayanai mai yiwuwa ba zai iya yaduwa kamar yadda bayanan karyar su ka riga suka yi ba saboda kamar yadda wani&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.bbc.com\/news\/technology-43344256\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>rahoton<\/strong><\/a> BBC ya bayyana, \u2018labaran bogi\u2019 sun fi yaduwa cikin sauri.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ko da shi ke domin yaki da yaduwar bayanan da ba daidai ba, DUBAWA ta samar da wata dabara wadda za ta iya taimakawa masu zabe a Anambara wajen tantance duk wata da\u2019awa da ta bulla ranar zaben.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>DUBAWA Chatbot ko kuma manhajar tattaunawa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ita wannan <a href=\"https:\/\/bit.ly\/4bJeKfd\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>DUBAWA Chatbot<\/strong><\/a> wata fasaha ce wadda za\u2019a iya amfani da ita cikin sauki. Ana iya samunta ne a manhajar WhatsApp kuma ta na iya tantance da\u2019awowi. Ta na iya amfanar masu jefa kuri\u2019a ranar zabe wajen tantance gaskiyar duk wani bayanin da suka yi shakkar sahihancin shi a yankunan zabensu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mahimman abubuwa biyar ne ake iya da wannan manhajar. Ta na iya taimakawa wajen tantance bayanai, samar da rahotannin batutuwan da aka riga aka tantance, kuma mutun na iya fahimtar burin DUBAWA, ayyukanta da abubuwan da ta ke darajawa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Masu amfani da manhajar kuma na yi mika korafinsu kan bayanan karya su kuma yi \u2018yan wasannin da za su kara mu su ilimin fahimtar na\u2019ura mai kwaikwayon dabi\u2019un dan adam wato AI.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ga wadanda ba su taba amfani da ita ba, ku na iya samunta idan kuka latsa wannan <a href=\"https:\/\/bit.ly\/4bJeKfd\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>makalar<\/strong><\/a>. Da zarar kuka rubuta gajeren sako kuka tura, ku na iya fara tattaunawa da ita domin nan da nan za ta gabatar da kanta ta kuma bayyana sharrudan amfani da ita.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayan haka za ta bayar da jerin ire-iren ayyukan da take yi ta bukaci mutun ya zabi abin da ya ke bukata a wannan lokacin. Idan har dan tantance gaskiyar da\u2019awa ne sai ku na iya zabar \u2018Tantance da\u2019awa\u2019<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Tantance Da\u2019awa:<\/strong> Da wannan masu amfani da shi na iya tantancewa ko karyata bayanan da ke da alaka da zaben. Alal misali, masu amfani da shafin na iya yin tambaya kamar haka, \u201cSu wane ne \u2018yan takara a zaben jihar Anambara?\u201d manhajar sakon za ta amasa tambayar da makalun rahotannin da ke dauke da cikakken bayani dangane da batun.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-gallery has-nested-images columns-default is-cropped wp-block-gallery-1 is-layout-flex wp-block-gallery-is-layout-flex\">\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img data-recalc-dims=\"1\" fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"683\" data-attachment-id=\"25692\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/anambra2025-how-voters-can-curb-misinformation-at-polling-units\/image-515\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-41.jpeg?fit=1170%2C780&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"1170,780\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"image\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-41.jpeg?fit=1024%2C683&amp;ssl=1\" data-id=\"25692\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-41.jpeg?resize=1024%2C683\" alt=\"\" class=\"wp-image-25692\" title=\"\" srcset=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-41.jpeg?resize=1024%2C683&amp;ssl=1 1024w, https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-41.jpeg?resize=300%2C200&amp;ssl=1 300w, https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-41.jpeg?resize=768%2C512&amp;ssl=1 768w, https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-41.jpeg?w=1170&amp;ssl=1 1170w\" sizes=\"(max-width: 1000px) 100vw, 1000px\" \/><\/figure>\n<\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hoton wata tattaunawar da aka yi da manhajar sakonnin<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Sami rahotannin bayanan da aka tantance da dumi-duminsu:<\/strong> Masu amfani da shafin da ke neman bayanai masu sahihanci dangane da zaben na iya amfani da wannan. Bayan sun latsa makalar, za ta fitar da duk sabbin rahotannin da aka yi dangane da zaben a babban shafin, daga nan masu amfani da shafin na iya bin makalun su ga sauran labaran.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Bayyana korafi kan da\u2019awa:<\/strong> Masu amfani da shafin na iya tura makalun duk wata da\u2019awa da suka gani a yanar gizo-gizo ranar zabe idan har suna bukatar karin bayani ko kuma sahihancin bayanan. Haka nan kuma ko da babu makalu, idan har akwai labari ko butun da ake so a tantance, ana iya rubuta korafin kai tsaye. Daga nan manhajar za ta sanar cewa ta tura batun ga wadanda ke tantance bayanan kuma za\u2019a yi bitar shi a ga ko ya cimma ka\u2019idoji gudanar da bincike.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"562\" height=\"1024\" data-attachment-id=\"25723\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/anambra2025-yadda-masu-jefa-kuria-za-su-iya-kaucewa-bayanan-karya-a-rumfunan-zabe\/image-523\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-46.jpeg?fit=562%2C1024&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"562,1024\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"image\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-46.jpeg?fit=562%2C1024&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-46.jpeg?resize=562%2C1024\" alt=\"\" class=\"wp-image-25723\" title=\"#Anambra2025: How voters can curb misinformation at polling units 3\" srcset=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-46.jpeg?w=562&amp;ssl=1 562w, https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-46.jpeg?resize=165%2C300&amp;ssl=1 165w\" sizes=\"(max-width: 562px) 100vw, 562px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hoton tattaunawar da aka yi da manhajar sakonnin<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><strong>Wasannin da ke kara fahimtar da jama\u2019a kan fasahar AI<\/strong>: Wannan na taimakawa masu amfani da shafin wajen fahimta da kuma gane yadda ake gyarawa ko kirkiro bayanai ta yin amfani da fasahar AI da ma yadda mutun zai iya karantawa ko kallon wadannan bayanan ba tare da an yaudare shi ba ranar zaben.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan manhajar ta DUBAWA chatbot kuma tana kara rufe gibin da ke tsakanin masu zabe da masu tantance bayanai a lokacin da suke matukar bukata, wato sadda masu zamba da yada labaran karya ke aiki da gaske wajen ganin sun alkinta bayani yadda za su yaudari jama\u2019a su haddasa rikici.&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wayewan garin 8 ga watan Nuwamba ne masu jefa kuri\u2019a a jihar Anambara za su nufi rumfunan zabe dan zaban sabon gwamnan. A lokutan zabe a Najeriya da sauran kasashen duniya, akwai salon yaudarar jama\u2019a da bayanann karyar da ya bulla. A zabukan baya, DUBAWA ta sanya ido wajen ganin yadda ake yada bayanan a yanar gizo-gizo dangane da yadda ma aka taba yin da\u2019awar wai wasu \u2018yan takara sun janye sa\u2019o\u2019i kadan kafin kaddamar da zaben. Sauran nau\u2019o\u2019in raba&nbsp; ire-iren wadannan bayanan sun hada da yada bayanan karya dangane da tashe-tashen hankula, wadanda burin kirkiro su shi ne yaudarar jama\u2019a wajen fargabar cewa akwai rashin daidaito a wasu yankunan. A wasu lokutan kuma, bayanan su kan yi kokarin ragekimar \u2018yan takara ne ko kuma hukumar zabe a idon jama\u2019a. Yayin da masu tantance gaskiyar bayanai ke iya karyata wadannan labaran,&nbsp; tasirin tantance bayanai mai yiwuwa ba zai iya yaduwa kamar yadda bayanan karyar su ka riga suka yi ba saboda kamar yadda wani&nbsp; rahoton BBC ya bayyana, \u2018labaran bogi\u2019 sun fi yaduwa cikin sauri.&nbsp; Ko da shi ke domin yaki da yaduwar bayanan da ba daidai ba, DUBAWA ta samar da wata dabara wadda za ta iya taimakawa masu zabe a Anambara wajen tantance duk wata da\u2019awa da ta bulla ranar zaben. DUBAWA Chatbot ko kuma manhajar tattaunawa Ita wannan DUBAWA Chatbot wata fasaha ce wadda za\u2019a iya amfani da ita cikin sauki. Ana iya samunta ne a manhajar WhatsApp kuma ta na iya tantance da\u2019awowi. Ta na iya amfanar masu jefa kuri\u2019a ranar zabe wajen tantance gaskiyar duk wani bayanin da suka yi shakkar sahihancin shi a yankunan zabensu. Mahimman abubuwa biyar ne ake iya da wannan manhajar. Ta na iya taimakawa wajen tantance bayanai, samar da rahotannin batutuwan da aka riga aka tantance, kuma mutun na iya fahimtar burin DUBAWA, ayyukanta da abubuwan da ta ke darajawa. Masu amfani da manhajar kuma na yi mika korafinsu kan bayanan karya su kuma yi \u2018yan wasannin da za su kara mu su ilimin fahimtar na\u2019ura mai kwaikwayon dabi\u2019un dan adam wato AI. Ga wadanda ba su taba amfani da ita ba, ku na iya samunta idan kuka latsa wannan makalar. Da zarar kuka rubuta gajeren sako kuka tura, ku na iya fara tattaunawa da ita domin nan da nan za ta gabatar da kanta ta kuma bayyana sharrudan amfani da ita. Bayan haka za ta bayar da jerin ire-iren ayyukan da take yi ta bukaci mutun ya zabi abin da ya ke bukata a wannan lokacin. Idan har dan tantance gaskiyar da\u2019awa ne sai ku na iya zabar \u2018Tantance da\u2019awa\u2019 Tantance Da\u2019awa: Da wannan masu amfani da shi na iya tantancewa ko karyata bayanan da ke da alaka da zaben. Alal misali, masu amfani da shafin na iya yin tambaya kamar haka, \u201cSu wane ne \u2018yan takara a zaben jihar Anambara?\u201d manhajar sakon za ta amasa tambayar da makalun rahotannin da ke dauke da cikakken bayani dangane da batun. Hoton wata tattaunawar da aka yi da manhajar sakonnin Sami rahotannin bayanan da aka tantance da dumi-duminsu: Masu amfani da shafin da ke neman bayanai masu sahihanci dangane da zaben na iya amfani da wannan. Bayan sun latsa makalar, za ta fitar da duk sabbin rahotannin da aka yi dangane da zaben a babban shafin, daga nan masu amfani da shafin na iya bin makalun su ga sauran labaran. Bayyana korafi kan da\u2019awa: Masu amfani da shafin na iya tura makalun duk wata da\u2019awa da suka gani a yanar gizo-gizo ranar zabe idan har suna bukatar karin bayani ko kuma sahihancin bayanan. Haka nan kuma ko da babu makalu, idan har akwai labari ko butun da ake so a tantance, ana iya rubuta korafin kai tsaye. Daga nan manhajar za ta sanar cewa ta tura batun ga wadanda ke tantance bayanan kuma za\u2019a yi bitar shi a ga ko ya cimma ka\u2019idoji gudanar da bincike. Hoton tattaunawar da aka yi da manhajar sakonnin Wasannin da ke kara fahimtar da jama\u2019a kan fasahar AI: Wannan na taimakawa masu amfani da shafin wajen fahimta da kuma gane yadda ake gyarawa ko kirkiro bayanai ta yin amfani da fasahar AI da ma yadda mutun zai iya karantawa ko kallon wadannan bayanan ba tare da an yaudare shi ba ranar zaben. Wannan manhajar ta DUBAWA chatbot kuma tana kara rufe gibin da ke tsakanin masu zabe da masu tantance bayanai a lokacin da suke matukar bukata, wato sadda masu zamba da yada labaran karya ke aiki da gaske wajen ganin sun alkinta bayani yadda za su yaudari jama\u2019a su haddasa rikici.&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":25694,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"default","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[1920],"class_list":["post-25722","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-6GS","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":1920,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"elizabeth-ogunbamowo","display_name":"Elizabeth Ogunbamowo","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/7043a07f4ff292637cb75d13c8340fa9afb2ec87eceec4eedd980077c8bfd304?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-18.png?fit=1200%2C675&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/25722","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=25722"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/25722\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":25726,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/25722\/revisions\/25726"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/25694"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=25722"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=25722"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=25722"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=25722"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=25722"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}